11
Dare ne sosai yayinda ko wani d'an Adam daren yakasance mahuta a gare shi, sa'banani Zaid" da sai faman juyi yake tunanin sa nazarin sa, duk suna akan UMAIMAH"baby, hakika reaction d'inta na yau akan sa ya matu'kar bashi mamaki tabbas ko ba'a fad'a masa ba baby haushin kalaman salma"taji shine dalilin da yatun zurata har taiwa salma wannan aika aikar,,
Wani juyin yakoma yi,, yasa ki tattausa murmushi dake sake nuna tsantsar nutsuwar sa. duvet yaja had'i da yin addu'a dga bisani yyi light off.
Asuba ta gari zaidu! 😂🕯️
*********kwanaki sunja, abubuwa da yawa sun faru wasu kuma suna kan faruwa, wanda tun ranar da tsautsayi yasa salma taiwa Zaid magana a gaban baby har yau bata koma ba,, saboda a cewar ta aljanun baby mahaukata ne. Gwara tanayin nesa nesa da ita....
a yanzun Zaid"yana matakin aji uku a makaranta,, yayinda baby jiki saidai neman sau'ki ga Allah,,
Yauma"a zaune suke palon ummi" yayinda Zaid yake d'an duba takardun shi haka kuma lokaci zuwa lokaci 'kirjinsa yake bugawa wanda yarasa dalilin haka baby tana zaune a kusa dashi rike da tap d'in ta da ya mata playing karatun alqur'ani da wata Yar yarinyar larabawa take karantawa, a lokacin ummi"tana kitchen ne tana ko'karin had'a abincin dare Kasancewar lokacin 'karfe biyar na yamma ne.
Zaid" daina karatun yayi, ya zubawa baby ido, cike da wani irin bugu da kirjin sa yakeyi,, tamkar tasan ana kallon ta tadaina kallon tap d'in tayi ta d'ora idanuwanta, saitin da yake, murmushi tasaki wanda har saida ha'kwaran ta suka bayyana masu d'auke da kyakyawar ushirya.
a lokacin da zaka ganta bazaka ta'ba cewa bata lafiya ba.
Zubawa juna ido sukayi na seconds daga bisani,, ya rike hannun ta cikin sautin sa mara hayaniya yasoma magana, yarinya ta! dubansa tayi wannan karon saidai batayi murmushi ba Sai idanuwa da ta zuba masa, murmushi yayi mai taushi kafun yace ... Mai yasa nakejin wani abu a game dake? Lokaci d'aya kuma da mummunar fad'uwar gaba? hakika inajin wani iri a game dake kema kinajin abunda nake ji ne?
Sake 'kura masa ido tayi,, a ransa yasake jin wani irin tausayin ta da kaunar ta suna sake huda shi, a lokaci d'aya...har baisan lokacin da hawayen son ta da tausayin ta suka zubar masa ba. bai Ankara ba yaji hannunta akan fuskar sa.. tana aikin share masa hawayen,, hannun nata yarike akan fuskar sa, kafun yace... INA SONKI.. yarinya ta! ke fa? Wani duban sa takoma yi.. Saidai wannan karon idanuwanta a lumsashe suke. Shiru suka d'auka duk su d'in,,
Kiran sallah, da kuma alamun shigo palon da ake ko'karin yi ne suka saka shi sakin hannun ta had'i da mi'kewa dan tafiya masallaci,, binsa da ido tayi har yafita.
***Boka a gaskiya ina cikin damuwa,, naso zuwa saidai hakan bai samu ba, shi yasa ma na kira ka dan in d'an fad'a maka kafun in samu zuwa,, dan a gaskiya abun yafi karfin tunani na.
daga d'aya bangaren boka yashiga cewa.. Maza fad'i damuwar ki tattaba tsine ya share miki hawayen ki... Cike da damuwa hajiya Rahamu"tashiga cewa.. Waton yata salma"ce ta d'auko mun rigima,, da sauri boka yace.. Nasan wannan fad'i wani inji.. sauke numfashi tayi kafun taci gaba da cewa.. Sai matsalar Alhaji,, koma dakatar da ita yayi yace... Nasan wannan ma.. to boka sune matsalolin da suka sakani a gaba,,
Ya"kike so ayi?
boka ya bu'kata.
Bayani tasoma yi masa... boka abunda nakeso yanzun shi yaron na"amince inason yata ta aure shi dan na hango amfanin da zaiyi, bayan auren zan San yadda zanyi yasamo mun duk wani sirrin arzikin Alhaji!
Angama! fad'i bu'katar ki ta gaba.
Cike da farinciki tace... boka inason Alhaji asake yi masa mugun 'kulli ta yadda sai abunda nace masa...
Hhhhhhh.. Rahamu"ki 'kaddara dan ke akayi Tahir!
Saidai akwai sharad'i akan aikin da za'ayi wa yaro Zaid".
Cike da fargaba tace boka meye sharad'in?
da muryar sa mai cike da amo mai razanar wa yashiga cewa.. Wannan yaron yanada matu'kar riko da addini ga addu'a, dan haka aikinsa zai wahalar damu kuma idan anyi ba Lallai yakama shi ba,, ko yakama shi to fa b duka ba. Sai kuma abu na gaba.. Aiki bazai yu ba saida abu d'aya!
Cikin rawar Murya hajiya Rahamu"tashiga cewa meye shi... boka?
Ba wani abu bane face sai idan ansame shi da rashin gaskiya,, a duk ranar da kika kamashi da rashin gaskiya to kiyi ko'karin sanar dani cikin gaggawa!
boka na gama fad'in hakan ya kashe wayar sa, wani irin gumi ne ya shiga ketowa hajiya Rahamu"
Fuuuuuuu! ta fitar da wani irin iska a bakin ta,, tunani da nazari tashiga yi na tayyada zata ga Zaid" cikin rashin gaskiya tsamo tsamo.
Haka ta 'karaci tunani da nazarin ta bata samu amsa ba dan haka tad'auka damarar Sanya wa Zaid ido!
***yayinda hajiya Rahamu" take sa'ka mugun nufinta, haka ma yarta salma a nata bangaren, nazari da neman mafita take ta yadda zata tikastawa Zaid son ta wanda har zai kaisu ga aure dan ita yawon tazubar d'in ta ya ishe ta so take ta ganta a gidan kanta da kuma miji na kere sa'a.
gajiya tayi da kwanciyar da tayi akan gadon dan haka ta tashi tashiga zagayar d'aki cike da neman mafita ko ta halin 'ka'ka,
Kwalbar gorar had'in kayan network d'inta ta d'auka ta d'an kur'ba a cewar ta ko kanta ya rage ciwo.
Allah y shirya!
A bangaren Zaid" kullum so da kaunar, baby guri yake dad'a samu a zuciyar sa, haka komai nata yayi masa saidai fargabar sa d'aya ko iyayenta zasu amince su bashi auren ta? duk da irin rashin nasaba da yake da ita? Wannan ne bai sani ba kuma shine abunda yake razani shi, saidai koma Menene... shidai yariga da yagama sa'ka sonta a zuciyarsa. ta yadda yayi mata guri ya alkinta ta, kuma yana addu'a da Fata ta kasance abokiyar rayuwar sa... Shi Sam baya duba nakasar ta hasalima bai taba mata dubin naka sashiya ba.
Kullum kallon ta yake a mace ya mutum mai yanci kamar kowa.
dan haka a gurin sa lokaci kawai yake jira ya bayyanar da sirrin dake ransa.
Toh ko haqar sa ta cimma ruwa! 😱
*****
Hhhhhhh,, yau nayiwa mai gadin gidanmu tsiya, kawata.. cewar zeema" 'kawar salma, a da'kile salma ta amsa da bngane ba?
Yayinda muryarta take nuni da abuge take..
Cikin dariya zeema tashiga cewa.. Bana taba fad'a miki yadda nake mutuwar sha"awar sa ba... Kuma shi d'in ai aramma ne... Hhhhh
. Shine fa jiya kawai na had'a shi da Lemo da maganin karfin sha"awa dakan iya zautar da mutum hhhh guy d'innan fa see.. ba dama ne.. Kutt!
Hhhhhhhh..... takarsa fad'a tana bingirewa!
******
Farkawa tayi daga nannauyan baccin da yadibeta bayan tadawo jiya daga clup,, kanta taji ya wani irin Sara mata,, dafe kan tayi,, had'i da sake kwanciya babu sallah bare salati,, dan dama ba yi take ba dan a lokacin karfe 8 na safe ne...
Wani irin zabura tayi lokacin da ta tuno firar su da zeema" kawar ta jiya a clup,, tabbas wannan maganar sunyi ta da zeema kuma a lokacin bata hau da yawa ba.
Murmushi tayi had'i da fad'in.. Fantastic! Just fabulous.
Yau takasance" lahadi dan haka ma Zaid yana gida,, salma ce tafito daga part d'in su, dube dube tashiga yi saida ta tabbatar da babu wanda ya lura da ita kafun ta nufa part d'in Zaid"dan tasan a daidai wannan lokacin yana part d'in ummi" dan haka tashiga palon sa hankali kwance,, cikin sa'a kuwa baya nan.
dan haka ma tasamu yadda takeso,, Kai tsaye fridge d'insa ta nufa,, favorite drink d'in shi taci karo dashi...a fridge d'in dubawa tayi taga wanda ya bude da alama sha yayi ya rufe, budewa tayi yaffiddo da 'kwayoyinta,, ta dama a wani cup data gani kan center table,, saida taji'ka kafun ta zuba cikin kwalin ta jijjiga,, sugar ta 'karawa lemon.. kafun ta mayar,, ta ajiye a sad'ad'e takoma part d'insu tana yi tana le'ke dan ganin fitowar Zaid daga part d'in ummi..
Am so sorry guy's, u won't hear from me because am going to travel, so am going to be off for some day's. 🙏📴😂😴😢
Gonnah miss umzaid.. I know u guys will miss them too 😊😝
Xinnee smart 😂👌💋💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro