BABI NA TALATIN DA DAYA
A galabaice ya fara buɗe idanunsa a hankali, ya sauke a kan mutane biyun da ke tsaye gabansa.
Mik'ewa yayi yana mai cigaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya ba tare da ya fahimci halin da yake ciki ba.
"Are you okay?"
Kallon mai maganar Sadam yake yana son tuna abinda ya faru, amma ya kasa, bai ce komai ba, ya mike, ya zira takalmansa da ke yashe a gefe, ya fito harabar hotel ɗin.
A gaban reception ya tsaya yana kalle-kalle, sai dai cajin da ke cikin kansa bai barshi ya tuna komai ba dangane da abinda ya wakana, idan ko har zai tuna wani abu, to ba komai bane illa lokacin da ya shigo wurin, ya zarce zuwa mashayar da ke cikin hotel ɗin.
Bai takura kansa ba wurin son sanin abubuwan da suka faru daga wancen lokacin, illa mik'ewa da yayi da zumar zuwa inda ya ajiye motarshi, sai dai kaf wurin, babu motar dake da k'arancin kuɗin tashi.
Manya-manyan jifajifai ne, da k'ayatattun motoci danginsu BMW, Mercedes, da makamantan irinsu, hakan yasa idanun Sadam suka fara rena fata, a karo guda ya tura hannunsa a aljihu da niyyar fito da makullin motar, ya latsa security, ko Allah zai sa a dace, sai dai makullin yace neme ni inda ka ajje ni.
Da gudu ya koma cikin reception ɗin, yayi sa'ar ganin mutumen da ya taimaka masa, ya isa gabanshi da sauri.
"Na manta key ɗin motata a ciki please."
"Bamu ga key ba gaskiya. Dan ba fito wurin ba sai da na tabbatar da cleaners sun gyara shi."
"No please. Kada kace haka mana."
"I'm serious Malam. Sai dai ko wani wurin ka jefar da shi."
Faɗuwar gabansa ce ta tsananta lokacin da ya tuno da inyamurin da suka haɗu, sannu a hankali abubuwan da suka faru a daren jiya suka dawo cikin k'wanyarsa, hakan yasa shi zubewa a wurin tare da tallabar kanshi da hannuwansa duk biyu.
"Ya kashe ni."
Yayi maganar a bayyane.
Ganin abin nashi ba na wasan yaro ba ne, yasa manager wurin ya kira securities suka fitar da shi har wajen hotel ɗin sannan suka koma ciki.
Zuciyarsa gaba ɗaya babu daɗi, ya rasa menene abinda ke shirin afkuwa a rayuwarsa, tashin hankali da rashin natsuwar da yake ciki gaba ɗaya sun wanzu a saman fuskarshi.
Dak'yar ya iya ɗaga k'afarsa ya fara takawa, sai da yayi tafiya mai 'yar tazara sannan ya samu taxi ya k'arasa da shi gida.
Hankalinsa bai gama tashi ba, sai da yazo gidan ya same shi rufe, kasancewar makullan gidan da ya haɗa tare da na motarshi.
***
"Sagiru ya batun maganarmu? Sanin kanka ne bazan taɓa barin Ummi ta koma ma yaron nan ba. Tunda naga alamar abinda kake so kenan."
"Wallahi ba haka bane Alhaji. Yanzu haka fitowa ta gida kenan, daga nan kuma wurinshi nayi, domin nima yau satina ukku kenan ban sa Kazaure a idanuwa na ba. Baya zuwa office, haka kuma baya ansa duk wani kira da nike mishi, dalilin da yasa nike son a bi komai a hankali ba komai bane, illa idan muka kai maganar court kamar mun daɓa ma kanmu wuk'a ne."
"Ban aminta da wannan shawarar ba. Tunda har yaron nan ya fara guje maka, tabbas yana da abinda yake shirin yi. A nufin shi ya gudu ya bar mun 'ya da aurenshi a kanta ko? To wallahi bai isa ba. Ba kuma zan taɓa lamunta ba. Ya bar ganin yayi na farko ya ci riba, wannan karon sai na yi mishi wulakancin da kare ma ba zai ɗauka ba wallahi. Ka dai ji na rantse."
"A yi hak'uri dai alhaji. In sha Allah yau ɗin nan za'a yi ta ta k'are."
"Kada ka ba kanka wahala Sagiru, dan na tabbata yaron nan ba zai bata takardarta ba har sai na bayyana gabanshi, dan haka ka jira ni ina nan tafe."
"Haba Alhaji. Kayi hak'uri ka bar komai a hannuna mana, zan kula da duk abinda ya dace."
"Hak'urina ya k'are Sagiru, haka zalika kana buk'atar mataimaki. Ina nan zuwa gobe in sha Allah."
Bai jira ansarshi ba ya kashe wayar, hakan yasa SS ya bi fuskar wayar da kallo, yana tunanin abin yi. Wayar Shamsu abokin aikinsu da ta shigo ne ta katse mishi tunani, haka ya ɗaga wayar da sallama ya kara a kunne.
"Weekend Alhamdulillah"
"Ina gida, yanzu dai nike shirin fita."
"A'a bani da labari wallahi."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Kazauren?"
"Shi yasa ya daina zuwa aiki kenan? Amma yayi ganganci. Bai taɓa sanar da ni ba wllahi."
"Zamu yi magana in sha Allah."
Ya kashe wayar ya fara kaiwa da kawowa, haka zalika ba zai iya jurewa abinda ake shirin yi ma aminin nashi ba. Duk kuwa da cewar babu wanda ya kaishi tsanar halayenshi a dai-dai wannan lokacin.
Motar ya shiga da sauri, a guje ya bar gidan zuwa gidan Sadam.
A kofar gidan yayi parking, ya fita ya kutsa kanshi ciki, tare da sallama, sai dai ba'a ansa ba.
Bakin k'ofar ya isa ya fara bubbugawa, cikin wata irin kakkausar murya aka ce
"Waye ne Dallah?"
"Ka buɗe ka gani mana."
A dai-dai lokacin ya buɗe k'ofar, idanunsa sunyi jazur, da gani a cikin maye yake, k'afarshi babu takalmi, cikakkar sumar da ke kanshi ta cukwikwuye alamar bata samu ajin sharta ba, wandon da ke jikinsa tamkar zai faɗi k'asa saboda mugun ass down ɗin da yayi, hatta da boxers ɗinshi gashi nan muraran ana kallo.
"Kana so ka kashe kanka ko? Wannan wace irin rayuwa ce ka jefa kanka Sadam? Wai kai wane irin mutum ne a duniyar nan?"
"Kayi abinda ya kawo ka ka k'ara gaba Dallah. Me ruwanka da rayuwata?"
"Wannan bak'in halin naka shi ke hana ka cigaba a rayuwa, idan zaka rufa ma kanka asiri ka koma mutumen arzik'i, ka rufa, idan kuma ba haka ba, wallahi rayuwarka tana cikin haɗari, hatta aikin da kake tak'ama da shi yana gab da barin hannunka, tunda ka ci kuɗin mutane, ba tare da saninsu ba, kuma manager ya rufa maka asiri, amma da yake kai butulu ne sai ka watsa masa k'asa a ido. Dalilin zuwa na nan bakomai bane illa in taimaka maka, ka kawo abinda yake hannunka, mu haɗa mu biya su kuɗinsu, kana sane da cewar gobe ne dateoline ɗin da manager ya baka, duk da ma maganar ta gama fitowa, sai kasan ya zaka yi da sauran k'alubalen da suke gabanka."
"Idan wannan ne ya kawo ka, gara ka ɓace ma ganina tun wuri, dan bana buk'atar taimakon kowa a wannan lokacin. A shirye nike in anshi duk wani hukunci da banki zata yi a kaina, sannan zan baka shawara da ka daina ba kanka wahala a wurin mutumen da bai san ciwon kansa ba iri na."
Ya juya da sauri zai koma ciki, amma SS yasa hannu ya cafko nashi hannun, ya tura k'ofar da k'afarsa, ya bi bayanshi suka shiga.
"Me sa baka tausayin kanka? Me sa baka tausayawa zuciya da gangar jikinka? Wai kai wane irin mutum ne dan Allah?"
Juyowa yayi yana kallon SS, kuka ne ya ciyo shi, take yasa hannu ya toshe bakinsa, a lokaci guda ya faɗa kafaɗar SS yana wani irin kukan da ya rink'a taɓa zuciyoyinsu.
"Kana ganin na cancanci a tausaya mun? Kana tunanin ina jerin mutanen da ya kamata a tausayawa ne? Ni kaina nasan bana ciki SS, na riga na wulak'anta rayuwata, na wulak'anta kaina, na kuma wulak'anta duk wani da zai iya yin taimako a gare ni. Me sa baza ka bari a hukunta ni ta hanyar da zata ladabtar da ni ba? Me sa baza ka barni in ɗanɗani bak'in cikin da wasu suka ɗanɗana ta dalilina ba? Ina tababar kaina da kaina, domin kuwa bani da wani mak'iyi, wanda ya wuce mun kaina."
Hawaye ne suka yayyafo a idon SS, duk da mugun haushinshi da ya ke ji, hakan bai hana mishi jin tausayin kalaman da yayi ba. Gefe Sadam ɗin ya koma ya zauna ya haɗa kanshi da gwiwa yana ci gaba da wani irin kuka, shima SS zama yayi a ɗaya daga kujerun palon, yayin da shiru na dogon lokaci ya cigaba da wanzuwa a wurin.
"Yanzu menene abin yi?"
"Ban sani ba SS. Ban sani ba wallahi, illa iyaka, ina maraba da duk hukuncin da banki ya yanke a kaina."
"Idan na fahimce ka, kana nufin baka da kuɗin da zaka biya su?"
"Bani da su."
"Ina motarka? Kuma wannan ma ai gidanka ne ko?"
"An sace ta. Wannan kuma ba gidana ba ne ba."
"Kana nufin shekaru kusan bakwai din da kayi kana aiki baka tsinana ma kanka tsiyar komai ba Kazaure?"
Bai bashi ansa ba, shima kuma baiyi tsammanin hakan ba.
"Ko da yake, tunda ka jefa kanka a bala'in caca, da shan giya, ai baza su barka ka tara komai ba. Allah ya kyauta maka halayenka Sadam."
Banza ya mishi, sai gunjin kukansa kawai da yake yi, haka SS ya k'araci zamansa ya mik'e.
"Ka tabbatar ka halarci meeting ɗin da za'a yi a bank gobe, ni kuma zan ga abun da zan iya yi."
Ya juya ya fita, zuciyarshi a dagule, yana tunanin mutum mai irin halayen Kazaure.
Mik'ewa Sadam yayi zuciyarsa na wani irin tafasa ya rasa menene abinda ke mishi daɗi, ta wani ɓangaren yana jin tsanar kanshi da halayenshi.
Wani wawan ihu ya saki, a lokacin da ya matsa gaban television ɗin dake girke saman tv stand yasa hannunsa tun k'arfi, yayi wurgi da ita, take tayi gefe ta bada tartsatsatsa!
Ya duk'e a wurin shi kuma yana cigaba da rizgar wani irin kuka mai azabar zafi da raɗaɗi.
***
B
abban ɗakin taron cike yake mak'il da duk wani ma'aikacin bankin. Manager ne ya mik'e tare da karanto sharuɗɗan da mutum kan ɗauka kafin fara aiki a kowanne irin banki na duniya.
Ya gama ya karanto hukunce-hukunce da su kan hau kan duk wanda ya saɓa ɗaya daga cikin dokokin da suka gabata, sannan ya bayyana laifin Sadam a matsayin wanda ya saci kuɗin banki ba tare da saninta ba.
"Wannan sata ce."
A cewar MD wanda shima yana zaune a wurin.
Ya gyara zamansa, sannan ya cigaba.
"Domin kuwa ba wai a banki ba, ko a ina ne mutum ya ɗauki abu ba tare da sanin mai shi ba, sata kawai za'a kira shi."
Da yawa a cikin jama'ar wurin kai suke girgizawa, alamar sun aminta da batun na MD, daga bisani ya buk'aci Sadam da yayi bayanin dalilin da ya sa ya ɗauki kuɗin, ya kuma kawo hujjojin kare kai idan yana da su.
A yadda yake a zaune, kanshi a k'asa yana wasa da yatsun hannayensa, ta gefe guda hawaye na silalowa a saman kumatunsa, ya fara magana.
Jawabin da ya yima manager shi ya maimaita a wurin, sai dai manager ya mik'e a fusace yana faɗin
"Wannan maganar banza ce. K'arya yake yi. Domin kuwa binciken dana gudanar a kanshi ya tabbatar mun maganar k'arya ce. Haka kuma nayi duk wani binciken da ya kamata, amma ban samu wata kadara k'wak'k'wara a tare da shi ba."
Bai k'ara cewa uffan ba tun daga nan, shiru kawai yayi yana sauraren abinda zai biyo baya. Hakan yasa MD ya cigaba da jawabi kamar haka:
"A matsayinka na ma'aikacin wannan banki, wanda ya ha'ince shi, ya kuma ci amanarshi, ya saɓa ma banki dokoki da hukunce-hukunce, daga rana mai kamar ta yau, bankin ya dakatar da kai daga aiki da shi. Haka zalika bankin ya gurɓata duk wasu takardunka, ya kuma kore ka daga aiki a k'ark'ashinshi, sannan kuma babu inda zaka je su anshe ka, a matsayinka na ha'ini, ma ci amana. Abinda ya yi saura tsakaninka da banki shine ka biya kuɗaɗen da ka ɗauka, sanin kanka ne banki baya ɗaukar asara ko ta kobo ɗaya."
Ya san k'arshen maganar kenan, ya kuma san wannan ne hukuncin da ya dace da mutumen da bai san daraja ko ciwon kansa ba. Handkerchief ya fitar tare da toshe bakinsa, yayi kukanshi son ranshi, wasu na tausaya mishi, waɗanda kuma suka san halinshi, suna cewa maganin irinshi kenan.
SS ne ya fito da kuɗi nera dubu ɗari biyar ya mik'a su ga Manager, tare da neman lamunin cewar zai cika sauran zuwa gaba.
"Kada ka manta ba loan muka bashi ba, balle mu k'ara mishi interest muyi mishi lamuni. Satar kuɗin mutane yayi, idan baya da su gaba ɗaya akwai police da na kira zasu wuce da shi su kai mana ajiyarsa prison har zuwa lokacin da zai biya sauran kuɗin"
MD yayi maganar gabanshi gaɗi, ba tare da ya tausaya ma halin da Kazauren ke ciki ba.
"Alfarma na rok'a a matsayina na ma'aikacinku nima. A yi mun wannan taimakon."
"Wannan abu fa doka ce SS, haka zalika ko ɗan dana haifa ne ya taka ta, iyakar abinda zan mishi kenan."
Ya juya yayi kiran wani security, yace ya kira police ɗin da suke waje.
Haka polisawa kusan bakwai, suka shigo cikin bak'i da blue ɗin uniform ɗinsu, MD yayi musu nuni da Kazaure, suka isa gabanshi, suka ɗora masa handcuffs suka mik'ar da shi.
Kukan da yake a wannan lokacin, sosai ya taɓa zuciyar SS, da duk wani mai imani a wurin, hakan yasa ya isa gabanshi, ya rungume shi.
"Zan fitar da kai Kazaure. Just trust me."
Ya sake shi suka tusa k'eyarsa gaba suka wuce, inda su kuma suka cigaba da gudanar da abubuwan da suka yi saura, suka fito zuciyoyin mutane da dama a wurin babu jin daɗin abinda ya faru.
****
Washe gari da misalin karfe ɗaya na rana, wayar Baffa ta shigo ma SS. Dagawa yayi da sallama ya ɗora a kunnenshi.
"Ina office."
"Zan zo yanzu in sha Allah idan na fito lunch."
Ya kashe wayar tare da mik'ewa, yana karasawa inda motarshi ke ajje.
Hotel ɗin da Baffa ya sauka ya isa, bai shiga ciki ba, ya mishi waya ya sanar mishi da zuwansa, hakan yasa ba'a ɗauki dogon lokaci ba suka fito tare da direbanshi.
Fitowa yayi a motar suka gaisa cikin karamci da girmamawa, daga bisani ya sanar mishi da tsautsayin da ya faru da Kazaure.
"Wannan ba damuwata ba ce Sagir. Yaron nan ai kaɗan ma ya gani daga abubuwan da zasu faru da shi, kuma ko da banki bata ɗaure shi ba, zuwan nan da ka ga nayi, da niyyar ɗaure shi na zo. Dan haka ka shiga muje inda ya ke, ni dai takardar sakin 'ya ta kawai nike buk'ata."
Bai yi gardama ba, ya juya ya shiga motarshi, su Baffa suka rufa mishi baya har zuwa Maiduguri Central prison.
Ba su sha wahalar ganinshi ba, haka kuma babu komai da aka taɓa a lafiyar jikinshi, illa kayan jikinsa da aka canja zuwa irin na sauran prisoners ɗin da suke gidan.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba yayi lokacin da ya hango Baffa zaune, a silale ya iso wurin, kanshi a k'asa ya zauna yana jiran abinda zai biyo baya.
"Wannan kaɗan kenan ka gani Sadam. Irin bak'in cikin da ka cusa ma zuciyata lokacin da ka gudan mun da 'ya, bi'izinillah, sai ka ɗanɗani wanda ya fishi. Ba zan taɓa yafe ma azzalimi irinka ba. Kuma a niyyar da nazo da ita garin nan, in sa a ɗaure ka, irin ɗaurin da ko labarin irin laifin da kayi, wani ba zai so ya ji ba, amma Alhamdulillah, banki ta gama mun komai, yanzu abu ɗaya yayi saura tsakanin mu, ga takarda da biro ka rubuta mun sakin 'yata."
Kuka yake marar sauti tare da girgiza kanshi, a yadda yake jin jay a zuciyarsa yanzu, ba zai taɓa gangancin furta saki a gare ta ba, balle kuma har ya rubuta. Jin son ta yake wanda bai taɓa jin kwatankwacin irinshi ba yana yawo a duk wani jini da yake gudanyawa a cikin jikinsa.
Ya san shi mai laifi ne a gareta, amma yana da yak'inin cewar har gobe akwai sauran soyayyarsa a cikin zuciyarta, kamar yadda ya wayi gari A DARE D'AYA, ya ji ya kamu da matsanancin son ta wanda ya fi gaban misali, ya kuma ninninka duk wani tarihin soyayya da ya taɓa wanzuwa a duniyar masoya.
A yanzu ji yake tamkar ya cire zuciyarsa ya nuna mata yadda soyayyarta tayi fata-fata da kowanne lungu-da sak'o na birnin zuciyarsa.
"Kayi hakuri. Amma bazan iya ba Baffa."
"What? Da sauran ka yaro. Nace da sauran ka. Ko dai ka rubuta mun sakinta, ko kuma in sa kurtayen nan suyi ta jibgarka, har sai ka kasa tashi wallahi."
"Da zaka mun haka, da zan kasance cikin farin ciki, kuma ko bakomai, zan samu natsuwa a zuciyata ta wani fannin, kasancewar an hukunta mutumen da ya fifita farin cikinshi akan na wasu. Mutumen da yayi gagarumin laifin da ya cancanci hukunci. Mutumen da ya banzatar da macen da ta bashi amanar ruhi da gangar jikinta, ya wulak'antar da 'yar da ya haifa a cikin jikinsa, saboda wani dalilinshi can marar tushe. Kayi hak'uri Baffa, amma ko da zaka ɗora mini bakin bindiga, bazan taɓa furta kalmar saki a kan Jay ba, ina k'aunarta, itama, tana k'auna ta."
"A da kenan, a yanzu kuwa ban da tsana da k'iyayyarka, babu komai a cikin zuciyarta."
Ya tsinkayi muryar SS cikin zafin nama yayi maganar, tamkar ba mutumen da ya gama tarairayarsa jiya jiyan nan ba.
"Me hakan ke nufi?"
Yayi maganar a cikin zuciyarsa. Amma ya kasa gano dalili.
"That will never happen Sagir. Jay is belong to me. Tawa ce ita. Numfashina ce ita. Matsawar ba ita bace tace in sauwak'e mata, to babu wanda zai sa in furta kalmar saki gare ta."
"Fine. Zan fitar da kai. In kai ka har gabanta, anan zaka fahimci rashin amfanin da kake da shi a wurinta. A lokacin zaka gane babban kuskuren daka tafka na tunanin cewar har yanzu tana k'aunarka. Baffa ka daure ka tashi muje, nayi alk'awarin jibi in sha Allah zan zo da Sadam har gida, kuma ba zai fito ba har sai ya bama Ummi shedar sakinta kamar yadda kuke bukata."
"Wannan maganar banza ce, ba kuma zan lamunta da ita ba. Haka kuma ba zan bar wurin nan ba har sai ya furta da bakinshi cewar ya sake ta."
"Wannan ba zai taɓa faruwa ba Baffa. Ba zan taɓa furta wannan mummunar kalmar da bakina ba, ko da zaka maida gabana gabas, ka kashe ni."
Hak'uri SS ya cigaba da bama Baffa, dak'yar ya lallaɓa shi suka tafi, akan cewar zai ida biyan bashin da ake bin Kazaure, zai kuma zo da shi har Katsina zuwa jibi in sha Allahu.
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro