31
Aisha Abubakar, na manta daga wani group d'inne gaskiya amma ai kinsan kanki, anyway 😁kinyi ko'kari but still dai baki canka duka ba 🤣 so here is ur page 😍sauran da kukayi trying am great full😘🤗
Sosai yake kallon abun zuciyar sa na wani irin bugu, sake zazzage jakar yayi, wani fad'uwar gaba ne yasake ziyar tar sa.
A hankali ya sulale kasa yana mamaki Kodai idonsa ne?
Kayan Zaid"ne yagani wanda aka ajiye sa gidan marayu a lokacin yana jin jiri kayan da yake sanye da su ne, wanda mus"ab d'in yasan yana jin jiri yana da irin kayan saboda pictures d'in sa na jarin ta da yagani a lokacin tabbas yana da irin kayan shi ma.
Mai hakan yake nufi, diary d'in da yagani ne yasa yaja tunga gefe ya soma karantawa jikin sa na tsuma.
11/2/18.
Nasha yiwa kaina tambaya ni Zaid" Kodai ni d'in ba halastaccen d'a bane? Wanda kunyar abunda iyaye na suka aikata yasa suka jefar dani......
tiryan tiryan ya soma bin diary d'in, wani gurin yayi gumi da ajiyar zuciya wani gurin yayi hawaye, har yakawo haduwar UMAIMAH da Zaid d'in haka ya dinga bin labarin daki daki Sala Sala, sanka sanka.
....bai tashi daga inda yake ba saida ya ya karance sa tsab. wani irin gumi ne ya shiga wanke masa jiki, da uban tausayin Zaid d'in da UMAIMAH"wacce ko tantama ba yayi itace ummi UMMIN gidan su yar Abba da Mami.
to waye Zaid"?
d'an uwanka ne wanda babu tantama ciki d'aya kuka fito wata kila ku yan biyu ne wannan ne yasa aka kasa gane ba kai bane Zaid. to amma ai iyaye na basu taba fad'a mun cewa inada d'an uwa ba bare inji ta Yaya suka rasa d'an su.
Amma inason haduwa da Zaid" ya zama dole in had'u da Zaid" but how?
Zuciyar sa ta tambaye shi, numfashi ya sauke, dole ina bu'katar inje kano dan sanin halin da iyaye na suke ciki saidai kuma babu dama mai zance wa su dad idan zan tafi kano bayan bani da kowa Bana magana.
uppppss"i have to think about it.
********
a hankali Zaid yake samun lafiya, wanda sosai hakan yake faranta ran iyayen sa, ga wata irin natsuwa da suke gani tattare da d'an nasu wanda hakan yake sake saka su farinciki.
a bangaren UMAIMAH" ma sosai abun yake bata mamaki. ganin wani irin kulawa da yake bata, haka kuma ko batazo asibtin ba shi zai neme ta dole Mami ta turo ta, sosai take mamakin sauya war sa lokaci d'aya.
Zaid"kam lafiya kawai yake jira ya samu ya bayyanar musu da gskiyar shi ba d'an su bane, dan sosai yake mamakin da suka kasa gane cewa shifa ba d'an su bane, har mamakin wannan kamar yakeyi yana matu'kar mamakin wannan wace irin kama yake da d'an su har haka?
Shikam jira yake ya warke ya fad'a musu gaskiya, daga bisani ya bayyanar da iyayen UMAIMAH" a gurin su, su karbi yar su, ko ba komai yayi farinciki sosai da ganin irin hannun da UMAIMAH" take. Kuma yana ji a jikin sa dole d'an su ya sake ta ya aure a barshi dan UMAIMAH tasa ce shi shi kad'ai!
Yau ma yana kwance kan gadon sa na asibiti kasancewar har yanzun ba'a sallame shi ba.
Baby" tayi sallama had'i da shigowa, matsawa tayi ta ajiye basket d'in dake hannun ta.
Kusa da shi ta ja kujera ta zauna, sai binta da ido yake,
Ina yini?
Yaji sassanyar muryar ta tana gaishe shi.
Murmushi ya sakar mata had'i da lumshe kyawawan idanun sa, daga bisani yace..
Ykk?
A kasalance ta amsa da,
"lafiya
Ko zaka ci abinci yanzun?
Idan Kinga ya kamata na ci ai sai inci,
d'an rausayar da kanta tayi kafun tace... nidai bansani ba.
murmushin sa mai sanyi ya sauke,
A ransa yana jaddada godiyar sa ga ubangiji wai wannan UMAIMAHr sa ce wacce bata cika lafiya ba yau gata a gaban sa sumul babu gidil gidil. Ohhh ikon Allah ko ya hakan ta faru?
Muryar ta ce ta katse shi.
ga abincin ta fad'a tana mai mika masa,
duban ta yayi kafun ya duba plate d'in hannun ta, mika hannu yayi zai karba wanda Hanna yen su suka goga juna, lokaci d'aya dukan su suka sauke boyayyen numfashi.
abincin ya soma ci yana duban ta fuskar sa cike da annuri.
******
Hajiya azumi a gaskiya wankin hula na shirin Kai mu dare.
bangane ba?
hummmm! Kina dai gani yaron nan mus"ab, da aka harbe shi madadin ya mutu ko ya nakkasa, a a sai ma ko'karin tashi da yakeyi.
Hmmmm! Hajiya azumi ta sauke numfashi tace hajiya Jamila"inada nawa shirin, garki damu wannan karon da wuri zaiyi aiki.
Kin tabbata,? Kwarai kuwa ko SHAKKA banayi idan dai muka Gina wannan ramin da wahala mus"ab da iyayen sa su kauce masa ya zama dole ma su fad'a.
Shikenan Kawa ta Allah yabamu sa'a.
bakida matsala!
******
to Zaid"koda dai baka magana zan baka shawara da kuma ja maka kunni, dan kaga dai ni yau zan koma kuma basai na sake maimaita maka abunda ake ciki tsakanin ka da Rahamu"ba, kasan zancen auren ku akeyi da salma" hasalima bacewar ta itace ta dakatar da komai.
Allah yasani bawai inason auren ku bane, na sha fad'a maka hakan saidai babu yadda zanyi tunda ka nuna kana kaunar ta,
Allah ya bayyana ta, ka sake ha'kuri d abunda ya faru dakai haka kuma ka kula da kanka, kaji ko?
Gyada mata kai yayi kamar kadangare,
Yawwa" Allah yayi maka albarka, kuma yau ma Rahamu naji Alhaji yace zata dawo!
Dummmm!
Yaji kirjin sa ya buga, Rahamu yau zata dawo! Tabd'i yau zaiga wannan HATSABIBIYAR matar? Kenan?"maganar ummi ce ta dawo dashi nutsuwar sa, ni zanje driver yana jirana, daga kansa yayi had'i da daukar yar karamar jakar ta dake gaban ta, d'auka yayi ya fita da ita zuwa mota.
d'aki yakoma bayan tafiyar ummi" sosai ya shiga nazari da tunanin ta ina zai fara? har tsimayin ganin wannan matar yake wacce kowa ke SHAKKA da fargabar haduwa da ita. a diary d'in Zaid" yaji irin hatsabibancin da ta buga yaga labarin duk irin shiga tsakanin uba da d'an sa da tayi.
Sosai yaji ya tsane ta, haka kuma yana jin haduwar sa da ita ba alkhairee bane, amma fa a gare ta.
domin ya riga da ya shirya wa duk wani hatsabibancin ta, duk wani shiri da za tayi to fa shi ji yake ya shirya wa gaba da nata shirin.
(toh fa ga mus"ab ga Rahamu. Chakwakiya 😂🤣)
****
Salma tun tana saka ran bangis ya sake ta har ta cire rai sosai ta rame ta fita hayyacin ta, saboda rashin ishashen abinci dan sai lokacin da yaga dama yake bata.
ga shi bangis ya maida ta sai kace wata sex machine d'in sa duk lokacin da yaga dama ya ke zuwa yahau halqan ta.
Babu tausayi bare tausayawa.
Yasha giya ya bugu ya jibgeta, sosai tayi yaushi, ta shiga nadamar Rayuwa.
Ranar ma toilet ta shiga ta rufe taki budewa, saida dare yayi sosai ta bud'e, aikuwa da yakama ta ta yabawa Aya zakin ta, saida ya mata lilis kafun ya nuna mata Hoton gawar Zeema". Sosai hankalin ta ya tashi da ganin yanayin halin da Zeema take ciki tamkar babu rai a tare da ita.... bata gama tunanin ba yace katse ta.
Gawar ta ce wannan dan tuni na kashe ta.
baki sake ta shiga kallon sa idanun ta na tsiyayar ruwan hawaye,.... jikin ta har rawa yake ta shiga cewa.... Ita kuma mai tayi maka bangis? na shiga ukku...... Wannan wa... Ce irin Rayuwa ce...? Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un... Bangis anya kanason gamawa lfy kuwa,?
d'au! ya d'auke ta da maruka har guda2. dan ubanki ni zakiyi wa wa'azi? aikuwa ya hau jibgar ta, daga bisani yace kema garki damu d'an lokaci kad'an nake jira in sawake miki zama tare da ni da duniyar gaba d'aya, dan haka Kidaina wani hanzari tabbas zaki bakunci kawarki ba da dad'e wa ba.
Haka ya tafi ya barta tana numfarfashi, sai juye juye take tana sakin waning irin kuka na nadamar rayuwar ta, da tausayin kanta mai cike da rashin madafa ko maka ma.
********
Lokacin da Rahamu" ta dawo gidan Zaid yana, ta balcony d'in sa yana tunanin yadda zai bullowa wannan abu mai sar'kaki,, dan ganin abun yake tamkar a film ko Littafi, ko kuma wani labarin da yashafi dai almara.
Kullum aikin sa kenan tunanin mafita, dan yana jin bazai iya barin wadannan mutanen cikin wannan halin ba, yanajin yana son samar musu mafita, saidai kuma shi kansa yana bu'katar mafitar kafun comma burin sa. dole zai zauna tare da su yasamar musu mafita, saidai dole zaije gida kodan ya sanar dasu komai da ake ciki su sani zuwa lokacin da Allah zai bayyana Zaid.
Horn"din da yaji ne yasaka shi kallon bakin gate d'in kasancewar yana facing gate ne daga inda yake zauna yana iya ganin komai da yake faruwa a bakin gate d'in.
Motar tana gama shigowa yaga driver d'in da mai gadi sai wani kakamewa sukeyi haka kuma jikin su sai rawa yake driver ne ya bud'e side d'in owners, saida aka dauki mintoci da budewar kafun wata hamshakiyar mata Yar duma duma ta fito daga motar, baka ce irin bakaken nan na gana, ga gajeren hanci, sai manyan idanuwan ta da ke d'auke da izza, bata cika tsawo ba saidai baza ace mata gajeriya ba.
Kallo d'aya zakai mata kasan cewa macece mai izza da ji da kanta, haka kuma mai cike da tarin alfahari.(innallaha"la'yu hibbu kulla mukhtalin fakhur, Lallai Allah baya son mai girman Kai da alfahari, Allah ka rabamu da d'aya daga cikin biyun ka kiyashe mu aikata su, Allahumma"jaddad Iman fi"qulubina 🙏) mai tafiya da girman Kai.
Wata irin fad'uwar gaba mus"ab yaji lokacin da yagama karewa Rahamu" kallo.
Lallai akwai aiki a gaban sa. dan matar kanta abar tsoro ce bare kuma kaidin ta!
Shiru yayi ya nutsu yana kallon ta har taga ma mulkin nata ta hanyar bada umarnin shigar mata da kayan ta, kafun ta shige apartment d'in ta.
Numfashi ya sauke yana mai kai lemon dake hannun sa baki.
*******
tunda ranar da Rahamu" ta dawo rabon shi da ganin ta, ga dukkan alamu bata fitowa tana daga ciki take zuba mulkin ta.
Kwankasa kofar sa da ake ne yasa ya dawo daga tunanin da ya fad'a, tashi yayi yaje ya bud'e, nuhu ya gani, hannu ya bashi sukayi musabiha, kafun nuhu yace, hajiya ce tace akira mata kai tanason ganin ka.
Gaban sa ne yayi mugun fad'uwa, saidai a Zahiri gyada kai yayi alamun to.
Ciki ya koma, fussssssss ya fitar da wata irin zazzafar iska a bakin sa, hakika ya najin fargabar haduwa da matar saidai yanaji a ransa ba gudu ba ja da baya, dole ma yasan abun yi domin shi dai ya najin cewa shine ma kashin duk wani makircin ta hakika, idan tanajin yake take to ga abokin karawa ta samu.
Idan kuma tanajin cewa wasa ne take bugawa ta hanyar gwara kan ahali d'aya basu ji ba basu gani ba, to fa Shima zai taya ta dan haka tasamu abokin wasa.
takalman sa ya zira, had'i da nufar apartment d'in ta gadan gadan, wata irin kwarin guiwar tunkarar ta yake ji.
Kai tsaye ya shiga parlourn. Saidai babu kowa a ciki, zama yayi a d'aya daga cikin kujerun, karewa parlour d'in kallo ya shiga yi, d'aya daga cikin masu aikin ta ne ta shigo parln ri'ke da d'an karamun tray wanda ke d'auke da cup cike da Lemo, ajiye wa tayi a gaban sa had'i da cewa hajiyar tana zuwa.
bai amsa ba haka kuma bai ko Kalle ta ba.
tana ficewa ya d'auka lemon yana jujjuya cup d'in a hannun sa hakannan yake jin bai yarda da lemon ba Sam.
d'aya daga cikin pillows d'in kujerun ya d'auka, zuge zip d'in pillow d'in yayi, daga cup d'in yayi ya tsulala duka lemon take dollop d'in ya shanye.
Murmushi ya saki had'i da zuge zip d'in ya maida pillow d'in ya ajiye, ya d'au cup d'in y rike a hannun sa, tamkar shi yasha.
Yana zune a parln sai ga Rahamu"ta fito cikin shiga ta alfarma, anji golds hannu wuya da kafa, sai izza ake, kujera ta samu ta zauna, kallon Zaid ta shiga yi shi kuwa tunda ta fito ya d'an daga mata kai bai sake duban ta ba Sai kansa dake kasa, yana d'an jujjuya cup d'in hannun sa.
Zaid!
ta kira sunan sa shi kuwa da har zai d'ago sai kuma ya fasa ganin hakan da Rahamu"tayi yasa ta ce,
au! mtss nama manta ance ka kurmance, (dan dad ya fad'a mata cewa Zaid baya mgana ita kuwa sai ta d'auka har ji baya yi)
"we'll hakan ma yayi, iyaka idan na kawo maka takardu ka danna musu biro ka bani, hhhh, naji dad'in hakan sosai, na kuma godewa wanda suka sace mun kai.dan haka aikinmu zai soma hankali kwance. tunda Yar banzar yarinyar nan ta kasa biya mun bukata ta, sai ma bin banzan saura yin ta da tayi, shi kuma Alhaji sai wani kashe kud'in sa yake ana cigiyar ta, Mtssss idona idon salma sai na tsine mata.!
tunda tasoma magana a ransa yake nazarin kowace Kalma da zata fad'a.
katse masa nazari tayi ta hanyar tasowa da tayi ta nufo shi, gaban sa ne ya fad'i.
Cup d'in hannun sa ta karba dan ganin ko yasha lemon ciki ko bai sha ba, ganin ya shanye duka yasa ta saki murmushi, tace yawwa zaidu gwara da kasha, ko kai fa.
Kaga Kai zaidu, tana maganar ne tana taboshi irin na kurame, tashi ka tafi side d'in ka.
Gyada mata Kai yayi bayan ya tashi ya d'an rusunar da kansa alamun godiya.
Kafun ya fice, yanajin lokacin da take cewa, a shirye na dawo maka Zaid a wannan karon dole inyi amfani da kai yadda ya kama ta dan in cimma buri na!
dariya yayi a ransa yace, idan ke sammako kika buga dan cimma burinki to ni a tafe na kwana, ba gudu babu ja da baya ni dake akaga wanda zai yi nasara, idan boka ne nasarar ki to ni ga Allah na dogara.!
Opppsss! na gaji 😂garku damu mun kusan gamawa insha'Allah 😁
Love u loads 💋
Xinnee smart 💋👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro