Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

15

       Sintiri hajiya Rukayya"tashiga yi cike da tsantsar damuwa da fargabar abunda tagani a takardar, Ha'ki'ka ta yarda da mijin ta yarda ba ta wasa ba. Amma kuma wannan zantukan sun rud'a ta had'i da shaid'an da ya kanainaye ta tabbas tana bu'katar sanin gaskiya cikin gaggawa, domin zuwa ko wani lokaci zuciyarta zata iya bugawa.

da hanzari tanufa side d'in Alhajin dan gwara tasan maike faruwa tun wuri kafun zuciyarta tagama yanke hukunci.

Assalamu"alaikum" hajiya Rukayya tayi sallama a kofar bedroom d'in Alhaji.
amsawa yayi da Wa"alaikissalam wa'rah matulllah. Wanda hakan ne yabata damar kutsa Kai cikin d'akin a sanyaye, Alhaji dake zaune kan resting chair ri'ke da wasu files da yake ko'karin cikewa, dubansa yakai kan Rukayya'da ta shigo tana ko'karin zama bakin gado.

a nutse yakare mata kallo, cikin dakakkiyar Murya ta mazan jiya yashiga cewa.. Lafiya kuwa Mami? Cikin sanyin Murya tace.. Abba a rud'e nake dan Allah ka sassauta wa zuciya ta Abba, a wahalce nake cike da gala ba ita wanda tashin hankali kan sanyawa mutum... Wai yarinyar ce Jikinta babu dad'i Mami? Abba ya katse ta dan shi kansa har yaji hankalin sa yatashi.

Girgiza Kai Mami tayi.. kafun tace ko d'aya Abb" hasali ma bacci takeyi, hmmmmmm"'yasauke ajiyar zuciya kafun yakoma kusa da matar tasa, d'agowa yayi da habarta cikin sigar rarrashi yace Rukayya"wani abun ne yafaru? Mai yasameki? runtse idanuwanta tayi yayinda shaid'an yake sake azalzalarta had'i da zuciyar ta dake ko'karin bata muguwar shawara, ta'awizi tayi a ranta had'i da fad'a wa zuciyarta Farouq bai cancan ci wannan tuhumar ba shi d'in mai kima da daraja ne a gareta ta Yaya zata iya yi masa wannan tuhuma haka yana bukatar kwantar da hankali yayin tuhumar sa kan laifin da ba tada tabbacin ya aikata.

Ya dade yana duban ta duba irin na tsanaki, daga bisani ya had'a ta da 'kirjin sa, Inna"ma'al wusri yusra. kintuna da wannan komai yayi tsanani tofa yanada sauqi Kisani duk yadda damuwa taimiki yawa to fa ubangiji yana nan kuma shi mai karbar kukan bayinsa ne dan haka ki Mika lamarin ki gareshi... nasiha yashiga yi mata kan tawakkali da ha'kuri da kaddara.

Har'batasan lokacin da hawaye yasauko mata ba dan tasani mijin ta bawan Allah ne salihi, mai Kyakyawar zuciya yanzun gashi yana danganta damuwar ta da wacce ta riga tabar wa Allah, domin ciwon baya goguwa saidai neman sauqi a gun ubangiji, wani sabon hawayen ne ya zubo mata.. Yazama dole fa tasanar dashi abunda kenan matu'kar lafiyar ta tana da mahimmanci a gareta.

Sauke ajiyar zuciya tayi, ta dubi gwarzon mijin nata mai kaunar ta da son farincikin ta.. Kai anya kuwa zata iya shaida masa damuwar ta? take zuciyarta tashiga tunatar da ita irin alkhaireen sa gareta hakan tamkar butulcewa ni"imomin ubangiji ne. Saidai ai kuma yakamata yasani ko dan gujewa abunda kaje yazo. But this is not the right time. tabawa zuciyar ta amsa, a hankali tayi lumm a kirjin sa Shikuwa lallashin ta yaci gaba da yi cikin kalamai masu dad'i da taushi. har batasan takardar ta fad'i daga hannun ta ba.

   

*******bashida za'bi yazamar masa dole komawa ko dan tseratar da lafiyar uwar rikon sa, dan babu shakka idan ummi tayi ido biyu da wannan video d'in zuciyarta tana iya bugawa. shikam bazai so suyi mugun gani ba... Jiki babu 'kwari yaja jakarsa zuwa cikin d'akin sa, da'bas yazauna a tsakiyar d'akin. Cikin damuwar da tunda yazo duniya baita'ba jin kwatan kwacin ta ba. Wannan wace irin masifa ce? Ya Allah ka kubutar da yarinya ta daga fad'awa mummunan hannu,, ka kare mun ita a duk inda take, ya Allah na rokeka ka kubutar dani daga kaidin wannan mata.... yakara sa rokon nasa yana mai zubda hawaye.
Mikewa yayi yashiga toilet alwala ya d'aura yashiga nafil fili...da rokon ubangiji da ya tsare masa yarinya.

****bata farka ba Sai gurin karfe3 na yamma' Koda ta farka kasa tashi tayi saboda yadda Jikinta yayi weak.  Shiru tayi a kwance tai wani lamo..tunani take son yi ita d'in wace ce? nan d'in inane? Saidai tana soma matsawa kanta tasoma jin ciwon kai mai tsanani da kyar ta daga hannunta zuwa goshin ta tadafe tana sakin numfashin wahala.. A haka Mami ta shigo ta same ta, cikin tausayawa ta dubeta yan mata kin tashi? da ido tabi Mami tana sake maimaita abunda namin tafad'a a ranta.

taimaka mata Mami tayi ta tashi zaune, sannu ko, bata amsa ba Sai bin Mami da ido takeyi, bari in had'a miki ruwa kiyi wanka kiyi sallah. bata jira cewar ta ba tashiga bathroom d'in tana mamakin yarinyar a zuciyar ta, dan yadda take kallon ta abun yayi yawa sai binta take da ido kamar zararriya?Kodai bata gama wartsake wa bane? haka dai ta had'a mata ruwan wankan zuciyarta fall sake sake.

Yarinya na had'a miki ruwan zo kiyi wanka ko? bari in taimaka miki, tafad'a tana mai ko'karin riketa zuwa bathroom d'in, baby kam binta takeyi ba tareda fahimtar mai take nufi ba...  Mami suna shiga ta zaunar da ita bakin bathtub d'in tace yawwa sai kiyi wankan.
tana fad'in haka ta fita had'i da janyo mata kofar...

****Zaid kake ko wa? What ever.. Inaso ka saurare ni da kyau domin gujewa yin kuskure, kasan mai nake so da kai? Zaid"bai kulata ba Sai ma wani'kunci dake taso masa, hajiya Rahamu bata damu da ko inkular sa ba, dan a cewarta shi ta shafa, bazata fasa aiwatar da kudirin ta ba.

taci gaba da cewa.. Zabi d'aya ne biyu zuwa uku idan kaso Zaman lafiya kayi ko'karin bin umarni na dan bijirewa umarni na daidai yake da faruwar komai, saida ta dubeshi duba na shu"umanci, kafun tace Idan nace komai zaidu to fa ina nufin komai,, d'agowa da kansa yayi cikin wani irin yanayi yayinda idanuwan sa sukayi wani irin ja mai ban tsoro wanda ita kanta Hajiya Rahamu da suka had'a ido saida kirjin ta ya buga. ji yake tamkar ya sha'ke matar saboda muguwar tsanar ta da yayi,

ci gaba da magana tayi cike da jarumta da karfun hali irin nata.

         Zaidu inaso kasani ga duk abunda zan fad'a maka to fa babu gudu babu ja da baya, har yanzun dai bai ce da ita komai ba,sai sauraren ta da yakeyi.

             Inaso ka auri SALMA....!   Wani irin duba yayi mata a ransa kuwa ko'karin tunawa yakeyi da wacece ma salma? dan shi yama manta Sam da wata yarta salma'. bata damu da irin duban da yake mata ha dan a ko'karin ta na cimma burinta, babu shakka komai zata iya iya fuskanta tariga da ta dadaukar da duk wani tarin kalubale da zata fuskanta da imanin ta, wannan shine kawai power d'inta da take ganin zata iya ja da koma waye bare kuma zaid karamun kwaro.

                 Ba wai rokar ka nake ba umarni nake baka! wani irin mi'kewa yayi yana huci, a zafafe yace... na fahimci dai idan ba anayi ana nuna miki hanya ba Sam bakya damuwa da irin guraren da kike jefa kafarki. Shin ke d'in wacece? meye had'in ki da rayuwar Zaid? Nidai nasan cewa babu wata halaka tsakani na dake ke d'in matar mai gida ce kawai wanda ya yimun halacci, da a ce ke d'in mutuniyar kirki ce hakika babu abunda zai hana ni ganin girman ki... Saidai Kash! Ke d'in bakin kumurci ce mai dafi mai radadi, gar kiga tamkar bansan dukkan kulekullen ki ba to nasani babu abunda bansani ba a cikin makirce makircenki tun daga kan sace sacen da kike yiwa dad kama kan yanda kike masa sihiri yake kin jin maganar kowa sai taki...... tunda yasoma magana gumi ke tsatsafo mata ga wata muguwar razana da tayi da kalaman sa.
           dukawa yayi saitin Fuskarta kinsan me? nasan cewa ke ce kikayi asirin da kika raba iyaye da d'ansu...... Enough... Zaid!

   Ya isheka haka.... Ni kake ko'karin to nawa asiri ni kake son tozar tawa,? To bari kaji wlh ka kiyaye da kalaman ka domin yiwa bakinka linzami da ko'karin shiga gona ta, kasan wacece ni kuwa? ba shakka kanason wuce gona da iri, kasan meye bandamu da insan a inda kasamu duk wannan labarin ba amma zan sake jaddada maka tabbas nice na aikata hakan, kuma tunda na fahimci bakada hankali bakason kwanciyar hankalin ka, shikenan nasan abunda zanyi..tana gama fad'in haka ta fice daga d'akin zuciyarta na Kuna kamar garwashin wuta haka tanufa side d'in Ummi a zafafe.

 

      "Ke matar nan take shirin yi karfa ta kaiwa ummi da dad video d'in.... Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un Allah ka shiga tsakanina da kaidin wannan azzalumar matar,, sintiri yashiga yi a d'aki shi d'aya, yagama sadakar wa komai zai faru ya faru Allah ne shaida baiyi wa UMAIMAH fyade yana cikin hayyacin sa ba, kiran sallar azhar ce ta tilasta masa fitowa.

          ********Mami ina wai ina yar taki ne? naganki a parlour ke d'aya badai har yanzun wankan takeyi ba? numfashi Mami ta sauke had'i da fad'in wlh kuwa har yanzun dai bata fito ba inaga dai kawai zan shiga inga ko lafiya, eh kam gwara ki shiga amma ace wanka tun d'azu? mi'kewa tayi tana fad'in wlh fa yayin da tanufi bedroom d'inta,

      Kai tsaye bathroom" d'in tanufa d'an kwankwasa wa tayi a takaice saidai shiru babu wani respond, sake kwankwasa wa tayi still no respond, hakan yasa ta d'an tura kofar a hankali.... Dummm! Kirjin ta yabuga.............

Hummmmmmm! Masha'Allah, dn Allah ina mai baku ha'kuri kan shiru na da yayi yawa hakan yafaru sakamakon, d'ana da bashi da lafiya, waya ta kuma tazo ta lalace, tohm Alhmdllh yanzun nayi wata kuma yarona yasamu lafiya,, nagode sosai wa wanda suka nemeni Allah ybar zumunci 👌💕🤞😂💞

Xinnee smart 👌💋

     


Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro