38
take salma ta zube jini na zuba,, bakin ta sai rawa yake alamun tanason tayi magana.
da sauri Rahamu" ta isa gunta ta tallafo ta tana fad'in sunan ta da wata irin muryar tashin hankali.
Jijjiga ta tashiga yi,, a a..... Salma karki mun haka.....Wayoooo na boni na lalace Wayoooo ni Rahamu.....
Salma idonta na lullumshe wa, ta dubi uwar,, mmn... Mommy..... Kiji tsoron Allah ki tuba da abubuwan da kikeyi ki nemi gafarar wanda kika zalunta, mommy nidai na yafe Miki.
Mommy... Ki.... Yafe mun.....
Daga haka jikin ta ya saki alamun rai yayi halin sa.
Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un.
Rahamu wani mugun ihu ta saki lokacin da ta fahimci yarta ta bar duniya.....
Jijjiga ta ta shiga yi tana ihu.
a lokacin mus"ab ma yana kan Dad yana faman jijjiga shi dan ganin ya farfado.
Su Shago" na tsaye ko a jikin su.
Police d'in da mus"ab ya kira kafun yazo gurin ne, suka lallabo suka zagaye su.
Rahamu"tana ihu da komai aka tusa keyar ta da handcuff.
da kyar Dad ya iya takawa da kafarsa saboda jiri da ke dibar sa,
mus"ab ne ya dinga taimaka masa har suka isa gida.
Police kam kwasar su Rahamu shago da gawar salma sukayi zuwa office dan yin bincike.
*****
Ummi tanayin tozali da halin da mijin ta yake ciki hankalin ta ya tashi.
Sosai ta rude mus"ab ne ya shiga kwantar mata da hankali.
Dad sosai ya shiga halin damuwa da tunanin d'an sa gudan jinin sa shekara days shekaru bai neme shi ba Yama manta dashi hakika yana cike da nadama Rahamu kuwa ta cuce shi shuta mai muni,
Sosai yake kuka da hawayen sa. ko a ina yaran sa suke?? Wani hali suke ciki?
Ummi" ma ganin yana kuka itama ta fashe da kuka,, duk da cewa bata San komai da yake faruwa ba saidai zata iya fahimtar wani abun a cikin kalaman sa.
Mus"ab kasa ce musu komai yayi face tausayi da ke masa yawo a zuciyar sa,, wace irin al'umma muke ciki? Wani irin zamani muke ciki? hakika Rahamu a cikin azzaluman mutane zaluncin ta mai muni ne.
Ki raba Yaya da iyayen su? Wannan wani irin girman haki ne? Ki nemi soyaya ta haramta ciyar hanya..... Kiyi zama na cin amana zama na yaudara da tsantsar sonkai ki ciyar da mutane najasa....abubuwan Rahamu sunyi yawa,, anya Allah zai yafe mata kuwa..??
Sallamar mai gadi ce ta dawo dashi daga tunanin da yake ciki,
fita yayi daga parlour zuwa gun mai gadin.
a bakin kofar parln ya same shi,, dama baki akayi nace su bari in sanar da masu gidan ko sun San da zuwan su, d'an jimmm!cewar mai gadi.
Mus"ab yayi kafun yace... Maza ko mata?
A a kamar dai ma gidanci ne da iyalin sa,, naga ma Mutumin yana yanayi da Alhaji"saidai dake ban taba ganin..... ganin mus"ab ya nufa bakin gate d'in yasa yayi shiru, had'i da bin bayan sa.
Kallo d'aya mus"ab yayi wa khaleefa ya gane shine d'an Alhaji Tahir yuguda"
Umarni yayi wa mai gadi da ya bud'e musu kofa kasancewar a taxi suka zo daga airport.
Bayan sun fito daga motar mus"ab ya baiwa khaleefa hannu suka gaisa. Matar sa ce ta gaishe shi cikin harshen turanci.
tare suke da yaran su uku kyawawa" kansu mus"ab ya shiga shafawa a ransa yana sake kad'ai ta Allah.
Yau ga dan wayann bayin Allah ya dawo garesu ba tare da zato ko tsammani ba.
dunguma sukayi cikin gidan.
Koda iyayen sukayi tozali da gudan jinin su kuma sanyin idanun su take suka sake sakin wani sabon kukan farincikin.
Dad har da sujood shukur"tsabar farin ciki.
Bayan anci abinci an huta,, khaleefa yake basu labarin bayan barin sa da auren da yayi,, ga kuma yaran sa, jasmeen, fudail, da haneefa.
Yaci gaba da cewa,, ban taba tunanin Koda sunan kasa ta ba bare kuma iyayen da suka haife ni wanda na rasa mai yahau kaina a wancan lokacin.
Watanni biyu da suka wuce a Facebook wani d'an Nigeria ya turo mun friend request nayi accepting, daga gaisawa muka soma zumunci sosai inda har yabani d'an takaitaccen tarihin sa, bayan naji sunan kasa ta sosai kewar ta ya kama ni, tunda na bar gida ban taba danganta kaina da kasa ta ba Sai wannan ranar nake ce masa nima ai d'an can ne,, wata rana muna fira dashi a Facebook, yake ce mun shi yana aiki ne a company,, na wani mutum mai mutumci da kirki Alhaji Tahir yuguda"!
Sosai hankalina ya tashi damuwa ta shigeni jin wannan sunan wanda tabbas sunan mahaifi nane, hakika haduwa ta da Abbas"Alkhairee ne. tun daga wannan ranar nake matu'kar kaunar son zuwa domin ingan ku sai a lokacin nake jin ban kyauta ba inajin bazan samu kwanciyar hankali ba matu'kar baku yafe mun ba, kuka yasa sosai, nan iyayen suka shiga cewa mun yafe maka khaleefa, Allah ya yafe mu.
Sosai ummi tayi farinciki kafun ta saki kukan kewar UMAIMAH" anan ta shiga bashi labarin bayan tafiyar sa, shi ma yayi kuka sosai na batan Yar uwar sa.
*******
Kashe gari.
Bayan mus"ab ya tashi da safe yasamu Dad da zancen yana son dan Allah zasu je wani guri gaba d'aya da alhalin gidan,, dan Allah Kar ya tambaya ko ina zasu je ko mai zasu je yi shidai bu'katar sa ya amince.
Sosai dad ya yarda da Zaid bazai taba cutar sa ba dan haka ya amince.
******
Sun isa kano misalin 12 na rana.
Kai tsaye mus"ab yayi horn a bakin gate d'in tafkeken gidan su.
Bayan mai gadi ya leko yaga mus"ab ne take ya hau mamaki,, yaushe ya fito da har yake dawowa gashi motar Bama ta gidan bace, haka kuma shi da ko tafiya yaushe 2 ya fara?
Ganin ba shida mai bashi amsa yasa ya bud'e gate d'in.
******a gaggauce 🤣😂
Mus"ab ne ya fara shiga gidan,, babu kowa a parln dan haka kai tsaye ya kira wayar Zaid"bugu 2 ya d'auka. Fad'a masa yayi suna parlour ya baiga kowa ba?
amsawa yayi da yana zuwa.
fita mus"ab yayi ya shigo da su dad.
bayan sun zazzauna sai ga Zaid ya fito yana d'an d'an gyasawa,, mi'kewa dukan su sukayi aka shiga kallon kallo, ga mus"ab ga Zaid,,.
Murmushi Zaid yayi had'i da fad'in ummi na Dad sannun ku da zuwa, gaban ummi ya buga kardai wannan ne asalin Zaid d'in? to idan haka ne shi wannan kuma wanene?
Abun dai da al"ajabi.
Zaid ne yaje har d'akin Abba ya fad'a masa bakin sun iso duk da dai ya fad'a masa da safe kan zasuyi baki idan son samu ne su hajiya ma su kasance a gurin ita da gwaggo Jamila. Wannan ne yasa Abban bai fita ba kuma duk yayi musu waya yana son ganin su a gidan sa,, wanda Shima a yau ya yanke zai bayyanar da abunda Jamila taimasa!
amsawa yayi da gashinan zuwa.
Bayan ya fito d'akin Abba parln Mami ya je anan ya sameta tare da UMAIMAH"suna fira.
Suma sanar dasu yayi"
Fitowar Abba daga daki yayi daidai da Fitowar Mami tare da UMAIMAH".
take parlourn ya kacame da abun mamaki kowa da abunda yake bashi mamaki, ummi kam kasa motsin kirki tayi.
Ana haka saiga hajiya da Jamila da su azumi wanda suka iso a tare.
Sun shigo cikin gidan suma suka tadda wannan abun al"ajabi.... take jikin su yahau rawa...... dukan su.
Mus"ab ne yayi karfun halin cewa,, wannan ba komai bane daga cikin iko da qudura ta ubangiji,al'amarin sa. Nan ya shiga bada labarin duk abunda ya faru tum daga lokacin da ya Sauka a Airport zuwa karon sa da Rahamu da yadda ya dinga binta cikin tako.
Sosai guri ya d'auka hayaniya.
Daga nan su Abba suka bada labarin tsintar UMAIMAH" har aurawa d'an su ita da sukayi.
Zaid ma ya bada labarin rayuwar sa, inda ya had'a da cewa saidai nasan ni ba d'an ku bane domin nafi tunanin iyayena bata halastaccen hanya suka...... da sauri Mami ta rufe masa baki had'i da rungume shi karon farko a rayuwar sa da yaji d'umin mahaifiya itama a gare ta hakan ne yau taji d'umin d'an ta da ta dade da fidda rai da shi.
Shiru yayi banda kuka babu abunda yake,,
Su hajiya suwaiba jiki yayi La"asar banda rawa babu abunda jikin su yake dukan su.
Jamila kam kuka take bihaqqi da gaskiya.
Abba ne ydauko CD da yayi, nan ya had'a komai take abu ya somayya fitowa kowa ya maida hankalin sa sosai akan TV.
Lokacin dariya Jamila ta gan kanta rado rado"sanda ta kawo abinci sosai gaban ta ya fad'i,, sauran mutanen dake gurin basu wani fahimci komai ba.
Abba ne ya soma bayani kamar haka....
Jamila"!!
Jamila jin ankira sunan ta take gaban ta yayi wata mummunar fad'uwa.
ba tare da ta amsa ba ta sake dukar da kanta dan tunda take yayan nata bai taba mata irin wannan kiran ba.
Ci gaba da magana Abba yayi...
labari ya shiga bata da ma wanda bai San matsayin ta a gidan ba,, tun lokacin da suka d'auko ta daga gidan marayu shi da mahaifin sa, zuwa irin rikon da iyayen sa sukai mata bayan basu San wacece ita ba sun taimake ta da abunda ba'a siya. (iyaye) sun bata tarbiyya wanda zasu iya cewa ta butulce musu.
yaci gaba da cewa wlh kin matuqar bani mamaki a lokacin da naji kina waya,, ya zayyano komai da yaji... Idon sa na fidda kwallah,, yace wlh da iyayena zasu dawo wannan duniyar suji abunda kika aikata mun nasan sai sunyi bakin ciki, ba dan komai ba Sai dan kinyi watsi da tarbiyyar su.
Wani irin gursheken kuka Jamila keyi mai kama da na nadama,, marar amfani.
Wayooo Allah na kaicona ni Jamila ban kulawa kaina alkhairee ba ina zan sa Rayuwa ta, tabbas ni butulu ce na butulce wa ni"imomin ubangiji na butuncewa iyaye burin ko wani d'a.
Wani irin kuka take muryar ta na bada wani irin sauti dake fitar da nadamar ta.rarrafa wa tayi gaban Abba,, Yaya dan girman ubangiji Allah.... Ka dubi niimar sa a gareka ka yafe min wlh ba'a son raina bane amma na roqe ka da kayafe min!
Jin zuciyar sa yayi ta karye yace na yafe Miki. Allah ya yafe mana saidai a gaskiya babu ni babu ke,! tace... Na gode Yaya da wani irin sauti mai ban tausayi.
Matsawa tayi gurin Mami ta nemi gafarar ta itama cewa tayi ta yafe,,
Zaid ma yace ya yafe.
Tana kuka tana komai ta kama hanya zata fita har takai kofa tace da hajiya suwaiba....
Hajiya". Kema na yafe Miki albarkacin yafiyar da nasamu!!
daga haka ta fice.
Hajiya kowa kura mata ido yayi,, ganin haka ta soma borin kunya,, tana ta zuba zance,,
Yawu ya cika baki bata cusa taba garin da boka yayi umarnin ta dinga cusawa idan zatayi magana ba, ai kuwa abu yazo da bacin rana take ta soma sambatu tana ta fallasa, Abba daki ya shige yana ta kuka"
Hajiya kam bihaqqi ta zare!!
UMAIMAH kam tunda ta shige jikin uwar ta bata ko matsa ba.
******
Jamila tana kuka ta shiga motar ta ta fice daga gidan tafiya kawai take amma ita kanta batasan yadda take juya motar,,, kawai tunanin butulci irin nata take Koda dai Allah yasani wani abun tanayi ne amma a ranta tanajin zafin abun,
Nadama ce keta kaiwa da kawowa a ranta,, tabbas bata zama d'iya ga wayann mutanen ba, Sam bata cancanci hallacin da sukai mata ba.
Ko su waye iyayen ta?
Wata qila ma Shegiya ce ita amma mutanen basu ji kyamar daukar ta ba duk da basu San asalin ta ba😭amma ta rasa da me zata saka musu saida butulci?
Wani irin kuka ne ya kwace mata tana yi tana fad'in,, Wayoooo Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un Allah Allahumma"ajirni fi'musibati wa"akhlifni khairan minha! Astag'firullah ya Allah ka yafe min......... tama manta da tuqi take yi,, ta dafe kanta a kan st ba tare da ta tsaida motar ba. daidai ta kawo flyover,, aikuwa ta yi wani irin mummunan hatsari. a take Jamila tace ga garinku nan.
Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un Allah sarki mai rai baqon duniya,, duk matsayin ka ko jin kanka wata tsiya wata rana sai an binne ka kazama abincin gara. Gamunan Kara jijjin gine, Allah kasa mucika da Imani.ka gafarta wa wanda suka rigamu 🙏😭
Next page insha'Allah ma qarasa. 😍
Garku ji bbu dad'i idn kunga errors kuyi haquri no time for editing 😥
Xinnee smart 😎
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro