40 MURFI TARE DA KAMMALA WA
Hhhhh ji da yawan ku kunsaka ni dariya 😂da masu cewa kansu ya qulle akan sidde da Zaid(to idan baku manta ba, bari mu d'an koma baya kad'an, lokacin Zaid yana gidan marayu ai anyi masa sharri yayi wa wata yarinya fyada yarinyar da ya d'auka matsayin kanwar sa, yawwa Fatn kun tuna yanzun to itace wannan yarinyar da mus"ab yake so ya akayi suka had'u da mus"ab? Sai ku biyoni Yar mutan RIJAU dan jin yadda abun yake 😀🤗)
Hhhh kuma wanda baku gane Murfi ba kunsani dariya fa sosai,, harda mai cewa wani novel d'in ne Murfi? Hhhhh to qarshen labarin😂
Thank you all for reading my story😍abunda yake daidai Allah yasa mu amfana wanda yake kuskure Allah ya gafarta mana,
Anan na kawo karshen wannan labarin na UMAIMAH🤗 masoya na na whatsapp da kuma Wattpad, babu abunda zance muku sai dai Allah yabar zumunci domin sunan ku bazai taba lissafuwa ba, Ngode sossai da qaunar ku a gareni hade da addu'o'inku, Allah yabar zumunci 😘😍😘
Sosai jikin ta yake rawa... ta dubi mus"ab ta dubi Zaid" ta kasa cewa komai.
Zaid ma sosai yake al'ajabin ashe zai koma ganinta a rayuwar sa?
Mus"ab jin shirun yayi yawa ne yasa ya shiga duban su, ganin irin kallon mamakin da sukeyi wa juna ne yasa yadan taba Zaid"hey what?
Numfashi Zaid ya sauke had'i da fad'in Allah mai iko.
bro dama kasanta ne?
madadin yabawa mus"ab amsa sai ya dubi siddifah had'i da fad'in ina ammi?
Sai yanzun tasamu nutsuwar amsa masa da tana cikin gida.
Yaya Zaid ina ka tafi ka barmu?
Na dade ina zargin mus"ab d'an uwanka ne amma tun lokacin da nafara ganin sa na zaci Kaine" saidai kuma yayi mun bayanin shi baima San wanda nake fad'a, Ammi ma tana ganin sa ta zata Kaine saidai amsa d'aya yabamu baisan wanda muke magana akai ba hasali ma shi kad'ai iyayen sa suka Haifa, a kullum ammi cewa take wannan kamar tayi yawa.
Gyada Kai mus"ab yayi had'i da fad'in hakane gaskiya ne na tuno lokacin da nafara ganin ki hakan kika hakikance kan Zaid ne saida na tabbatar miki da banma San wanda kike nufi ba,, kafun kika yarda a tsorace.
Allah sarki ashe d'an uwana ne.
Numfashi Zaid"ya sauke, kafun yace mai ya faru bayan Bana nan.??
Hawaye ta sauke masu d'umi kafun ta fice daga motar Kai tsaye cikin gida ta nufa.
Ido suka bita dashi.
Ammi.... Ammi.... Ammi kizo ga Zaid d'inki.
d'akin mahaifiyar ta tanufa tana kwala mata kira,, Ammi dake gyaran kaya a closet da sauri ta ajiye kayan hannun ta ta taro siddefah.
Ke lafiyar ki kuwa?
Tana haki kamar wacce tayi gudun klm 30
tace Ammi yau dai Allah ya karbi addu'ar ki ga Yaya Zaid"!!
Wani irin gingirim ammi taji maganar.
Za... Z... a... Zaid?
gyada Kai siddi ta shiga yi kamar qadangaruwa.
Ke siddifah kin tabbatar kuwa shine?
Wlh ammi shine har munyi magana dashi yana ma kofar gida ashe d'an uwan mus"ab ne.
Fiddo ido ammi tayi Kai haba? Koda naji ai biri yayi kama da mutum.
Maza bude musu d'akin baki,, bari in d'auko mukulli.
mukullin ta d'auko ta bata.
Itakuma waya ta d'auka ta shiga kiran,, mai gidan yana d'auka ta nemi izinin shi kan tanada bako yaron da tasha bashi labarin ya bace a gidan marayu yau shine a gidan, (kasancewar ta boye asalin abunda ya faru)
Izinin ganin sa tayi masa had'i cewa Shima gashi a kan hanya ya kusan gidan, fatan isowa lafiya tayi masa kafun ta kashe wayar ta.
Hijab d'in ta tasaka,, ta nufa guest room d'in.
sallama tayi a bakin kofar had'i da shiga bakin ta a washe.Lokacin siddi ta kawo musu ruwa kenan' zama tayi a d'aya daga cikin kujerun parlourn murmushi take mai hade da hawaye,, Allah sarki zaidu na ashe zangan ka,?
Ammi" Zaid ya fad'a da wata irin Murya mai tsananin nuna kewa, hade da tunano abu uwa da yawa.
gaisawa suka shiga yi,, saiga Alhaji ya shigo parlourn. Nan suka gaishe shi,
Ammi ce tashiga magana cikin hawaye,
Alhaji akwai abunda nasha boye maka tun Zamana dakai saidai abunda yasa ban fallasa maka ba shine, a ganina babu amfanin ka sani saboda ba abu bane na dad'i.
Labari ta shiga bashi tun shigowar ta Nigeria har yadda ta samu aiki a gidan marayu. Wanda wani yasani ta fad'a masa wani kuma bai sani ba musamman da tazo lokacin da aka kirata taga Zaid yayi wa siddifah fyade,, sosai abun ya girgiza shi musamman mus"ab,, dokawa kirjin sa ya shiga yi dan baisan cewa itace wacce Zaid ya bashi labari ba Sai yanzun kansa yake kawo wuta tabbas siddi ce akayi masa sharri da ita.
Ammi" taci gaba dacewa..... bayan guduwar ka daga gidan marayu,, na d'auka siddifah,, zuwa d'akin mu na samu ta farfado na gyara ta, da tadawo hayyacin ta tashiga tambaya ta ina kake, a lokacin zuciya ta tahau a kanka sunan ka ma da take kira banaso dan haka na shiga yi mata fad'a akan karta koma kiran sunan ka ai Kaine kaji mata ciwo.
Sai ta soma kuka tace Ammi bashi bane shi fa inata kiran sa yazo ya taimake ni amma baizo ba Ammi"
Wannan shugaban ne ya sace ni a d'akin nan Ammi"
Jin kalaman bakin ta ba karamun bugawa kirjina yayi ba take na shiga tunanin abubuwan da suka faru tabbas biri yayi kama da mutum.
Take hankali na yatashi na shiga nadama da dana sanin abunda nayi maka tun wannan ranar har yau da na ganka dan Allah ka yafemun. ta karasa fad'a tana zubar da hawaye.
Ammi na yafe Miki wlh ni dama ban rike ki ba.ko ba komai yaya ne yafi cancanta su nemi gafarar iyayen su.
Share hawayen ta tayi kafun taci gaba dacewa,, banda inda zani banda wanda zan fad'awa ba laifin ka bane saidai Allah mahallici dan baya bacci haka kuma baya zalunci, dan haka shi na shiga kaiwa kukana, Allah Maji rokon bawan sa, cikin ikon Allah da yake halin sa ne sai gashi ranar ankama shi yana lalata wata yarinyar Yar karama da bata ko Kai siddi ba a lokacin.
a wannan ranar ne mutane suka shiga yi masa tofin Allah tsine bayan yasha uban duka hukuma kuma ta tafi dashi.
Ganin hakan yasa wata rana na yanke shawarar neman aikin yi wanda zan bar gidan marayu,, saboda a lokacin komai ya gurbace,, Yara da yawa ana safarar su zuwa wasu kasashe wasu dan aikatau wasu dan iskanci,,bazan jure ba dan watarana akan yata za'a dire wannan ne yasani zage damtse gun neman gidan aiki,, (Shima ai sai dace idan ba haka ba kina aiki ana aiki akan yarki, Allah dai yasa mudace ya tsare mana imanin mu)
Wata rana Allah ya had'ani da hajiya asabe uwar gidan Alhaji, rufa'i, itace ta daukeni aiki a gidannan na d'auko siddifah muke aikin mu cikin rufin asiri kasancewar su mutane masu mutunci da Karamci.
Wata rana Allah yayi wa hajiya rasuwa,, bayan rasuwar ta da watanni nice nake kula da yaranta da gidan baki d'aya.
Har Alhaji y tuntubeni akan yana neman aurena ganin bani da wani zabi sama da hakan kuma Alhaji Mutumin kirki ne shi yasa na amince.
Aka d'aura aurena dashi.
Lokacin da siddifah tazo mun da zancen mus"ab sosai nayi mamaki da al'ajabin kamannin ku dan har wasu yan tambayoyi nayi masa saidai ya tabbatar mun dashi bashida d'an uwa.
Numfashi kowa ya shiga sauke wa.
Zaid ne ya dubi Ammi yace to Ammi a madadin d'an uwana mus"ab ina nema masana auren siddi dan Allah.
Jimmm!! Ammi tayi dan da kunya Zaid yanemi abu a gunta bai samu ba saidai kuma bazata iya watsa kasa a idanun miji irin Alhaji rufa'i ba, dan haka cikin sanyin jiki tace....
Allah sarki Zaid d'an uwanka ya makara a gaskiya mahaifin ta ya rigada ya bayar da ita.
A sanyaye Zaid yace shikenan Allah yasauke shi yafi alkhairee.
Amin.
Wani d'an siririn kuka siddi ta saka.
Mikewa Zaid yayi had'i da kama d'an uwan sa zasu fice har sunkai kofar parlourn,, Alhaji rufa'i, yace ku turo magabatan ku Bana son adau lokaci.
Wani irin juyowa mus"ab yayi da sauri yayi zube gaban Alhaji rufa'i yanata faman zuba masa godiya murmushi kawai Alhaji yake. Kafun yace ni dama bansan da zancen ka ba ai,, Ammi so take ta had'ani fad'a da siddifah kiga yanda take kuka kalan anjima ince amun shurba a kiyi ko?
Dariya dukan su suka saka,, da gudu siddifah ta fice zuwa d'akin ta.
******
Bayan watanni!
A Sanya auren Zaid da UMAIMAH" mus"ab da siddifah".
Ko wani bangaren shiri akeyi sosai,, UMAIMAH anje Niger an kwana biyu anata shan gyara, kala2.
Sai uwar soyayyah suke zubawa ita da Zaid d'in ta ko wannen su ji yake bazai rayu babu d'an uwan sa ba. Su duka biyun sunyi fama da kaddarori da suke shige da juna. a da Zaid yana tunanin A DARE da rana anya zai iya cika BURIN YA MACE a tareda yarinyar sa? saboda yadda yake mata duban MATAR MANYA! saidai FAHIMTA tafi komai a Zaman sa da ita ya fahimci cewa ita d'in wata irin kaddara ce da yasamu daga wata irin HATSABIBIYAR TAFIYA, bazai yi wasa da itaba UMAIMAH rayuwar sa ce, yayi ammana da komai MUKADDARI ne daga Allah.
A yau jumma'a 28th7/219 misalin karfe 2:30 na rana dubban jama'a suka shaida daurin auren yayan gata mus"ab da siddefah Zaid da UMAIMAH" akan sadaki naira dubu50 ko waccen su an d'aura auren ne a babban masallacin birnin TARAYYA Abuja.
Sai fatan Allah ya tabbatar da alkhairee.
Iyayen Zaid sun so matuka ya zauna a kano saidai Dad yayi musu shigar sauri kasancewar,, ya rigasu fad'a cewa yayi wa Zaid gida halak Malak, nasa ne.
Dole suka hakura shi mus"ab zai zauna tare dasu anan kano Shima dandatsetsen gidan sa yake wanda ya kawatu da kayan alatu.
Ankai Amarya UMAIMAH d'akin ta bayan taci uban kuka,,
Bayan kowa ya watse ango ya shigo shi d'ayan sa babu wasu gayyar abokai. dan shi dama bai damu da abokai ba idan ba wanda sukayi karatu tare ba.
Ya samu amaryar sa kudundune cikin lafaya sai kamshi take zubawa.
Hawa gadon yayi, had'i da yaye lafayar,, daga kanta.
idanuwan ta are lumshe suke gashin idanun nan gazar 2 Masha'Allah"
iskar bakin sa ya hura mata a fuska, wanda ya tilasta mata bude idon,
A hankali ta dube shi da kyawawan idanun ta, murmushi ya sakar mata, ita kuwa cuno bakin ta tayi ita a dole tana fushi an rabota da ummi" dariya yayi a ransa yace zanyi maganin lips d'innan,, aikuwa cafka yakai musu" yashiga tsutsa kamar ya samu gurbin zuma,
Saida ya tabbatar ya ladaftar da ita kafun ya sakar mata bakin.
Ita kuwa wata irin kunya ce ta shiga zagaya wa da ita. ta ma kasa bude idon.
Alwala yayi mata umarnin tayi ta sanar dashi tanada,, nan yaja su suka gabatar da sallah"sukayi godiyarku agun mahalicci mai kowa mai komai da yanuna musu wannan ranar daga qarshe suka nemi tsarin sa da kariyar sa akan sharrin shaid'an zuciya da na mutum da aljan.
Sunci sunsha daga naman da ykawo musu da kayan lambu zuwa lemuka.
brush sukayi suka bi lafiyar gado, kallon ta yayi ganin tabbas da lafayar zatayi bacci bayan shi har yaje d'akin sa ya canza.
Dariya yayi a ransa yace ohhh yarinyata kunya ta ake ji.
hannun sa yasaka ya shiga warware lifayar,, ita kuwa rintse idonta tayi, yana cire lifayar yayi jifa da ita duban ta yayi,...... Numfashin sa ne ya tsaya na d'an lokaci ganin kayan dake cikin lifayar" aikin wata Yar uwar ummi ce Aunty Aichtou"
Sosai ya kurawa hallitar ta ido, a ransa yana tasbihi ga sarkin kaga Halitta"
Sosai ya shiga ruda jikinta da kyakyawan romance,, mai wuyar Fassa rawa.
Tabbas wannan ranar sun kafawa juna tarihin da baya taba goguwa Koda da digo d'aya.
*****
A bangaren ango mus"ab ma kusan abun d'aya ne Shima ya kasance cikin farinciki, wanda bangare d'aya na zuciyar sa yana sake girmama iko na ubangiji"gashi dai ya saki wata saboda rashin budurci gashi ya auri wata babu virginityn kuma baiji komai ba Lallai ya yarda so yana da matu'kar tasiri a tausayi.
Dan shikam tausayin ta ma yake ji.
A daren sum sun faranta ran juna cike da kafa tarihi mai wuyar manta wa.
*****
Bayan biki kowa ya watse yan Niger ma ankoma su Yaya khaleefa ma ankoma,
Ummi zuciyarta wasai yaranta suna lafiya cikin kwanciyar hankali mai yafi wannan?
Dan haka itama ta zage damtse gun bautawa Allah dare da rana had'i da man sake shimfida kyakyawan zama tsakanin ta da mijin ta.
Sai fatan gamawa lafiya.
*****
Baby... Ko muce babyn Zaid anyi Kiba anyi freesh! daga ita har Zaid d'in, yaso ta koma makaranta amma kememe tace ita dai baya so wanda tayi ma Allah yasa masa albarka, tana son ko wani lokaci mijin ta ya so ganinta ya same ta.
Sosai yaji dad'in hakan,, kuma yasake jin wata irin soyayyarta a zuciyar sa, ga wani irin girma da kimar ta da yakaru a idanuwan sa.
Shima yafara aiki a wani babban asibiti dake nan Abuja.
Zaman su dai Masha'Allah.
KAMMALA WA......
Bayan shekaru uku"
Zaimah"anakai ga 2 bbys na farko mace na biyu namiji... Huda da kuma fu'ad.
Sunan ummi da Dad.
*****
Mussad" ma ankai ga Yara biyu"suma Amir da mimi
Ammi da Abba"
Ko wanne a family yana cikin farinciki da annushwa"sai fatan gamawa lafiya. Nasarori da sa'ar Rayuwa kullum shigo musu suke dama masu iya magana suna cewa bayan wuya sai dad'i.
MIENNEH..... MIENNEH.... MIENNEH fa...
Baby ce ke kwala wa Zaid kira"
Lokacin yana library"yana binciken wani littafin sa da ya shafi harkar likitanci.
tsayawa tayi bakin kofar ta wani cuno baki kamar wata baby.
jin alamun mutum yasa ya d'ago"ganin itace yasa yayi murmushi"
Yahdai yarinyata?
Sake shaka tayi waton ma baiji dukan Kiransa da takeyi ba.
Kawai sai tasa kuka.... ware hannayen sa yayi alamun taje. ba musu ta karasa gareshi.
Kirjin sa ta shige tana sauke ajiyar zuciya, can kuma kamar wacce ta tuno wani abu ta wani sake shi, tasoma kunkuni.
dariya yayi dan dama yasan yau yayi laifi,, amma kam bazai Barta tayi ta shan tsami ba.
Yo yayi kamar baisan mai ke faruwa ba, yace" wai meye ne uhmm? Ya fad'a yana shinshinar gashin ta da yaji gyara sai kamshi yake fidda wa.
Allah.... Allah... ni.... ni... nidai ina Lemo na?
Lemo kuma? Ya fad'a yana yatsina fuska, ba wani nan kana wani basar wa nasan Kai ka kwashe mun bayan.....
Shirun dole tayi saboda wani irin cafka da y akaiwa bakinta, tsotsa ya shiga yi son ransa saida ya tabbatar ya kashe bakin tsanyar kafun ya sake ta, yana murmushi had'i da lumshe ido.
Allah yarinyata yanzun kin iya rigima"kamar bakya ganin su fu'ad?
Kodai babyn nan mai rigima muka samu ne ya fad'a yana shafa marar ta,, jin abunda ke cikin ya dan motsa yasa yace ehenn!
Nikam nace wannan rigimar ba ta yarinyata bace,, babyn nan ne.
Kinsan meye?
Gigiza Kai tayi tana murmushi.
A kasalance tace sai ka fad'a.
Saitin kunnin ta ya rada mata,, this time I need twins baby's.
A aaaaaa....... Ta fad'a tana bude baki.
dariya yayi had'i da fad'in ok...... Naki wasa ne, bari kigani.
Daukarta yayi cak,, suka shige ta kofar baya.
Aka barni sake da baki 😨
Masha'Allah.
Alhmdllh!
Alhmdllh!
Alhmdllh!
Duka duka anan na kawo qarshen wannan littafin. Allah yabamu ladan alkhaireen dake ciki sharrin ciki ya yafe mana.
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci su tabbata ga shugaban hallita Annabi Muhammad(Saw)
Godiya mai tarin yawa ga masoya na kawaye na. Nagari love u guys.
My beautiful fans, thank you for everything
My group XINNEE SMART NOVELS 😍ONE LOVE 😘
MY WATTPAD PEOPLE ANATARE 😍
FATAN ZAKU BANI HAD'IN KAI A LITTAFAI NA MASU SHIRIN ISOWA GAREKU AMMA BA YANZUN BA 😂😂
HERE IS THE NAME OF MY NEXT NOVELS.
HATSABIBIYAR TAFIYA..... NA FARA D'ORAWA ZAMUYI 😂🤣
MUKADDARI
(THE DESTYNY)
ZINNIRA MUHAMMAD
Xinnee smart 😍😘
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro