BABI NA TALATIN DA TAKWAS
***Sadam.
Da gaggawa nurses suka turo gadon dora mara lafiya zuwa kofar Emergency room din, kafin suyi komai, oxygen suka fara daura mishi domin samun daidaituwar numfashinsa, sannan suka dora shi, suka tura zuwa ciki.
Duk da kasancewar Sa'id likita, amma a wannan gabar ya kasa yin komai, banda kaiwa-da-kawowa, babu abinda suke daga shi har sauran 'yan uwanshi saboda al'amarin na Sadam yayi matukar girgiza su, tare da haifar musu da tunani kala da kala a cikin kwakwalensu.
Bayan kamar minti arba'in wani dogon Dr ya fito, kai tsaye ya tunkari inda suke tsaye, ganin hakan yasa Sa'id yayi saurin k'arasawa ya mik'a mishi hannu.
"Barka da aiki Dr. Fa'iz. How's he?"
"Alhamdulillah Dr. Sa'id."
Ya juya suka fara takawa a tare zuwa office d'inshi.
"Dr issue din Sadam babba ne gaskiya, wanda har bansan ta ya zan fara yi maka bayani."
"Kamar ya kenan Dr? Please meye matsalar ne?"
"Ka san komai Dr Sa'id. Amma me yasa kuka yi irin wannan saken har kuka barshi ya yi reaching this kind of situation?"
"I don't understand what you're talking about Dr. What's going on?"
Zama yayi, a karo guda ya cire labcoat din da ke saman kayanshi, sannan ya juya yana kallon Sa'id wanda shima ya sama ma kanshi mazauni a daya daga cikin kujerun da ke girke gaban teburinshi.
"Kana nufin baka san Sadam yana shan giya ba?"
A zahirance ba zai ce bai sani ba, haka kuma ba zai ce ya sani ba, sai dai idan ya tuna da kwalaben da ya gani dazu a dakinshi, to ba zaiyi tantamar yana sha din ba.
"I can't say actually, but naga kwalaben giya a dakinshi yau din nan, which I think he had too much to drink, that's why ya samu kanshi a halin da yake ciki."
"Sure, but this not the first time da ya fara, and you already know how excessive drinking of alcohol yake causing matsaloli kala daban-daban a lafiyar dan Adam, dama rayuwarsa baki d'aya."
Gyara zamansa ya yi, kafin ya ci gaba
"Bayan kasancewar giya cikin manyan kaba'irai da Allah Ya yi hani da su, mashaya giya suna tare da babban kalubale masu tarin yawa a tarihin rayuwarsu. A duk lokacin da mutum zai sha giya, abu na farko da zata fara yi, shine zata tafi direct zuwa bloodstream nashi, daga nan zata yi distributing ma gaba d'aya sauran sassa na jikinshi.
Tana farawa da excretory system na mutum, inda take haifar da alcoholic hepatitis which can lead to the development of jaundice. Shine wanda zaka ga fatar mutum ya lalace yana wani yellow-yellow, haka ma idanunsa. Wannan zaiyi causing serious liver problem, wanda muke kira cirrhosis a likitance.
Daga nan zata yi transferring to central nervous system na mutum shine zaka fara ganin canji a dabi'u da kuma halayyar mutum, idan tafiya tayi tafiya, giyar zata fara shiga cikin brain din mutum, ta haifar mishi da blackouts or memory loss, in sometimes, abun yana komawa mental problem.
Excessive alcohol drinking, yana damaging salivary glands na mutum, ya hana shi jin dad'in komai, yayi causing mishi appetite loose. Daga nan zai fara haifar mishi da cututtuka irinsu:
Gum diseases,
Tooth decay,
Stomach ulcer,
Heartburn, &
Dangerous internal bleeding.
Giya tana taka muhimmiyar rawa wurin dakusar da digestion na dan Adam, ta wannan bangaren tana haifar da cututtuka irinsu
Mouth cancer
Throat cancer &
Esophagus cancer (hanyar da abinci ke bi zuwa cikin dan Adam.)
In the case of person's circulatory system, giya tana lalata zuciyar mutum, and it will lead to
Heart attack
High blood pressure
Heart failure, &
Stroke.
Giya tana lalata immune system na mutum, ta inda zata hana su yak'ar cututtukan da ake kamuwa da su ta wannan hanyar irinsu
Tuberculosis (TB) & Pneumonia."
Ya saita dubansa a kan Sa'id
"Dr. Wannan kad'an kenan daga cikin abubuwan da giya ke haifarwa a lafiyar dan Adam, kafin kuma mutum yaje ga Allah ya had'u da azabar da aka tanada ma mashaya giyar a nan duniya. Nasan kuma ka riga ka san wadan nan abubuwan, sai dai ina mamakin yadda baka dakatar da Sadam daga fadawa wannan mummunan hali ba."
Shiru Sa'id yayi, tare da jinjina bayanan na Dr. Fa'iz, sai dai hankalinshi gaba daya ya fi karkata akan son sanin halin da dan uwan nasa ke ciki.
Bakinshi ya cika da iska, ya furzar, ya dago a raunane yana duban Dr.
"Now what's wrong with my brother?"
A hankali a ajje pen din dake hannunshi, ya d'ago ya kalli Sa'id.
"I'm so sorry to say, but he's suffering from one of the most life threatening diseases."
"What's that?"
Sa'id ya tambaya hankalinshi a tashe.
"Cirrhosis, I mean liver inflammation (liver disease)"
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Wannan wane irin tashin hankali ne?"
"Hak'uri za'a yi Dr. Ga wannan zaku je ku karasa sauran test a lab ku dawo da results din, then sai mu san wane magani ya kamata mu dora shi a kai."
Bai iya cewa komai, yasa hannu ya ansa, ya mike dakyar ya fita inda 'yan uwanshi ke tsaye suna jiran fitowarshi.
***
A
hankali take juya steeringwheel din motar cikin gwanancewa da kwarewa, hankalinta a kwance da alama bata da sauran damuwa, illa lokaci zuwa lokaci da take tunanin mutumen da bata taba tsammanin zata so ba ko a mafarki.
Mutumen da ya canja duk wani tsari nata, ya mantar da ita rayuwar bak'in cikin da ta riski kanta a baya.
Alal hak'ika soyayyar SS tayi mata k'ulli mai dabaibaiyi, wanda bata san ta kamu da ita ba sai a daren jiya, kasancewar kalaman da ya rink'a shirya mata a cikin waya sun sa ta tsinci kanta cikin wata duniyar k'auna mai wuyar fassaruwa.
Jin soyayyar tashi take har a cikin jinin jikinta, wanda a yanzu har mamakin kanta take, sai dai bai kamata ya zama abin mamaki ba, idan tayi duba ga yanayinta na mace mai son tsananin kulawa da tattali, haka kuma ya zo mata da wani SABON SALO na daban, domin a zahiri na shi salon ya sha banban da irin salon soyayyar Kazaure. Nashi salon soyayyar, wani irin salo ne mai tsayawa masoyi a k'ahon zuciya, ya mantar da shi komai, face soyayyar masoyin da zuciyar ke so da gani.
Murmushin da ke fuskarta ta fadada, a lokacin da ta kawo 2nd gate na shiga FMC.
Bayan securities sun gama bincika boot dinta, ta murza motar ta wuce ciki, direct amenity din da yake ta isa, tayi parking a waje, sannan ta fito da basket din lafiyayyen breakfast din data shirya mai, ta dauka tare da rufe motar ta juya domin k'arasawa ciki.
Kwance yake ya zuba ma k'ofar shigowa ido, da alama akwai abinda yake jira, hannunsa na dama rik'e da wayar da ke saman kunnensa yana ansawa, Hajiya na zaune k'asan dan k'aramin carpet din da ke shimfid'e tsakiyar d'akin, Jay ta turo k'ofar bakinta k'unshe da sallama ta shigo.
Tsab, ya sauke idanunsa a kanta, a lokaci guda ya ja wata sassanyar ajiyar zuciya, tare da narkar da idanunsa, tamkar mai shirin yin kuka, yana kallonta.
"I'm sorry."
Tayi mishi alama da idanunta, sai dai bai ce komai ba, ya kashe wayar, ya juya musu baya, duk kuwa da yadda ya kwadaitu da son k'ara kallon fuskarta wadda yake ta zaman jiran gani tun bayan tafiyarta.
Murmushi tayi, ta k'araso inda Hajiya ke zaune ta duka suka gaisa, sannan tayi mata ya mai jiki.
"Alhamdulillah Ummi. Ya su Hajiya?"
"Suna gaishe ku. Sai anjima zata zo, Baffa ne zai tafi Lagos yanzu, shi yasa ma bamu taho tare ba."
"Babu komai ai, da ta zauna ta dan huta ma. Allah ya kaishi lafiya."
Juyowa yayi yana kallon yadda ta zauna a gefen Hajiya bata da niyyar isa inda yake, ya manta da fushin da ya ke yi ma, domin kuwa ya shagaltu sosai wurin kallonta, yana ganin yadda ta sake suna maganarsu da Hajiya cikin natsuwa da wata irin kamalar da ta k'ara mata kyau da kwarjini.
"Patient."
Muryarta ta dawo da shi daga tunanin da ya fad'a, ashe har ta taso ta iso gabanshi ba tare da ya ankara ba.
"Yawwa, to sai na dawo Ummi."
"Sai kin dawo Hajiya."
Ta juya ta fita, shi kuma ya k'ara juya mata baya ba tare da yace k'ala ba.
"Ya Sadic ya jiki?"
"Ba ki so ki sani ba ai tunda kike zuwa yanzu."
"I'm sorry Ya Sadic. Wallahi breakfast dinka ne ya tsayar da ni, kuma ma ai na zo da wuri ko."
"Ki duba agogonki zaki gane."
"10:30 fa Ya Sadic. Kaga ko ai na zo da wuri."
"Amma ya muka yi da ke jiya?"
Ya juyo da shiny idanunsa yana kallonta.
Kwantar da murya tayi, a karo guda ta dan langabar da kai.
"I'm sorry I said. Nasan nayi laifi ai. Now daure ka ansa ni ya jikinka?"
Murmushi ya saki, wanda ya k'ara ma doguwar fuskarshi annuri, sannan ya fara k'ok'arin mik'ewa, amma ya kasa, hakan yasa ya saki dan k'ara kadan
"Arrrgh!"
Ya koma ya kwanta yana kallonta.
"This is your answer."
Yayi maganar yana nuni mata jikinshi da ido.
"I'm sorry ka ji. Sannu, lemme help you ka mik'e zaune, na san ko abinci baka ci ba."
Bai ce komai ba, ya tsaya yana k'ura mata ido, yayin da ita kam ba tare da damuwa ba ta zame pillow daya dake k'asan wanda kanshi yake, ta jingine da gadon, sannan ta d'ago wanda yake kai, ta k'ara jinginewa.
Hannu ta mik'a zata kama kafadarshi, taji wani irin yarrr, ya shiga ta hannun, ya bi duk wani jini da ke aiki a jikinta, a k'arshe ya isa har zuwa k'wak'walwarta.
Da sauri ta sake kafadar, ta matsa tana dan matsa hannun, ta kasa cewa komai, haka kuma ta gagara sauke idonta a kanshi.
Hakan ne ya faru da SS, shima kuma kasa maganar yayi, a lokaci guda ya saki ido yana kallonta.
Dak'yar ya iya dai-daita tunaninsa, yayi gyaran murya kadan yana tambayar
"Any problem?"
"Errrnmm.. ka tashi ka zauna."
Ta fara gyara murya tana in'ina.
"Alright."
Ya fada yana gyara zamansa.
"Sannu Ya Sadic. Are you okay?"
"I'm fine."
"Sannu to, barin sa maka abinci. Nasan ko magani baka sha ba ko?."
Murmushi yayi, sannan ya girgiza kanshi a karo guda yana lank'wasa yan yatsunshi yace
"Wa yace miki ban sha ba?"
"Zuciyata."
Bakinta ya furta kai tsaye, domin bata san lokacin da maganar ta fito ba.
"But why? I mean why zuciyanki?"
Shiru tayi, ta cigaba da hada tea a mug din da ke hannunta, ta gama tass, ta dago da plate din da ta sa mishi abincin, ta iso gabanshi ta dora saman table sannan ta juya tana nuni mishi da gefen da zuciyarta take.
"Tambaye ta, zata baka ansa."
Shiru yayi yana kallonta, nisan da ke tsakanin su ba wani mai yawa ba ne, daga inda ya ke yana jin saukar numfashinta da ke fita da wani irin k'anshin da ya dauke shi, ya kaishi wata duniya ta daban, hakan ya sanya shi lumshe ido, ya bude a hankali.
Har yanzu tana tsaye yadda take, tana kallonshi.
"Ehhnn now."
Tayi mishi alama da idanunta.
Murmushi kawai ya iya yi, domin baza ta gane yadda yake jin ta a cikin tashi zuciyar ba.
"I'm hungry."
"Oops. I'm sorry."
Da sauri ta juya ta dauko mug din ta mik'a mishi, amma ya k'i ansa, ya tsaya kawai yana dan tura baki kadan.
"Amma kinsan bana da lafiyan hannu ai. Ina zan iya rik'e k'aton mug din nan."
"Ka warke fa ya Sadic. Kuma ba wani nauyi ne da shi ba ma. Try it please."
Ta fad'a idanunta a kanshi, itama tana dan tura bakinta gaba.
"I can't. And idan kinsan zaki bani wahala me sa kika bar Hajiya ta fita?"
"But Ya Sadic..."
"But what Angela? I can't, bazan iya rikewa ba. Can't you see that imma patient here?"
Yayi saurin katse ta da maganarshi, wacce yasa ta sake baki tana yi mishi kyakkyawan duban yadda yake abu kamar wani Jafar.
"Naji. Ka sha tea din ni sai in baka abincin."
"If that's the case, then na hak'ura da both. I told you hannuna ba zai iya dauka ba."
"Amma Ya Sadic sai ka daure fa, a haka zai warke ai. Issokay zan baka yanzu, but na gobe da kanka zaka sha. Promise me?"
Wani lallausan murmushi yayi, ya mik'a mata dan autan yatsanshi yana fad'in
"I promise you Angela."
Noke nata yatsan tayi cikin mug din da ke hannunta, tai mishi nuni da ido, tace
"I trust you."
"Ki kawo mana inyi proving miki."
"Never mind patient. Now have your breakfast. Aaahh."
Ta k'arasa tana bude bakinta kadan, lokacin da ta matsar da tea din zuwa bakinshi.
Bud'e bakin yayi tana bashi a sannu-sannu, ya dan ci ba laifi suna fira kadan-kadan, cikin dan lokaci sun saba da rayuwar soyayyarsu, mai cike da shauki, kauna, kulawa, tattali, da kuma aminta da juna.
Sooooo
This is where we're heading to 😁😁
Ina Mr. Kazaure?
Shin ya hakura ne?
Will SS wins the race?
Stay tuned, to find your answers out.
Lubbatu😍🔥
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro