37
Rahamu"tana shiga office d'in doctor. Ya soma yi mata bayani.
Hajiya waton a gskiya yar ki tana matu'kar bu'katar kulawa,, saboda a binciken d mukayi mun gano ta kamu da cutar ulcer. ga kuma juna biyu da ke tare da ita. Waro ido waje Rahamu tayi kafun tace Kai likita salmar ce ke da ciki?
'kwarai kuwa hajiya cikin nata ma yayi girma dan yanzun haka yana wata biyar ne.
Eeehhh!
gyada Kai likitan yayi kafun ya gyara Zaman glasses d'in sa.
Yaci gaba da cewa. hajiya cuta ai ba mutuwa bace kuma a duk lokacin da ta samu mutum ana ko'karin bashi kulawa da shan magani yadda ya kamata to cikin ikon Allah sai kaga mutum yazo ya warke ma.
Kuma an dace to dan haka kiyi ko'karin kwantar da hankalin ki ta yadda zaki samu damar kulawa da mara lafiyar ki.
Waton hajiya bayan abubuwan da nake fad'a miki a yanzun haka ma yar ki tana d'auke da cuta mai karya garku war jiki.....
Kai dakata dan ubanka!
Cewar Rahamu wacce ke faman zaran ido kamar wacce tayi wa sarki qarya.
Na bonu ni Rahamu"ciki kuma salma"!
da wanne zanji?
ga uban kankatt.... kanjamau?
Numfashi ta shiga sauke wa kamar mai cutar athma.
Zani a hannu ta fita daga office d'in.
Yana fad'in hajiya ga takardar magunguna.... Ina bama tasan yana yi ba.
d'akin da salma ke kwance ta shiga.
Jijjiga salmar ta fara yi,, Salma!
Salma dn ubanki ni zaki tozar ta? ni.... Ni.... Ni Rahamu"yar mai layu?
baki isa ba what's kinyi kad'an, dukan ta ta shiga yi tamkar wacce ta zare.
Nurse d'in d'azu ce ta shigo dan Bawa Rahamu" takardar drugs din da bata karbo ba.
Tana zuwa tasamu Rahamu sai auna wa salma duka take bilhaqqi.
da sauri ta shiga janye Rahamu.
Rahamu ganin an hanata dukan salmar sai kawai ta koma gefe ta zauna had'i da aza hannu a ka. Kuka take son yi amma ta kasa.
Nurse d'in dai ganin ta daina dukan ta ta fice daga d'akin salin Alin karatun kurma.
salma da tasha wuya a hannun Rahamu".
Sai ajiyar zuciya take,, wani tunani ne ya fad'o mata, a hankali ta shiga cewa.
Mommy dan Allah kiyi ha'kuri.
Nayi alkawarin yin duk abunda kika ce zanyi miki. Ko ba komai ke mahaifiya ta ce.
Mommy da cewa nayi mai zai hana kiyi ko'karin ganin anyi aurena da Zaid?
Kinga sai muce cikin sa ne ko bayan na haihu,, in yaso sai muce tun kafun muyi aure yamun cikin.
tunda tasoma magana sai yanzun Rahamu ta dube ta.
Shiru tayi tamkar tana nazarin salmar a zahiri ita take kallo amma a ba d'ini Sam ba ita take kallo ba. nata tunanin take, zuciyar ta ce tace ai salma bata San tana da kanjamau ba" dan haka Za tayi amfani da salmar gurin ganin ko bayan auren su idan dai Zaid d'in yana samu ai shikenan kanjamau ai hanya ce barzahu.
Idan dukan su suka mutu ai shikenan,, zata samu yadda take so komai zai zo mata da sauki wannan shine mafita.
tashi tayi taje gun Salman shikenan na amince da shawarar ki.
Hawayen ta ta shiga gogewa.
*******
Kwanan Zaid" hud'u bayan abunda ya faru cikin ikon Allah yasamu lafiya dan tafiya ma yanzun yana iya d'an taka wa.
Wannan yasa doctor d'in ya bashi sallama.
Suka koma gida.
Suna komawa Mami ta sa suka koma sashin su, wanda Sam Zaid baiso hakan ba dan shikam Allah yasani yana fargabar kebewa da baby ko ba komai yanzun tayi girma ta mallaki duk abunda namiji ke bu'kata a gun mace haka kuma ga tarsirin da so keyi tsakanin ma"aurata baya fatan ya sake maimaita kuskuren baya wanda har yanzun yake na dama.
Koda suka koma kowa d'akin sa ya nufa.
Abba" bai nuna wa Jamila komai ba har tazo ta sake duba mus"ab d'in.
Wanda yana daga cikin shirin sa, na kin nuna mata yasan abunda take ciki.
********
Hello" Assalamu"alaikum"
Wa"alaikissalam.
Ummi"
Na"am wa nake ji kamar Zaid? Ummi ta fad'a excitedly.
yar dariya mus"ab yayi a ransa yace to muryar ma kama muke kenan?
Ni ne ummi.
Masha'Allah Masha'Allah Zaid baki yadawo kenan,, mun godewa Allah.
dariya mus"ab yayi kafun yace...
Ummi dama nace idan babu damuwa dn Allah kizo Nigeria" sabida akwai maganar da ya kamata muyi, dan Allah ina neman alfarmar ki zo.
to Zaid fatana dai Allah yasa lafiya.
Lafiya fa ummi,, wani abune dai da ya Shafe mu, akwai bu'katar kizo d'in dan Allah.
Shikenan Zaid insha'Allah zan zo cikin satin nan.
Yawwa ummi nagode,, amma ina neman wata alfarmar a gunki.
Ina jin ka Zaid.
Ummi Bana son ki fad'awa Dad munyi waya.
d'an jimmm! tayi kafun tace shikenan insha'Allah bazai sani ba.
Nagode ummi.
****
Shiru yayi bayan yayi waya da ummi.
tunani yake ta inda zai fara.
a dole yana bukatar yakar Rahamu saidai dole yayi taka tsantsan dan mace ce mai hadarin gaske.
Dole ya kula.
Shirya wa yayi ya nufa asibiti.
*******
Mommy" na koshi fa,, ai shikenan tunda dai kinaji likita yace ulcer ta kama ki, gaki kuma da kayan wannan shegen ai gwara kina cin abinci ko ba komai halittar ki ta dawo kamar da.
Amma yanzun dan Allah dube ki ai sai ayi saurin gane abunda ke damun ki.
Ita dai salma bata ce komai ba. tana dai sauraren uwar tata.
tashi Rahamu tayi had'i da fad'in bari nidai in d'an shiga ban d'aki.
Salma na ganin shigewar ta,, ta d'auka wayar ta ta shiga bincike,, 'kilaun!
Sako ya shigo,, da sauri salma ta duba.ga abunda ta gani.
Na samar mana inda zamuyi wannan taron malam yace a nan zaki fashe wancan kwalbar wanda idan kika fasa ta tamkar zuciyar Tahir kikace bude kika shiga.
Sai kuma wancan zancen da mukayi dake zan zo akan lokaci ni da Yara na dan haka kema kizo kan lokaci.!
tana gama karanta wa da sauri ta ta maida wayar inda take kirjin ta yana bugawa.
Wai sai yaushe ne mommy zata San akwai Allah? Sai yaushe zata soma yiwa kanta tunanin kyakyawar Rayuwa? hawaye ne ya sauko mata na tausayin uwar ta da ita kanta.
Motsin fitowar uwar ne yasa tayi saurin goge hawayen ta. tayi lumm kamar yadda take d'azun.
naji kamar an turo mun Sako ko? Cewar Rahamu" gaban salma ne ya fad'i dan dole ta gane ta bud'e,, yau ta bonu.
Rahamu na daukar wayar wani sakon ya sake shigowa, irin wancan ne hakan yasa bata tsaya tunanin wancan na farkon ba, da sauri ta shiga had'a kayan ta.
A duk lokacin da kika ga zatayi wani abu mai mahimmanci,, to kiyi ko'karin sakala mata wannan camerar d'in zata taimaka mun 'kwarai da gaske.
Maganar Zaid ce ta fad'owa salma lokacin da yasake zuwa asibitin dan jin ko akwai wani abu.
tunanin ta ne ya dawo ganin Rahamu"na sakala jaka alamun ficewa zatayi.
da sauri salma ta ri'ke cikin ta, had'i da fad'in Wayoooo Allah na cikina.
Sai ga hawaye na sauko wa.
duban ta Rahamu tayi cikin damuwa,, tace na bonu ni Rahamu" salma meye kuma?
Cikuikuye Rahamu tayi tana fad'in Wayoooo mommy ciki na,, d'an zama gefen gadon Rahamu" ta yi had'i da fad'in Ayya sannu.
Salma,, sannu kanta ta d'ora akan kafar ta tana mata sannu ita kuwa sai kuka take bilhaqqi da gaskiya dan tausayin uwar dama kanta.
dukawa Rahamu tayi saitin cikin tana sha shafa mata tana fad'in sannu salma, sannu Allah yabaki lfy.
hummm! Hummm!
Kawai salma ke fad'i kamar gaske.
saitin hular uwar inda ya zame ta samu ta makala camera d'in kasancewar karama ce sosai kuma Plat babu wani nauyi.
Rahamu hankalin ta na kan yar bata San ma anyi ba.
Ajiyar zuciya salma ta sauke had'i da fad'in, mommy ai saida nace miki na koshi na koshi kika ce dole sai naci.
Wlh kuwa...... Ai shikenan bazan sake baki da yawa ba.
Ni zan d'an fita ai cikin yayi sau'ki ko.
Eh yayi dama cikar da yayi ne. ta fad'a tana murmushin yake.
dungurin ta Rahamu tayi had'i da fad'in shegen raki dai, sai na dawo.
Har takai kofa salma ta kira ta.
Mommy!
juyawa tayi tana duban yar ta cike da soyayyah bata taba jin kaunar yar ba irin yau.
Ki kula da kanki.
Salma ta fad'a hawaye na sauko mata kasancewar tana kwance ne yasa uwar bata lura da hawayen ba.
Ta ce ki jirani zan dawo, zanyi waya laraba zata zo ta zauna dake.
OK bye.
Bye.
Da sauri ta fice Kai tsaye motar ta tanufa.
Da uban speed ta fice daga asibitin, zuciyar ta fal murna ansamo abunda zata mallake Tahir. ai hakan ma yayi kawai sai ta kashe Lubabatu da wani banzan Zaid"
Gwara ta zauna da yar ta du duniya bata da sama da yar ta dan haka tunda ga mafita kawai zata zauna da salmar suci dukiya suyi wadaka.
Abunda zata Haifa yazo cikin gata, Koda salma ta mutu d'an ta yana nan zai maye mata gurbun salma.
da wadannan tuna nukan ta dinga bin hanya, tana yi tana waya da shago.
******
Mus"ab yana ganin ficewar Rahamu" ya fad'a d'akin.
Salma tana ganin shi ta fashe da kuka.
Shiru yayi yana duban ta, Lallai uwa uwa ce banda haka mai ake da uwa irin Rahamu"
Kinga kiyi ha'kuri ni ki fad'a mun ya ake ciki?
Cikin karfafa wa kanta guiwa da tunanin wannan yana daga abunda Za tayi a rayuwar ta na alkhairee ne.
Hakan yasa a sanyaye ta kwashe komai ta fad'a masa. Jikin mus"ab har rawa yake.
da sauri ya fice daga d'akin.
Da sauri itama salma ta bi shi.
tuni yaja motar sa,
Gida yaje Kai tsaye!
System d'in sa ya d'auka.
Da uban gudu ya koma ficewa,, dubawa yayi yaga ina take nufa abun yana reading ga location.
Kai tsaye office d'in dad yaje yace yazo su je.
Ganin yadda Zaid yake a firgice ne ya daga hankalin dad, tambayar sa dad yake amma ina sai cewa yake ina zuwa dad.
Dad kam a ransa sai fargaba yake ina yaron zai Kai shi?
Salma ganin bata ga Zaid ba ne yasa ta samu Aron waya mommy ta kira a lokacin Rahamu tana gab da isa inda Za ta.
Ganin kira da bakuwar lamba ne yasa ta d'auka a zaton ta su shago ne.
Hello" shago gani na kusan isowa yanzun haka ina,, daidai night clup d'in na fita gari gani zan d'auke hanya kenan.
tana fad'in haka ta kashe waya" dan bata son tana tuki take magana.
Salma najin haka ta baiwa mai waya wayar sa, taxi ta samu ta hau Kai tsaye ta fad'a masa inda zata. tana fad'in yayi gudu.
*******
Rahamu"tana isa gurin ta samu su shago sun baje cikin wata Yar rumfa sai shaye2n su suke yi.
ga wani mutumi durkushe,, sun daddaure shi. Sun kulle masa bakin sa ma sai mutsu mutsu yake gwanin tausayi.
tana isa suka sa ihuuuuuuuuuuu, sai hajjaju. tamu kona gari, ki dade kiyi qarqo, kowa ya daga miki d'an yatsa mu karya shi.
Wani azababben girman Kai ne yasa ke taso mata, kujera aka bata ta zauna wacce take ta musamman ce.
Shago godiya nake.
*****
tafiya yake wacce kana gani kasan koya yake,, a cikin lambun gidan. Yana yi yana tsayawa ya huta, duk ya had'a uban gumi.
dukawa yayi daga tsaye yana sauke numfashi. d'agowa yayi dan jin alamun mutum a kusa da shi.
Idanuwan sa ne ya Sauka cikin nata.
hannun ta ya kalla ruwa ne a cikin cup ta mika masa. Amsa yayi had'i da fad'in na gode.
Murmushi ta sakar masa.
Shima maida mata yayi, kafun yakai cup d'in bakin sa.
Saida ya shanye ruwan tasss, ya bata cup d'in.
Amsa tayi ta ajiye.
kujera ta d'auko ta ajiye a saitin inda yake tace...
Ya kamata ka huta.
bai zauna ba Sai cewa da yayi,
A a ba yanzun ba ina bu'katar na sake yi bakiji likita yace nake kokarta wa ba. Ko so kike mijin ki ya zama gurgu.
A"uthubillahi....!
ta fad'a tana rufe baki.
dariya ya tun tsure dashi....Ba kyason na zama gurgu kenan?
Itama dariya tayi tace insha'Allah ma zaka koma yadda kake da saidai banda halin.
Bangane banda halin ba?
Sai yanzun ta gane katobarar da ta tashi yi.
Ba komai tace tana murmushi.
Shikenan tunda bazaki fad'an mai kike nufi ba.
Gefe ta koma tna duban shi yana ci gaba da zazzagawa,, tray d'in ta tasa ruwa da cup akai ta d'auka zata koma daidai yana yo wa ta kusa da ita.
Aikuwa ya zame zai fad'i da sauri ta tallafo shi yayi mata nauyi, dan haka ba bata lokaci sukayi kasa tare.
Kan grass d'in gurin suka zube kowa yayi gefen sa daban saidai suna fuskantar juna.
qurawa juna ido sukayi,, kafun ya lumshe idanun sa yana budewa suka sake had'a Ido a tare suka saki murmushi.
Da sauri baby ta mike.
Daukar tray d'in tayi zata tafi,, shagwabe fuska Zaid yayi yana duban ta, waye ne zai tashe ni?
Au nice na fad'ar dakai kenan, ta fad'a tana rausayar da kanta gefe d'aya.
Washhhh! Ya fad'a tamkar wanda yaji ciwo.
da sauri ta ajiye tray d'in hannun ta had'i da isa gurin sa, ayya kaji ciwo ne?
sannu.
duk ta wani rude,, taimaka masa tayi ya tashi.
dariya ya sa mata, had'i da fad'in na miki wayau!
dariyar itama tayi, had'i da daukar tray d'in saida tayi gaba kad'an ta juya ta dube shi.
Mutum dai ya dinga jin maganar matar sa tom.
tana fad'in haka ta shige abun ta.
dariya Zaid" yayi had'i da fad'in ohhh I can't believe it wai wannan yarinya ta ce Allah mai iko!
**********
Shago akawo kayan aiki a fara, yata na asibiti gaba d'aya hankali na yana kanta.
Ai hikenan hajjaju" wizgiji miko wannan kwalbar ayi mata Eh yane!
Ya fad'a cikin muryar su ta yan shaye2.
d'auko kwalbar akayi,, amsa Rahamu tayi tana ko'karin doka ta da kasa.
da sauri shago yace a aa Dakata hajjaju... Ai bawai haka kawai zaki yi mata wannan rotsen ba.
Sai kin yi mata fitsari tukun,,
Sai a d'auko wancan Mutumin a cire hannun sa mai cindon,,, kin gane ai to jinin sai a tarara shi a kwalbar. Sai ki kalla kudu ki qunduma ashar da sunan duk wanda kike bu'katar mallaka.
Eee yawwa sai ki saki kwalbar ta fashe.
Aiki ya kammalah!
Janyo Mutumin nan sukayi suka cire masa hannun yana ji yana gani.
daidai isowar su mus"ab,, dake tun a baki baki suka ajiye motar su. ba wanda ya lura da zuwan su a cikin su shago.
A sad'ad'e suke kallon duk abunda ke faruwa lokacin da Rahamu ta d'auko kwalbar bayan an gama zuba jinin ciki.
Dad a lokacin ya gane ta kad'an ya rage bai fad'i ba. Bakin sa sai rawa yake yana nuna ta da d'an ya tsan sa duk da har lokacin bai gama fahimtar maike faruwa ba.
fitsarin ta duka a gabn su shago ba kunya babu tsoron Allah tayi fitsarin a cikin kwalbar.
Mikewa tayi ta yarda d'an kwalinta kamar yadda sharadin boka yake, ta dubi kudu, tasoma qunduma ashar,, sunaye ta soma zayyano wa.
Tahir..... Tahirrr..... Lubabatu..... Lubabatu...
Zaid..zai.....d'au! d'au!
Aka d'auke ta Mari har sau biyu,,
Saurin sauke kwalbar hannun ta tayi tana duban waye wannan da wannan danyen aikin.
Ido cikin ido sukayi da mus"ab.
Wanda ya kasa cooling temper d'in sa har saida ya gansa a gaban ta, jikin sa har tsuma yake.
Ke wace irin mushurikiya ce?
Duk abunda kikayi a baya bai isheki ba har sai kin dad'a da wani yanzun?
Wata irin fad'uwa gaban ta yayi Lallai yaron nan waton tana masa kallon biri yana mata kallon ayaba?
Bata gama sauke tunanin ta ba Dad ya shiga zuba mata nasa mahaukatan marukan, har saida ta gaji ta fad'i kasa kamar zararriya sai tusoshi da ihu ta keyi.
Su shago ne suka zagaye su.
Ganin hakan yasa Rahamu tasamu kwanciyar hankalin mi'kewa.
Wata irin dariya ta saki had'i da fad'in,, nama har gida wannan shine kun hutar dani.
Ashe ke shaidaniya ce? Rahamu kin cutar dani.
Cewar Dad da Idanuwan sa sukayi mugun ja na tashin hankali.
Wata dariyar Rahamu ta saki.
Had'i da fad'in,, iya wannan kawai ka sani amma kasan wani abu?
Ni d'innan da kake gani na aure ka ba a son ranka ba ta hanyar asiri, na rabaka da d'an ka ta hanyar asiri na saka wa Yarka cuta ta hanyar asiri..... Hhhhhhh ba iya shikenan ba, ni d'in nan dai nayi sanadin da wannan shegen yaron yayi wa Yarka UMAIMAH fyade!
Alhaji abubuwan da yawa amma inason ne kasan kad'an daga ciki kafun kabar duniya.
Fad'uwa Dad yayi ya suma tsabar tashin hankali, da sauri mus"ab yayi kansa yana fad'in Dad dad...
A zuciye ya dago ya sake sakarwa Rahamu mugun bugu a baki wata qara ta saki had'i da tazge bimdigar hannun d'aya daga cikin yaran shago.
Ta saita mus"ab d'in.
Da gudu salma ta shiga gaban sa tana sakin harsashin sai kan cikin yar ta.
Nayi ko'kari fa 😂
Son so 😘😍😘
Xinnee smart 😘👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro