4
Ummi"sosai tashiga damuwar rashin mafita,, Koda Dad yadawo a matu'kar har gitse tashiga kuka tana zayyana masa dan tayi ta neman number sa ba tashiga,, wanda a lokacin yashiga meeting ne da ma aikatan company d'insa.
Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un "" yashiga maimaita wa cike da damuwa,, nan take yafita da kansa yashiga nema had'i da yin report a police station mafi kusa da unguwar su,, nan take aka shiga nema abunka da mai kud'i......
*******
tunda tasoma tafiya bata tsaya ba bare wai wayawa,, har takama hanyar fita garin.... Kasancewar Abuja bariki ce kazo nazo babu wanda ya damu da ita duk da irin mutanen da ta had'u dasu a hanya kuwa,, wasu ma idan sunganta Allah Allah suke su wuce dan tsoron yanayin ta,, tazo kwanar wani d'an karamun gari nan kusa da fita a buja da ake cewa damba"daidai kan wata kwana.... wani mai mashin yazo shigowa itakuma tana ko'karin fita sukayi kici'bis....
take yabuge ta ta fad'i,, Shima ya fad'in saidai cikin ikon Allah babu abunda ya sameshi dan haka cikin sauri ya tashi yana ko'karin duba ta,, a zabure tami'ke,, tashiga ja dabaya Shikuwa ko'karin rikota yake ganin yarinya ce karama,,
Duk da fargabar da take ransa a game da ita"kasancewar gurin shiru bakajin hayaniyar komai gashi duhu yafara dan wasu masallatan har sun fara kiran isha"i.
Cike da jarumta yashiga... Mata magana.... Yarinya ina zaki cikin dare haka? itakam ko'karin ci gaba da tafiya take,, ganin haka yasa ya kyaleta"zuciyarsa naci gaba da gargadinsa,, akan ta...
Take yahau babur d'insa,, ya burga yatafi.. Aikuwa kamar jira take taci gaba da tafiyar.
L
Saida yabada baya zuciyarsa tashiga wasi wasi da tunanin kila wa kala,, bayason ya maimaita yar gidan jiya domin kuwa har yanzun zuciyarsa takasa man tawa da kuskuren da ya aikata wanda yayi sanadin rabuwarsa da alkaryarsa"duk da ba gida bane kamar sauran gidaje yana matu'kar so da kaunar gidan duk da tabon dakega duk wanda yafito a cikinsa hakan bai hanashi kaunar gurinba,, saidai kuskure d'aya tal yayi sanadin da rabuwarsa da gidan ta zamto ta har abada.
Tunani yakeyi yana dad'a wai wayenta,, baiyi aune ba ya hango wata babbar mota..... irin masu zuwa Lagos d'innan,,, tayi kanta yayinda itakam ko a Jikinta tafiyar ta take kan titi kereriya"duk da horn d'in da mai motar ke rafka mata Sam batayi tunanin,, Sauka kan titin ba hasalima batasan yanayi ba,,
Da wani irin mugun speed ya isa kanta wani irin fizga yayi mata kan mashin d'in Allah y agaje su basu fad'i ba,, kuma mai motar yawuce ba tareda ya bugeta ba,,
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke,, cike da tsantsar,, fargabar abunda yake son yi,, ya dubeta jin ta sake a jikinsa,,
Abun mamaki baccin ta takeyi hankali a kwance wani sabon fargaba ne yakama shi,, gashi rungume da Yar mutane da baisan ta ba mutum ce? Aljana ce? shidai gata ya rike nannauyar ajiyar zuciya yasauke,,
Haka yaja babur d'in har cikin karamun garin,, daidai kofar gidansu abokinsa,, inda yake samu Shima yake ra'bawa ya tsayar da babur d'in.
Parking babur d'in yayi,, kafun ya Sauka da ita rungume a kirjinsa,, yayinda zuciyarsa ke wani irin Bugawa.
Key d'in d'akin ya d'auko a aljihunsa yashiga bud'ewa"dama abokin nasa baya gari dan haka yashiga da ita kan yar shafaffiyar katifar d'akin ya sauke ta, kwantar da ita yayi ya'kurawa Kyakyawar fuskarta ido"take yashiga karanta ayatul"kirsiyyu. Yashiga tofa mata a zuciyarsa yana cewa idanma aljana ce ke kisan inda dare yayi miki
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro