Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

29

****
'karfe goma na safe"Mus"ab ya farka daga allurar da akai masa, a hankali ya shiga bude idanuwan sa, sauke su yayi kan Dad dake dannar waya ba images San ya farka ba.

     Sosai ya shiga mamakin mai ya kawo shi asibiti? Sai dai cikin yan mintinan da basu fi biyar ba kwakwal warsa ta shiga fad'a masar komai tun daga saukar sa Airport zuwa abubuwan da suka faru dashi, saidai akwai tarin tambayoyi a zuciyar sa kwarai zai so sanin amsoshin saidai wa zai tambaya?

Ko ina wacce ta d'auko shi? ta fad'a masa akwai abubuwan da take son sanar da shi, to meye su?

   Dad d'agowa yayi dan Kai duban sa gun da Zaid"yake dan akai akai yake duban sa dan ganin ko ya farka,  aikuwa akayi sa'a ya farko, cikin farinciki ya'karasa gun shi.

Zaid" ka farko kenan? Masha'Allah, sannu"sannu Zaid! Y jikin naka?

duban sa mus"ab ya shiga yi shikam dai wannan abun yana bashi mamaki, waye ZAID? da ake kiransa da shi? Kodai na hau kace ne? to Kodai nine nakejin ba daidai ba, to su waye wadannan?

Yana da tarin tambayoyi birjik, saidai kuma waye zai fad'awa? Waye zai bashi amsa?

Dad"ganin yadda Zaid d'in ya zuba masa ido ne yasa, yayi tunanin ko dai bai dawo hayyacin sa bane?

Da sauri ya fita dan kiran likita.

Tare suka shigo da doctor d'in.

Kallon sa doctor fahad yayi, yayi ya ce, ya jikin naka?

Kallon sa mus"ab yayi ba tare da ya"amsa ba.

Doctor ganin irin kallon da mus"ab yake binsu da shi ne yasa, ya shiga yan goje2,

Kallon dad yayi yana mai cewa, Masha'Allah Alhmdllh" komai lafiya yanzun zamu d'ora shi akan magani saboda zama da yunwa har ulcer na ko'karin kama shi amma insha'Allah idan ya kiyaye ka'idoji da shan magani akan lokaci to zai samu lfy.

Masha'Allah" to doctor nagode sosai.

Yanzun dai ayi ko'karin bashi abinci yaci kafun akawo maganin sa.

********
Wayooo Allah na!........ Ni Jamila na tsallake rijiya da baya!

Wannan shine abunda hajiya Jamila take fad'a lokacin da taga kanta a tsakiyar parln ta.wayar ta ta ciro daga jaka sai haki take faman yi, layin hajiya azumi ta shiga kira sai ringing yake ba'a d'auka ba, dan haka ta zauna jugum tana dad'a gwada wa, saidai yayi ringing ya gaji ya Katse babu wani respond.

Cizon lips d'in ta tayi, saida yayi jini saidai Sam bata ma ji zafi ba tsabar tashin hankalin da take ciki, dan sam hankalin ta ya kasa kwanciya.

Sai uban gumi take had'awa tamkar babu na"urar sanyaya d'aki a parln.

****
Sosai Abba"ke kuka ganin halin da tilon d'an nasa yake ciki dan sam bai San waye a kansa ba, a cikin daren akayi masa aiki aka fito da harsashin,

Saida safe Abba" yasamu yayi waya da Mami, kwatanta mata asibitin da yake yayi, had'i da Umar tar ta tazo da kayan break.

Haka kuwa akayi, karfe 8.30am sai ga ta tazo da uban basket. shake da kayan kari.

Tana yin arba da tilon d'an nata taji wani mugun fad'uwar gaba, lokaci d'aya kuka yazo mata, kansa tayi tana kiran mus"ab d'ana, Alhmdllh Allah na gode maka, ashe zan sake saka ka a idanuna?

       Sosai take kuka tana zubawa d'an nata addu'ar samun lafiya.

Abba" ne ya shiga rarrashin ta, had'i da nuna mata a asibiti suke fa, da kyar yasamu tayi shiru.

Sallama yayi mata da zummar zai je gida yayi wanka, zai sa driver ya kawo ummi dan ita yafi dacewa da tayi Jinyar mijin ta.

******
Zaid" mai yake damunka?  tunda ka farka baka magana, ko wani abun yake damunka ne?

Shiru mus"ab yayi yaki cewa komai, sai sake bin dad da idanuwa da yayi.

Ikon Allah!

Dad ya fad'a yana mamakin wannan abun.

Ficewa yayi daga d'akin ya nufa office d'in doctor fahad.

Yana Ficewa mus"ab, ya sauke ajiyar zuciya.

A ransa ya shiga magana, wannan wani irin al'amari ne haka,? Su waye ne su?

Duk yadda akayi akwai lauje cikin nadi Kodai d'an sa kama yake dani ne? to amma wannan wace irin kama ce? koma dai meye zan zuba musu ido dan ganin, iya gudun ruwan su, kuma zan jira wannan yarinyar saidai kuma ko tana Raye? Allah masani.

Kofar da aka turo ne yasa yayi saurin lumshe idon sa ba tare da yaga waye ya shigo ba,

Ummi"ce da saurin ta ta'isa gare shi tana fad'in Zaid" d'ana Masha'Allah Alhmdllh Allah mun gode maka,  sannu Zaid Allah yabaka lfy ya tona asirin wanda sukai maka wannan abun. ta karasa maganar tana sakin siririn kuka, kife kanta tayi ta shiga rera kuka mai taba zuciya. wani bangaren na zuciyar ta yana tunano mata da yarta tana jin inama ta ganta?

Mus"ab shiru yayi yana sauraren sautin kukan, a hankali ya bud'e idonsa, ya d'an dubeta ganin kanta a sunkuye ne yasa ya bud'e idonsa da kyau dan kare mata kallo.

A ransa yana cewa ko wannan ce mahaifiyar Zaid d'in? bari ta d'ago inga ko muna kama da ita yadda zan tabbatar da kamar da nake da d'an su da har suka kasa gane ni ba d'an su bane, nasan dai dole akwai wanda ya biyo a cikin iyayen sa, Kodai mahaifin sa ko mahaifiyar sa. Kuma naga Sam babu wata kama da suke da uban.

******
Ummi" ki shirya driver ya Kaiki asibiti gun mijin ki....Abba" angan sa ne?
tayi saurin tambayar Abba" wanda shi kansa saida ta bashi dariya yar dariya yayi yace Eh angan shi, yanzun kuka ya 'kare ko?

         Sai yanzun ta lura da sakin layin da tayi, murmushi tayi had'i da shigewa d'akin Mami cikin jin kunya.

Tsayawa tayi tsakiyar d'akin, tana mai sake jin fad'uwar gaba zata had'u da mus"ab bayan tsawon lokaci da basa tare, sosai hankalin ta ya tashi take jin fad'uwar gaba. Fiye da ko yau she.after dress d'in ta ta zura kan riga da skirt d'in atamfa da yake jikin ta.

Komai bata shafawa fuskar ta ba, ta d'auka wayar ta, da Yar karamar jakar ta ta saka wayar a ciki da tissue. (na goge hawaye maybe idan mus"ab yayi halin sa 😂🤣)

A nutse ta fito daga d'akin, a hankali take tafiya cikin sanyin ta, har waje gurin parking lot, driver ne ya hango ta da sauri ya taso, sannu da fitowa hajiya karama.

Yawwa sannu idi.

daga haka ta bud'e motar ta shiga shima shiga yayi ya zauna, had'i da yiwa motar key. suka fice zuwa asibitin.

******
Mus"ab ci gaba da rufe idanuwan sa yayi yana jin duk firan iyayen zaid d'in da bai sani ba, kuma suke d'aukar sa shi.

Ummi" ce ta dubi dad tace Alhaji" ya labarin ita salma? Ko angan ta?

      Shiru dad yayi saida ya d'an jiman ta kafun ya ce, wlh Lubabatu, salma dai babu labari ni wannan abun daure mun Kai yake dan dai musulunci, kariga da kayi imani da kaddara, amma irin wannan wanda basuda tawakkali ai sai su had'a da malaman duba.

Wlh kuwa Alhaji'abun kam da daure Kai gaskiya.    Amma ina Rahamu" ita tasan anga Zaid kuwa?   tana can ta tafi Ghana, kuma ma bata da lafiya yanzun haka itama tana asibiti, ita kanta kafun ta tafi saida naja mata kunni, dan ranar na je office sai na tuno akwai takardun da ya kamata na kawo.

Kuma babu wanda na amince dashi ma zuwa gidana gashi Zaid babu da waya kawai zan masa ya kawon, Allah dai yabaka lafiya Zaid.   ya fad'a da sassan Yar Murya. yaci gaba da cewa.....

dole sai zuwa nayi da kaina, tun a bakin gate nasoma jin wani irin wari mai tayar da zuciya, ina shiga cikin gidan warin nunkin ba nunkin, Kai tsaye sashin ta na fad'a, abun mamaki samu nayi wai ana mata hayaki ne daga ita sai zani, nace hayakin meye wannan wai magani ake Allah bayyana salma" nayi mata tass dan sosai raina ya baci na kori shaid'aniyar. Shine fa Wai batajin dad'i zata tafi Ghana nce Allah ya kiyaye hanya ya bata lafiya.

Amin ummi"ta ce tana jinjina lamarin a ranta, saidai ita tuni ta gane inda zancen ya dosa babu wani maganin bayyanar salma face sihiri na neman biyan bukata.

Allah dai ya shirye mu.

Motsin Zaid ne yasa duka suka maida duban su gun shi.

a hankali mus"ab ya shiga bud'e idon sa, gaban sa ne yayi mugun fad'uwa lokacin da idonsa ya Sauka kan na ummi" ana kama a duniya! Shine abunda ya fad'a wa kansa.

Saboda kamannin baby da ummi" har yayi yawa,

Zaid" yarona ka farka? Sannu

Zaid sannu kaji?

Mai kake son ci yanzun?

Wannan shine Tambayoyin da suke binsa da shi, wanda har ya rasa wa zai kalla a cikin su saidai yayi alkawarin kin yin magana zuwa lokacin da ya dibar wa kansa.

Zaid"...... Zata  sake yin magana Dad ya girgiza mata kai, kallon rashin fahimta tayi masa, a sanyaye yace tun lokacin da Zaid ya farka baya magana kuma an yi bincike saidai ba'a gane mai yakawo hakan ba.

Wani irin hawayen tausayin Zaid d'in ne ya zubowa ummi" yanzun dad Zaid d'in nawa ne baya magana,? Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un  y Allah!  a a Lubabatu, ha'kuri zamuyi likita ya tabbatar min watarana zai iya yin magana, saboda duk abunda mukeyi yana jin mu maganar ce dai shiru wanda su kansu duk bunciken su sun kasa gane meye dalilin rashin maganar.

Cikin tausayawa ummi ta sake duban mus"ab tace sannu Zaid Allah yabaka lafiya, ya tona asirin azzaluman da sukayi maka wannan abun, Amin y Allah

Wannan shine abunda dad ya fad'a, yana mai tausayin Zaid d'in a ransa.

Abinci ummi"ta shiga had'a ma Zaid". bashi abincin ta shiga yi a baki cike da tausaya wa.

cin abincin yake yi Shima cike da tausayin UMMIN yadda take kulawa dashi a tunanin ta ko d'an ta ne. to ya zata ji idan ta gane ba d'an ta bane shi?

Ya zamar masa dole ya binciko komai game da su, abunda yafi damun sa inda zai samo wannan yarinyar dan yasan a gunta ne zai samu duk irin baya nan da yake so.

To ina zai ganta?

Yaji mahaifinsa Zaid"yana bada labarin wata matar kenan matan sa biyu ne... Kuma a sunan yayi iri d'aya da wanda yarinyar da ta taimake sa ta fad'a masa, haka kuma yaji sunan salma a gun yarinyar kuma yanz ma yaji sunan,   sosai kansa ya kulle, mafita kawai yake nema kota halin Yaya, abu d'aya yasani bazai koma gun iyayen sa ba har sai yagano wayann su waye da gaskiya dake rufe.

****
Hajiya Rahamu"tunda taje Ghana take zarya gurin boka dan komai ya lalace mata a cewar ta babu Zaid babu salma ya zatayi ta samu cikar burin ta? dole ta shiga zaryar bokaye, saidai kullum maganar d'aya ce akwai lokaci!

       Ciwon kai ya taso ta gaba kamar masifa dan jin  take kamar ana kwara mata dalma, wanda har yakai ta da kwanciyar asibiti.

Kusani a addu'a ciwon kai kamar me 🤧

Xinnee smart 💋

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro