20
Saida tayi wankan ta, ta kimtsa ta tabbatar duk inda Zaid"yake yana gida kafun ta fito ri'ke da kwallin ta na sa'a.
part d'in sa ta wuce Kai tsaye cikin sa'a taga kofar ma a bude da alamu ya dawo kenan yakeson koma fita. kwallin ta bud'e ta zizara ma idon ta, murmushi tayi kafun ta tura kofar d'akin ta shiga,, daidai yana shirin fitowa suka had'a ido wani juyawa kansa yayi... Ya d'an dafe gefe d'aya had'i da cewa washh". Kallon sa Rahamu tayi kafun tace, zauna magana zamuyi ai....
Babu musu yanema guri ya zauna, itama zama tayi a kan d'aya daga cikin kujerun paln, d'ora kafa d'aya kan d'aya tayi,, kafun ta zuba masa mugwayen idanuwan ta, sai da tayi nazarin sa dakyau, kafun tasoma magana.... Maganar mu ta baya ce ta kawo ni.
sunkuyar da kansa ya dad'a yi dan shikam yau baisan maike da mun shi ba Sam bayason had'a idanuwa da ita dan wani 'kwarjini take masa ga wani tsoron ta da wani 'bangare na zuciyar sa yakeyi!
ci gaba da magana tayi, wato maganar auren salma da nakeson kayi, bayan haka inason ka fad'amun yadda akayi kasan sirrina!
Shiru yayi yanason Musa mata kan zancen sa da salma saidai baisan mai yahau kansa ba Sam yakasa yi mata musu sai was wasi da zuciyarsa takeyi,
Kai nake saurare!
bashida zabi bayan accepting abunda tazo masa dashi dn idan yana matsawa da son nazari sai yaji kamar ana dukan kansa, dan haka kamar wani dolo yace babu komai mommy yadda kika ce haka za'ayi. ko yaushe kika shirya sai ayi auren saidai ina neman alfarmar in kammala karatu na.
Babu wani dogon tunani tace wannan ba wani abu bane za'ayi muku engagement,, so that idn ka gama sai ayi aurn dama dn kowa yasani ne Kaine mijin salma salma ce matarka, dan haka idan Dad d'in yadawo zamuyi magana dashi..
Sai magana ta gaba.... A ina kaji sirrina? Inason sani dan a wancan karon da kaga ban ce sai ka fad'a mun ba, dan nasan bazaka fad'amun bane amma yanzun nasan dole zaka fad'amun....
Da wani irin Murya yace... Ko yanzun bazan fad'a ba.
Saurin dubansa tayi, kafun tace bazaka fad'a ba?
Da daburcewa yace Eh gaskiya.
Shikenan! tace bayan ta tuno da zancen boka kan cewa banda takura wa dan matu'kar tana takura wa to fa zai shiga wasi wasi wanda Sam basa son sa a cikin aikinsu, sunfi son mutum yayi ta fama dolon sa.
Mikewa tayi ba tare da tace masa komai ba ta fice daga d'akin, tana zuwa bedroom d'in ta tayi wata yar siririyar gud'a,, ta zauna bakin gadon ta cike da farin ciki taci gaba da sa'ka yadda next move d'in ta zai kasance .
*****Koda su baby suka koma gida da 'kyar tabi Mami ita saidai tabi mus"ab... saida aka lallashe ta kafun ya haura sama d'akin sa...
Yana shiga yacire kaya ya fad'a wanka, yana fitowa pyjams d'insa yasaka ya fad'a gado, cikin shau'ki ya d'auka wayar sa, masoyiyar sa ya kira, tana d'auka yasauke sassanyar ajiyar zuciya... Kafun yace,
Favorite" ykk?
daga nata bangaren, amsawa tayi cikin siririyar muryar ta, da lafiya lau, ftn Kai ma haka?
yanzun ba! dan d'azun ba lafiya nake ba.
Sub"hanallah, mai yasame ka?
Hey" hold on... Garki mun kuka mana, ai yanzun naji sauqi, dama rashin jin muryar ki ne fa"sai kum...a...shiru yayi dan baisan ya zai bata labarin baby ba, katse masa tunanin tayi da cewa..
Sai kuma me?
Yar dariya yayi kafun yace.. Sai karatu da yayi yawa... Ni bnma tambaye ki ba ina ammin kuwa? Ya fad'a a ko'karin sa na kawar da wancan mganar dan yasan ta Sarai idn baiyi saurin d'auke mganar ba to ta dinga tambayar sa kenan.
Amsawa tayi da.. tana nan lafiya,
Yawwa, ki gaishe ta, bari inbar ki dan nasoma jin bacci..
OK Allah tashemu lfy,
I love you!
dariya tayi mai d'an sauti, Shima dariyar yayi, ya katse kiran shidai kunya da kawaicin favorite na mugun burgeshi Sam bata da rawar Kai kamar wasu matan.
gyara kwanciyar sa yayi da zummar ci gaba da tunanin masoyiyar tasa, sai dai me?
fuskar wannan yarinyar ce ta fad'a masa da yanayin, haukar ta dan shi kallon mahaukaciya tuburan yake mata, tsaki yasake, a ransa yana mai jin haushin ta.
A haka bacci yayi awon gaba da shi.
tunda safe Mami da ta tashi ba taga ummi ba tashiga neman ta, shiru shiru babu ita babu labarin ta,
a firgice ta fito daga d'akin takoma d'akin Abba", Abba ganin ta a firgice ne yasa yashiga tambayar ta ko lafiya,,
Abba" banga ummi ba fa!
Wace UMMIN?
Ummi dai wacce kasani, garin Yaya?
Nima naje d'aki ne ban same ta ba,
Da sauri yafita harabar gidan suka nufa, security suka shiga tambaya ko yagan ta, saidai cewa yayi babu wanda yafita daga gidan tun jiya da dare.
Hankali tashe suka koma cikin gidan, lungu da sako babu inda basu duba ba saidai babu ko alamu ta, hakan yasa, Mami hankalin ta ya Bala in tashi kardai aljanun ne suka d'auke ta.
Wayar mus"ab Abba" ya kira dan sanar dashi abunda ke faruwa, ringing d'in wayar Abba" yaji a kusa dasu dubansa yakai gurin mus"ab ya gani yana sakowa yayinda UMMIN ke biye dashi, a baya kamar jela...
Da sauri Mami ta karasa gurin ta, yata shine kika fita inata neman ki?
Murmushi baby tayi, tace naje gunsa ne mami, ta fad'a tana duban mus"ab da murmushi akan fuskar ta,, duk da irin rakwashin da tasha a hannun sa.
Rungume ta mami tayi.... to muje ayi brush, ayi breakfast ko? dariya tayi... Suka tafi.
Ko a gurin breakfast d'in, haka baby taita shigewa mus"ab shikam ko lokacin ta bai da, ganin idon iyayen sa ne ma yasa bai rarran kwashi kanta ba.
*****
Dad" yasaka cigiyar UMAIMAH, duk inda ya kamata tun lokacin da abun yafaru saidai shiru babu wani labari hakan yasa, ya hakura ya fawwala wa Allah" haka kuma kullum cikin rarrashin ummi"yake.
Yau ya dawo guda da wuri, dan haka yana shiga d'akin sa, yakira hajiya Rahamu"(uwar d'akin yan xinnee smart novel🤣😜).....
Minti goma sai gata ta shigo a 'kasaice... tana wani ji da kanta, mai aikinta na biye da ita da katon tray da aka jero abincin sa da yasha had'i da magungunan sa na yau da kullum, wanda da ace ciwo yake to insha'Allah da tuni ya warke saboda shan maganin kan'ka' Ida..... Saidai maganin na sharri ne wanda babu alkhairee a cikin sa.
mai aikin kam tana ajiye tray d'in kan dinning, ta fice kanta a kasa.
Zama Rahamu tayi a kusa dashi, tace Alhaji,, sannu da dawowa, y office d'in?
Alhmdllh ya fad'a yana duba abu a wayar sa,
To ga abinci can kan dinning idan ka shirya,
Tsaki yayi a ransa... Yace inda lubabatu tafita kenan da itace da yanzun, sai ta cire mun kaya tas tabani ruwan sanyi insha, ta had'a mun ruwan wanka, ta kaini dinning tayi serving d'ina abinci, amma ita wannan babu ko d'aya sai....... Maganar tace ta katse shi.
Idan baka tashi cin abincin bane akwai maganar da nake so muyi"
Shiru yayi,, daga bisani yace ina jinki!
dama akan maganar Zaid" da Salma" ne, bansani ba ko ya fad'a maka sun daidaita?
d'an jimmm" yayi kafun yace, ban fahimce ki ba,
To ina nufin Zaid yana son auren salma, kuma itama ta amince,,
Cike da mamaki yace shi zaidun ya fad'a miki?
A a a.... Ji Alhaji" da wani zance to karya zan maka?
A a ni bance karya bane Rahamu" kawai dai mamaki nakeyi yadda ni bai fad'a mun ba, sai inji a bakinki? to tunda bai fad'a maka ba ya fad'amun shikenan yayi laifi ko?
tana maganar ne tana dialing number Zaid d'in,
Yana d'auka tace kasame mu parln Alhaji"
Amsawa yayi da to.
Yana zuwa dad ya dubeshi bayan yaimasa sannu da dawowa,
da gaske ne abunda Rahamu"ta fad'amun cewa kana son salma?
Cikin damuwa yace hakane Dad"
Saidai da yake kansa a sunkuye yake basu lura da damuwar ba,
Shikenan Zaid Allah yatabbatar da alkhairee, amma karatun naka fa? Rahamu ce ta amshe da cewa ai ba yanzun za'ayi bikin ba,, sai ya gama karatun.
Gyad'a Kai dad yayi yace shikenan Jeka.. Allah yyi maka albarka!
Amin Zaid ya amsa, yana fita daga parln.
Nan Rahamu" akaci gaba da fele'ke da iyayi,, ana lissafe lissafen bikin da baiko zo ba,
Dad kam jinta kawai yake dan hakannan ya kejin hankalin sa bai kwanta da auren ba.
*********
Ban amince ba! Ummi"ta fad'a da hassalalliyar Murya, taci gaba da cewa akan me? wlh Sam Salma bata dace da Zaid ba,
Haba lubabatu, yanzun a gaban idona kike fad'ar wannan maganar,?
Alhaji saifa na fad'i gaskiya ta da ra'ayina, wlh ko me zaka ce kace... Amma muddin dai ina da rai to fa Zaid bazai auri Salma ba!
To ai Nima ba cewa nayi dole ya aure ta ba, ki saurara dan Allah" Zaid d'in ne fa ya fad'a mun yana son ta bayan na kira shi, amma ki Kira shi kiji,
Shiru tayi zuciyar ta babu dad'i, ita kam idan Zaid Zaiji maganar ta to fa bazai taba had'a zuri'a da Rahamu" ba, dan sam ba irin arziqi bace,,
Wayar ta ta d'auko takira Zaid d'in, cikin ladabi ya gaishe ta, bayan sun gama gaisawa, take tambayar sa game da abunda taji" tabba mata yayi da hakan,
A sanyaye tace to Kai Zaid kanason ta ne?
Cikin d'an jin nauyi yace,, kawai Ummi"inaji idan ban aure ta ba mutuwa zanyi!
Bugawa kirjin ta yayi a ranta tashiga jero Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un!
Mai yarage tace? Babu! Zuciyar ta tabata amsa.
Shikenan Allah ysanya alkhairee,, kawar da fuska tayi, wasu irin hawaye ne suka sako mata,
Yaushe ne Rahamu" zata barta ta zauna lafiya? Yaushe ne zata bar duk wanda ya rabeta ya zauna lafiya?
Azza' nnu zambun" saidai ko rantsuwa tayi baza tayi kaffara ba,, wannan yana daga cikin muna kisoshin Rahamu a kanta da alhalin ta, Kai harma da wanda ya rabeta!
Dad ganin halin da take ciki sai yaji duk ta bashi tausayi, baisan mai zai ce ba dan Haka kawai sai ya rungume ta,
tana jin ta a jikinsa ta sauke wata irin ajiyar zuciya mai tafe da hawaye.
******
Sosai su Rahamu ake ta faman shiri dan baikon Yar ta,,
A bangaren salma abun yafi tsauri dan sosai suke shirya party na kece raini ita da, kawar ta zeema,,
a cewar su dole a rakadhr dn sunan bikin bikin Yar gata Yr guda guda a gun uwar ta.
bangare d'aya bangis na shirin cin uban salma,, dan sam bata fad'a masa ba a gun zeema yaji,
Makashin ka yana tare da kai abunda salma bata sani ba, auren nan da zatayi ba karamun hassada yasawa zeema ba, dan ita yanzun burinta d'aya ta janyo abunda zaisa a fasa auren, ko da bala'i.
Lots of love 😘
Xinnee smart 👌💋
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro