21
Shiri akeyi babu kama hannun yaro,, salma"sai salailai ake tayi,
Rahamu". Wannan duk bai dame ta ba idan da abunda ya dameta to cikar burin ta ne.
Zeema" ce ta dubi salma da sai faman sakin tsaki take hannun ta ri'ke da waya, tace saly yahdai?
Wani tsakin salma tasaki kafun tace wlh zeema"bangis ne yabi ya ishe ni, wai Lallai yau inzo mu had'u,! Kuma nasan Sarai idan na kuskure na je to wlh bazai barni in dawo kan lokaci ba, inda ma naji dad'i d'aya ne baisan cewa aure nake shirin yi ba da nasan sai ya mun rashin mutunci.
Hmmmm" Zeema ta ja kafun tace ni fa kina ban mamaki saly, yanda kike tsoron wannan bangis d'in, yanda yake ta'kamar gidan su akwai arziki ai kema gidan ku akwai shi, idan kuma sonsa kike to kawai ki fad'a masa yafito ayi dashi a fasa da wanna......
Zeema!... Ki rufan asiri dan Allah Kar ma mommy taji wannan zancen, kinsan irin wahalar da aka sha kafun Zaid ya amince zai aure ni?
Anzo gurin! Zeema ta fad'a a ranta, saidai bata nuna komai a fuskarta ba, tace wai bangane mai kike nufi... hmmm Zeema abar maganar nan kawai amma idan na fad'a miki ai mommy sai ta kusa kashe ni yadda take da burin cikar burin ta!..... Salma.....'kundun ubanki.... Nace kaniyar ki.... Shasha wacce batasan ciwon kanta ba.!
Rahamu" ce mai wannan zancen bayan taji zancen da su Salman su keyi. jikin salma ne ya d'auka rawa dan tasan mommyn na iya cewa anfada auren...da sauri ta shiga baiwa Rahamu" ha'kuri,,
Ko kallon ta Rahamu"batayi ba, ta dubi zeema wacce ke duban su cike da tuhuma... tace fita tana nuna mata hanya, jakar ta ta d'auka ta fita, a ranta tana kitsa yadda zata samu jin dukkan abunda suke boye wa tasan salma wawuya ce, ta bugawa a jarida ba zata sha wahala gun jin sirrin ba, kuma ma ga hanya mai sau'ki.... ta fad'a wa kanta kawai kayan maye zata loda mata ta kwaye mata komai suke rufewa ita da azababbiyar uwar ta,
Dan ta dade da tuhumar ba Kai tsaye Zaid zai auri salma ba saboda yadda salma tasha bata labarin yadda take sonsa yake wula'kanta ta. hakannan taji tanason taimakon zaid d'in ko dan hassadar da takeyi wa salma, bata shirya salma tabar bariki yanzun ba so take ko barin ne to Sai dai su bari tare. da sa'ke sa'ke tabar gidan.
*****
Salma ashe ke wawiya ce? wa ya fad'a miki ana amin ta a bariki? Waton da banzo kan lokaci ba da yanzun sirrin mu yakoma hannun wata, wacce kuka had'u wurin yawon club... Ko kin d'auka bansan iskancin da kuke yi ke da azeemar bane?
Wawuya kawai,, to wlh bari kiji in fad'a miki duk ranar da kika sake kika fad'awa wani wannan sirrin ina mai tabbatar miki da babu ke babu zaidun har abada kuma mutuwa zakiyi dan ubanki!
Mommy ni dai dan Allah kiyi ha'kuri, wlh ni dama ba fad'a mata zanyi ba, kawai dama bangis ne yadameni wai sai nazo mun had'u shine nake fad'a mata shine wai in auri bangis d'in, shine fa nace ta daina wannan zancen batasan yadda na sami zaid d'in bane,,... shine fa muke maganar,
Tsaki Rahamu tayi, kaji irin sakarcin naki ba, Sam bakida wayau, ni wani lokacin jinki nake kamar ba jini na ba saboda rashin wayau, haka kika ga ina al'amura na?
Dan haka idan zakiyi hankali kiyi hankali na fad'a miki kenan dan wlh wannan sirrin da kika gani shine rayuwar mu u better be careful.
ficewa tayi daga d'akin tana kaiwa nan a zancen ta, d'akin ta, ta koma... Zarya ta shiga yi yazama dole ta d'auka mataki akan haduwar salma da azeema, bangare d'aya ga d'an iskan saurayin ta, tasan mai zatayi... Murmushin samun mafita tayi.
*********
Zaid" bawan Allah gaba d'aya ya maida hankalin sa kacokam akan karatun sa, wani 'bangaren na zuciyar sa na cike da tsantsar kewar Yarinyar sa, tunanin sa yazame masa jiki dan har lokaci yakan ware dan yin tunanin ta,
wani abun yayi Murmushi wani yayi dariya, haka yake kullum zuciyar sa cikin azalzalar sa take a kanta, saidai abun haushin Sam ba shida wani kata'bus akan yadda zai nemawa kansa mafita...
A bangare d'aya Sam auren Salma bai dad'a shi da kasa ba. Saidai abu d'aya ne duk wanda ya tambaye shi to idan zai bada amsa, ji yake Lallai sai ya fad'i idan bai aureta ba ji yake kamar zai mutu,.... shi dai yasan cewa ko kallon ta baya son yi, dan duk lokacin da tazo gurin sa haka Za tayi ta zuba ita d'aya idan ta gama ta tafi, baya iya yi mata wata magana mai tsayi,
Shi dai yasan so d'aya ne kuma ya baiwa UMAIMAH" fatan sa Allah ya bayyana mai ita.
(ko burin sa zai cika?)
****Abba" nifa sha'kuwar ummi da mus'ab yana bani mamaki yarinyar tana matu'kar sonsa tamkar wanda suka fito ciki d'aya... Koda..... Sai kuma tayi shiru.
Wani duba Abban yayi mata, Murmushi yayi had'i da girgiza kansa,
tashi yayi ya nufa wata jakar takar dun sa, ya d'auko wasu takardu,, zama yayi a kusa da ita yace Rukayya" ina ce akan takardar nan kike tuhuma ta' a zuciyar ki da kuma wasu daga cikin kalaman ki,?
Ya fad'a yana nuna mata takardar da ta gani a hannun baby"....
Shiru Mami tayi, a ranta tana cewa ashe dama takardar tana gurin shi? shi yasa ta nema ta rasa? Katse mata tunani yayi da ci gaba da magana....
Tun ranar da kika zo d'akina kina ta kuka kina wasu zantukan da ni na d'auka saboda tsohuwar damuwar mu ce, ashe Sam ba haka bane a gurin ki,,!
Bayan kin tafi sai na lura da takardar da ta fad'i daga hannun ki, wanda na lura da ita tun lokacin da kika shigo d'akina. bud'e takardar nayi dan ganin meye a ciki abunda na gani ya daga mun hankali matu'ka saidai ni nasan wannan wani sharrin ne ake son laka mun wanda banji ba bangani ba,
Kuma a lokacin ne na fahimci akan takardar kika zo, saidai bansan dalilin da ya hanaki magana akan takardar ba,, dan haka na yanke nima bazan miki maganar ba sai ranar da yarinyar tasamu lafiya tayi mana bayani a kan iyayen ta,
Sai kuma gashi yadda abubuwa suka kasance,, ranar da ta yanka hannunta da kwalbar turare, na d'auka jinin ta nakai asibiti domin ayi awo a gano ko ina da wata nasaba da ita?
Bayan gojin Likita ya tabbatar min da babu wata ala'ka a tsakanina da ita,, nayi hamdalah a gun ubangiji.
Mika mata takardun yayi yace gashi ki duba ki gani idan baki yarda ba Sai mu koma asibiti anan kasar Kinga ma sunfi mu kayan aiki sai a sake gwajin...... Rukayya" wlh wlh wlh... bani da wata nasaba da wannan yarinyar, sharri ne kawai a keson laka mun wanda abun ya daure mun kai wanda da fari saida nasaka wa yarinyar idanu dan haka naji ban wani yarda da ita ba, dan ganin nakeyi kamar da ita akeson a had'a baki dan cuta ta, saidai zuwan mu gaban sheikh na yarda da cewa anyi amfani ne da rashin hnkalin yarinyar dan amun sharri... Wanda na rasa a duniya mai na tsarewa mutane duk tarin abunda sukai mun bai ishesu ba har sai sun had'a da bani Yar da ba tawa ba, wanda ganin fushin ki akan abun yasa na fahimci duk wanda yayi abun yayi ne dan ya had'ani da ke.
Amma wlh... Ina sake tabbatar miki wannan yarinyar ba jinjina ba ce..... Ko qu'ani zan iya d'auka in rantse miki matu'kar hakan zaisa ki ki gamsu.....
Rungume shi tayi tashiga rera kuka a hankali, tace na yarda dakai, kuma zuciya ta tasha fad'amun cewa bazaka aikata hakan ba, saidai narasa kwarin guiwar amin cewa da cewa sharri ne,
Kayi ha'kuri mijina" na zarge ka da laifin da ba naka ba.... ta sake fashewa da kuka, d'an bubbuga bayan ta yayi, kafun yace nasan mata ta, rudani ne ya shige ta, dan da wata ce to Lallai da sai tayi mun rashin da'a yadda kuke da kishin nan, nagode ma Allah da yayi ki da karfun yakar zuciya dan nsan kinsha artabu da zuciyar ki.... ya karasa fad'a da Murmushi....
Babu abunda zance sai Alhmdllh, Madallah da ke, Macce mai hankali"
Sake tura kanta tayi a 'kirjin sa tana yar dariya....
*******Lubabatu" ka kyautata wa mutum zato fa, to dan yana daga cikin cikar imanin mutum kyautata wa d'an uwan sa musulmi zato, cewar Hajiya mahaifiyar, ummi,
Wacce ummi takai mata kukan ta kan btason wannan auren da Rahamu ke shirin 'ka'kabawa zaid, dan sam hankalin ta bai kwanta dashi ba,
Ummi, tayi shiru.... Hajiya taci gaba da cewa, lubabatu dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kedai kiyi addu'a idan da alkhairee Allah ya tabbatar idan babu alkhairee Allah ya zabi abunda yafi alkhairee, babu wanda yasan mai ubangiji ya boye, kuma wannan ma zai iya shiga daga cikin mabud'an gaibi,
(Annabi Saw. Yace makullan gaibi guda biyar ne babu wanda yasansu face Allah.. 1babu wanda yasan me mahaifa ta 'boye 2babu wata rai da tasan mai za' a aikata da ita a gobe 3babu wata rai da tasan mai zata aikata a gobe 4babu wani d'aya da yasan yaushe za'a zubar da ruwan sama 5 babu wata rai da tasan a ina zata mutu bukhari/)
Dan haka dagani har ke bamu San mai zai faru da mu ba a ko wace safiya rana ko dare, dan haka zaidu ma bakisan mai Allah ya shirya wa rayuwar sa ba.
kuma Kisani babu abunda Rahamu ta isa taimasa wanda Allah bai masa ba wani lokacin was wasi daga shaid'an ne, dan Allah ki daina wani tunani mara kyau akan wannan al'amarin da kike zancen rashin tarbiyar yarinyar,
Ake ganin karuwa a gaban magajiya ma a auro bare wannan da kinsan uwar ta, kedai lubabatu kiyita addu'a kamar yadda na fad'a miki dan addu'a'o saiful, mumin.
Gwauron numfashi ummi"ta sauke, cike da Karayar zuci tace to hajiya insha'Allah.
******
Rahamu,, ta gama shirya komai da take kulawa, dan haka tace wa salma ta shirya zata je Ghana ta karbo mata sako,
salma bata kawo komai a ranta game da uwar ba ta hau shiri, ranar littinin ta d'au hanyar Ghana dake a jirgi ne, a ranar ta isa, tana zuwa tasamu taxi na jiran ta tana shiga aka bushe ta da cocaine, waya sukayi wa uwarta komai ya kammala, godiya tai musu had'i da tura musu, kud'in aikin su,
*******
Abba" ne a parln abu haula" bayan sun gama gaisawa yake tambayar sa jikin yarinyar, nan Abba yake sake fad'a masa yanzun matsalar su d'aya Sam yarinyar ko abinci bata ci idan ba mus"ab bane a guri...
Idan kuwa ta tashi bacci bata ganshi ba to babu Zaman lafiya,, gashi hutun su ya 'kare
Wani sati zasu koma Nigeria,,
Shiru sheikh yayi yana jinjina lamarin ubangiji,, shawara yashiga ba Abba"
Yace mai zai hana to ita ku barta nan a gun shi mus"ab d'in, in yaso sai ku d'aura musu aure gudun, barna,
Shiru Abba" yayi daga bisani yace,, aure fa sheikh"?
Gyada Kai sheikh d'in yayi yace to gani nayi kamar shi yafi alkhairee, ko da iyayenta sun bayyana dai baza su ce araba sunnah ba, ni a ganina shine abunda yafi, jinjina Kai Abba" yayi. Kafun yace shikenan hakan ma yayi, inaga idan munyi sallar azhar, yanzun sai a gabatar da d'aurin auren.
Boring chappy 🤐🏃🏃
********
Lots of love from zinnira 😘
Xinnee smart 💋💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro