2
'karfe 4na yamma suka iso gidan Alhaji Tahir yuguda"dake unguwar wise2 Abuja Nigeria. wangale musu gate d'in gidan akayi,, parking Bala yayi a parking lot,, bud'ewa Hajiya Rahamu,, kofa yayi jikinsa na wani irin rawa dan sosai yake tsoronta dan duk wanda ya kwana yatashi a gidan to fa yasan hajiya Rahamu gurin shinfid'a mulki,, isa da gadara wanda..... Babu wanda ya isa yake tare umarnin ta Koda kuwa mai gidan ne,, shi yasa Kowwa yake kaffa kaffa da ita.... Idan bata nan kuwa tamkar anyi wa gidan bushara duk ma'aikatan gidan sun samu freedom kenan,, da Zarar ta dawo kuwa... tofa shikenan sunkoma zamn makoki.
Cike da isa da gadara,, tafito daga cikin motar,, tana cika tana batsewa,, wata matashiyar budurwa ce tafito itama sai wani fizgar kai takeyi,, kallon Bala tayi a wula'kance tace... Ka kwaso mana kayan mu.. Amsawa yyi da to jiki na bari,, su kuwa gaba sukayi zuwa part d'in Rahamu,,
*****
Hajiya lubabatu nasamun labarin isowarsu tasaka uwani ta Deba abincin su takai musu,, cike da farga ba tashiga palon samu tayi babu kowa dan haka ta sauke ajiyar zuciya Kai kayan tayi kan dining ta ajiye ta fita,, tana ganin kanta a waje lami lafiya ta sauke ajiyar zuciya had'i da fad'in Alhmdllh a sarari!
Hajiya lubabatu bayan tayi sallar la'asar ta tabbatar da, yanzun sun d'an huta tasaka hijab d'inta tanufi part d'inta dan fita hakkinta Koda dai Annabi (SAW) cewa yayi mai tafiya ya gaida na zaune,, ita ta amince taje Tai mata sannu dan tasan idan ta Rahamu ne Kowwa yayi harkar gabansa ita kuwa baza ta iya Zaman gaba ba,, shi yasa duk inda suka had'u takanyi mata magana Koda bazata amsa ba,,, takance rayuwar duka nawa ce da kishi zaisa kayiwa kanka dakon shiga wuta?
Sallama tayi a palon ba a amsa ba dan haka tashiga da niyyar ta sake rafka wata idanma suna ciki ne su jiyo ta,,. Saidai ga mamakinta.... Salma tagani Yar Hajiya Rahamun.. dubanta tayi taga sai faman dannar wayarta take ko a jikinta,, danne damuwarta tayi kafun tace.... Salma... Bakiji ina sallama bane? cikin gwatsine da sakarci tace.... Naji mana... Shine kika kasa amsawa? Kinsan ladar sallama da amsata kuwa?
Mtssss.... Ke fa hajiyar nan kincika takura daga zuwa na zaki wani fara damuna da surutu kuma ma gani nayi ai dai d'akin mahaifiya ta ne.... ko ban amsa ba babu ruwanki..... Saki baki ummi tayi tana kallonta,, a ranta tace tirkashi... A Zahiri kuwa cewa tayi Allah ya kyauta... Ina mommyn ki?
bata amsa mata ba cikin sa'a kuma sai ga hajiya Rahamun nan tafito,, tana ganin ummi ta wani tabe baki irin kinji dashi d'inan.
Hajiya Rahamu sannu da zuwa..... Ummi tafad'a cike da karfin Hali,, a da'kile ta amsa da lafiya Kuna lfy?
fuska a sake ummi ta amsa da lafiya lau Alhmdllh.
daga haka gurin tad'auka shiru,, dan haka tasaka Kai zata fita tana cewa Allah ya hutar da gajiya,, ko amsawa basuyi ba suka vita da mugun kallo musamman ma mommy,, dan ji tayi tamkar ta janyo lubabatu ta shake ta har lahira saidai babu yadda ta iya,, dan boka yace mata akwai lokaci kuma dama ita bataso tai mata kisan wuri tafison sai ta d'an ji a jikinta kafun kuma daga dukkanin alamu bata cikin walwalarta dama abunda take bukata kenan..... ta ganta a damuwa wahala ciwon rai kuma ga alamun nasara..... Wani irin shu "umin murmushi tasaki. had'i da jin ita d'in wata ce.
********
Alhaji Tahir yuguda! Shine asalin cikakken sunansa haifaffen garin yuguda ne kuma bafulatani,, inda yawon biggali yakai iyayensa wani kauye kusa da Abuja ana kiran kauyen ruggar mai danmma. Anan ya rayu da iyayensa kasancewar shine kawai d'ansu,, wata rana masu satar shanu suka shigo rugar inda duk wanda yafito ko zai kawo musu gardama saidai su kashe shi cikin rashin sa a mahaifinsa Umar yuguda yayi ja yayya dasu take suka kashe shi babu imani ko tausayi.
Da gari ya waye gari tad'auka koke koke,, tsabar bakin ciki da yai wa uwarsa Hari katutu yasa take ta yanke jiki ta fad'i,, itama anan tace ga garinku.
Tundaga nan rayuwar Tahir tashiga garari,, wata rana yafito cikin garin Abuja dan a lokacin yanada shekaru 18 a duniya,
cike da rashin makama dan tunda iyayensa suka rasu yake zaune a gidan ard'o,, ganin soyayyr da ard'o yake masa yasa yayansa suka fara hassada dashi shi yasa ya yanke shawarar fita neman kud'i..... Ko ard'o bai fad'awa ba yakamo hanyar Abuja.... Tundaga ruggar mai danmma.... Allah ya had'a shi da mahaifin lubabatu Alhaji Garba da magaran... A lokacin yazo kawo wasu fatoci ne na harkar kasuwa cin sa.
Allah ya had'a su,, bayan yaji labarin sa ya tausaya masa dan shi mutum ne mai son taimako da tausayin marasa karfi shi yasa ko a garinsu ake mutunta shi, har yatafi dashi Niger, da magaran! Makaranta yasaka Tahir,, Alhaji Umar yanada mata d'aya zainab wacce yayanta ke Kira da momma. Momma mace ce mai saukin Kai da sanyin Hali shi yasa Koda mijinta yayimata bayanin Tahir, ta amince da yazauna tare dasu.
Alhaji Umar yana da Yara guda biyar,, Ayuba Kamal fauziyya nura da kuma lubabatu wacce itace karama a cikinsu.
Karatu sosai,, Tahir yayi da taimakon Allah dana Alhaji Umar,, ya kammallah jami'a a harkar kasuwanci tun kafun sakamako yafito yasoma bin Alhaji kasa kasa gurin harkar kasuwancin sa na saida fatoci. A lokacin lubabatu tana ss2 soyayya ya kullu tsakaninta da Tahir sosai suke son junansu,, har iyaye suka fahimci haka dama yayyinta duk sunyi aure nura ne kawai baiyi auren ba.... Sosai Alhaji Umar yayi farincikin abun a take aka soma shiri kan tana gama jarabawar fita Za ai auren..... Aikuwa tana gamawa aka d'aura musu aure aka kaita gidan da yabasu dan su zauna anan cikin garin da magaran, rayuwarsu gwanin sha"awa sosai suke nuna wa juna soyy,, a haka har Tahir ya rike kasuwancin kansa Shima dai harkar fatar ce,, daga baya zamansu yakoma Abuja inda yasamu kud'i sosai yagina tamfatsetsen gida suka koma,,
Babu ce kawai babu a gidan shekarar su uku da aure suka Haifa d'ansu kyakyawa dashi aka saka masa Umar suna kiransa khaleefa........ Tundaga nan bata sake haihuwa ba.... Har khaleefa yashiga jami'a.... A lokacin ne yasake samun kud'i sosai ya Gina wani katafaren shoopin mall.
Dama yana yawan zuwa gana to idan yaje akwai gidan abincin da yake cin abinci,, a gurin akwai wata mata Rahamu... da take aiki a gurin tunda taganshi ta addabi kanta kan sonsa Shikuwa dayake ba mutum bne mai hayaniya saidai yace mata kiyi ha'kuri banida ra'ayin Kara aure mata ta ta isheni. Kullum haka yake Gaya mata hardai yagaji da nacin ta yadaina zuwa gurin cin abinci.
Aikuwa sosai hankalin Rahamu yatashi,, nan tashiga tafita har tasamu Bokan da yanemo mata soyayyar Tahir,, take akayi komai na aure dan dama Rahamu bazawara ce ta taba aure suka rabu da mijin dan a cewarta talaka ne shi bashida arziqin da zata iya ci gaba da zama dashi ta gaji ya d'aya ta Haifa tare dashi...
Bayan boka yagama gindaya mata sharadi ta amince akan cewa bazata ta'ba haihuwa da Tahir ba kuma ta amince da hakan dan idonta yariga da ya rufe a kansa...
Lokacin da lubabatu tasamu labarin auren dazai Kara sosai hankalinta yatashi dan haka kawai taji tamkar auren nasa shine karshen farincikin ta. neman izinin zuwa Niger tayin Yakuma amince mata... bayani taiwa mahaifiyar ta inda tabata shawarwarin 'kwarai satinta 2ta dawo... ta dangana tabarwa Allah ikonsa,, lokacin ne Khaleefa yanemi izinin fita waje domin sake gogewa a harkar karatunsa wanda dama engineering ya karanta.... Kasancewar hankalin Alhaji Tahir yana kan aurensa shi yasa bai wani damu ba ya bashi izinin tafiya yayinda umminsa Sam bataso hakan ba'saidai babu yadda ta iya tunda yanuna yanaso kuma mahaifinsa ya amince masa sai kawai takawo idanuwa tasaka musu. da yatashi tafiya taimasa fatan alkhairee.
Bayan aurensa da Rahamu"ya wuto da ita Nigeria,, tunda Rahamu tazo gidan tadauki gabar duniya da lubabatu wanda idan Alhaji yanan bata yi saidai idan taga baya nan,, tadinga jangwalo fitina kenan duk da ba side d'insu d'aya ba ko wacce da part d'inta Kasancewar gidan irin tafkeken mantion d'inan ne.
Ko wacce da masu yi mata hidima saidai hakan bai hana Rahamu takura wa masu aikin lubabatu ba, zamane akeyi kadaran kadahan....
Shekarar Khaleefa d'aya da tafiya.,, ciki ya bayyana a jikin lubabatu,,, tayi hamdala agun Allah babu a dadi, haka Shima mai gidan sosai yayiwa Allah godiya da wannan kyautar,,
Sa'banin Rahamu"da sosai wannan karuwar tai mata zafi dan sosai ta tsani cikin jikin lubabatu tun kafun yazo duniya sau biyu tana attempting dukanta saidai ita lubabatun ce take hana hakan faruwa tunda tagano cikin take wa bakin ciki sai ko hango ta ta kan hanya Sam bata bi saidai ta canza tata, dan ita kam sosai take kaunar cikinta bata neman abunda zai yasamu matsala. Niger ma sosai sukayi murna da samun cikin......
Ranar da nakuda ta kamata Allah yasauke ta lafiya ta haifa yarta mace kyakyawa da ita sosai ta sake nuna godiyarta ga Allah,, ranar suna yarinya taci suna UMAIMAH! tunda UMAIMAH tazo duniya take shan gata iri iri komai Dad yagani siyo mata yakeyi babu abunda ba a tanada a d'akin da aka ware mata wanda yadanganci kayan wasa ba,, UMAIMAH ta tashi yarinya mai shiga rai gata lukui lukui kamar Yar larabawa... Gwanin sha"awa da ita, iyayenta da kakkaninta sosai suke 'kaunarta. Rahamu kam tuni tacika duniyar ta da muguwar kiyayyar yarinyar musamman dataga yadda Allah ymata baiwar kyau ga soyayyah both side uwa da uba,, UMAIMAH nada wata shida a duniya khaleefa yazo Nigeria,, dama yana ganin pictures d'in UMAIMAH da kuma videos d'in ta da dad ke tura masa, dan haka Koda yaganta yasake jin kaunarta ta sake shiharsa d'an uwa kenan kullum UMAIMAH tana gunsa saidai idan zata sha nono ne kawai yake kaita sai kuma kwanciyar bacci sosai yake kaunar kanwar tasa,, saida yayi wata d'aya kafun yakoma cike da kewar UMAIMAH!
Saida yayi shekara biyu kafun yazo lokacin UMAIMAH tanada shekaru biyu,, da watanni itama,, yana ganinta ya Cilla ta sama yace.... Baby... Aikuwa ta wangale masa baki itama kamar ta ganeshi,, lokacin da yake sanar dasu dad cewa yagama course d'in da yaje yi ba karamun farinciki sukayi ba saidai bayaninsa na karshe ya jefasu a cikin rudani dan kuwa cewa yayi yasamu mata acan kasar Mexico dan haka nema yazo ya fad'a musu idan yakoma Za a d'aura aurensu,, sosai ran iyayensa ya baci musamman ma ummi...... anan Dad yakada baki yace... ai na rigada namaka mata,, a tare suka kalleshi... jin Jina Kai yayi yace kwarai kuwa nayi masa mata.... Salma ita zan aura masa dan haka ku fara shiri..... a take ran ummi yabaci domin kuwa duk uwa ta gari tanaso d'an ta ace yau auri abun arziqi,, itakam Sam salma bata mata a matsayin suruka ba yarinyar da Sam bata ganinta da kima.... Saidai kuma bata isa tanuna hakan ba,, kuma bazata iya bari d'an ta ya auri mace kamar salma ba.......
.. shikam khaleefa kasa boye bacin ransa yayi yashiga cewa... a gskiya Dad banason salma dan halayyarta batamun ba... Tsawa dad d'in yadaka masa,, ohh mai Jan kunni ce waton tarbiyyarta taimaka ko? to idan dai nine mahaifinka Bakada mata sai salma dan gwara ita da ka fira, wlh dad ba kafira bace asalin yan Sudan ne,, kuma muslmai ne,,... Kaga dakata nrigada nagama magana.... Ya karasa fad'a had'i da karkade rigarsa yabar... palon,, wata irin damuwa ce tacika zuciyar khaleefa,, ummi ma haka amma ganin halinda yake ciki ne yasa ta dubeshi baba na... Bai amsa ba Sai dubanta da yayi, a sanyaye tashiga cewa"kayi ha'kuri ka auri zabin mahaifinka.... wani irin duba yayimata... haba ummi da bakinki kike ce wa in auri yarinyar da kinsan wacece ita a matsayin ki na uwa? Zan iya yiwa dad uzuri akan shi ba zama yakeyi a gida ba wata kila baisan wacece salma ba.... Yarinyar da a gabana tasha rungumar maza,, wacce bata daraja ni bare mahaifiyata wlh da na auri salma gwara inmutu banyi aure ba.... Ya karasa fad'a yana fidda huci mai zafi. rarrashin sa ummi tashiga yi had'i da bashi shawarwari,, kasancewar dare yayi sosai yasa tace yaje ya kwanta..... Yana zuwa d'aki yadannawa abokinsa waya wanda yake yana aiki ne a airport.
Ummi kam batayi baccin arziki ba
, har garin Allah ya waye,, har gurin 11 bataga khaleefa ba take hankalinta yatashi,, part d'in sa taje babu shi babu alamun sa nan tashiga tashin hankali,, bayan takoma ta xauna ne taji shigowar sako..... Koda ta duba tabbatar mata yake da yakoma inda yafito domin idan aka aura masa salma zai iya kashe d'aya a cikinsu shi ko ita, shi yasa yakoma ta gafarce shi,,,
Hankalinta ba karamun tashi yayi ba Koda Alhaji yadawo ta tarbeshi da zancen sai cewa yayi yafi ruwa gudu duk sanda yadawo ba shida mata sai salma! hankalin ummi ne yasake tashi d al'amuran Alhaji a kwanakin Sam bashida sau'ki kiris yake jira,, dan haka ma tafita harkar sa d'an ta kuwa yakan kirata, shi yasa ma hankalinta yadan kwanta.
******
Rahamu"ce durkushe a gaban bokanta can wani kauyen Ghana. Kallonta yayi tsawon mintina bayan tagama yi Masa bayanin yadda takeso ayi da matsalar ta.
Magana yashiga yi kamar haka... Yarinyar bazata mutu ba domin mutuwar ta a halin yanzun ba ganshi a hannun mu ba,, haka Shima yaron Lallai sai ya auri waccan yarinyar Koda zai auri yarki.... Shiru tayi kafun tace to meye mafita yanzun? sake duba ruwansa dake cikin kwarya yayi kafun yace... Abu d'aya ne zan iya tura mata aljani ya maida ta wata aba daban,, gata da rai saidai babu hnkali..,, kuma hakan shi zai d'auki hankalin iyayenta, musamman mahaifiyarta zata shiga damuwa da kunci, sai shikuma yaron za'a iya sake nsanta shi da iyayensa ta yadda zasu cire sa a ransu Shima haka zaici gaba da zama a inda yake,, haka ma yayi boka.... Saidai da sharadi!
Meye shara d'in? Shara d'in shine kar asake namiji yasadu da ita matukar namiji yasadu da ita tofa aiki ya lalace!
Cike da rashin fargaba tace na amince,, dan nasan babu namijin da zaiso musaka ta fad'a a ranta,, take akayi komai ya sallame ta.
Wannan shine dalilin asalin ciwon UMAIMAH,, wacce iyayenta ke kira da baby kasancewar khaleefa ne yasanya mata babyn sai yabita Kowwa baby har mantawa wasu suke da sunanta UMAIMAH"
Tun daga ranar tasoma yin abubuwa,,, sai tadinga ihhu tana canzgan gashi kanta a lokacin tanada shekaru uku ne kawai a duniya,, kanta yadaina tsayuwa,, haka magana ma d'ib ta d'auke.... Goshinta kuwa kullum cikin rauni yake..... Anyi yawon asibiti da ita har angode Allah,, idan lubabatu tayi zancen zuwa gun malamai sai yace wai bai amince ba, wanda Rahamu ce ta kitsa masa hakan.
Akwai lokacin da mahaifin lubabatun yayi shirin kaita kasar saudiya.... Rahamu tashiga ta fita ta lalata tafiyar tun daga lokacin ta rufewa kowa baki akan nemawa baby lafiya....sai lubabatu ne idan abun ya ciwo ta takan ta magana saidai itama bata iya tabuka komai abun Yna matuqar damunta.
Khaleefa kuwa sai karkashin zuciyarta ne kawai take jinsa,, yayinda shikam dad Yama manta da yanada wani d'a.
Wannan shine ASALIN labarin Alhaji Tahir da iyalansa....
Muje zuwa ✌️😂
Xinnee smart 💕💋👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro