Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

28

Abba" bai isa gurin ba saida Cp yazo suka tsara duk yadda za"a tunkari gurin kasancewar da dare ne.

         Wayar Abba"ce ta sake yin kara, wancan number dai ce, dan haka jiki na rawa ya daga Cp ne ya karbe wayar had'i da saka ta hands free. ga dukkan alamu Alhaji"baka son d'an ka!

Abba"jiki na rawa ya shiga cewa ina... S... on... sa wlh dan Allah garku cutar mun da yaro shi kad'ai na mallaka a duniya.

Ko nawa kuke so zan baku.

Kayi mana shiru! Kaji ko, an fad'a maka dukiyar ka muke so ne?

to bari kaji, mu ba kud'i ne yasa muka d'auko d'anka ba dan cewa akayi mu kashe shi, shine na tausaya maka na ce kazo kafun mu kaddamar masa, shine ka kwaso zugar kwala"wa.

to matu'kar kana bu'katar d'anka ka gaggauta sallamar su idan kuma ba haka ba.... to ka shirya makoki.

Muryar Abba cike da damuwa yace shikenan, zan sallame su dan Allah nidai garku cutar mun da yaro, d'iff aka katse kiran.

Shiru Abba yayi yana duban Cp"kwantar masa da hankali Cp ya shiga yi.

******
Sautin horn mai karfi da security d'in gidan su kaji ne yasa suka fito da sauri dan ganin maike faruwa, basuga kowa ba Sai mutum da suka gani yashe a kasa, a hankali suka karasa gurin sa, suna masu saita shi da bindigu, dan shirin ko ta kwana.

     Asalin mai gadin ne ya gane Zaid" da sauri ya karasa gunsa yana fad'in zaidu... Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un,  take sauran suka gane waye a gurin da sauri suka d'auke shi zuwa cikin gidan, zuwa wannan lokacin tuni ya sume.

******
Hajiya azumi" na shirya fa, cewar Jamila.. OK tom kawai ki d'au hanya ai kingane kwatancen. a d'aya bangaren hajiya azumi ta bata amsa kasancewar duk maganar da suke sunayin ta a waya ne.

to shikenan Kawa ta nagode.

daga haka Jamila ta sauke wayar, jakar ta ta d'auka, sai key d'in mota.

Kasancewar mai gidan ta ba mazauni bane yau ma anyi sa'a baya kasar ma gaba d'aya.

sauri2 ta isa gun motar ta, key tayi wa motar, mai gadi ne ya bud'e mata gate d'in gidan ta fice yana binta da adawo lafiya.

******
Da hanzari mai gadi ya nufa part d'in Alhaji" ya nufa, kwankwasa wa ya shiga yi jikin sa sai rawa yake.

Alhaji Tahir"da dama ba wani isheshen bacci yake samu ba, dan yau ciwo gobe lafiya haka yake fama.

               da sauri ya fito daga d'akin sa, yana fad'in lafiya... dan ya gane muryar mai gadin gidan sa ne. jikin sa sai rawa yake sabida yasan ko meye yake kiran sa kanshi to ba alkhairee bane dan wannan kiran baiyi kama da na lafiya ba.

Yana fitowa mai gadi ya shiga nuna masa 'kofa, kallon sa yakai kan kofar dan ganin mai yake nuna masa. idanun sa ne suka Sauka kan security d'in gidan da suke d'auke da mutum a hannun su. Kasancewar gurin da wadataccen hasken solar.

'karasa wa gurin securities d'in sukayi da zaid dake sume.

kallon Zaid dake hannun su Alhaji" yayi, take ya gane shi. da sauri ya karbe shi daga hannun su ya durkushe a gurin tare da Zaid a hannun sa. Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un.  Zaidu zaidu.... Kai ne?  Sub'hanallah... Zaid"! sambatu Dad ya shiga yi, tamkar yaro ko wanda ya zare, yi yake yana jijjiga Zaid d'in.

Saidai shi bai masan mai yakeyi ba.

*******
Ko da hajiya Jamila ta isa titin gidan, parking motar ta tayi a d'an nisa da gidan.fita tayi daga motar ta rufe ta, a hankali ta karasa gidan, a sad'ad'e ta shiga samun yaran da suka sa aikin tayi a gidan.

Dariya ta saki lokacin da taga mus"ab" a tsakiya gashi galabaice, sosai hakan yayi mata dad'i, duban d'aya daga cikin yaran tayi kafun ta ce,  zaku iya gabatar da kisan.

d'aya daga cikin yaran ne yayi wani muguwar dariya dan shi yasan komai da aka tsara musu sabanin hajiya jameela da kawai sai abunda hajiya azumi tace mata wanda Sam bata San meye kullin azumi a gare ta ba.

Harbi babban cikin sun yakai wa, 'kafar mus"ab, wata irin razananniyar kara ya saki dan azabar da yaji ta ratsa shi.

Wani irin banko kofar akayi. Abba"ne ya shigo jikin sa na rawa kamar mazari.

take yayi kan mus"ab dake kwance cikin jini. Hajiya jamila tana ganin haka ta ja jiki ba tare da kowa ya lura da ita ba ta bar gidan jikin ta na rawa.... to wa ya fad'a wa Yaya, mus"ab na gidan nan? Ko dai Jami'an tsaro sun gano su ne?

Inna"lillahi yau na shiga ukku Allah yasa dai Yaya bai ganni ba.
Haka ta dinga sambatu har ta'isa jikin motar ta. da kyar tayi mata key jiki na rawa ta nufa gidan ta, wanda Allah ne kawai yakai ta lafiya dan sam bata cikin hayyacin ta.

******
Fitowar hajiya jamila babu jimawa yan sanda suka iso had'i da zagaye gidan.

Abba kam kuka ya shiga yi ganin halin da d'an nasa yake ciki sosai ya shiga damuwa,

take police d'in sukayi arresting. yaran dukan su.

Mus"ab kuma asibiti aka nufa dashi cikin daren dan tuni ya sume.

       ********
Abuja, hospital.

Alhaji Tahir" ne a zaune gefen gadon da aka kwantar da Zaid" ya zuba uban tagumi,

A ransa yana mamakin wannan abun, waye wannan da yake neman salwantar masa da Yaya"? baby dai babu ta bata babu labari gwara ita ace yanayin rashin lafiyar ta ne, to ga Zaid ansace badan da rabon yasake shan ruwa ba da yanzun Shima shikenan.

     to ga kuma salma"wacce itama har yanzun babu labarin ta. Wannan abun sosai yake daga masa hankali,  yayi imani da kadddara mai kyau ko sabanin haka.hasali ma shine silar da yakawo yanzun ba tare da ya fad'i jinya ba.
hakika abun yana matu'kar damun sa.

Knocking door d'in akayi had'i da shigowa" doctor ne tare da wata nos.

Alhaji" antashi lafiya?  Cewar doctor d'in had'i da mika masa hannu, amsawa dad yayi yana mai basa hannun shi ma.

Ya"mai jikin Alhaji?

Gashi nan Alhmdllh, saidai har yanzun bai farka ba.

to Masha'Allah ai saboda wannan allurar da muka mishi ne amma nasan baya nisa ga farkawa insha'Allah.

            matsawa yayi gurin gadon da Zaid d'in yake a kwance, tattaba shi ya shiga yi yana bincike irin nasu na likitoci.

duban dad doctor yayi, yace idan ya farka, ayi ko'karin bashi abinci yaci saboda harda yunwa ma tana damun sa duk da dai mun d'aura masa drip, still ya kamata yaci wani abu, zan dawo idan ya farka d'in.

to likita sannu da ko'kari na gode.

Allah ya bashi lafiya, Cewar likitan yana ficewa daga d'akin.

Amin y Allah!

*****
Ni zaki ciwa Amana Zeema?

Cewar bangis da yasa yaran sa suka kamo masa ita, wani irin numfashin wahala ta sauke, da kyar ta bud'e bakin ta ta shiga cewa. Bangis, hakika na soka so irin na bariki, so na cin Amana tunda nasan Kai saurayin Kawa ta ne, kuma ma banda Kai wawa ne" ta Yaya zaka amince min har haka bayan kasan cewa karuwa ba abar yadda bace, haka kuma da cin Amana na gina soyayyar ka ta Yaya kake tunanin zatayi 'kwari?

Ka sani Bangis nayi nadamar harkar bariki gaba d'ayan ta, dan na fuskanci sharri ne kawai a cikin ta babu wani alkhairee.

Kuma Bana nadamar kubutar da Zaid"da nayi daga hannun azzalumi irin ka,.... Wani mugun Mari ya sauke mata wanda ya saka bakin ta fashewa, maimakon tayi shiru,

Sai sakin murmushin takaici tayi, taci gaba da cewa, kasani ina baka shawara da ka tuba daga wannan mummunar rayuwar dabancin da ka d'aukar wa kanka, dan nima ina Fata Allah ybani ikon gina kyakyawar rayuwa, a nan gaba, dan sosai nake nadamar kasance wa ta daga cikin matan bariki.

                     Sake taka mata kafa yayi, a kausashe yace, wai bazaki yi shiru ba dan ubanki?

Naki in tuban, kuma kema kashe ki zanyi kamar yadda zan kashe salma,

               'kafar sa ya d'ora daidai saitin, inda yaron sa ya harbe ta wani irin murtsika yaiwa gurin. wani irin waha lallen numfashi ta sauke, idon ta na wani irin lumshe wa.

    Babu tausayi ko imani Bangis ya saita daidai inda yaron sa ya harbe ta yasake sakar mata harsa shi.

                      Ragwaf jikin ta yasa ki,

Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un.

🤧🤧🤧🤧

Anamun uzuri mana dn Allah, inafa da iyali abubuwan da yawa Kuna ha'kuri dn Allah 🙏😢

Son_so fi'sabilillah 💋

Xinnee smart

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro