Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

9

Sosai na rud'e na gigice,, da sauri naji an juyo dani, a matu'kar raunane naji ance... Zaid"mai nayi maka?
Muryar wacce naji ko a mafarki naji ta tabbas zangane bude idanuwa na nayi dakyau a kanta, Ammi"ce!

Hawaye da tashin hankalin dana gani akan Fuskarta ne suka sake rudani,, wanda har banga cin cirindon jama'ar dake gurin ba, na isa gareta ko'karin rike hannunta nake dan intambaye ta, mai yake faruwa nasan zata fad'a mun kodan shakuwar da qaunar da da mahaifi dake tsakanin mu,, abun mamaki!
Wani irin warce hannun ta tayi, tasauke mun wani irin mugun Mari da tsabar mamakin sa yafi zafin sa yawa a gare ni. banga ma dawowa duniyar mamakin da na Lula ba naji, wasu irin kalamai na fitowa a bakinta wanda dasu gwara saukar aradu.

Zaid"  Allah ya isa tsakani na dakai, Zaid kacuceni ka yau dare ni, ashe lambu lambu kamun dan ka lalata gobe na? bayan kuma ni ina ko'karin gyara taka goben?

a rude nazube gabanta,, wanda sai a lokacin na lura da seedifa, wacce take kwance a gabanta, a sume... ga jini dake zuba ta 'kafar ta. A matu'kar razane nace... Seedifah! Mai yasa me ki? Ammi jini na zuba... Mata mu.. kait.... Ai ban'karasa ba naji saukar duka a jikina wanda na rasa ta inda yake fitowa,, Ammi ce tadakatar da masu duka na.. cikin kuka tazo gabana wanda a lokacin na gama gala ba ita.
Zaid"  a duniya bantaba tunani wannan rashin d'ar daga gareka ba kodan irin tarbiyyar dana baka saidai kashh ashe nayi kuskuren fahimta,, domin kuwa tuwo kullum sunansa tuwo,, kuma barewa ba zatayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba, duk inda kafito baka fito gurin mutumci da da'a ba,, Halama iyayenka cikinka sukayi uwar ta jefar dakai? Babu mamaki, Zaid ban yafe maka ba wannan abun dakai wa yata wlh sai ka biya shi komai daren dad'ewa.

Wani irin ihun kuka tasaka had'i da kaimun wata muguwar sha'ka. Wanda nayi fatan ta kashe na huta dan na fahimci duk bayanin da zan mata bazata gane ba tagama gurbata tunanin ta a kaina.
Jin nayi an janye ta daga jikina,, bude sauran ganina nayi,, shugaba nagani tsaye a kaina, bai cewa kowa komai ba ya dagoni muka fita daga d'akin jama'a sai surutun Allah wadai dani suke, ni kuwa seedifa kawai nake hangowa a kwance cikin jini...

Office d'insa muka shiga,, sai a lokacin nafara jin kiran sallar asuba wanda ya fahimtar dani cewa duk wannan abun tun cikin dare ake yinsa, shugaba baice dani komai ba. Sai da zai fita sallah... Yace ka jirani ina zuwa ka kwantar da hankalin ka ko bakomai yanzun nasan ka d'auka darasi cewa ba'ayiwa manya gardama!

Yana fad'in hakan yafita,, shiru nayi ina nazarin kalaman sa, take kwakwalwa ta tafiddo mun da komai Sala Sala sanka sanka. tabbas wannan tugu ne aka had'a mun to amma waye yayiwa seedifa fyada? Amsar dana rasa kenan har yau.
take nabaiwa kaina shawarar barin gidan dana taso narayu a cikin sa, dan kuwa ko Za ayanka nama na danye bazan aikata abunda akeso in aikata ba, a hankali na Mike duk da tsamin da jiki na yakeyi,

Haka nafito, cikin sa'a mai gadi ma yatafi masallaci, har nasamu na fice babu wanda ya Ankara dani bare yayi ko'karin dakatar dani.
tafiya nake bansan inda nake nufa ba Sai jefa kafata danake,,  har wani mai babur yatashi kadeni,, ana na zube tsabar wahala da gajiya, duk da kuwa babur d'in ko tabani baiyi ba.

Mai babur d'in ne ytaimaka mun nahau yakaini gidansu yakira mai chemist ya yayi treatment d'in raunuka na. Wannan shine asalin haduwa ta da auwal, a takai ce!

Bayan nasamu sau'ki nabasu labari na,, take auwal ya tausaya mun sabanin mahaifiyar sa, wacce taki amin cewa dani har saida auwal d'in yanuna bacin ransa, kafun ta yarda na zauna tare dasu, nayi musu godiya matu'ka,, tun daga nan nashiga neman kud'i nine dako nine kwasan shara haka nake fita in nemi kud'i har nashiga wani dashi da su auwal sukeyi cikin ikon Allah na kwasa kud'i masu d'an kauri auwal ne yabani shawarar siyan babur,, inda kud'ina ba sukai ba, auwal d'in ne yaranta mun da zummar idan nasamu sai inbiya shi.

Aikuwa haka akayi nasiya nasoma ja cikin ikon Allah ina samu sosai a harkar babur d'ina,, wanda dashi ne nake taimakawa umma sosai dan har nafi auwal hidima dasu,, wannan ne yadan janyo mun farin jini a gun umma"  har take sakar mun fuska.

Shiru Zaid"yayi na yan dakiku kafun ya d'ora da basu labarin yadda ya ga baby d irin rayuwar dasuka yi har zuwa randa yaci uban duka. duk bai boye musu ba ya zayyana musu komai da komai.

Shiru palon ya d'auka bayan Zaid"yagama bada labarin sa.

Jinjina Kai Dad yashiga yi,, kafun yace... tabbas! wannan yaro ka had'u da jarabawa kala kala, saidai fatan Allah ya kiyaye gaba. Kuma insha'Allah wannan shine zai zamo na karshe ina fatan hakan.

Zaid" idan dai zaka iya zama damu ka d'auke mu tamkar iyayenka to insha'Allah mukuma Za mu d'auke ka da,

Ko kuwa hajiya lubabatu? yayi tambayar yana dubanta cikin murmushi da tausayawa had'i da kaunar yaron tace,, Alhaji wlh na amince tabbas wannan shine ya dace kuma kayi tunani mai kyau, harga Allah na amince..... Nidai ban amince ba!

Su kaji an fad'a a bakin kofar shigowa palon, dukkan su duba sukayi izuwa ga mai maganar, hajiya Rahamu ce,, wacce dawowarta kenan daga Dubai a cewarta taje check up. tasamu labarin ganin UMAIMAH ne a bakin mai aikin ta laraba, shine tayi musu dirar bazata inda taji ana ko'karin maida d'an da ba'asan asalin sa ba d'an gida.

Cike da isa gadara da jin ita d'in wata ce,, tace...tabbas! tana wani kad'a Kai ban amince ba, ta sake fad'a tana zama a d'aya daga cikin kujerun palon, d'ora 'kafa d'aya kan d'aya tayi.... Ita dai ummi sai kallon ta take, tana rayawa a ranta kan itakuwa bataga wanda ya isa Hana zaidu Zaman gidan ba. saidai zata jira jin cewar mai gidan....

A bangaren Alhaji Tahir shina shiru yayi yana dubanta duk da wani irin kwarjinn ta da yake ji a jikinsa musamman bayyanar ta gurin,, hakan baisa yaji zai iya bin maganar ta ba, saidai Bari yaga gudun ruwanta.

Cike da isa, ta dubi Zaid"tace Kai! Kaine ka tsinto UMAIMAH... ko? bata jira cewar sa ba, ta ruga masa rafar dubu dubu, tace d'auka katafi wannan gidan bakada masauki a cikinsa matu'kar ina matsayin matar gidan.. Zaid kasa motsi yayi ganin wannan isa da mallakar ta mtar gidan, a tsawace tace tashi kafita nace!

a matu'kar sanyaye Zaid"yatashi ajiye baby dake kan kafarsa gefe yayi kafun, yasoma barin palon hajiya lubabatu na ko'karin magana,, taga baby ta janyo Zaid"hannun sa tarike har zuwa gurin mahaifin ta... Cikin wata iriyar Murya wacce tasaka dukkan al'umar palon tsit tashiga cewa..... Dad.... MI.... Jin... UMAIMAH!.. ne... fa.... daga haka tai shiru tamkar ba daga bakinta maganar tafito ba, mamaki farinciki tsoro sune suka samu shiga zuciyar mutanen hud'u yayinda uku suke mamaki da farincikin jin yau baby tayi magana.

Sabanin hajiya Rahamu"da wani irin tsoro ya kamata.

Cikin jarumta Alhaji"Tahir yace... Kai zaidu daga yau ka zama d'an gidannan kuma zansa a gyra maka wancan bangaren,, sauran shirin kuma idn na kammallah zan sanar dakai. Nagama magana,, yana gama fad'in haka ya fice daga palon Zaid ma fita yayi dan ko damar godiya bai samu ba, hajiya lubabatu ma kama hannun yarta tayi suka fice.

*****
Sosai ran hajiya Rahamu yabaci da wannan abun da Alhaji yayi mata, yanzun ma sai zagayar d'aki take dan neman mafita,

Cikin damuwa da masifa tashiga cewa.... dan iskanci ina musaki yasan wata soyy bare wani miji,, Lallai dole in d'auka mummunar mataki akan mutanen nan gaba d'ayan su,, Salma ce ta dafa ta,, mommy!

Inason sa!

da wani irin mamaki hajiya Rahamu ta dubi yarta tace.. wa d'in?

Cikin ko inkula salma tace bakon gidannan!
Da wani irin sauri takoma duban yarta tace.. Ke dan rashin hankali inason rabuwa da kaya zaki ce wani kina son shi? to ban amince ba,, mommy dan Allah ki fahimce ni da gske nake tun ganin farko dana masa naji ina sonshi, mommy naga idan hagu takiya akoma dama, kawai tunda Khaleel bai samu ba ga wannan d'in.... Shiru hajiya Rahamu"tayi

Take wani mugun tunani ya shige ta wani irin mugun murmushi tayi kafun tace shikenan salma!

Tunda kina son shi ya zanyi dake?

Nasani is a short chappy please manage it kunsan condition d'ina murar nan dai tana nan😥 gskiya whattpad Kuna son ku daina ganina d alama babu vote babu comments? 🤔My WhatsApp people Son_so 😘

May be idn naji dama dama in d'an karo muku anjima 😂Amma fa bnyi alkawari ba tom 😮

Xinnee smart 😍😘

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro