Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA TALATIN DA SHIDDA

Hawayen da ke zuba a fuskanta ta shafa, ta dago da hannun tana kallonsu, ta tabbatar da kuka ne take yi, amma ta rasa dalilin da ya sanya ta zubar hawaye har haka.
Murmushi ta saki, ta fara shafe fuskarta, ta mik'e da sauri ta bi bayanshi, sai dai a lokacin da ta fito, ta hangi motarshi na barin gate din gidan.
Da sauri ta koma ciki ta d'auki waya ta fara kiran shi, amma har yayi ringing ya gama bai daga ba.
Ta rasa dalilin da yasa ta kasa natsuwa saboda fushinshi, sai dai idan ta tuna cewar tayi provoking dinshi, sai ta ji hankalinta sosai ya tashi, hakan kuma ya sa ta k'ara kiran wayar a karo na biyu, amma shiru, ba shi da niyyar dauka.
5 Missed calls ta bar mishi ba tare da ya biyo bayan kiran nata ba.
Ta rasa duk wata natsuwarta, ta kasa zaune ta kasa tsaye. A ganinta laifin duka nata ne, ta bata ma mutumen da ya taimake ta, wanda yake sonta da gaskiya, tsakaninshi da Allah ba wai dan wani abu da take da shi ba.
Mutumen da ya mutunta, ya dawo mata da darajarta ta 'ya mace, ya kuma dawo mata da farin ciki da jin dadin da ta dunga ganin kamar tayi bankwana da su.

Da sauri ta fita, inda tayi parking ta tasan ma, ta shiga ta tada motar ta dauki hanyar gidan Hajiya, domin ta gama yanke shawarar ansa tayin soyayyarshi wadda a da take jin kamar baza ta iya ba, amma idan tayi duba da abubuwa da dama, sai taga a duniya babu wanda ya cancanta da ita bayan shi, shine zai so ta as who she is, ya kulan mata da 'yarta, rabin ranta. Haka kuma tayi alk'awarin zata koyar da kanta soyayyarshi, tunda dama bata jin kiyayyarshi, sai dai son da take ma Kazaure ya hana ta tantance abinda take ji game da shi.
Da wannan tunanin ta iso k'ofar gidan, zuciyarta na ta faman sake-sake, ta yi parking a waje ta fito, ta shiga ciki da sallama kunshe a bakinta.

"Wa alaikumus Salam."

Hajiya da ke zaune a palo ta ansa ta da fara'a sosai a kan fuskarta.

"Ai ni nayi fushi Ummi. Sai yau ake ganinki?"

Kanta a k'asa ta karasa ta zauna tana dan murmushin da ya fi kama da na dole.

"Hajiya ina wuni"

"Lafiya lau. Alhamdulillah. Ya mutan gidan?"

"Lafiya lau wallahi."

"Masha Allah. Ina ta zuba ido ko Rukayya in gani amma naji shiru."

"Ina ta son zuwa nima, abubuwa ne sai a hankali."

Ta k'arashe tana kallon Hajiyar.

"Haka ne kam. Allah yayi taimako."

"Amin ya Allah. Ina Yaya Sadic kuwa?"

"Dazun nan muka yi bankwana yace zai biya ta can kafin ya wuce, ashe bai je ba?"

"Ina zai wuce?"

Ta tambaya da dan sauri, cikin razana, idanuwanta a waje.

"Borno mana. Ko me ya hana shi zuwa?"

Murmushi ta kakalo, a karo guda idonta ya cike da kwalla tace

"May be yana sauri ne."

Ta mik'e tana gyara gyalen abayanta.

"Dama na zo ta unguwan ne na shigo in gaishe ku."

"Har kin tashi kenan?"

Hajiya ta fada lokacin da ta mik'e ta shiga d'aki ta fito da turare a leda, ta mik'a mata tana fad'in

"Ki gaishe da mutan gidan."

Ansa tayi tana godiya, sannan ta juya ta fita, hankalinta a tashe, tana tunanin halin da SS ke ciki, kasancewar tunda ta san shi bata taba ganin abinda ya bata mishi rai kamar wannan ba.

***Sadam.

Tunda suka fita ya dukar da kanshi a tsakanin kafafunsa, kuka yake wanda bashi da sauti, hawaye kawai ke kwarara daga idanunsa, a lokaci guda yake da-na-sanin kofsawar da yayi a iya zaman da suka yi da Jay.
Da ya san akwai irin wannan rana a duniya, da babu abinda zai hana shi mutunta ta, ya rik'e ta da daraja, ya bata dukkan soyayyar da tayi deserving, sai dai shi kanshi ya san is too late for him to cry, ya riga yayi loosing opportunity din da ya samu a baya, ya kuma san wutsiyar rakumi tayi ma k'asa fintinkau!
Ya san ba shi da sauran amfani a wurinta kamar yadda ta fada, most especially idan yayi duba ga yanayin da yake ciki na rashin aikin yi a yanzu.

"She's yours. And you alone."

Wata zuciyar ta tunatar da shi. Hakan yasa a bayyane ya furta

"And I'll fight for her. To me she belongs."

Da sauri Salis da ke zaune a gefenshi ya d'ago da kanshi yana tambayar

"Me ke damunka?"

Kamar dan k'aramin yaro, sai ya fashe da kuka, ya fada kafadarshi yana fad'in

"I love her Yaya. So very much."

Bayanshi ya fara bugawa a hankali, sannan ya tadar da shi daga kafadar tashi.

"You've to face the reality Sadam, yarinyar nan da wuya ta hak'ura ta koma maka, ka daure ka cire ta a zuciyarka."

"But she loves me. I saw it wallahi, she still do loves me. Bazan iya daina sonta ba har izuwa k'arshen rayuwata. And I promise sai na dawo da ita gare ni ko da hakan na nufin zan rasa rayuwata ne."

"Kai kana da matsala wallahi. Yanzu ka kwantar da hankalinka ka magance matsalolin gabanka kafin ka fara wani tunani."

Banza ya mishi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba, ya juya ya cigaba da kukanshi, a haka har suka iso gida, ya fita da gaggawa bai ce ma kowa komai ba, ya wuce dakinshi ya shiga ya maida k'ofar ya rufe tare da sanya mata jamlock.
Dan k'aramin room fridge din da ke gefen tv stand ya dosa ya bude, yasa hannu ya fito da kwalbar giyarshi, kallonta yake a hankali, rabon da ya sha yau kusan watanni hudu kenan, wanda a lokacin yayi alkawarin ba zai kara ba, amma a yanzu baya ganin wani abu da zai taimaka mishi ya mance abubuwan da suka faru kamar barasar.
Daga kwalban yayi ya fara tuttula ma cikinshi, sai da ya shanye tass, sannan yayi wurgi da ita, ya fada saman gado yana cigaba da rera kukanshi, wanda duk wanda ya gani ya san soyayya ce ke azabtar da zuciyarsa.

***SS.
Tuki ya ke a babban titin Kano zuwa Maiduguri, amma zuciyarsa gaba d'aya bata tare da shi, haka ma tunaninshi.
Tunda ya ke a duniya bai taba ganin macen da yake mutuwar so kamar Jay ba. Jin soyayyar ta yake tamkar da ita aka halicc zuciyar shi, amma ba zai iya jure ganin yadda take daukaka soyayyar Kazaure a kan tashi ba, wadda ya tabbatar da duk duniya babu wanda ya kaishi kaunarta.

"Why wud she take me for granted?"

Ya tambayi kanshi tare da buga steering hannunsa.

"I love her so much, but i can't take this anymore. I can't bear seeing her loving someone else...."

Bai k'arasa rufe bakinshi ba babbar trailer da ta taho ta daga motarshi sama, ta watsar a gefen titi, hakan ya sanya shi fad'in
"La'ila ha illallahu, wahdahu la shari kala, lahul mulku wa lahul hamd, wa huwa ala kulli shai'n kadir."
Tun daga nan bai kara sanin inda kanshi ya ke ba.
Dakyar trailer drivern ya samu daidaituwar tunaninshi, da sauri ya taka birki, hakan ya ba motocin da ke bayansa damar tsagaitawa suma, kafin wani dan lokaci wurin ya gama cikewa da mutane.

Dakyar suka fito da shi, saboda yadda motar ta lankwasa, tamkar babu halittar dan Adam a ciki.
Wayarsa suka lalubo, a karo guda suka danna number Better half, wacce take a farkon call log dinshi, ta inda suka fara tunanin may be matarshi ce.

Kwance take a ruf da ciki, bugun zuciyarta ya tsananta sosai, haka zalika faduwar gaban da take ji bata taba experiencing irinshi ba.
Wayarta da tayi k'ara ne yasa ta mik'a hannu dakyar ta dauka, ganin number SS, yasa tayi saurin dagawa ta dora a kunnenta.

Muryar da taji tabbas ba tashi bace, hakan yasa ta tambaya

"Wa ke magana?"

"Yawwa. Hajiya mai wayar ne ya samu accident, wanda a halin yanzu bamu da tabbacin yana mace ko yana raye."

Da sauri ta mike tsaye zumbur, zuciyarta ta buga daaaaam! Hankalinta ya tsananta tashi, yayin da a lokaci guda taji wasu zafafan hawaye sun sauka akan kumatunta!

"Kuna ina yanzu?"

Ta tambaya dakyar lokacin da ta fito palo ta samu Goggo da Baffa a zaune.
Bata iya cewa komai ba ta mik'a ma Baffa wayar.
Ido ya bita da, ya ansa ya dora a kunnensa anan mutumen yayi mishi kwatancen inda abun ya faru, shima cikin tashin hankali ya mik'e yana fad'in

"Ku taimaka ku kaishi asibiti mafi kusa, gani nan tafe yanzu-yanzun nan."

Ya kashe wayar ya juya yana salati yana kallon yadda Jay ke kuka tsakaninta da Allah, tana yi ma Goggo bayanin abinda ya faru, lokaci guda fuskarta tayi jajur, ta fita a kamanninta.

"Barin je. Kada wanda ya sanar da mahaifiyarshi a cikinku."

Da sauri ta mike ta bi bayan Baffa, hakan yasa ya juyo yana kallonta,
"Ki koma ki zauna Mamana, yanzu zamu dawo tare da shi in sha Allah."

"Ka taimaka muje tare Baffa, ba zan iya zama a nan ba."

Kukan da take shi ya fi bashi tausayi, hakan yasa yace ta zo suje kawai.

"Nima ba kwa barni anan ba ai."

Cewar Goggo da tayi gaggawar shiga ta fito da hijabinta, suka dunguma zuwa harabar gidan.
Da sauri driver ya iso da katuwar Jeep, suka shige suka d'auki hanyar gidan Dr. Mukarram wanda ya ke kwararren likita, kuma shi ke duba Baffa a duk lokacin da bashi da lafiya, ko wani daga cikin iyalinshi.
Cikin sa'a suka same shi, basu bata lokaci ba suka kama hanyar Kauyen da SS yayi accident din.

Tafiyar ta d'auke su kusan awa d'aya, kafin suka isa clinic din da SS ya ke da taimakon mutumen da ya d'auki wayarsa, wanda shine ya rink'a directing dinsu.
Kai tsaye dan k'aramin d'akin da aka kwantar da SS Dr ya zarce, anan ya fara aikinshi cikin kwarewa, sai dai ba zai iya yi mishi komai ba saboda karancin kayan aiki, hakan yasa ya bashi taimakon gaggawa, sannan suka saka shi a mota suka d'auki hanyar gida.
Kuka Jay take mai azabar zafi, bata damu da su Baffa da ke cikin motar ba, ta kama hannun SS wanda bai san abinda ke faruwa ba ta rik'e karkadam, ta rasa dalilin da yasa ta shiga wannan mummunan tashin hankalin ganin shi a cikin irin wannan yanayin.
Federal Medical Center suka zarce lokacin da suka shigo Katsina, direct A&E suka wuce da shi domin ceto rayuwarshi ciki

Da sauri Dr Mukarram ya juya zai shige ciki, Jay ta matsa tayi gaggawar rik'e rigarsa, ya juyo a hankali yana kallon yadda gaba d'aya ta fita a kamanninta.

"It's okay Ummi. I'll in sha Allah try my possible best."

"It's all my fault Dr. Please I'm begging you to save his life no matter what. Just promise me."

Tayi maganar idonta taf da hawaye, yayi jajur, ya dade da canja color tuntuntuni.
Hannu yasa ya cire rigarsa da ke hannunta, a karo guda ya gyara zaman face mask din da ya riga ya daura a fuskarsa.

"I promise you, zanyi bakin kokari na, I mean zanyi duk iya abinda Allah ya bani iko. So kici gaba da addu'a kawai."

Bai jira me zata ce ba ya juya da sauri ya wuce ciki, Goggo ta isa gare ta, tana juyowa ta zube a jikinta tana wani irin azabtaccen kukan da ke azabtar da idanuwa da kuma zuciyarta, Allah ya sani tana da-na-sanin abinda ta yi ma mutumen da ya mik'a mata soyayyarshi kacokam, ya kuma 'yanta ta, ya daukaka mata darajarta ta 'ya mace.

"Laifina ne Goggo. Idan ya mutu ya zanyi da rayuwata? Me zan fada ma Jafar? Goggo me zan ce ma Hajiya? Ya zanyi da rayuwata ni JAMEELA!"

Ta kuma sakin kuka mai zafi, wanda sai da yasa Goggo ta matse nata hawayen, ta ja ta zuwa kujerun da ke girke a gefe suka zauna, kuka take mai tsuma zuciya, dak'yar Goggo ta fara lallashinta, sannan ta tsagaita kukan a nan ta fara nusar da ita illar abinda take fada.

"Ba laifinki ba ne Ummi, wannan iko ne na Allah, wanda rayuwar dan Adam kacokam take hannunsa. Kiyi hakuri ki daina kukan nan, a halin yanzu babu abinda Sagir ke buk'ata wanda ya wuce addu'armu. Kiyi hakuri dan Allah."

Shiru tayi, sai ya zamana ta koma tana yin kukan na zuci, tare da addu'ar Allah ya tashi kafadun SS ko dan ta rama mishi alkairan da ya yi ma rayuwarta.

***Sadam.

Duk da kwalbar giyar da ya tuttula ma cikinshi, hakan bai hani hotunan abubuwan da suka wakana dawowa a cikin k'wanyarsa ba.
Kuka yake yana jijjiga gadon da ya ke kwance, a k'arshe ya mik'e ya k'ara bude fridge ya fito da wata kwalbar giyar, ya daga yana zazzaga ma cikinshi, tamkar wanda bai san illar da hakan zata haifar masa ba.
Cikakkun mintina goma ba'a yi ba ya fara wani irin tangadi, jiri ya fara dibansa, a lokaci guda ya ga d'akin na birkicewa, yana komawa up-side-down, hankalinsa gaba d'aya yana neman barin jikinshi, sai dai har iyanzu ya gagara daina ganin picturen Jay da SS lokacin da suka jera a gabanshi, ya gagara daina tuno kallon da SS ke jifarta da shi mai cike da salon so, da kuma kauna mai dukan zuciya.

Wani irin kururuwa ya fara, a take ya cigaba da faffasa abubuwan da ke cikin d'akin, hakan ne kuma ya jawo hankalin sauran jama'ar da ke cikin gidan.

"Sadam. Sadam. Lafiyarka kuwa?"

Yan uwanshi da ke bakin k'ofar d'akin suke tambaya tare da k'ok'arin bude k'ofar, sai dai ya datse ta gam, daga ciki, haka kuma bai daina bige-bigen da ya ke ba, bai kuma damu da ya bude k'ofar da suke ta faman bugawa ba.
Wani wawan bugu Salis ya kai ma k'ofar, amma ko motsi bata yi ba, a karo na biyu ya ja da baya yayi mata kyakkyawan bugun da yasa jamlock din ya fita daban daga jikin k'ofar kasancewarta ta katako, hakan kuma yayi dai-dai da zubewar Sadam a tsakiyar d'akin yana wani irin gurnani, tamkar zakin da ya ci karo da nama.
Da sauri-sauri numfashinsa ya fara fita, daga bisani yayi wani razanannen kara, sannan numfashin ya d'auke gaba daya.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."

Suka fara nanatawa a lokacin da kusan mutum bakwai suka fad'o d'akin abinka ga gidan yawa.
Sa'id wanda ya ke likita shi ya fara dudduba shi, amma kasancewar ba shi da komai na aiki, yasa yace su d'auke shi su wuce asibiti kawai, haka zalika yanayin na Sadam ya tashi hankalinshi sosai, bama ya kwalaben giyar da ya gani suna yawo a tsakiyar d'akin.

Salis, Saheeb da Shu'aib suka ciccibo shi dak'yar, suka saka a mota, Saheeb ne ya zagaya ya tada motar suka d'auki hanyar Dan Masara Specialist Hospital, kasancewar a can Sa'id din ke aiki.

***SS.
Wasa-wasa sai da suka shafe kusan awa biyu zaune a wurin amma shiru babu wani labari, har kuma a lokacin Jay bata daina zubar da hawaye ba, lokacin da ta ke zaune saman sallaya dan nesa kadan, da inda Goggo da Baffa ke zaune saman kujeru.
Gaba d'aya fuskokinsu sun shiga alhini, babu wanda ya ke cema dan uwansa wani abu, har zuwa lokacin da Dr Mukarram ya fito, a lokaci guda yana cire gloves din hannunsa, hakan yasa Baffa yayi gaggawar mik'ewa ya isa gabanshi, kafin yace wani abu wata nurse ta turo SS saman dan k'aramin gado fuskarshi lullube da farin mayafi.
Hakan da Jay ta gani yasa tayi saurin tasowa itama, a tare suka iso gaban Dr suna tambayar abinda ke faruwa.

"I'm sorry."

Ya fada yana kallon Jay. A take ta wara idanunta tana fad'in

"Sorry for what Doc?"

Bai ansa ta ba yace da Baffa

"Muyi magana a office."

Ya juya ya fara tafiya, har kuma a lokacin bai bata ansar tambayar da ta yi mishi ba.
Ganin hakan yasa suka yi gaggawar bin bayan nurse din da ke tura gadon da SS ke kwance, zuwa wani dan karamin daki wanda babu kowa a ciki, haka kuma bai yi kama da inda ake kwantar da marassa lafiya ba.

"Ina ne nan?"

Ta tambayi nurse din.

Instead of ta bata ansa, sai ma juyowa da tayi da sauri

"Please ku dakata a waje Hajiya, idan an gama komai za'a muku magana.

"Komai? Kamar ya kenan?"

"Kuyi hakuri ku jira a waje, babu wanda ake bari ya shigo nan."

"I'm going nowhere Ms. Nurse."

Ta tafi da sauri ta yace mayafin da aka lullube fuskarshi, gani tayi ya k'ara wani mugun kyau wanda tunda take bata taba ganinshi a tattare da shi ba.
An wanke bruises din da ya samu, an kuma zagaye goshinshi da farin bandage, sai dai babu wani wuri da ke motsawa a gaba daya sassan jikinshi.

"Nooooooo!!!!! This can't be."

Ta fad'a tana zara idanunta da suka cike taf da hawaye, tana girgiza kai, a lokaci guda ta kama hannunsa tana jijjigawa.

"Dont do this to me please. I love you SS. Kada ka tafi ka barni please, wallahi zan kula da kai, ina sonka, ka taimake ni kada ka mutu ka bar rayuwata a cikin tashin hankali. Wake up please. Please ba dan ni ba Ya Sadic, dan Allah, saboda k'aunar da nike maka, idan ka mutu ba zan taba yafe ma kaina ba, nice sila, ni nayi sanadiyyar mutuwarka. Ka tashi dan Allah. Wallahi ina sonka da gaske, ba wasa nike yi ba..."

Cak bakinta ya datse, jin da tayi hannunshi da take rik'e da shi ya k'ank'ame nata hannun, a tsorace ta fara dawo da kallonta gare shi, sannu a hankali ta sauke idanunta a kan nashi idanun da suka bude tangaram tamkar ba wadanda ta gani dazu ba.
Ganin haka yasa nurse din da ke tsaye gefe ta fita da gudu, har tana bige Goggo da ke tsaye a wajen k'ofar.

"Do you really love me?"

Taji shakakkiyar muryarsa ta fada, labbansa kunshe da wani kyakkyawan murmushin da ya k'ara mishi haske da kwarjini.

"Of course Ya Sadic, and will always do, please don't leave me."

Kafin ta kara cewa wani abu taji hannunsa da ya rike ta ya fadi kasa, idanunsa sun koma sun rufe ruf tamkar ba shi yayi maganar ba.

😭😭😭😭😭😭😭😭😭

Our SS please....👏👏

Lubbatu😍✌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro