20.
Kafin Maryam ta ce me har hutun ya ƙare. A haka ma wai sun ƙara sati ɗaya ita da Hamida. Ta ji daɗin hutun sosai. Ita da ʼyan uwanta sun yi ta hirar yaushe gamo. Tun suna ƙanana sun girma da shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsu. Wannan tarbiyar Abba da Umma ne. Har yanzu tare su ke cin abinci a kwano ɗaya sai dai idan ba su haɗu ba. Zuwan su Anti Firdausi da Anti Jamila ya sake sa hutunta daɗi. Yaran su Hamza da Nawal sun ƙara girma sun yi wayo.
Ta yi aikin snacks da yawa da hutun. Wannan matar da ta taɓa yi wa meatpie ta ƙara aikowa a yi mata da yawa. Yawanci ʼyan asibitin Umma sun fi yi mata ciniki. Ta tara ʼyan kuɗaɗenta babu laifi.
Kaf tsawon kwanakin nan maganar Khalid na maƙale a ranta. Ta yi tunani ta yi nazari amma har yanzu bata san amsar da zata bashi ba. Ta amsa duka tambayoyin da malamar soyayya ta yi mata wato Hameeda amma har yanzu akwai wani abu a ƙasan ranta da ke ce mata bai kamata ta amince ba.
Na farko dai ita bata ma san ya ake (relationship) ba. Za su yi ta waya ne kaman Summy da saurayinta ko kuwa? Ta san dai Da Baban Hamza ke neman Anti Firdausi yana yawan zuwa taɗi. Ko me ake cewa? Oho!
Na biyu kuma tana so ta maida hankalinta sosai kan karatunta. Babban burin mahaifinta kafin ya bar duniya shine yaga sun yi karatu me zurfi. Ta yi mai adalci kuwa idan ta fara yin saurayi daga zuwanta?
Na ƙarshe idan suka fara soyayyar sai me kuma? Aure?
Abubuwan da take ta saƙawa da warwarewa kenan a ranta. Ta yi zurfi cikin tunani bata ji an shigo ɗakin ba saida aka taɓa ta. Ai kuwa ta firgita.
Anti Firdausi ta kalleta. "Ya Maryam tunanin me kike yi haka ina ta kiran ki ba ki ji ba? Har na shigo ɗakin ma duk ba ki sani ba."
Ta yi murmushi. "Ba komai fa Anti."
"Zo ki tayani yin cincin dinnan dan Allah. Idan ban yi ba na shiga uku wurin Baban Hamza."
Maryam ta yi dariya. Kowa ya san mijin Anti Firdausi da ciye-ciye shi yasa ga shi nan Masha Allahu.
"Yaushe ze dawo?"
Ya tafi aiki Legas shine ta zo gida ta yi kwana biyu. Babu irin mitar da Mama bata yi mata ba ita da Anti Jamila da ta zo tun daga Bauchi.
"A ce yara baza su iya zama a gidajen su ba kullum kuna hanyar zuwa nan. Yayar ku da tana Kano sai jefi jefi ta ke zuwa ku kuwa yaran zamani ko? Harda ke Jamila da kike da nisa. Kodayake ba laifin ku bane, na mazajen ku ne da su ke biye muku..."
Sai da Baba Malam ya bata haƙuri kafin ta daina mitar.
"Jibi da safe. Shi yasa na ke so in yi yau dan gobe da sassafe zan tafi. Na san gidana na chan ya yi ƙura."
"Sai mu je mu taya ki gyara gidan."
"Shi yasa na ke son ki Yaya Maryam. Ai kuwa da kun kyauta. Yaushe za ki koma?"
Kiran komawar da Anti ta yi yasa jikinta yin sanyi. Duk sanda ta zo gida bata taɓa ɗokin komawa makaranta ba. "Ranan Lahadi in Allah Ya yarda."
"Allah Ya kaimu."
Kicin su ka nufa inda Anti Firdausi ta ciro komai na yin cincin din. Maryam ta auna komai sannan ta fara kwaɓawa. Idan ta yi ta gaji Anti Firdausi ta karɓa har kwaɓin ya haɗe sosai. Anti Firdausi ta kwalawa Zee da Safiya kira su zo ayi murza. Kowaccen su ta ɗauki wuƙa da faranti. Abun mutane da yawa aikin na su ya yi sauri. Ana yi ana hira. Anti Jamila ke soyawa. Cincin din ya yi auki sosai, aka raba aka ba kowa na shi, Anti Firdausi ta adana sauran.
Suna zaune a falo Anti Firdausi ta ciro kuɗi ta ba Maryam. Umma ta kalle ta. "Kuɗin me ye Firdausi?"
"Baba Hamza ya ce a bata." Anti Firdausi ta yi saurin cewa ganin kallon da Umma ke mata.
"Mene ne na wani bada kuɗi idan banda abun shi, bayan tare aka taru aka yi aikin."
Mama da ke zaune kan kujera ta ce, "A'a Sa'adatu aiki ta yi aka biyata fa. Ita ce jagorar aikin ai. Wannan salon shi ke karyawa mutane jari. Idan ka yi wa mutum aiki ya biyaka babu wani dan gida ne."
Umma ta gyada kai. "To Mama."
Maryam ta shiga ɗaki ta tura kuɗin cikin asusu. Asusun ba laifi ya fara nauyi. Umma ce ta bata shawarar siyan asusun sai ta riƙa raba kuɗin gida biyu tana adana rabi.
Falo ta koma aka cigaba da hira. Suna zaune wani ƙaramin yaro ya yi sallama, daga maƙota ya ke ya kawo goro da katin bikin yayar shi.
Umma ta karɓa katin daga hannun Anti Firdausi. "Duka yarinyar nawa ta ke za a yi mata aure? Tare fa suka gama sakandire da Maryam."
"Mijin ya zo Sa'adatu ba sai a yi ba." Mama ta ce.
"Mama shekara sha shida duka me ta sani tsakani da Allah. Ya kamata a daina aurar da yara ƙanana a bari sai sun mallaki hankulan su."
"Zamanin mu ai wannan ta yi tsufa da yawa ma."
"Zamanin ku ki ka ce Mama. Yanzu zamani ya chanza. A bari ko sha takwas ne su yi mana. Bare yaran yanzu girman ne kawai amma babu hankali sam."
"Toh Allah dai Ya kyauta," Mama ta kalla Maryam. "Toh ke kin ki ji tsohuwar ki bata shirya aurar da ke yanzu ba. Babu ke ba kula samari."
Duka a ka yi dariya. Maryam ta ji cikinta ya kulle dan irin kallon da Umma ta ke yi mata dagaske ta ɗauka abun. Maryam ta ɗauke kai tare da kawar da tunanin daga zuciyarta.
Washegari ita da Safiya da Zee su ka je gidan Anti Firdausi taya ta shara. Gaba ɗaya yinin ranan a chan su ka yi. Bayan sun gama Anti Firdausi ta tura Zee da Safiya kicin su dafo musu taliya.
Wayar Anti Firdausi ta yi ƙara. Tana ganin wa ke kira ta miƙa wa Maryam Hamza ta yi ɗaki. Ko bata faɗa ba ta san Baban Hamza ne. Maryam ta shiga yi wa yaron wasa. Girman yaro babu wuya duka yaushe aka haife shi amma har ya girma sosai.
Chan itama wayarta ta yi ƙara. Ta yi zaton Hameeda ce dan sun yi da ita za su yi magana ɗazu da safe. Amma a maimakon sunan Hameeda kaman yanda ta yi tsammani sai taga sunan Khalid.
Da kamar ba zata ɗauka ba dan har yanzu bata da amsar da zata ba shi. Ki ɗauka mana Maryam, wata zuciyar ta tunzurata. Kafin ta ɗauka wayar ta tsinke. Har ta fara murna kaman kuwa ya sani sai ga kiran shi ya ƙara shigowa.
"Yaya Maryam..." muryar Khalid ta yi mata sallama.
Ta haƙura ta fara amsa Yaya Maryam ɗin tunda ya ƙi ya dena. "Na'am. Ina wuni ya makaranta?"
"Lafiya lau. Makaranta kuma ba daɗi. Gata nan kaman an yi shara babu kowa."
"Dama mana. An yi hutu kowa ya tafi gida sai irin ku masu son zaman makaranta."
Khalid ya yi dariya, "ba ki san zaman makaranta ya fi zaman gida daɗi ba."
"Makarantar? Hmm mmm. Ai babu ma yanda za a haɗa. Kowa ya san gida ya fi daɗi."
Ya sake yin dariya. "Dole ki ce haka. Ni dai makaranta tafi mun." Sai kuma ya chanza zancen gaba ɗaya. "Na san kina nan kina cinye wa Umma abinci."
"Duka abincin da na ke ci nawa ya ke..."
Sun yi ta hira Maryam na ta jira ya dauko maganar amma abun mamaki be ce komai dangane da zancen ba. To ko dai ya manta? Har su ka yi sallama bata daina tunanin ba. Hala shi ya manta ma ita kaɗai ta damu kanta.
Girkin mutane biyu ashe Safiya ta saka gishiri Zee ta ƙara zubawa. Abincin dai daga ƙarshe ba su iya cin shi ba sai indomie Anti ta bada aka siyo.
Hutu ya ƙare a yau ne Maryam za ta koma Zaria. Tun jiya ta shirya kayanta ta yi ʼyan tsince-tsincen kayan abinci da ta san na su sun yi ƙasa.
"Maryam wannan wayo ne ai. Bayan kuɗin da aka baki kin zo kina kwasar mun kayan abinci." In ji Umma.
Maryam ta yaƙe mata haƙora tana dariya. "Ummanaaa..."
"Matsa mun kin gama kwashe mun kaya. Kin shirya komai da komai dai ko?"
"Eh Umma."
"Toh. Zo ki zauna." A ƙasan kafet ta zauna yayin da Umma ke zaune kan kujera. "Duk abunda zan faɗa ba sabon abu bane amma ya zama dole in maimaita. Kin san abunda ya kai ki makaranta Maryam. Kada ki bari freedom ɗin da ki ke ganin kin samu a jami'a ya ruɗe ki. Kin san irin tarbiyar gidan nan, duk wanda ki ka ga tarbiyar ku ba iri ɗaya ba ce babu ruwan ki da ita. Ki maida hankali sosai kan karatun ki. Course ɗin da ki ke yi na ɗaya daga cikin masu wahala dan haka banda wasa. A yanzu ne maza da suka kusa gama makaranta za su nemi su bata miki lokaci."
Tana furta jumlar ƙarshe Maryam ta ɗaga kai ta kalleta. Umma ta gyada kai. "Su sun gama makaranta ke yanzu ki ke farawa. Dayawan su neman wanda za su ɓata lokaci da ita su ke yi kafin su gama makaranta. Da yawan su daga nan ba za ki sake ji daga gare su ba. Ki maida hankali kan karatu ina sake maimaita miki. Idan dagaske ya ke ya fara zuwa gida. Idan kuma bai shirya ba ya yi gaba. Dan ni ban yarda da alaƙar nan ta zamani tsakanin budurwa da saurayi har na tsawon shekaru ba."
Kaman an zubawa tana gishiri. Jikinta ya yankwane gaba ɗaya. Toh Umma ko ta san abunda ta ke ciki ne shi yasa take mata wannan nasihar?
Umma ta ɗaura ta nanata mata riƙe adhkar. Kaman haɗin baki Mama nasihar da ta yi mata kenan. Ko da zata tafi ba a yi mata nasihu ma su ratsa jiki haka ba.
A tasha ta haɗu da Hameeda. Baya su ka shiga su ka biya kuɗin mutum uku dan su zauna a wadace. Mace ɗaya kawai ta ƙara shiga motar ta tashi, sun samu maza biyu a gaba dama.
"Kin dai yi mana miya ko?" Hameeda ta tambaya.
"Ba dole ba. Ai ko zan manta da komai ba zan manta miya ba."
Iskan mota yana ta kaɗawa har ya so ya yi mata yawa. "Dreba dan Allah a rake window."
"Ya ku ka ƙare da MK wai?"
"Hmmm Hameeda ba wannan ba..." ta kwashe yanda su ka yi da Umma ta faɗa mata. "Kaman ta sani Hameeda bata taɓa jaddamun maganar haka ba. Tana yi jefi jefi amma na yau ya fi tsanani dan da kakkaurar murya ta yi magana babu alamun wasa."
"Tabdijam. Umma ai abun be yi serious haka ba. Ni zancen zuwa gida ma bai taɓa zuwa mun kai ba. Zuwa gida aure fa kenan! Ɗan relationship de za a yi kafin Allah Ya kawo miji."
Maryam ta gyada kai. "Hameeda kenan."
Umma na da tsauri sosai. Ko lokacin da Abba ke da rai ya fita sassauci. Bare kuma baya nan yanzu. Tarbiyarsa da nata ta haɗa ta ke yi musu. Ko dan kar mutane su samu abun faɗi kan tarbiyarsu ze sa ta ƙarfafa tsaurinta.
Akwai wani lokaci da su ka je suna nan cikin unguwa, Idris na ta rashin ji har su ka yi faɗa da wani yaro ya ji mai ciwo. Buden bakin matan da ke kusa da Maryam sai cewa su ka yi ai ɗan mace ne, uban ya mutu ya barta da yara ta kasa tanƙwara su ta ba su tarbiya mai kyau.
Abu ya daɗe bai tsaya mata a rai irin wannan ba. Tun ranan ta gane wato ana yi musu wani kallo saboda mahaifinsu ya rasu. Tun lokacin ta ke takatsantsan dan gani bata janyo maganar da zai sa a ce Umma ta gaza wurin tarbiyarsu ba. Allah ne shaida Umma ta na iya bakin ƙoƙarinta.
"Toh yanzu ya ke nan? Kina son shi?"
Maryam bata iya ba Hameeda amsa ba. Ta juya kai tana kallon titi yanda motoci ke wuce su suma suna wuce wasu.
***
Umma Sa'adatu na zaune tana duba takardun da ta dawo da su daga asibiti Mama ta yi sallama. A gefe ta ajiye takardun ta maida hankalinta gaba ɗaya kan mahaifiyarta. Babu alamun tsufa tare da dattijuwar. Da yawa mutane na mamakin ita ta haifi Sa'adatu.
"Aikin a ke ta yi?"
"Wallahi kuwa. A cigaba da yi mana addu'a."
Aikin asibiti na ɗaya daga cikin ayyuka mafi wahala a duniya. Sai me haƙuri da juriya ze iya, kuma jajirtacce. Cike ya ke da abubuwan al'ajabi, mamaki da ban tausayi.
A kullum Umma Sa'adatu ta dawo ta kwanta a kan gaɗonta tana gode wa Allah da ya barta da lafiyarta. Lafiya ba ƙaramar kyauta ba ce daga Ubangijinmu mai Rahama. Idan Ya baka lafiya Ya yi maka komai!
"Kullum cikin yi muku addu'a na ke yi Sa'adatu. Da ke da marayunki."
Umma ta yi murmushi. Tabbas iyaye rahama ne. Mama da Baba Malam sune jigon rayuwarta. Sun tsaya mata a lokacin da duniya ta yi mata zafi. A kullum tana hamdala da iyayen da Allah SWT Ya bata, tabbas ta yi dace.
"Sa'adatu...."
Rabon da gabanta ya faɗi haka an daɗe. Sunan Allah ta kira a zuci ta kalli mahaifiyarta. "Na'am Mama?"
Mama ta gyara zamanta. "Sa'adatu," ta sake kira. Umma ta san inda maganar ta dosa dan haka ta sadda kai ƙasa. "Da wuya a samu irin Ahmad.."
Sa'adatu ta yi murmushi mai cike da ciwo. Irin Ahmad dinta ɗaya ne tal a duniya. Ba za a sake samun kamarsa ba. Ya yi tafiya mai nisa, tafiyar da ba a taɓa dawowa.
Rasa masoyi taɓo ne da ba ze taɓa ɓacewa ba. Shekara huɗu da rasa Ahmad ɗinta amma har yau radaɗin rashinsa bai rage ko kaɗan a zuciyarta ba.
"Mama. Dan Allah a ce musu su yi haƙuri."
Rasuwar Ahmad da shekara biyu a ka fara sallama da ita. Ba dama ta fita sai an samu wani da ze yi mata magana. Da suka ga bata kula su sai su ka fara sallama da Baba Malam.
Tun yana cewa bata shirya ba har a ka kai ga ya fara yi mata magana akan ta saurari ko mutum ɗaya ne. Ana cikin haka ne dan aminin Baba Malam ya nuna ra'ayinsa a kanta. Baba ya ji nauyin ce mai a'a kaman sauran shine ya haɗa Mama da aikin shawo kanta ko sauraronsa ne ta yi.
Taya su ke zaton zata iya sauraron wani ɗa namiji bayan Arc na nan a zuciyarta kaman yau ta fara son sa? Babu abunda ya rage mata a duniya sai bautar Ubangiji da kula da yaranta. Arc ya tafi da duka wani jin daɗinta na rayuwa.
"Sa'adatu haka za ki yi ta zama? Kina buƙatar abokin rayuwa. Ke mace ce me rauni. Idan yau kika wayi gari babu ni babu mahaifinki fa? Ki yi tunanin rayuwar ki da ta yaran ki."
"Mama ko na gayyato wani cikin rayuwata zan cutar da shine." Sa'adatu ta ce tana girgiza kai. Taya za ta iya rayuwa da wani ba Ahmad ɗinta ba? "Ba zai taɓa samun abun ya ke so daga gareni ba. Ba zan iya ba Mama, ba zan iya ba."
"Ahmad ba ze so haka ba. Nasan ze so a ce kin cigaba da rayuwar ki kamar da ko fiye da haka."
Shiru ya ratsa wurin, dukan su suna saƙa da warwara a zuciya. Mama sheda ce akan irin kulawa da ƙaunar da Ahmad ya nunawa Sa'adatu. Tabbas ta san da wuya ta iya rayuwa da wani amma gaba ta ke hange.
Mama ta dafa kafaɗarta ta dan matsa kafin ta fita.
Sa'adatu ta saki ajiyar zuciya sai kuma ta fashe da kuka. Ba za su taɓa fahimtar ta ba.
***
Summy ta riga su dawowa dan haka a gyare su ka samu ɗakin. Maryam ta hau gyara kayanta dan so ta ke yi ta huta gaba ɗaya. Hameeda kuwa ta bi lafiyar gado ta ce sai anjima.
"Yauwa Maryam, ga saƙon ki daga ƙawar ki." Sumayya ta ce chan anjima bayan ta gama aikin gyaran.
Maryam ta karba tana murmushi. "Allah sarki Bilkisu Kabir. Na gode. Bari in kirata dama mun kwana biyu ba mu yi waya ba."
Hameeda ta dago kai daga kwance. "Summy na lura Bilkisun nan nema ta ke yi ta ture mun fadata wurin Ya Maryam. Ki ce mata ita tsohuwar yayi ce ni ce new catch."
Duka su ka yi dariya. Maryam ta buɗe ledar, kayan maƙulashe ne sai gyale da doguwar riga. Ta ji daɗin kyautar sosai. Ta kira Bilkisu ta yi mata godiya, sun ɗauki lokaci me tsawo suna hira.
Washegari litinin a ka fara lectures. Yanzu sun gane kan makaranta sosai sai dai su nuna wa wasu hanya. Hameeda da Sumayya su ka yi hanyar su Maryam ta yi tat hanyar. Sai ta ji ina ma kwas ɗaya ta ke yi da su Hameeda.
A gaba ta zauna kan kujera ta ci sa'a ta zo da wuri. Lecturer ɗin be iso ba ana ta hayaniya.
"Dan Allah Microbiolgy ki ke yi?" Wata yarinya daga gefe ta tambaya.
Yawanci tare su ke aji da wasu departments ɗin a faculty ba duka bane ʼyan Biochem. Maryam ta girgiza mata kai. Wasa ta riƙa yi da hannunta. Ina ma a ce kamar Hameeda ta ke, da ta yi ƙawa yanzu. Zama kai kaɗai ba daɗi.
Kaman daga sama ta ji muryar Zuby. Murmushi ya bayyana a fuskarta. Bata da kirki, tunda a ka yi hutu bata nemi Zubaida ba.
"Maryam kin dawo ashe." Zuby ta ce bayan ta samu ta kutso tsakanin jama'ar da ke tsaye gaban benchin.
Maryam ta matsa mata, duka ba su da girman jiki wurin ze ishe su. "Jiya na dawo. Ya hutu?"
"Lafiya lau Alhamdulillahi."
ʼYar hira su ka yi har lecturer ɗin ya shigo. Bayan awa biyu Maryam da Zuby su ka kama hanyar ɗaki. Ba su da wani ajin sai da yamma.
Ni dama sun haɗe mana classes ɗin, ka gama gaba ɗaya kawai ba ka je ka yi ta dawo ba."
"Idan kuma a ka yi su a jere ai zamu wahala Zuby. Ba lallai ma mu fahimci abunda a ke yi ba."
Awa biyun ma ya a ka ƙare.
"Eh kuma hakane."
A gaban Ribadu su ka yi sallama. Maryam ta kusa shiga ta ji Zuby na kiranta.
"Dan Allah Maryam mu riƙa zuwa aji tare wallahi ba daɗi tafiya kai kaɗai."
Maryam ta yi murmushi. "Kaman kin sani abunda na gama tunani ɗazu kenan."
"Kin gani. Sai mu riƙa haɗuwa a nan tunda ni ina chan ciki. Anjima in na fito zan kira ki."
"Toh shikenan."
Satin gaba ɗaya tare su ka je aji su ka dawo. Hakan ya yi wa Maryam daɗi ta samu abokiyar tafiya da hira duk da ita ba gwanar surutu ba ce.
Tunda ta dawo bata ji daga Khalid ba itama bata neme shi ba. Hakan ya dameta amma ba zata iya kiransa ba. Kar ya yi zaton abunda ba shi ba.
Ranar Monday ya kasance public holiday suna zaune a ɗaki. Summy ta yi musu girki sun gama cin abinci kenan ko dauƙe kwano ba a yi ba wayarta ta yi ƙara.
Tashi ta yi ta tafi da kwanon ta ajiye kan tebur sannan ta ɗauki wayarta a kan gado. Baƙuwar lamba ce. Tana tunanin waye ta ɗauka.
"Yaya Maryam...salamu alaikum."
"Wa'alaikumus salam Khalid?"
"Na'am. Kin ji ni shiru kwana biyu ko. Wallahi wayata ta lalace na rasa numbers ɗina sai yau na gyara."
"Allah sarki. Allah Ya kiyaye gaba."
"Ameen. Kin dawo ko har yanzu kina gida kina cinye wa Umma tuwo?"
Ta yi dariya, "na dawo tun last week."
"Kai Yaya Maryam shine ba ki nemi ni ba."
"Kai da ka ce wayar ka ta lalace ina zan same ka toh."
"Duk da haka dai. Sannun ki da dawowa. Ina su Hameeda."
Maryam ta kalla Hameeda da Sumayya, ba su motsa daga wurin ba. "Ga su chan."
"Ki gaishe su. Me kika kawo mun daga Kaduna?"
"Ni kuwa me zan kawo maka?"
"Kayan daɗi mana. Kin manta ban je ko ina ba bawan Allah da ni."
"Wannan ai kai ka so."
Haka de ya yi ta jan ta da hira. Daga ƙarshe ya ce, "anjima zan zo mu gaisa in sha Allah."
A take cikinta ya ƙulle, da kyar ta iya furta; "sai ka zo."
Tana ajiye wayar ta koma wurin su Hameeda. "MK ze zo!"
Summy ta yi shewa. "Kin shirya karɓar soyayyarsa kenan."
Maryam ta kalli Hameeda. Maganganun Umma na nan maƙale a ranta. Hameeda ta gyada mata kai ba tare da ce komai ba.
Bayan isha'i kiransa da wannan baƙuwar lambar ya shigo. Saving ɗinta ta yi bayan ta amsa. Hijabi maroon ta zumbula har ƙasa ta fita. Zuciyarta na duka da ƙarfi kaman zata faɗo.
Wurin da ya saba zama ta same shi. Sanye ya ke da jeans da riga me dogon hannu. Yana ganinta ya yi murmushi.
Nesa da shi ta zauna kaman yanda ta saba. Su ka sake gaisawa.
"Ya lectures?" Ya tambaya.
"Lafiya lau Alhamdulillah. Ya naka?"
"Lafiya. Da yake babu lectures ɗin sosai, an fi karkata kan project."
"Oh. How does it feel to be in your last semester?"
Khalid ya yi dariya, "exciting. Daga nan sai NYSC in sha Allah. Sai kuma neman aiki. Abun dai ba ya ƙarewa."
"Allah Ya taimaka Ya bada sa'a."
"Ameen Ameen Ya Maryam."
Shiru ya ratsa tsaknin su. Kaman an sa loud speaker a ƙirjinta sannan aka kara a kunnenta. Haka ta ke jin ƙaran bugun zuciyarta.
"Maryam..." ya kira sunan da yanayi me shiga rai. "Kin shirya ba ni amsa?"
Ta gyada kai ba tare da ta kalle shi ba. Duka natsuwarta da ƙarfin halinta ta tattaro ta juya ta kalle shi.
Khalid ya karkata kansa gefe yana kallonta. "Na ji kamar in ce ki riƙe amsar ki. Ba wanda na ke so za ki bani ba ko?"
Maryam ta yi murmushi me cike da ban haƙuri. "Ka yi haƙuri."
Ƙafadunsa su ka yi ƙasa kamar kalamanta sun zare me ƙarfin jikinsa gaba ɗaya. Ya juya kansa gefe.
Gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Sai da ta yi nazari me tsawo kafin ta yanke wannan hukuncin.
Khalid ya juyo ya kalleta. Fuskarsa ta kasa ɓoye abunda ke ransa. He looked defeated and sad. "Zan iya tambayan dalili?"
Maryam ta gyada kai. "Ka yi haƙuri. Ba wai bana s..." ta fara cewa sai ta yi shiru. "Kawai ban shirya bane."
•
•
•
•
Ku faɗa mun, amsar da ku ka yi tunanin zata ba shi kenan?🤭
Asslamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh... Barkan mu da dawowa!
Toh ya babin nan? Kun ji daɗinsa ko kuwa. Shekaran jiya na yi tambaya a shafina na Instagram, zan yi a nan saboda da yawan ku ba ku following ɗina (ga username din @maymunatu_bukar. A dannan mun follow please🤭)
"Ya ku ke ganin littafin zai kasance?"
Na san ban ba ku (blurb) ba🙈 na barku kuna ta kacici-kacici. Amma ina son in sani daga abunda ku ka karanta ya kuke tunanin za a ƙare?
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro