18
... misalin 'karfe 1pm Shago"da yaransa suka shigo gidan bayan Rahamu ta bud'e musu'kofa,,
side d'in Zaid suka nufa cikin iya sad'ad'e sak mara sa gaskiya" wani yaron shago wanda ake Kira fele, shine ya sa'ba Zaid a wuyan sa har cikin mota yakai shi sauran suka rufa masa baya nan suka ja motar su,
Nannauyan ajiyar zuciya hajiya Rahamu" ta sauke ganin komai yatafi successfully"
Tana shiga d'akin ta ta Kira boka ta fad'a masa tasa a d'auke Zaid,, dariya yayi kafun yace... ayi ko'karin ganin baiyi sallah ba na tsawon kwana 3" ta yadda idan akayi tsafin a jikin sa zai zaunu da kyau dan rashin yin sallarsa na tsawon wayannan kwanakin shi zai karawa tsafin karfi,, ko yayi sallah tsafin zai yu saidai rashin sallah zaisa yayi karfin da bama tunani, dan haka ki tabbatar da abunda na fad'a miki yana kaiwa nan ya kashe wayar sa.
Dariya tayi... Zaid sai yadda Rahamu"ta juya ka...
****
Zaman UMAIMAH" da sabbin iyayenta zama ne na walwala bbu takura sai tsantsar tausayin ta da suke ji,, bata da matsala da kowa face wannan d'an nasu wanda idan a gaban iyayen sa ne sai yayi ta treating d'in ta kamar kanwar sa, amma a bayan su ya dinga hararar ta kenan,, dan shi hakannan kawai baya son yarinyar wanda baisan dalili ba, ita kuwa kullum cikin makale masa take duk da irin yadda yake hantarar ta, saidai Sam hakan bai wani yi tasiri ba a gun baby,, kullum cikin dokin ganin sa take tamkar wacce tasaba dashi ko dama can tasan shi, idan zai fita schl kuwa ta dinga rigima kenan da kyar ake rarrashin ta,,
Ranar da suka samu ganin 'kwararren likitan kwakwalwa,, duba d'aya yayi mata yafa himci akwai sammu a jikin ta ba tabin hankali ne na asibiti ba, kasance war sa malami bawai likita kawai ba.
kiran Abba yayi ya masa bayani kan abunda ya fahimta game da yarsa,, sosai hankalin Abba ya dugun tsuma cike da tausayin yarinyar... Shikam mutanen duniya na bashi tausayi da tsoro yanzun wannan Yar yarinyar ko mai tayi wa mutane da har Za ai mata wannan mugun shirin? Allah masani.... Wannan shine amsar da tazo masa"
an yanke kan za'a soma yiwa baby( wacce yanzun takoma Rukayya" saboda Abba yace Za a dinga kiran ta da wani sunan kafun su San sunan ta shine yasaka mata Rukayya" sai yake ce mata ummi")
Magungunan musulunci, wanda sunnah ta amince dashi,..
*****Shago"..... Haka mukayi dakai? Idan bazaka iya wannan aikin ba ai kasanar dani in nemi wani... Kinga hajiya jameela... wlh har da tawa idea na 'Kara dan insamu banzar matar ta fita amma bansan ya akayi ba, cikin takaici hajiya jameela tace to satin can ya kirani wai zasu Saudia'"ni da naji kiran ma na zata fad'a mun zaiyi sun rabu da Rukayya" sai kuma naji sabani haka wlh ji nayi kamar in mutu...
Ta dafe Kai cike da bacin rai.
Shago ya sassauta Murya" dan bayason jameela ta daina aiki dashi dan yana matu'kar ta tsa a gurin ta, yace hajiya kiyi ha'kuri idan suka dawo nayi miki al'kawarin wannan karon baza'a sa'ba ba Kai ko bata fita gidan ba Sai in kashe ta, inyaso sai muji da d'an ta,, Kitt hajiya jameela ta kashe wayar ta ta dafe Kai.... Wai sai yaushe ne zata yi nasarar mallake dukkan arziqin yayan ta? Yaushe ne zatayi nasara akan Rukayya" da ahalin ta?
Wannan burin ta Jima dashi tabbas idan burin ta bai cika ba a wannan karon bata kuma San mai zatayi ba.
****ummi" ce zaune a parlour, damuwa ce kwance a kan fuskar ta, to ina Zaid" yashiga? Kar dai Zaid neman baby yaje da gaske? Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un" ya Allah ka kawo mana mafita, mai yasa Zaid zaiyi mata haka? Cikin damuwa takira dad"bugu d'aya biyu ya daga, da sallama... Amsawa tayi kafun tashiga cewa... Alhaji Zaid da gaske neman baby ya je.... ta karasa fad'a da muryar tausayi, cikin damuwa yace.. Kinga ki kwantar da hankalin ki lubabatu" nasan duk inda Zaid yaje insha'Allah wataran zai dawo,
Cikin damuwa tace Allah yasa... Amsawa yayi da amin, ftn zaki kula da kanki kafun indawo? Insha'Allah, a dawo lafiya Allah yabada sa'a. Amin ya amsa, dukan su kashe waya sukayi kowa da damuwa a zuciyar sa.
****lokacin da Zaid ya farko yashiga karewa d'akin da yake ciki kallo d'akin tamkar kango, gashi duk anbi an daddaure shi a had'a da kujerar da yake Kai, salati da hailala yashiga yi, kansa na wani irin juyi,, tsabar yadda yake ji ji yake tamkar an d'auko katon dutsi an d'ora masa a Kai.. Wani gabjejen Kato yagani yazo kusa dashi ya d'ago da ha'barsa, saida ya kare masa kallo tsaf kafun ya yanka masa Marin da yasake jagula d'an ganin da yakeyi,
Sharaf yasaka masa fuska takoma ta langwa'be, a wahalce yashiga cewa mai nayi muku? Su waye... ye.. k..u?
Au tambaya ma kake? dan uwarka? cewar wani daban ba wanda ya dake shi ba... Wanda ya mare shin ne yace barshi mango zan bashi amsa yanzun kuwa, ya 'karasa fad'a yana kaiwa sigarin sa kyakyawan zu'ka, ya fesar da ita kan fuskar zai kafun ya Kai masa mugun sha'ka, yasoma jibgarsa kamar Allah y aiko shi... Bawan Allah Zaid" sai ihu yake zuba wa, wanda muryar tuni ta dishe fele bai daina dukan Zaid"ba saida yaga baya motsi kafun ya 'kyale shi...
Kaga d'an durin uwa da ba tambaya kake ba? to ga amsa an baka. ya fad'a yana zama kan wani dutse dake gurin... Mango" yakira mango dake kofar d'akin, amsawa yayi... debo ruwa a bokiti ka she'ka wa shege ko ya farfado.. ni dama dukan d'aukar da nai masa ne na d'an 'barje..
dariya mango ya'ba'b'baka.... Kai fa fele mugu ne..... Hhhhhhhhhh suka sake fashewa da dariya yayinda fele ke sake cewa Eh billahillazi to ni mugu ne suka sake saka dariya.
****kwana goma kenan da fara yiwa baby magani cikin ikon Allah sai tasoma mugayen mafarki ana cewa ta gudu.. Ko kuma a mafarkin sai ta d'ebo abu a cup zata sha kawai sai a barar. gefe d'aya ga mus"ab da kullum take mafarkin sa,, wai yana ce mata ina tashiga yake ta neman ta?
a cikin baccin bakinta yasoma bud'ewa.... da magana... Mami na ji ta Godewa Allah da hasken da ake ganina cikin al'amarin..
Sunkoma gun sheikh nasirufeen"abu Haula"wanda doctor Ilyas ne ya had'a su da shi...
Mami ce tayi masa bayanin ci gaban da ake samu da kuma yawan mafarki musamman na ban tsoro da take,, duban baby yayi yace.. Rukayya" mai kike gani a mafarkin ki?
a mamakin su Mami sai su kaji tana bayani tiryan tiryan,, duk irin razana ta da ake da komai,, tana gama bayani yace Alhmdllh Allah shine abun godiya, ga dukkan alamu sau'ki yana samuwa yanzun insha'Allah za'ayi mata ruq'ya, wanda idan ma da aljanu a jikin ta, zamu iya mu sani.... Abba yace to malam,, duk maganar da suke sunayi ne da harshen turanci dan bancin mus"ab dukan su babu mai jin larabci,
Nan yace a shigar da Mami cikin gida gurin iyalin shi,, a take yasoma ai watar da ruq'ya, yayi tsawon minti talatin yana karatun sai dai ko gyizau batayi ba,, har yafara tunanin ko babu aljanun..... Can ta zabga wani irin ihuuu....
Ahhhhhhhhhhhhh"" hhhhhhhhh ka..... Ka.... Ka...... Kadaina..... Qonani.........yashiga roko yayi da yaren Ghana yayi da hausa yayi da turanci yayi da larabci..... Malamin najin yayi da larabci, yashiga masa magana
Waye? Kuma mai yakawo ka jikin wannan baiwar Allah? Mai taimaka?
Hhhhh.... Hhh.. Bah... Bah.. Babu ruwan ka". Bai shafeka ba aiki na nakeyi.... Ni...
Ohh aikin ka kakeyi ko? to kuwa yanzun zan qarar da kai da aikin naka da ayar Allah..
Yaci gaba da karatun,, da suratul mulkh!
...... Hhhhaa dan Allah kadaina banasooooooo.....
A a kam kana so tunda kaki fad'amun gaskiya..... Amma naji ka ambaci Allah, Kai nan kasan Allah?
Malam ni musulmi ne... Qarya kake Kai ba musulmi bane, domin musulunci Zaman Lafiya da lumana ne had'i da tausayi... Wannan shine islam, haka kuma wanda yayi ni yayi ka yayi wannan baiwar Allah kuma mai misuluncin ya qyqmaci zalunci dominate shi ba azzalumi ba ne,, hakan kuma yayi hani da cuta da cutarwa,
Danmi zaka cemun Kai musulmi ne?
Wannan ba dabi'a bace ta musulmin kirki"
Ahhhhh.... Ni... Ni.. Ma sakani akayi bani bane turoni akayi... Kuma wanda ya turoni yace idn na tona asirin sa sai ya kashe ni kayi ha'kuri zan fita jikin ta zan Nisan ce ta.... Bazan sake kusan tar ta ba idan na sake ka Qonani.........
Kafun sheikh yace komai yaji baby na ta jero atisha wa, a wahalce ta zube gurin tana raba ido,, Abba" dake gefe yashiga yiwa Allah godiya, had'i da jinjina wa sheikh d'in domin malami ne na sunayi wanda yasha sunnah yagaji,,kuma ya kware kan aikin shi.
Sheikh waya yayi cikin gida, take wata yarsa ta shigo, sanye take da jallabiyya,, har qasa kafafun ta da safa fuskar ta ce kawai a bude, ko ina kipp...
Sallama tayi ta gaishe da Abba" amsawa yayi dan kuwa yasan gaisuwa,
Gaban mahaifin nata taje tace gata, nan yace mata ta taimakawa baby ta shigar da ita gida, amsawa tayi da to....kafun ta nufi gun baby dake zube,, taimaka mata tayi suka shiga gida d'akin su tanufa da ita, mahaifiyar ta ce takira ta tace takawo ta d'akin ta,
Kan gadon UMMIN nasu ta taimaka mata ta kwanta,, lumshe ido tashiga yi Mami ta zuba mata ido,, daga bisani bacci yayi awon gaba da ita.
Ajiyar zuciya Mami ta sauke a ranta tashiga zancen zuci,, yanzun ai yarinya ta warke yanzun ne daidai yin zancen had'in Alhaji da ita wannan ma dole ne.
******
Yau ce ranar da za'a tafi da Zaid"zuwa Ghana, dan haka suka shashaqa masa abun saka bacci, tuni ya bingire,, jirgin 'kasa suka bi dan zuwa Ghana, hajiya Rahamu dama tun asuba tabi jirgi,,
Ummi jiki ya Kiya,, kullum cikin ciwo take wanda Dad yanzun Sam hankalin sa baya jikin sa,, dan haka ne ma ya d'auke ta ya mayar da ita Niger, mahaifiyar ta sosai taji dad'in haka dan a cewar ta ai harda kad'aici ai ya dame ta.
Cikin ikon Allah Zaman ta a Niger d'in sai tasoma samun sauqi, hakan yasa dad yabarta a nan dan yaga hankalin ta zaifi kwanciya a nan d'in.
****ranar da suka isa Ghana gaba d'aya Zaid yafita a hayyacin sa duk yayi wani iri dashi saboda abun baccin da suke yawan fesa mishi idanuwan sa kuwa sunyi wani luhu luhu dasu....
Kai tsaye qauyen da boka yake suka nufa dashi, kallo d'aya boka yayi masa yaji gaban sa ya fad'i... Saidai da yake mugun mushiriki ne baiko ji d'ar ba.
Nan yasa aka kwantar da Zaid Saman wata tabarma wacce take kamar da fatar dabba akayi ta wanda kafun ma a kwantar dashi saida ya yayyafa wani ruwa a kanta, ana kwantar da shi yasoma zuba surkulle a kansa wanda Zaid d'in idonsa biyu a lokacin haka kuma yana jin zantukan saidai baya tantance mai ake cewa ne haka kuma yana ganin mutane a kansa bazai ce dai suwaye ba saboda galabaita da yayi ga yunwa... ga kishi ga wahala da yasha a gun su fele.
Boka saida ya zagaya Zaid sau goma sha biyu kafun yayi wasu surkulle ya daga hannunsa sama kaza ta fad'o.. Salma dake kusa da uwarta ta saida ta razana yanke kazar nan yayi ya zuba jinin ta a wata qwarya,, ya yanki hannun Zaid ya tarara jinin a cikin na kaza...
Ya baiwa Rahamu" yace ta sha babu gardama ta karba ta shanye,, harda lashe baki......ihhhhhuuu boka yayi yashiga cewa Rahamu kinsamu duniya.... Rahamu kinsamu duniya... Rahamu kinsamu duniya kinsamu Zaid a tafin hannunki sai yadda kika ce.... Hhhhaaaaahhhhhaaaaa suka she'ke da dariya har saida Zaid d'in yaji kansa na jujjuya wa,, take kuma Rahamu tasoma kakarin amai..,
I know there is a lot of errors... Bnsamu nayi editing ba so u guys should manage 😖
Xinnee smart 👌😘💋💕✌️
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro