23
****
Su Abba" daga tafiyar su, sukayi a bisa shawarar da suka yanke na saka baby makaranta, hakan kuwa akayi an nema mata makaranta, inda aka saka ta secondary, a aji 3,
Wanda Za a dinga yi mata nata extra lesson, ita d'aya,
Saida komai ya kammallah, suka samar mata driver da zai dinga Kai ta makaranta, baby kam dad'i tayi ta ji gashi sun bata uniform,
Ranar da su Abba zasu tafi sosai jikin Mami yayi sanyi kan barin baby da mus"ab da za suyi, Abba ne yayi ta kwantar mata da hankali da kyar ta kwantar da hankalin ta, ranta Sam babu dad'i,
'karfe 8na dare suka nufa airport dukan su, baby na nanuqe da mus"ab,shi kuwa sai tsaki yake saki, a ransa.
Koda suka isa airport sosai iyayen suka shiga yi masa nasiha, kan ummi, saidai zamu iya cewa tabi ta bayan kunne..
Lokacin da aka kira su, sosai jikin Mami ya koma sanyi ta kankame baby a jikin ta, baby ma rungume ta tayi tana kuka, dukan su su ukun jikin su yayi sanyi, banda uban gayya dake jira a su tafi, su koma gida y yasoma cin ubanta.
Dan alkawari yayi yau sai ta fad'a masa uban da tazo yi cikin rayuwar sa, dan shi Sam bai yarda da ita ba.,
Haka suna ji suna gani suka tafi suka bar UMAIMAH" baiwar Allah,
Sosai tayi kuka kamar me ko a mota dunkule wa tayi tana ta kuka.
ci kanki baice mata ba,
Ko da suka koma gida dare yayi dan haka Kai tsaye ya wuce d'akin sa.
Ita kuwa d'akin ta tashiga ta cire kayan ta tayi wanka kamar yadda Mami ta sabar mata, kayan baccin ta ta saka riga da wando pink color masu kauri.
bedroom slippers ta zira a Kyakyawar Farar kafar ta.
Kai tsaye sama ta hau zuwa d'akin sa.
Salamu"alaikum!
shiga ciki tayi bayan sallamar da tayi da siririyar muryar ta.
A kwance yake kan makeken gadon sa sai faman girgiza 'kafar sa yakeyi,
A hankali ta hau gadon ta kwanta, duk yana jin ta, baice mata komai ba Sai da ya bari bacci ya d'auke ta sosai, ya tashi kallon ta yayimata na seconds,
d'aukar ta yayi ya sauke ta daga gadon...
A 'kasan tiles ya kwantar da ita,
Ya koma kan gadon, remot d'in Ac ya d'auka ya'kara masa'karfi, yaja duvet, ya shiga baccin sa hankali kwance bayan ya rufe d'akin ya rufe dukkan wardrobe d'in d'akin
Cikin bacci taji wani irin sanyi na shigar ta har 'kasusuwa,
Sake dun 'kulewa guri d'aya ta yi.
hannunta ta shiga mikawa dan Jan duvet, saidai ji tayi tamkar ba a kan gado take ba.
Idanuwan ta, ta bud'e dulum taga d'akin yayi uban duhu dan ko Dumm light bai bari a kunne ba, wani irin tsoro ne ya kama ta gashi tsabar duhu ko hannun ta bata iya gani, take tasoma kuka tana kankame jikin ta tamkar wani zai gudu da ita ne.
a lokacin ne ya bude ido dan jin sheshekar kuka, kallon position d'in ta yayi, a ransa yace yanzun kika soma kuka, maida kansa yayi yaci gaba da baccin sa, baby kam tayi kuka har ta gode Allah" dan duk fuskar ta tayi wani irin ja, musamman hancin ta,
guraren asuba bacci yayi awon gaba da ita daga zaune duk tabi ta, ta Kure ga hawaye duk sun bushe mata a fuska, kallo d'aya zakai mata ta baka tausayi.
*****
Kiran sallar da ake ne ya farkar da shi, mika yayi had'i da addu'ar tashi daga bacci, switch d'in d'akin ya kunna, ganin ta yayi dun'kule guri d'aya, wani irin tsaki yayi ya shige toilet.
Sai da ya d'aura alwala, ya fito.
Ganin har yanzun bacci take ne yasa yayi wata irin 'kwafa. Jallabiyyar sa ya d'auko ya saka kalar brown.
Kai tsaye gurin ta ya nufa, ganin bata da alamun tashi ne yasa yayi tsaki, gurin dispenser dake d'akin ya nufa ruwa ya debo masu sanyi cikin cup d'in dake gurin,
watsa mata ruwan yayi a kanta zuwa fuska.... a rude ta farka, Jikinta take ya shiga makyar kyata.
kallon sa take da Idanuwan ta, cike da sanyi a ranta tana jin wani iri a kan wannan d'in, wancan ba haka yake ba Sam baya mata haka, why wannan d'in?
d'auke Idanuwan sa yayi daga kallon da take masa fuskar sa a daure dan haka kawai sai yanjin kallon a ransa jin kallon yake tamkar na, Kaci Amana ta ba haka mukayi da kai ba, ka yaudare ni.
Shi kuwa baya son Yama tausaya mata dan tun ranar da yasoma ganin ta yaji kawai yanjin haushin ta, gashi daga karshe tasa an'ka'kaba masa auren ta.
tashi yayi, zai fita sai da yakai bakin kofa, ya tsaya, ki tabbatar kin shirya da wuri dan zuwa makaranta.
Yana kaiwa nan yafice abun sa, wannan fad'a matan da yayi ma dan Mami tana ta jaddada masa ne, ya tabbatar yana saka ta zuwa makaranta a kan lokaci,
tana ganin ya tafi ta mike jikinta na mata wani iri, kamar zazza'bi na son kama ta, haka ta nufa room d'in ta a kasalance, tana zuwa ta shiga bathroom wanka tayi da ruwan zafi ta gasa jikin ta sosai, ta d'aura al'wala.
tana fitowa tasaka jallabiyyar ta, ta kabbarta sallah, saida ta sallame tahau azkar d'in ta, tana gama wa ta yi rak'atanil Fajr d'in da batayi da farko ba, saboda kurewar lokaci.
tana sallame wa, tayi shiru... ta rafka ta gumi, a ranta take zance,
To ni ina iyaye na? Kodai sun mutu ne?
To amma ai Mami tace mun tsinta ta sukai a kofar gida, ni shikenan bnda Mami banda Abba"? a a Mami ta ce sune iyaye na, shi kuwa wannan d'in yace mun shine. Zai zame mun uwa da uba..
Shiru tayi..tanason tuna sauran maganganun nasu,, saidai bata iya tuno komai ba Sai wannan kyakyawan murmushin nasa.
Wasu irin hawaye masu zafi ne suka sauko mata, tana jin wani iri a ranta, tanason sanin kanta da kyau dan tana bu'katar hakan.
tunanin abunda yafaru jiya take yi har zuwa yau da ya zuba mata ruwan sanyi.
Wannan kam baya son ta to mai tayi masa bata da amsar hakan, dan haka dole ta tashi ta shirya tsab cikin uniform d'in ta,
Ko da ta fito dalha mai girkin gidan ya gama, zama tayi a kan dining d'in,, tea kawai ta iya tasha dan bata jin dad'in bakin ta ko kad'an.
Security d'in bakin gate ne yayi sallama kofar parlour,, wai ta fito ga driver d'in ta ya zo. a kasalance ta d'auka jakar ta, ta fito.
*****Zaman baby, da mus'ab zama ne na kadaran kada han dan kuwa ba karamin gasuwa take a gurin shi ba, sosai yake wahalar da ita da salon zalinci kala kala,
tuni tabi ta lalace tayi yaushi da ita,
Yau ma, ana ruwan sama yasaka ta wankin kana nan kayan sa, kuma yace a waje Za tayi, babu yadda ta iya dan ita yanzun tsoron sa take matu'ka,
Haka ta fita cikin ruwan, tasoma wanke masa kayan, duk da injimin wankin da ke gidan, ga ma'aikata, amma tsabar mugunta yace dole ita ce zata wanke.
tana wankin tana hawaye ruwa na Sauka a jikin ta sai rawar sanyi takeyi, duk da dama sanyi ya dade da kama mata jiki ko dan kwana da takeyi a kan tiles.
Saida ta gama wanke wa tas ta ci gaba da zama a ruwan sai kuka takeyi.. Mai cike da sauti. da damuwar da ita kanta ba zata misalta ta ba.
Sai da ruwan ya daina zuba ta tashi, shanya wa tayi, taje da d'aki ta fad'a wanka tana fitowa ta Shafe jikin ta da mai, tasaka kayan ta.
Buks d'in ta ta d'auko tahau dubawa, dan baby akwai ko'kari sosai take maida hankalinta a kan karatun, duk da irin damuwar da take ciki.
Sai da ta tabbatar da kayan sun bushe kafun ta d'auko, tasoma gogewa, bata lura ba Iron d'in yayi zafi sosai ta manna wa wani wandon aikuwa take yayi uban map na Kuna, hankalin ta ne yayi waninn irin tashi,
Dan yau tasan idonta idon mus"ab... bata gama tunanin mafita ba yashigo d'akin.
dan dama d'akin sa ne take gugan, jikin ta ne ya d'auka rawa dan ga wandon shimfide kan dadduma, babu halin boyewa..
take tasoma hawaye, shi kuwa yana shigowa d'akin da wandon ya fara tozali dan konuwar ba kad'an ba ce, aikuwa yana gani ransa yayi mugun baci.
isa yayi gaban ta, ya duka ya d'auka wandon yana mata wani mugun kallo,, kirjin ta banda bugawa babu abunda yake,..
Sosai take cikin fargaba, hannuwan ta ta had'a tana bashi ha'kuri, kallon ta kawai yake,
Ita kuwa idon ta a rufe sai kuka da ban ha'kuri take, bata ankara ba taji wata muguwar azaba kan cinyar ta, wata gigitacciyar Kara tasa had'i da somewa,
dan azabar zafin ya game mata da tsoron da ya kama ta.
haushi ne yasake Kamashi d'aukar ta yayi zuwa d'akin ta, a gado ya dan gwarar da ita. Ruwa ya debo ya kwara mata a fuska, take ta shiga sauke ajiyar zuciya, wani rada d'in azaba ne yayi mata sallama.
take ta dinga kuka kamar ranta zai fita, wani irin muguwar tsanar sa da tsoron ne, suka sake samun muhali a zuciyar ta.
Ganin ta farka ya fice daga d'akin yana mai yin tsaki.
Saida tayi kukan ta ma"ishi ta lallaba taje d'akin Abba ta d'auko first aid box,
Cikin azaba ta dinga wankin gurin dan tuni ya daye yayi ruwa,
Wankewa take tana kuka gwanin tausayi,
Saida ta gama tasha paracetamol, ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita.
Kamar kullum yau ma a cikin baccin tayi mafarkin sa yazo mata yana mai cewa...
Yarinya ta" ina kewar ki.
Zumbura baki tayi cikin fushi, tace ni yanzun ai baka sona, nima na daina sonka!
Wani irin ja taga idanuwan sa sunyi,
Yace karki soma karya alkawari, son junan mu wani irin abu ne da Allah ya hallita a tsakanin mu wanda babu ranar dainawa,
Ina son ki ban taba jin zan ko da misalin jin haushin ki ne bare kuma daina son ki alkawari ne da na daukar wa kaina, son ki zai zamo abokin Rayuwa ta ko babu ke, tunani kan ki kawai sun ishe ni, a barni dasu,
Ko bani da aikin yi son ki zai zamo abun yi na.
kallon sa tayi da idanuwan ta da suka sake lumshewa saboda tsananin shaukin kaunar sa dake dawai miya da ita,
ta ce.. to mai yasa a zahiri kake hora ni?
Sosai nake jin haushin ka, akan yadda kake mun Bana so.... ta fad'a da wata irin rainanniyar Murya, idanuwan ta na kawo ruwa,.
Sake matso wa yayi kusa da ita, habarta ya tallafo,
Yarinya ta, ki kalli cikin idanuwa na, na tabbata zakiga soyayyar ki dake ciki son ki a gare ni ba abu bane mai sau'ki da har zan yikes wasa rere dashi, hakika son ki a gareni abu ne mai matu'kar girma da daraja, wacce ta kere dukkan abunda na mallaka ko da kuwa numfashi na ne,
Sake kallon sa tayi wasu hawayen suna zubowa, tace.... kana yaudara ta da kalaman ka masu matu'kar zafi a kwakwalwa, kana bari na cikin rudani da waswasin soyayyar ka a gare ni yayin zance soyayyar ka abar saurare ce...
Yayin ai katawa abar kyama ce da gudarwa, Kai....ni....bana son ka.... Na tsane... Ka....
Da wani irin ihu yce karya kike....!
Kina so na kuma baki tsaneni ba, nine burin ki muradin ki....... Nayi alkawari Koda auren ki shine abu na karshe da zan aikata to fa saina aure ki..
A a nidai... dan Allah kabarni.... Wlh bnason ka........
Ya isaaaaaaa!
Ya fad'a da wata irin tsawa... Itama a tsawace tace. na fad'a,
Na tsane kaaaaaa!..........
Xinnee smart 💕💋👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro