Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

5

   Wani irin rawa zuciyarsa tashiga yi ciike da tashin hankali.

         Wani irin ihu tasaka wanda yatilasta masa fad'awa jikin gini Allah yatai ma kesa bai fad'i ba.
ci gaba tayi da wani irin gurnani mai gigitar da mai saura, sossai yasake shiga wani hali mai wuyar fassarawa... Sai wani irin gumi dake tsattsafo masa wanda tamkar ana watsa masa ruwa,, ganin dai tabbas idan ya barta zata iya illata kanta ne yasa zuciyarsa tashiga bashi shawara da yaje ya janyeta daga jikin ginar.. Amma kuma ta Yaya?

Shi fa bashida tabbacin cewa mutum ce ko kuwa aljana? to ta ina zai fara? Shi kansa bazai ce ga a halinda yake ciki ba, dan kuwa sosai ya razana da yanayin ta. ta Yaya zai fuskance ta da zummar janyeta?

  wata irin hargowa tasaka tamkar zata tashi d'akin, da wani irin mugun sauri ya bud'e d'akin. fita yayi yana wani mugun haki tamkar wanda yayi tsere......sunkuyawa yayi yana sake sauke numfashi,, wani tudun yasamu ya zauna a kofar gidansu awal"abokinsa.

Shiru yayi zugum cikin duhun daren, wani irin tsoro ne yasake kamashi,  addu'o'i yashiga jerawa duk wacce tazo bakinsa fad'a yakeyi.

    Cikin ikon Allah wani irin bacci na rashin sukuni mai tattare da tsoro ga gajiya, yayi awon gaba dashi ba tare da yashirya ba.
Kallo d'aya zakai masa kasan bai shirya wa baccin ba.

A d'aki, baby saida tayi abun har aljanin ya gaji ya barta,, ya yarda ita a d'akin tashiga baccin wahala ga wani irin run da tajiwa kanta, gwanin tausayi tabi ta 'kudundune, tamkar mai jin sanyi.

********
Kiran sallar asuba da ladan yafara Kwad'awa ne, ya farkar da Zaid, a firgice ya farka,, kansa da yayi nauyi ya dafe yashiga jera addu'ar tashi daga bacci.
A sanyaye yanufa d'akin'kirjin sa na wani irin bugawa dan sosai yake fargabar mai zai tarar a d'akin.

Saidai sa'banin tunaninsa, samun ta yayi a kwance ta 'kudundune,a sanyaye ya karasa kusa da ita tamkar mai tsoron karta farka, y isa kusa da ita.

duban ta yayi yaga yadda Kyakyawar fuskarta tayi ja' ga goshin ta yayi suntum dashi ga jinin da yayi ta zuba duk y'bata mata fukarta duk yabi ya bushe, da sauri yakai idanuwansa kan 'kafarta dama tun jiya yakeson'kare musu kallo ya kasa...
Sai yanzun yasamu damar hakan, dan yaji ance aljanu 'kofato ne dasu, shi yasa yakeson tabbatar da ita d'in mutum ce ko aljana?
Ganin kafafun nata dai irin nasa ne masu d'auke da yatsu biyar yasa baisan lokacin da yasauke numfashi ba.

Mikewa yayi yafita domin yin al'wala dan har anfara tayar da sallah.

Alwala yayi ya nufi masallaci. bayan yayi sallah yadawo cikin rashin sanin mafita yashiga d'akin, har lokacin bacci take, shawarar da zuciyarsa take bashi yayi tunanin d'auka. dan haka yayi ko'karin ai watar da shawarar tunkafun gari ya dad'a haske.
A hankali ya d'auke ta. fita yayi da ita cikin fargaba... d'ora ta yayi akan babur d'insa.

    Kafun Shima yahau tayar da babur d'in ya tayar yasoma tafiya har lokacin baccin ta takeyi batasan wainar da ake to yawa ba,

Cikin rashin sanin mai yake aikata wa yayi ta tafiya da ita zuwa wani d'an jeji gaban 'kauyen. abunka da karamun kauye har suka fita babu wanda ya gansu.

**************
Alhaji"ta tabbata na rasa yata,wanda nasani hakan yana tabbatar da nakusan barin duniyar Nima... ta karashe da wani irin gurshe'ken kuka.

   Cikin wata irin damuwa da yake dawainiya dashi, yadubeta lubabatu"ya kikeso inyi da rayuwata? ni kaina ina cikin tashin hankalin rashin baby... Gashi kinason ki sake Sanya mun wata damuwar.

   Idanuwanta da sukayi jajir dasu, tadubeshi dasu a take shi kansa taji yabata tausayi tabbas yana bu'katar a rarrashe shi. dan a duniya yaga jarabawa, ta rashin iyaye ko wani ma kusanci dan bayan ita da yarta ba shida wanda zai kalla yace nasa ne, to amma Yaya zatayi? Allah ne shaidar halinda take ciki damuwar da take tare da ita ba karama bace.
Tanason yarta duk da yadda Allah yayi ta tana dad'a gode masa da kyautar ta da yabata, ba laifin ta bane halinda take ciki wata uwa ce zata rasa d'an bata shiga tashin hankali ba? Yar ma mace,, macen ma mara cikkaken lafiya, haka kuma mai 'karancin shekaru. tabbas ko wace uwa ce dole tashiga tashin hankali, kwatankwacin wanda take ciki koma wanda yafi haka..

    Wasu irin hawaye ne suka sake surnano mata takoma'karshen gado ta takure guri d'aya had'i da d'ora kanta kan 'kafafun ta. tashiga wani irin kuka... Mai taba zuciya bakinta har wani d'aci d'aci yakeyi ga zuciyarta dake zafi mara misaltuwa  bugu da kari dga ta runtse idonta fuskar yarta take gani yadda duk abunda takeyi idanunta yana kanta. Sake rushewa tayi da kuka wanda bata isa ta dakatar dashi ba.

Babu yadda ya'iya, dole ya lallashe ta. domin yasan raunin mace duk yadda yakeji yazama wajibi a gareshi yayi ko'karin rarrashin ta had'i da kwantar mata da hankali.

Matsawa yayi kusa da ita zama yayi a gabanta hannayenta ya rike cikin nasa, a tausashe yasamu yashiga rarrashin ta da kalaman karfafa zuciya, da haka yasamu har tasha tea.

A take batan baby UMAIMAH"yashiga cikin yan uwa da abokan arziqi kota ina addu'a ake Allah ya bayyana ta.

Hajiya Rahamu"koda tasamu labari wani irin fari ranta yayi... Take takira bokanta dan taji ko shi yakada UMAIMAH?
Bayan tagama masa bayani yashiga dube dubensa a abubuwan tsafinsa.
Koda ta kirashi dan jin ya ake ciki, ce mata yayi....
Shi baiga komai ba duk lokacin da yashiga duba UMAIMAH. Wani irin haske yake gani a tare da ita wanda yake hanasa ganin taka mai man abunda ke tare da ita.

  Haka kuma aljanin da ya tura mata yana tare da ita saidai duk lokacin da yakira aljanin dan jin mai yake faruwa sai yakasa masa bayani dan dama aljanin tababbe ne ba Kowani lokaci yake iya magana ba.

Hankalinta ne yatashi, tace boka To meye ma'anar hasken dake tattare da ita?

     Eh to dole yazama d'aya cikin biyun da zan fad'a miki,
Ko yazamana hasken alkhairee ne ko kuma yazamana sharri ne ke sake bibiyart.

       Wata zufa ce ta tsattsafo mata, take hankalinta yatashi bangare d'aya kuma tana jin farinciki, dan haka sai kawai farincikin yafi tasiri a tare da ita (saboda son zuciya 🤧)

   Take tayi wa boka godiya,, sukayi sallama akan zai dinga dubawa dan tabbatar da mai ke wakana,, take ta tura masa kud'in sa.

********
Bai daina tafiya ba saida yazo gurin wani ruwa wanda ciyayi yayi masa 'kawanya  ga itace masu ni"imtacciyar Inuwa parking babur d'insa yayi karkashin wata bishiya.

Sauka yayi itama yasauke ta, bakin ruwan yaje da ita yasamu wani dutse yazauna. Ya zaunar da ita kan 'kafarsa  fuskarta yashiga kallo, a hankali ta bude manyan idanuwanta, wanda saida ya razana da ganin girman su da yadda take zazzare su, ayatul"kirsiyyu yashiga karantawa a ransa.

dubansa tashiga yi ba tareda tace komai ba dan dama ba maganar take ba, sai binsa da idanuwa kawai takeyi.

A hankali yashiga wanke mata fuskarta cike da fargaba, itakuwa komai batayi ba Sai kallonsa da takeyi.

Tas ya wanke mata fuskarta cike da fargaba,
Ganyen yaza'wa ya samu a gefen ruwan cikin gan yayyakin gurin yashiga goga mata agun da taji ciwon, d'an kuka tasaka masa na yarinta cikin Jin ciwon ganyen dan ganyen yana da d'an zafi,, a hankali yaci gaba da goga mata yana mai cewa....

Yi ha'kuri... da zafi ko? ai nasan da zafi yi ha'kuri,,

da haka har yagama goga mata, zuba mata idonsa yayi yayinda itama shi take kallo. kafun can tayi ko'karin tashi daga zaunen da take a hankali ya dubeta, yace.. Mai kikeso? batace dashi komai ba tayi ko'karin du'kawa... da sauri yace fitsari zakiyi? Kashi? ganin dai idan baiyi wani abun ba tabbas zata bata kayan ta gashi babu wanda zata saka idan ta bata wannan d'in.

   da sauri ya daga ta yacire mata pants a sanyaye, ya tsugunar da ita bayan ya gyara mata rigarta, take tashiga sakin fitsarinta hankali kwance tana ganawa yashiga debo ruwana yana watsa mata saida ya tabbatar da ta tsarkaku kafun yatashe ta ya maida mata wandon ta.

Zama suka koma yi,, yashiga saka da warwara... Itakam ganin duwatsu a gurin tashiga wasa dasu... haka taje fa 'kafarta cikin ruwa tashiga wasa da ruwan wanda ga dukkan alamu tana jin dad'in abunda takeyi..'kura mata ido yayi inda a hankali yaji kaunar yarinyar da tausayinta suna shigarsa,,

bai Ankara ba har tazo inda yake tayi shiru ta zuba masa ido,, can kawai tasaka kuka dubanta yayi yashiga tambayar ta mai yasameta mai take so? haka yashiga jero mata tambayoyi kala kala. duk da ya fahimci bata magana,, daga baya dai ya fahimci kamar yunwa take ji.

Dan haka ya d'auke ta ya d'ora kan babur yatashe shi yanufa wani d'an karamun kauye kusa da nasu,, gurin wata mai koko da Koda yaje ya siya yakoma gefe da ita yashiga bata tana sha cike da kulawa, da fari yanata fargabar ko taki sha sai kuma yaga tana sha dan haka hnkalinsa yadan kwanta.

Ganowa yayi ta koshi dan da yabata kin karba tayi ta zura masa ido dan haka ya gane ta koshi ne. Murmushi yayi, yaje ya siyo wani Shima yashiga sha saida ya koshi duk da dai kunu ne kawai yasha... Shima ba da wani yawa ba Kasancewar tashin hankalin da yake ciki.

Yana gamawa,, ya siya bread da ruwa ya rike musu suka koma cikin d'an dajin,, suka ci gaba da zama na tunanin kila wa kala.

Amma, wa"shi.  dan itakam ko a Jikinta sai wasanta take duk da fuskarta bata nuna hakan.saida yayi magriba da Isha kafun suka koma gida saida ya lallaba ta tayi bacci yafito yashiga cikin gida gun ummar su auwali, nan yadawo da abinci

Ajiyewa yayi dan bazai iya ci ba.



****
Kwanan UMAIMAH. hud'u a gun Zaid, saidai babu wanda ya taba lura da ita.. Kullum zai d'auke ta suje bayan gari su wuni yana saka da warwara wanda har yanzun ya kasa samun mafita. Kullum kuma sai wata irin boyayyar sha'kuwa suke dad'a yi... UMAIMAH"yanzun har d'an Murmushi takeyi, kamar yadda taga yakanyi idan tayi wani abun,, dan shi mutum ne mai saukin Kai da fara'a duk da halin Rayuwa da yake ci ki.. hakan baya hanashi murmurshi.

 

  *******
A kullum dare dama sai tayi buge buge, tunda yagane matsalar ta daga ta fara sai yashiga tofa mata addu'o'i, cikin ikon Allah bata dadewa sai tayi bacci.

Ashe duk wannan abun da ake ciki umma mahaifiyar su auwal"takan ji, tun abun baya damunta har tasoma zargi yau kuwa akan idonta Zaid yafita da UMAIMAH"

      dan haka tad'auka alwashin yana dawowa zata tu humeshi, aikuwa sun dawo bada jimawa ba, aka turo kofar aka shigo lokacin yana ko'karin gyara mata lullubinta dan da sanyi...

A razane ya dubi waye, ganin ummi sosai zuciyar sa ta bugu, ganin kallon da take masa yasa yashiga kame kame, ummi shine baki aiko inzo ba.... Ku.. ma.. ma.. yanzun nake shirin shigowa.... Wani duba ta masa. kafun tace......Zaidu"wacece wannan?
ta fad'a tana nuna baby dake baccin ta hankali a kwance,.. shiru yayi ya sunkuyar da kai

Dama na fad'a... A a umma ba yadda kika fad'a bane,
Amma zakamun bayani ne ko Yaya?

Umma tsintar ta nayi!
Wani irin mugun kallo ta watsa masa kafun tace,, wlh Allah shaida ne Sam banso zamanka a gidannan ba amma d'ana ya nace saida nabaka mahalli a zuciya ta yanzun gashi kanason janyo mun magana to ba dani ba,

Yazama dole ka zaba matu'kar zaka zauna damu to kasan inda ka Kai Yar mutane, tunda kace tsintar ta kayi...

Idan kuma da ita zaka zauna to fa Lallai sai dai kabar gidannan,

Kasan nayi kafun gari ya waye namaka wannan alfarmar!

Tana kaiwa nan a zancen ta ta tafi ta barshi ba tareda ta bashi damar bayani ko kare kanshi ba,,

Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,, ya shiga fad'a gumi na karyo Masa duk da irin sanyi da akeyi. duban baby yakeyi cikin rashin sanin mafita,  wani bala'in a karo na biyu ya biyo rayuwar sa kuma duk akan mace!





*****

Xinnee smart 👌💞💅💋👍💕
#vote
#comments
#share&follow xinnee_smart1

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro