Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

35

Wannan shafin na kune mutane na whattpad, ina jin dad'in yadda kuke bibiyar wannan labarin, Kuci gaba da bani had'in kai gun voting da kuma commenting.love u all. 😍😘😍

Da sassafe mus"ab yaji ana knocking kofar sa, sosai yake ma making waye wannan amma sai ya share ai a gidan ansan baya magana saidai kuma sun San yana ji, a gidan Rahamu ce kawai ya nunke a baibai.

bud'e kofar yayi" ganin Laure yasa mamakin sa ya kasa boyuwa har saida yace Laure lafiya kuwa? rabawa tayi ta gefen sa ta shige d'akin.

bin bayan ta mus"ab yayi yana mamakin mai ya kawo ta da sassafe haka.
yana shigowa ta maida kofar ta rufe.

Jikin ta sai rawa yake, d'an muskutawa tayi kad'an had'i da yin d'an waige2 kamar wani zai ganta. kafun ta ce Zaidu" dama tun jiya naso zuwa in fad'a maka to bansamu damar hakan ba shi yasa nace bari inzo da sassafe in sanar dakai,

Gyada kansa yayi alamun ina jinki.

ci gaba da magana tayi muryar ta kasa kasa.

Dama jiya da daddare ne bayan na gama aikina na koma sashen mu, Hajiya ta kirani, bayan naje shine tace inyi mata farfesun kaza.

Bayan na gama ina zubawa a bowl d'in da zan kai mata sai ta shigo kitchen d'in.

dube dube tayi a kitchen d'in kafun ta bani wayar ta wai in saka mata charge a parlour.

Karba nayi na tafi,, tunda na karba wayar hankali na bai kwanta ba dan idan dai tayi irin haka to barbade 2n ta take son yi.

Wannan yasa nayi hanzarin zuwa da sauri na saka charge van tsaya dubawa ko yayi ba kawai na dawo na labe ina kallon ta ta debi farfesun da na juye mata ta rabashi biyu.

ta zuba rabin are wani plate, daga bisani ta zuba garin wani magani a cikin paper soup  d'in.

ganin ta gama barbaden na koma gun charge ina dubawa ko wayar ta sawu a zuciya ta ina tunanin waye zata baiwa wannan mai maganin?sai ga ta tafito daga kitchen d'in hannun ta ri'ke da duka plate d'in d'in. Kallona tayi tana murmushi tace Laure sarkin aiki, nima murmushin nayi saidai yafi kama da yake. Ajiye plates d'in tayi had'i da cewa wannan farfesun ai yamun yawa Laure, ina zan iya cinye wa.

dan haka kizo ki d'auka wannan ki cinye, wani yawu Laure ta had'i ya makutt, dan Allah yasani Laure akwai son nama saidai wannan shine kabewar kan kabari.

Zancen nan da ake wai a nawa mutum asiri da abunda yafi so to shine tabbas da Laure bata gani ba tsab zata cinye ta lashe ta tande. Amma kiri2 yau nama ko burgeta bayayi.

Wani gumi ne ya sauko mata mai cike da fargaba, murmushi hajiya tayi had'i da fad'in Laure Laure zauna ki cinye abunki idan kin gama ki d'an matsan kafa ta dan yau fitar nan da nayi duk tsami take min.

Matsawa Laure tayi gurin farfesun, sai zaran ido take itakam taga ta kanta kilan ma kashe ta hajiya zata yi.har ta tsoma hannun ta ciki ta daddage ta zuba uban ihu hajiya tace lafiya lafiya??

Cinna... Ka.... Ccinnaka!

Shine abunda Laure ke fad'a tana zazzage zani.

Mtssss hajiya tayi tsaki, daga bisani ta tamke fuska, Laure wai sai yaushe zaki daina gidadancin nan ne.?
Kinga kije kiyi abunda nace miki ki gama kiyimun tausar kafa ta bacci nake.... bata gama rufe bakin ta ba wayar ta ta soma ringing.

d'auka tayi ganin mai kiran ne yasa tayi saurin shigewa bedroom tana amsawa muryar ta kasa kasa.

Laure na ganin haka tayi hamdala.

daukar plates d'in tayi ta shige kitchen jiki na rawa tayi musayar ko wanne.

Ta mayar da nata a plate d'in hajiya na hajiya ta juyewa kanta.

tana gama wa takoma parlour.

Ta ajiye ko wanne a inda yake.

Cikin sand'a tabi bayan hajiya,, makala kinnin ta tayi dan jin mai hajiyar take fad'a aikuwa tayi nasarar jin wasu daga cikin mganganun ta. ji nayi tana ce wa.... Eh duk yadda za'ayi kuyi ko'karin dawo mun da salma ku fataffaki su bangis d'in dan uwar sa karamun d'an iska dama saka masa ido nayi naga gudun ruwan su daga shi har Salman yar banza abubuwa sun lalace mun anan tanason ta karasa mun su.

jin alamun tana shirin yin sallama da wanda take wayar ne yasa nayi saurin komawa inda ta barni.

Soma cin naman nayi tamkar babu abunda ya faru, tana fitowa taga ina ci sai murmushi, tayi had'i da fad'in yawwa Laure aci anata cin naman kenan?

gyada mata Kai na kawai nayi, ina ci gaba da cin naman zuwa lokacin na kusan cinye wa.

zama tayi ta d'auka nata ta soma ci, saida na gama cin naman na shiga kitchen dan wanke hannu na d parantin. sosai nake cikin fargaba dan nidai duk a tunani na maganin mutuwa ne.
Saidai sabanin in same ta tana kakarin mutuwa Koda na fito samun ta nayi ta baje a inda take cin naman ko wanke hannu ba tyi ba.

Sosai abun yabani mamaki baccin ta ta keyi hankali kwance, matsawa nayi kusa da ita ganin wani d'an kulli a gefen zanin ta(ha'ba).

kaga abun ma, mikawa mus"ab maganin tayi wanda yake tablet ne saidai akwai wanda aka da daka a ciki wanda shi d'in ne aka da daka, duba maganin yayi yaga na mura ne wanda yake da karfi sosai.

Gyada Kai yayi yace ya akayi kika fito to?

Bayan na d'auka maganin ne na fito daga parlourn,, ba tare da kowa ya ganni ba,

Naso zuwa gurin ka saidai kuma bansamu kwanciyar hankalin hakan ba a jiya, shine yau na doka uban sammako.
Ni yanzun fargaba ta d'aya kar hajiya ta farka ta gane abunda nayi mata. ta karasa maganar tana fyace hanci da gefen zanin ta.


*****
Numfashi mus"ab" ya sauke a ransa yana jinjina sharri irin na Rahamu" to ko mai Za tayi wa Lauren?

duban Laure yayi kafun yace baaba Laure ya zama dole in nema miki gun buya saboda bansani ba ko hajiya ta gano wani abu ne. Saboda haka kina bu'katar tsaro na d'an wani lokaci.

dan haka ki hada kayan ki yanzun mu had'u a karshen layi.

Laure jiki na rawa ta amsa da to.

*******
Gudu Alhaji farouq" yake zabgawa, wanda bai taba kwatanta irin sa ba (hausa suka ce kowa yace duhu baiji zawo ba)

bai tsaya ko ina ba Sai harabar asibitin. Ko kashe motar bai tsaya ba ya fice, sauri2 gudu2 ya isa emergency, yana zuwa daidai wani ma'aikacin yana fitowa daga d'akin.

da sauri ya tare Abba da jikin sa sai rawa yake, yana kallon sa ya gane shine mahaifin mai Jinyar. Alhaji dan Allah ka kwantar da hankalin ka INSHA'ALLAH zai samu lafiya muna bakin ko'karin mu yanzun haka, kwantar masa da hankali ya shiga yi,

Zaid sosai ya galabaita domin kuwa gubar da yaci tana da matu'kar karfi wanda zata iya masa illar da zai rasa ransa a lokaci d'aya, saidai Allah y taimaka wanda Jamila ta siya yayi expired dan haka sosai karfun nasa ya daku she.

******
Mami tana farka wa taga babu Abba a kan gado, hakan yasa tayi tunanin ko yana ban d'aki ne, saidai shiru tsawon mintina goma babu shi babu alamun shi.

A hankali ta Sauka daga kan gadon tana gyara Zaman hular kanta.

jikin band'akin ta tsaya shiru babu alamun akwai mutum dan haka, ta d'an tura kofar saidai wayam babu kowa, gaban ta ne ya fad'i, amma sai ta fito parlour wata kila ko yana nan.

Nan d'in ma shiru babu shi, wayar ta ta d'auko ta shiga kiran wayar sa saidai me? Ringing d'in ta taji a bedroom d'in sa.

Sosai hankalin ta ya tashi, tana ta saka da warwa ra to ina ya nufa cikin daren?

safa da marwa ta shiga yi gashi dare yayi a lokacin, bare ta fita. ganin tunane2 bazai fishe ta bane yasa ta d'aura alwa'la ta soma gabatar da nafiloli.

*******
Koda aka fito da Zaid" daga emergency, bai farfado ba yana baccin wahala.

Doctor ne ya shiga yiwa Abba bayanin cewa guba yaci a cikin abinci, wanda ba dan yana da sauran kwana ba da kuma rashin karfun ta ba da saidai wani bashi ba.

Duk da Abba ya san abunda ya faru hakan bai Hana shi nuna mamakin sa ba da al'ajabin ta Yaya mus"ab yaci guban?

Bayan ya fito daga office d'in doctor d'in d'akin Zaid d'in ya nufa, shafa kansa yayi hawaye na Sauka masa wanda baisan lokacin da suka zubo ba Sai jin digar su da danshin su yayi. da sauri yasaka hannun sa ya goge.

Zama yayi a gefen gadon yana mai kallon sa cikin soyyar da da mahaifi.

Bai runtsa ba har garin Allah y waye.

**********
ba tare da kowa ya gansu ba suka bar gidan, kamar yadda ya fad'a a bakin layin suka had'u.

Abun hawa ya samar musu da kyar.

tunani ya shiga yi dole yana bu'katar ya baiwa Laure Kariya haka kuma da mafaka.

to amma.... Ina zai Kai ta. yana wannan tunanin yaji tana cewa...

Nayi tunanin ko in tafi kauye gurin yan uwa na?

Inane kauyen?

Ya tambaya.

Can yake kano cikin kauyen Rano.

Kina ganin babu matsala?

Babu insha'Allah kuma ma ai hajiya bata San Yar inace ba ni.

to shikenan yanzun bari muje tasha kawai.

Mai taxi yayi wa magana yakai su gun shiga mota.

Saida ya tabbatar yasa ta mota ya bata kud'i masu d'an kauri had'i da rubuta mata number d'in sa. Ya kuma Kara tambayar ta cikakken address d'in ta. ta fad'a masa.

Yana tsaye a gurin har saida motar su ta tashi kafun ya koma gida.

******
Rahamu" bata farka ba Sai guraren 9 da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi.

da kyar ta fad'a toilet tayi wanka, sai a lokacin ta tuno da abunda ya faru wata irin ashar ta lailayo ta maka. kafun ta shirya cikin doguwar riga bubu. ta saka wata hula da sauri ta kira layin masu aiki.

Bina ce ta d'auka cikin maseefa ta soma magana.

Ina Laure?

Laure ta zo ta same ni yanzu yanzun!

Cikin ladabi biba ta shiga cewa hajiya tun jiya da Laure tazo kiran da kikai mata ai bata dawo ba.

What??
katse kiran tayi tana sake maimaita maganar tun jiya bata dawo ba?

Kardai matar nan guduwa tayi.

da sauri ta d'ora hannun ta akai tana fad'in da ta kashe ni.
Na bonu wai mai yasa abubuwa suke jagule mun ne?

tana wannan nazarin wayar ta tayi Kara.

Sai a lokacin ta lura da miss calls d'in dake gare ta.

Ganin mai kira ne yasa jiki na rawa ta amsa had'i da fad'in Yaya an dace?

Yar dariya tayi had'i da fad'in nagode sosai, a kashe kowa ma ba bangis ba karamun d'an iska. yawwa babu damuwa garka ji komai yanzun nan kuwa.

Cikin farinciki ta ja mayafin ta ta fice daga d'akin. lokacin da ta isa jikin mota Shima Dad lokacin zai fita.

Ko duban inda yake batayi ba.

Kallon ta yayi kafun ya kira sunan ta, tana ko'karin shiga mota ta daka ta had'i da duban sa.

Matsawa yayi kusa da ita, fuskar sa babu annuri yace... Ina zaki Je?

anguwa ta bashi amsa itama tana wani bata fuska.

Yanzun saboda Allah Rahamu ina matsayin mijin ki a cikin gidannan ina nan ba wai bana nan ba? amma ace zaki fita bazaki iya ki nema izini daga guri na ba? Wace irin Rayuwa ce wannan?

Kallon says take shekeke,, yo ita dama ai ba saba wa tayi da neman izinin fita ba bare ya dinga fada mata wannan zancen Koda yake ga dukkan alamu Alhaji ya fara dawowa, ya zama dole na maida ka, ta fad'a a zuciyar ta.

A Zahiri kuwa yake tayi had'i da fad'in ayyah Alhaji uzuri ne ya taso ba jima wa zanyi ba yanzun zan dawo.

Girgiza kansa kawai yayi ya nufi tasa motar a ransa yana jin haushin mai ma yasa ya auri wannan matar ne?

Jin kansa ya soma masana ciwo ne yasa ya share zancen, ya fice daga gidan.

Yana fita Rahamu ma tabi bayan sa.

Zuciyar ta cike da damuwar yadda abubuwa ke ta warware mata.

Amma tayi alwashin gyara komai yadda zata murza sitiyarin Rayuwa yadda take so!

Ko burin Rahamu zai cika?




Xinnee smart

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro