14
Abba"kamar fa ta farka, hajiya Rukayya ta fad'a tana matsawa kusa da UMAIMAH"wacce dama tuni take a farke, Masha'Allah shine abunda Abba ya fad'a, tallafo da kanta Hajiya Rukayya, tayi cikin tausayawa tashiga shafa kanta a hankali baby ta bud'e idonta kallon su tashiga yi kamar mai nazarin wani abun, a sanyaye Alhaji farouq yashiga fad'in sannu yarinya, koma dubansa tayi.
Kallon hajiya Rukayya"yayi yace... Shiga da ita ciki ta d'an samu nutsuwa, amsa masa tayi, kama hannun baby tayi zuwa cikin bedroom d'inta, kwantar da ita tayi kan gadon ta,
Fitowa tayi gun mai gidan nata, tace... Abba! a ina kasamu wannan yarinyar wai? Saida yasauke numfashi kafun yace, kamar dai yadda na fad'a miki ne a 'kofar gate nagan ta. muyi addu'a dai Allah yasa tadawo nutsuwar ta, daga baya sai muji komai daga bakinta. Allah ya kyauta amin ya amsa mata yana ficewa daga parlour.
itama kitchen tanufa a ranta tana addu'ar Allah yasa yarinyar tadawo nutsuwar ta.
******
Ummi"ce a gefen gadon da aka kwantar da Zaid" cikin muryar ta da ta disashe saboda kuka ta tace sannu Zaid" Allah yabaka lafiya.
baice mata komai ba Sai ido da yazuba mata, yayinda a zuciyarsa tsantsar damuwa ce fal a ciki ga tarin tunanin baby, ga girman zunubin da ya aikata wanda yake ji shi kansa bazai yafewa kansa ba dan hakan nan yakejin baiyi wa son da yake wa baby adalci ba, yabata gobensa, yabata goben baby, a bangare d'aya ga mutane masu daraja da tsantsar hallaci a gareshi, wanda bai duba duk girman alkhaireen su a gareshi ba, har ya iya keta alfarmar Yar su, shi kuwa ina zai Kai wannan abun kunyar, runtse idanuwansa yayi yayinda zuciyar sa taci gaba da wani irin suya...take kuma 'kwa'kwalwar sa tashiga bashi labarin batan UMAIMAH wanda shine sanadin sunan sa,
Wani irin zabura yayi daga kan gadon, ya Mike daidai shigowar dad, ummi ma tuni ta mike.
Lafiya Zaid!?
Dad"yarinya ta dad, ina take....a wani hali take? Zanje nemanta dad.
Wani irin kuka ummi"ta fashe dashi had'i da yin waje, dad kama Zaid yayi, ya zaunar dashi, haba zaidu ka nutsu mana kadawo nutsuwar ka baka ganin Bakada lafiya ne?
baka ga halin da UMMIN ku take ciki ba Uhmmm? Kuma ma insha'Allah Za a ga baby, ka kwantar da hankalin ka.
Kuka Zaid yafashe dashi.. Dad ni..dai.. zan nemota a duk inda take a fad'in duniya dad nayi alkawarin nemota dad.
Rungume shi dad yayi, take yasake kanka me shi yana koma sakin wani irin kuka mai tattare da tsantsar damuwa,
Ummi"itama gu tasamu a waje taita rera kuka mai tsuma rai, tana mai yin addu'a Allah ya bayyana mata yarta Yakuma baiwa Zaid lafiya.
Dad haka yashiga rarrashin Zaid" da 'kyar aka samu ya d'an kwantar da hankalinsa, kwanan sa hud'u a asibiti, ya matsa kan a sallame shi.
Duk kwanakin da yayi hajiya Rahamu' bata zo ba bata aiko ba,
***
Salma tunda saura yinta yatafi da ita matatar iskanci bai barta ta dawo ba kullum cikin d'in kira mata kayan maye yake wanda a karkashin ranta tana matu'kar son tadawo dan ta aiwatar da mugun nufinta kan Zaid"dan tasan yanzun wancan yayi exper, dole sai tayi sabon zubu.
Dan haka ma tashiga sake neman wata mafitar ta yadda zata kama Zaid a hannunta yadda idan yashigo babu shi babu kubucewa.
Zaid"ka kwantar da hankalin ka dan Allah kadaina zancen fita neman baby da kanka, tunda jami"an tsaro na bakin ko'karin su dan haka kayi ha'kuri mu zubawa sarautar Allah ido. Muyi ta addu'a insha'Allah zata bayyana a garemu a duk inda take,, lumshe idanuwa Zaid"yayi.
Bayan fitan dad". Janyo wayarsa yayi yashiga gallery d'insa
Pictures d'in baby yashiga kallo d'aya bayan d'aya Yawanci yana daukanta sune ba tare da sanin ta ba.
d'ayan Pic d'in ne ya d'auka hankalin sa, da kayan bacci take a Hoton riga da wanda baby pink. Kanta babu ko hula gashin duk ya wani har gitse, ranar rigima take ji anyi anyi ta bari uwani taimata wanka taki bari gashi ummi ranar batajin dad'i,, shine kawai tafito parlour a haka babu abunda ya dameta, a lokacin shi kuma yashigo parlour yana sauri yayi break dan yanada test a ranar,
Shine ya hango ta a kan kujera zaune ta kurawa TV ido bazaka ta'ba cewa tanada matsala ba idan ba fad'a maka akayi ba,
tsayawa yayi yashiga d'aukar ta pictures, wani ma Hamma tazo yi kawai ya d'auka, haka ya shagala da kallon ta har saida uwani ta miko masa tea d'in ya ankara.
Wani irin hawaye masu zafi ne suka sirnano masa take yaji wani irin mugun sonta mai zafi da wani irin kewar ta na sake kamashi,, moment d'insu ne yashiga dawo masa, from the first day da yafara ganin ta wani abun idan ya tuna yayi murmushi wani yayi kuka wani yasha gala kun kallon Pic d'inta. Ga sonta dake sake azalzalar zuciyar sa...
yarinya ta! Ko ina ina...?
Kidawo gareni Zaid"yana tsananin kewarki, sonki yana damunsa, idan baki dawo ba mutuwa zanyi, meyasa? Me yasa? Kika tafi kika barni wannan Karan kaddarar da tasa kika bata babu tantama rayuwata take son d'auka, rayuwata ce burinta a wannan karon... Mai yasa banzo a mutane masu sa'a bane? Komai yashigo Rayuwa ta sai na rasa shi?
kaddarar rayuwata baki mun adalci ba kullum binki nake sau da kafa kullum biyayya nake miki mai yasa ke baki tausaya mun ba a wannan karon, ko kinsan Zaid yana da matu'kar rauni a bangaren so? Son ma na yarinya ta UMAIMAH?
Wani irin kukan yasake na wani irin bakinciki,
zuciyarsa ce tashiga bashi shawarar duk yadda za'ayi yau yasamu yafita dan neman cikon alkawarin sa. Babu fashi ya fad'a a ransa yazamar masa wajibi yafita neman yarinyar sa farincikin sa dariyar sa murmushin sa, dan tabbas idan yarasa ta tofa yarasa dukkan wayannan abubuwan, yanason umaima Allah yasani dan haka ma yake da rauni a kanta.
******
Hajiya Rukayya" ce rike da tea cup a hunnunta, wanda yasha had'in tea a cikin sa.
Bedroom d'inta tanufa, ajiye cup d'in tayi a kan stool, matsawa tayi gun UMAIMAH dan tashin ta ko tasamu tasha tea d'in, saidai baccin ta kawai takeyi hakan yasa tayi murmushi dan hakannan taji kaunar yarinyar,
Ganin yadda ta takure gu d'aya alaman sanyi yadan yi mata yawa ne yasa ta rage mata karfun ac d'in duvet taja ta rufe ta gashin kanta ta mayar mata baya, har ta tashi taji ta taka abu Koda ta kalla taga Yar peper ce haka wacce tabi ta takure saboda matsa da tasha a hannun baby, d'auka tayi da zummar jefawa shara.
tunawa tayi da a hannun yarinyar tafara ganinta wanda yanzun ma da dukkan alamu batasan ma ta Yar ba.
bud'e takardar tashiga yi... cikin nutsuwa,
Alhji farouq" tsawon shekaru Kahana zuciya ta sukuni, ka Hana ni nutsuwar zuciya, ta yadda darare da yawa banyi bacci ba, bayan ka had'a muguwar gaba tsakanin ya da iyayenta saboda hud'ubar ka ta sharri, wanda daga karshe ka yaudare ni... Saboda zalinci irin naka baka tashi yaudara ta ba Sai da kasan inada ajiyar ka a jikina,, kuma kabar garin Lagos dan mugunta irin taka dan kasan bansan garinku ba, to Alhmdllh yau rana ce da nayi niyyar sadaka da yarka gatann na kawo maka abarka, nima kuma nakoma gun iyayena.. Na barka lfy, ka gaida matarka marar dad'i.
Wani mugun jirin tashin hankali ne,, yasoma kwasar Mami,, da sauri ta dafe bango.
Wannan wani irin masifa ne ke ko'karin tunkaro su? Alhaji nada shegiyar ya? to a yaushe? Kai ba zata amince da wannan zancen ba, toh.. Amma..kai take shedan yace mata na rabaki maza munafukai ne.. Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un!
dabas ta zauna a kasa tana mai tsananin jin zafin abun.
*******
Dare ne sosai wanda zai iya kawai misalin karfe 2 , jakarsa da ya had'a yan kayan sa ciki ya d'auka had'i da rataya wa a hankali yafito daga part d'in hawaye na Sauka akan fuskar sa cikin damuwa ya tunkari gate d'in gidan dan ko'karin fita,, tsayawa yayi yana karewa gidan kallo, hawaye naci gaba da Sauka akan fuskar sa, da sauri ya juya had'i da d'ora hannun sa ga kofar da zummar bud'ewa.
Ina zaka?
Yaji an fad'a,
Wani irin tsoro da fargaba ne suka dirar masa a lokaci d'aya, cikin karfun hali yajuya dan ganin waye wannan karaf! Idonsa yasauka akan hajiya Rahamu"
Wacce ke dubansa a 'ke'keshe.
Juyawa yayi ba tareda yace mata komai ba sake ko'karin bude gidan yakeyi, yaji tace...
Kafun ka tafi inason ka kalli wannan, bai Kai ga juyowa ba yasoma jin sautin numfashi, dummm! kirjin sa yabada wani irin sauti.
a lokacin da yayi arba da video d'in da sauri ya runtse idonsa, cikin tashin hankali, murmushin mugunta tayi kafun ta kashe video d'in,
Kasan meye? bata jira amsar shi ba taci gaba da cewa... Wannan talla ne, sauran show d'in yana nn nasa anbuga mun shi,
Idan kaga dama zaka iya komawa kajira ni da safe mu tattauna daga nan sai ingoge video d'in, idan kaga dama katafi, daga nan gobe da safe Alhaji da lubabatu sunsamu abun breakfast. Fine.
ta karasa fad'a tana daga ka fad'a,
Zabi yarage ga mai shiga rijiya!
Tana kaiwa nan a zancen ta takoma part d'in ta ba tareda ta saurari mai zaice ba.
Wani irin kunci da takaici ne yakama zaid" da wata irin zuciya yakama kofar zai fita...
Masoya ina alfahari da ku komai yawa ko qanqanta👌😘😍😘
Domin ku kawai yau nayi typing, dan hr yau bta dawo ba Tohm 🤣😂
Xinnee smart 👌
I need ur vote&comment 😴
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro