Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

36

Wannan shafin naku ne admins na groups d'in da nake ciki na novel, musamman, Zeebucolections😘Mrs Idris(Alhusna) ♥️murja Na"ikke 🙏💞fannah's💕mum Khady❣️maman Ansar😘feary😍da sauran wanda ban fad'i sunan su ba, Allah yabar zumunci 🙏😍🤗

tari Zaid" ya soma wanda ya fargar da Abba da gyangyadin da ya kama shi bayan ya sallame Sallahr asuba. da sauri ya nufa gun Zaid d'in yana d'an yana shafa kansa, a hankali tarin ya lafa, bude idanuwan sa yayi a hankali.

kallon sa Abba yake yana jin soyyyar d'an nasa na sake ratsa shi.

Sannu mus"ab" sannu kaji.

murmushi yayi wa abban ganin yadda duk ya firgita ya rude, Shima abban murmushi yayi yana maida hawayen dake son sauko mishi.

Alhmdllh" na godewa Allah da yasa kana da rabon shan ruwa, murmushi Zaid yayin yace Abba" baka son na mutu ne? duban sa abban yayi na yan seconds kafun yace mutuwa dole ce mus"ab saida bana fatan kabar duniyar a yanzun da nake tsananin bu'katar ka.

Abba yana gama fad'in haka ya nufi kofa  had'i da fad'in bari inkira doctor, saida yakai kofar ya juya yana cewa saura Kaci wani abun kafun indawo silly boy.

d'an murmushi yayi, abban ya fice.

Yana ficewa ya shiga share hawayen dake sauko masa, yana jin wani iri a ransa waton har haka ya ke son d'an sa amma ni ko ohhho, to kai wai ka yarda wannan d'in mahaifin ka ne? cewar zuciyar sa.

Wani sashen na zuciyar sa ne ya shiga fad'a masa wannan kamannin d kake da d'an sa Kai harma dashi kansa ai ya isa ya tabbatar da zancen mus"ab na cewa ku yan uwa ne wanda kuka fito ciki d'aya.

Lumshe idanuwan sa yayi wasu hawayen suka sake zubo masa a hankali.

Yayinda zuciyar sa ke ci gaba da sake2.

Ba jimawa saiga Abba da doctor sun shigo, sannu likitan yayi masa kafun ya soma gwaje2n sa.

Murmushi yayi bayan ya gama yace Alhmdllh jiki yayi kyau haka muke so Allah ykara lfy. amin y Allah Abba ya amsa, yanzun Alhaji idan ya karya sai a bashi wannan magungunar.

*******
Mus"ab gida ya koma. yana zuwa side d'in sa ya nufa, wanka yayi ya shirya cikin kanan kaya riga da wando,

Tea yasa aka kawo masa ya sha. yana gama wa ya fito zuwa apartments d'in Rahamu" cikin sanda ya shiga parlourn ta jin motsi a kitchen yasa ya gane larba ce biba ce ko laraba, dan haka a hankali ya shige bedroom d'in ta.

Cameras d'insa ya cire, saboda zuwa yanzun sunyi aikin su.

Ficewa yayi daga part d'in ta ba tare da kowa ya ganshi ba.

d'akin sa ya koma yana sake2 ta yadda zai bullo wa komai cikin ruwan sanyi ba tare da rahamun ta gano takun sa ba.

system d'in sa ya d'auka,, ya shiga Facebook searching Khalil ya shiga yi wanda Zaid ne ya fad'a masa account d'in sa.

Cikin sa'a ya samu,, friend request ya tura masa.

Ya Jima a Facebook d'in dan jiran ko zaiyi accepting?

Saidai shiru har lokacin sallar azhur yayi bai ji daga gare shi ba, dan haka ya tashi ya d'aura alwala dan gabatar da sallah.

*******
tafiya mai nisa Rahamu" tayi kafun ta isa inda sukayi da sukayi zasu had'u da shago.

Ba tayi minti 10 da tsayuwa a gurin ba Sai ga su sun iso.

basu tsaya magana ba kawai bayan mota ta bud'e musu suka saka mata salmar ita kuma ta basu wata jaka wacce take ta kud'i ce.

Jan motar ta tayi.

bata tsaya a ko'ina ba Sai gida, tana isa ta kira su idi, had'i da nuna musu salmar.

Ku shigo mun da ita ciki.

Jikin su na rawa suka kin kime ta zuwa parlourn,, har cikin d'akin salmar suka shiga suka kwantar da ita kan gadon ta, kafun suka fice salin Alin babu damar tambayar ina aka ganta tunda sun San an sace ta.

Saidai babu halin tambaya, ko aradu na tsoron rani😂.  haka kowa ya barwa cikin sa Tsegumin da ke cizon sa,, saidai idan ansamu sawa a rakube ayi a tsakani.

Rahamu" wayar ta ta ciro ta soma kiran family doctor d'in su. yana d'auka ta sanar dashi yazo gidan yarta bata da lafiya.

ba'a Jima ba yazo kasancewar asibitin da yake aiki babu nisa.

Yana zuwa ya soma yiwa salmar gwaje2 wacce a kwance take kawai kamar matacciya,, saidai idon ta dake bude had'i da kyaftawa ne zasu tabbatar maka da tana Raye.

Yana gama wa ya dubi Rahamu had'i da fad'in hajiya a gaskiya idan son samu ne kawai a kaita asibiti domin tana bu'katar gwaji sosai haka kuma tana bu'katar karin ruwa da jini.

Jinjina kanta tayi had'i da fad'in yanzun doctor babu yadda za'ayi a duba ta anan dole sai anje hospital d'in?

a gaskiya hajiya idan dai ana son gano abunda yake damun ta ta yadda za'ayi treating da kyau to gwara kawai a kaita asibitin inaga shi zai fi.

Shikenan yanzun ma sai muje. OK tom.

Su idi ta koma kira, ko kishin yar ta batayi. tunda ga su laraba nan tsab zasu iya daukar ta tunda dama salmar ba wani jiki ne da ita ba. haka kuma gashi duk ta dad'a ramewa ta lalace tamkar mai wata cuta.

Haka aka saka salma mota zuwa asibiti.

*******
Yanzun duk irin maganar dana ke miki yarinyar nan Sam bakya ji?

Allah yasani nidai nayi iya bakin ko'kari na dan ganin na kula dake duk da kasancewar ke kad'ai ce wacce ke gareni a duniya amma kin kasa hakura. Cire mus"ab a ranki.

ga huzaifa nan sosai yake kaunar ki. Ki kwantar da hankalin ki ki amince masa haka kuma kiyi addu'a... daga nan kuma ta koma nasiha da lallashi.

SIDEEFA"kam banda kuka babu abunda take.

Ita dai tana matu'kar kaunar mus"ab. har a ranta, saboda irin soyayar sa mai tsaya wa Arai ce ko ba komai mus"ab abun so ne a gun duk wata macen da tasan me kalmar namiji take nufi. ita dai tana son mus"ab.

ganin ba shiru zata yi bane yasamu ammi Ficewa daga d'akin.

Ammi na Ficewa SIDEEFA"ta fad'a kan katifar ta had'i da sakin wani irin siririn kuka. Mai taba zuciya. Soyayyar ta da mus"ab tamkar rai da rai ne. hakika tana son samun ta goma shin so tana son cin alfanun so, ita dai tana son more wa romon so. idan ma zata rabu da mus"ab ta ina zata fara? bata tunanin rayuwar ta zata moru idan babu mus"ab shi d'in jinin jikin ta ne. Son sa a ranta daban ne!

Sosai take rusa kuka tamkar ranta zai fice.

*******
Mami tana gama sallar asuba" ta fice gurin mai gadi,, tana tambayar sa ko ya ga Ficewar Abba"?

Amsa ya bata da Eh yaga Ficewar sa dan shine ma ya bud'e masa kofa, ya Kara da fad'in.

Kuma naga yadda ya fice ma Sam babu natsuwa a tare da shi gaskiya.

Numfashi ta sauke cike damuwa, shikenan ta fad'a had'i da komawa cikin gidan jikin ta sai rawa yake.

zagayar daki ta shiga yi cikin halin rashin sanin mafita.

daga karshe ma zama tayi akan gadon ta, had'i da fashewa da kuka.
Sosai take kukan zuciyar ta na wani irin buga wa. dafa ta akayi wanda a tunanin ta ko baby ce.

Saidai sabanin hakan tana d'agowa taga Abba"!

Wani irin tashi tayi da sauri ta shiga shasha fa shi tana fad'in Abba ina kaje da muryar ta da kuka ya gama dusashe ta. Zaunar da ita yayi kafun Shima ya zauna.

bayani yayi mata akan jikin mus"ab ne ya tashi aka kirashi amma da sau'ki, saboda bai shirya fad'a mata Yar uwar sa tana son kashe gudan jinin sa ba.

Numfashi ta sauke,, amma yanzun da sau'ki ko Abba?
Alhmdllh ya samu sau'ki Masha'Allah.

Amma wlh ka daga mun hankali, ai da ko da wayar ka sai ka tafi. to ayi ha'kuri madam"

Dariya ta tuntsure da ita saboda tuno baya da tayi idan yace mata madam ta dinga maseefa kenan, tana fad'in madam sai kace wata kafura.

Shima dariyar yayi dan Shima ya tuno lokacin.

Shiru yayi daga baya yace tom tunda hankali ya dawo a taimaka mun in d'an kwanta.

dariya tayi had'i da ficewa daga d'akin.

Kai tsaye kitchen ta nufa.

*******
Kayan bacci ne a jikin ta tun lokacin da ta tashi ta kasa Sauka daga gadon bare taje kitchen dan taimaka wa Mami kamar ko yau she.

hakan nan take jin sa a ranta.

Sake mirginawa tayi a Karo na ba a dadi.
Sai tin zuciyar ta ta dafe tana jin wani irin yanayi mai wuyar misaltawa yana shigar ta a game dashi.

Mai yasa nake jin hakan a kansa?

ta tambayi kanta.

Son sa kike!

Zuciyar ta taba ta amsa.

Yaushe nasan so bare in soma yin sa?

Ai lubna (sit mate d'in ta) tasha fad'in irin yadda take jin uncle Ahmad a ranta.
Kuma kema kina jin kwatankwacin abunda lubna take fad'a koma fin yadda take fad'a.

Rolling eyes d'in ta tayi tana sakin murmushi.

Zuciyar ta ce ta jefo mata tambaya.

Kenan kin yafe masa?

Murmushi" tayi kafun ta fad'a a Zahiri.... Wa yake fushi da gwarzon maza? ni dama ban ri'ke shi ba.

lumshe idanuwan ta tayi tana tuno da kyakyawan murmushin sa mai tafiya da zuciya. sake lumshe idanun tayi. Idanuwan sa masu saurin karya lagon mutum ta hango a nata idon da sauri ta bud'e idanun, kamar wacce wani ya ganta.

dariya ta saki had'i da kan'kame pillow a kirjin ta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da sauri,, wanda ke nuni da so yayi wa zuciyar mugun Kamu, wanda za'a iya kiran sa da kamun kazar kuku.

Mami ce a tsaye tana kallon ta dan har ta shigo d'akin baby bata sani ba.

Ummi!

Mami ta kira sunan ta,, a d'an firgice ta bud'e idon ta, ganin Mami ne yasa ta sauke ajiyar zuciya.

a hankali tace Mami yanzun fa nake son fitowa.

Murmushi Mami tayi... ai naji ki shiru nace bari inzo in duba ko lafiya?

yanzun nake son fitowa Mami na.

Masha'Allah tunda kina lafiya ai.

daga haka Mami ta fice daga d'akin.

Ganin ta fita ne yasa baby sauke ajiyar zuciya itama ta mike.

*********
Anya kuwa kin zuba yadda ya kama ta?
Haba dan Allah zan miki qarya ne? Wlh na na zuba har dad'in abunda kika ce.

Kedai ki kwantar da hnkalin ki na San saidai inji labarin mutuwa. Kuma ma ai tun d'azu nake kiran wayar Yaya bata tafiya kin sani ko yana can hankali tashe Rabin rai ana barin duniya?

Hhhhhhh"suka saki uwar dariya suna tabawa.

*********
Mom... My......!

Wayooo mommy.... Mutuwa zanyi Wayoooo.

Wannan shine abunda salma take ta fad'a tunda ta farka.

mtssssss hajiya Rahamu" ta saki tsaki.

Wai dan ubanki ba zaki yimun shiru ba? Wani shegen ne ya kaiki gun bangis d'in? Idan ba tsiyar iskancin ki ba.

Wlh ni garki dame ni. to

Mommy..... dan Allah kiyi ha'kuri wlh duk ke ce kika jamun wannan matsalar saboda Sam baki bani tarbiyya ta gari ba mommy.

Ohhhh dan ubanki ai da ban baki tarbiyyar kwarai ba ai kuma bance kibi na miji ba ko?

Shegiya dangin masifa da tsiya.

Haka na auri ubanki ban ganewa wa komai ba,, har na rabu dashi babu wani abun albarka, yanzun gaki kina ko'karin tuno mun da bara ma tsiya cin ubanki har ya bar duniya baisan romon ta ba.

Nima haka kike son inbar duniya ban lasa rabona ba? Ina! Bazai yu ba. dole ki mike kiji sau'ki mu d'ora daga inda muka tsaya. duk wa nake wa gatan ba ke ba?

Katse ta salma tayi da fad'in.

a....aa mommy ni kam na tuba wlh ki barni ma kawai da maseefa r ciwon da nake ji a jikina dan Allah.

Wlh kiyi mun shiru kafun in sassaba miki.

Mommy nidai ko mai zaki ce ki ce amma wlh abunda kike Sam ba mai kyau bane kuma bazai taba fishe ki ba.dan Allah mommy ki tuba ki roki yafiyar Dad ummi da kuma Zaid....... tauuuu! ta d'auke ta da mahaukacin Mari.

Ni kike fad'awa in nemi yafiyar makiya na? Wlh gwara duk abunda zai faru ya faru da dai in nemi gafarar wadannan mutanen.

Kuma dole in....... Knocking kofar da akayi ne yasa tayi shiru had'i da duban kofar.

Wata nurse ce ta shigo.

Sannu da jiki tayi wa salma.

Kafun tace hajiya doctor ne yake son ganin ki a office d'in sa.

Saboda sakamakon gwaje2n sun fito.

a turbune Rahamu ta amsa.

Bayan nurse d'in ta fice ne ta dubi salma da har lokacin tana dafe da marar ta.

Bari inje in dawo zaki gane kuran ki.

Ficewa tayi daga d'akin tin'kis2.

Bata Jima da fita ba aka sake turo kofar.

Zaid! Salma ta fad'a ganin wanda ya shigo d'akin.

a dake mus"ab ya isa kusa da gadon.

Kallon ta yake. Yayinda itama take kallon sa.

daga baya kuma ta saka masa uban kuka,, tana fad'in dan Allah Zaid ka yafe mun na rokeka.

Wlh nayi madamar duk abunda nayi maka.

Lissafa wa ta shiga yi tun sanda ta soma son shi da maganin da tasa masa a Lemo.

Komai saida ta fad'a, masa har zuwa gun boka da sukayi da kwaryar da aka baiwa mommy ta boye.

Tana gama wa ta shiga rokon sa ya yafe mata.

bai ce mata komai ba saida tayi shiru ta shiga she's hear kukan ta.

Ina kwaryar take?

Ya tambaye ta.

Cike da kuka tace wlh bansan a inda mommy ta ajiye ba.

Shiru yayi kafun yace inason kiyi mun wani abu guda d'aya.

Meye shi? Wlh ko mai kakeso zan maka ka fad'amun.

Inason garki sanar da mommyn ki na zo bare kuma abunda muka tattauna.

na biyu ina son ki sa mata ido duk abunda ake ciki idan na sake zuwa ki sanar dani.

Kinji mai nace ai.

Eh naji insha'Allah zan sanar da kai.

Kuyi hakuri bana jin dad'i ne wlh naso a page d'in yau muyi semifinal😂Amma hakan bai samu ba.


Xinnee smart 😘

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro