BABI NA TALATIN DA BIYAR
Kamar baza ta ɗaga ba, sai kuma ta ɗauka, ta ɗora wayar a kunne tare da faɗin
"Hello."
"Yes dear. Ga ni cikin Katsina, ban san ina zan dosa ba."
"Lallai kai ɗin nan. Amma ya muka yi da kai dan Allah?"
"Batun ya muka yi duk bai taso ba, I'm already here. Just text me your address."
"Ni bana gida wallahi, and ba yanzu zan koma ba, so ka jira idan na koma I'll let you know."
"C'mon Jay, annabi yace mu daraja bak'onmu fa. Why not ki texting mun address ɗin inda kiken inzo, tunda dama dai ganinki ya zo da ni garin."
"Okay. I'll."
Ta kashe wayar, ta juya tana kallon Miemie da ta zura mata ido, saukar da wayar tayi, tare da juya idonta, ta langaɓar da kai alamar 'kinga wani ɗan wahalar ko'.
Dariya Miemie ta yi,
"Kina nan dai da halinki Jay. Well lemme guess..."
Ido ta fito da waje,
"Guess what? Abeg stop it girl."
"Girl you said?"
"Yes now. Ain't you?"
"No! Not at all Jay. Ko dan kinga kin ajje Rukayya kike kira na girl."
Murmushi kawai tayi, a lokaci guda ta tura ma Faisal address ɗin gidan su Miemie, sannan ta dawo da hankalinta gare ta.
"Tashi ki shirya please, akwai wanda zai zo ganinki."
"Gani na? Waye shi?"
"Dallah ki tashi, naga baki da buri a rayuwa wanda ya wuce miki boko, to ni zan haɗa ki da Mr. Right. Oyaa get ready sweetheart."
"Hey, wai yaushe kika koyi manyance haka? Kina wani abu kamar babbar mata. Idan ma baki sani ba ki sani, soyayya baya gaba na wallahi."
"Saboda kin rasa wanda kike so ko? Na gudan miki da crush nko."
"Abeg, stop it mana. Ko lokacin yarinta ne kawai wallahi, sai daga baya na dinga dariyan abun, and yanzu da kika faɗa mun yadda zamanku ya kaya da kuma halayenshi, sai naji na k'ara tsanarshi wallahi. Ba dan ya haɗa jini da baby na ba ma da sai na mishi RM mai license."
Kallonta Jay tayi, ta kuma gaskata abinda take faɗa. Bata ce komai tayi ɗan murmushi, a karo guda tace
"Well, ki tashi ki shirya dai, cuz I believe zaki so guy ɗin da na kawo miki."
"Really? But ki faɗa mun yanayinshi. Is he cute? Attractive? Good looking? Handsome? Or what?"
"Da zuwan shi ya zo babe girl, he's just your type."
"I hope so."
Tayi maganar da murmushi a bakinta, sannan ta mike ta zaunar da rukayya a inda ta tashi, ta faɗa toilet.
Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba wayar Faisal ta shigo ma Jay, bayan ta ɗauka ya shaida mata zuwan shi unguwar, daga nan tayi directing ɗinshi har k'ofar gidan su Miemie.
Suna kashe wayar Miemie ta fito cikin baby pink ɗin abaya, tayi kyau ba kadan ba, yanayinta sosai ya bayyanar da kalar gayunta, haka zalika duk wanda ya dube ta, zai gane ta sha boko yadda ya kamata.
Dakinta ta shigar da Rukayya ta haɗa ta da chocolates da teddies ɗin da ke ajje saman gadonta, sannan suka fita zuwa wurin Faisal.
A wajen gidan suka same shi tsaye jikin mota, ya haɗa hannayenshi ya rungume yayin da ya baza idanunsa ma k'ofar fitowa gidan.
Miemie ce a gaba, Jay na rufa mata baya, hakan yasa ko da ya ɗago sai ya sauke idonsa kan 'yar kyakkyawar budurwar da ke ta tsaye gabanshi.
Bata damu da kallon da ya bita da shi ba, a haka suka iso inda ya ke, suka ɗan gaisa sama-sama, sannan suka yi mishi iso zuwa cikin gidan.
A palon Abban su Miemie aka sauke shi, ta wuce ta kawo mishi ruwa, da abubuwan motsa baki. Sannan ta koma kujerar da ke gefen ta Jay ta zauna tana latsa wayar da ke hannunta.
Sai da ya ɗauki ruwan da ta tsiyaya mishi a cup ya kai bakinsa, Jay ta kalle shi da murmushi,
"Meet my friend, Barr. Miemie Hussain."
Cup ɗin hannunsa ya ajje ya juya yana kallonta.
Jay ma kallonta tayi, tana nuna inda ya ke zaune
"Faisal Goni."
"Pleasure to meet you Barr."
Yayi saurin faɗa. Hakan yasa ta ɗago da murmushin ta,
"Same here."
"Ina son magana da ke please."
Faisal ya faɗa yana kallon Jay, lokacin da ta mik'e tana shirin barin wurin.
"Please. This is all I can do for you Faisal. She's my best friend, so treat her well. I mean well, well."
Bai iya cewa komai ba, illa ido da ya bita da shi. Ta juya inda Miemie ke zaune.
"Barin shiga wurin Hajiya."
"Alright, will join you in a bit."
Kallonta tayi, irin kallon da ke nuni da 'haba munafikfik.. ta saki dariya mai ɗan sauti ta juya ta shige ciki.
D'akin Miemie ta koma ta kwanta rigingine, tana kallon yadda fan ɗin dake mak'ale jikin ceiling ɗin ɗakin take juyawa, sai dai a zahiri ba wannan ba ne abinda ya addabi zuciyarta, tunanin ta inda zata ɓullo ma SS yanzu, shine damuwarta.
Ba tare da ta samo mafita ba, wayarta da ke cikin hannunta ta fara ruri, hakan ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninta, ta ɗago da wayar tana kallon screen ɗin.
Da ɗan sauri ta ɗaga ta ɗora a kunnenta tare da sallama.
"Muna gidan har yanzu."
"Ok gani nan zuwa yanzu in sha Allah."
Ta kashe wayar, ta juya tana kallon Rukayya da hankalinta gaba ɗaya ya tafi a wasan da take yi.
"Babe tashi muje gida kinji, Goggo na nema na now now."
Babu gardama ta ajje teddy da ke hannunta ta mik'e ta iso wurinta, tana tsaye tana gyara gyalen abayanta, ta ɗauki jaka da key ɗinta suka fita suka yi ma Hajiya sallama suka wuce, ba tare da ta shiga wurinsu Miemie ba.
***
Ko da suka shigo harabar gidan bata kawo komai a ranta ba, duk kuwa da bak'in motoci biyun da ta gani girke a cikin gidan, haka ta gyara parking, ta fito hannunta cikin na Rukayya suka sanya kai zuwa ciki.
Palon bak'in shine a farko, kafin ka mik'a wani dogon corridor da zai sada ka da sauran sassa na gidan, ga mamakinta, sai ta tarar da takalman maza a k'ofar shiga kusan guda biyar, a take kuma ta ji gabanta yayi wata mummunar faɗuwa, bata yi k'asa a gwiwa ba ta tura kanta ciki a hankali.
Zaune yake a kujerar da ke kallon k'ofar shigowa, ganin mutumen da bata yi zato ba yasa wayar da ke hannunta ta sunɓule ta faɗi k'asa, hakan kuma ne ya jawo hankalin sauran jama'ar da ke wurin.
Bata damu da yanayin da zuciyarta ta shiga ba, na tsananta wurin bugawa, ta duk'a a hankali, ta ɗauki wayarta, ta ɗago da fuskarta a ɗaure tam, tamkar bata taɓa dariya a duniya ba.
Hannun Rukayya ta k'ara matsewa a nata, ta juya da sauri tana shirin komawa da baya.
"Jay..."
Ya kira ta da sark'ak'k'iyar muryarsa.
Chak ta tsaya, ba tare da ta juyo ba, hakan yasa Rukayya juyawa ta kai kallonta inda ta ji maganar ta fito.
Kuka ta saka mai k'arfi, tare da tura kanta tsakanin kafafuwan Mammynta, ga dukkan alamu, hakan ba zai rasa nasaba da fuskar Sadam da ta kalla ba.
A lokacin sai da ya ji tamkar k'asa ta tsage ya shige tsakaninta saboda kunyar da ya ji. Dak'yar ya ɗaga k'afarshi ya tunkari inda suke tsaye, sai dai sallamar Goggo da ta 'yar budurwar da ta biyo bayanta ɗauke da tray ya sa shi dakatawa, ba tare da ya kai inda suken ba.
"Dawo nan ki zauna Ummi."
Dak'yar Rukayya ta yarda suka juya cikin palon, har kuma yanzu bata daina kukan ba, tana kallon Sadam zata k'ara fashewa da wani sabon kukan tamkar wacce taga dodo.
A gefen Goggo suka zauna, hakan yasa shima sadam ya dawo inda ya tashi ya zauna, sai dai ya gagara sauke idonshi akan Jay da Rukayya ganin irin canjin da aka samu a gaba ɗaya yanayinsu.
Brothers ɗinshi maza guda huɗu da suka zo tare, su suka fara gaishe da Goggo, ta ansa fuskarta ba yabo ba fallasa, sai a sannan Jay ta gaishe da su, suka ansa cikin sakin fuska, haka kuma ko da basu sani ba sun tabbatar da ita ɗin ce tsohuwar matar Sadam, saboda Rukayya da suka gani mai asalin kama da shi.
Shiru na wani ɗan lokaci ya cigaba da wanzuwa a wurin, daga bisani Sa'id yayi gyaran murya ya fara magana.
"Mun so ace mun tadda Alhajin, sai dai cikin rashin sa'a bamu samu ganinshi ba. Amma tunda mun samu damar ganawa da ku zamu yi amfani da wannan damar mu bada hak'urin abinda ya faru. Wallahi babu ɗaya a cikinmu da ya san halin da Sadam ke ciki, sai fa bayan afkuwar abin nan sannan ya sanar da mu."
Salis da ke gefenshi ya ɗora da bayanin yadda rayuwar Sadam ɗin ta kasance, rabonshi da gida, da kuma dalilin barinshi gidan baki ɗaya. Yana gamawa Sa'id ya cigaba.
"Duk da akwai makircin asiri a tattare da shi, amma yayi gangancin wulak'anta matar da ta sadaukar mishi da farin cikinta, ya kuma guji 'yarsa, wacce ya tabbatar jininshi ce. Yanzu ku duba ku ga yadda yarinyar ke kuka saboda ganin fuskarshi. A yanzu bamu da abinda zamu faɗa, saboda abinda ya faru, ya riga ya faru, illa muna masu baku hak'uri akan abun, ayi a hak'uri a gafarta ma juna dan Allah."
Shiru Goggo tayi tana saurarensu, ta wani ɓangaren tausayin Sadam ɗin ya tsirga zuciyarta.
"Tabbas abinda ya faru ya riga ya faru, fatanmu ɗaya Allah ya yafe mana baki ɗayanmu."
"Madallah, mun gode k'warai, Allah ya sa mu fi k'arfin zuciyarmu. Kema kiyi hak'uri dan Allah, ki yafe duk wani abu da ya shiga tsakaninku."
Ya k'arasa yana duban Jay da kanta ke k'asa, a karo guda kuma Sadam ya rink'a yi mishi alama da hannu cewar yayi maganar maida aurensu.
Wata muguwar harara ya daka mishi, a haka suka ɗan sha lemun da aka kawo masu, sannan suka mik'e, Goggo ma mik'ewar tayi, suka yi sallama ta wuce ciki, su kuma suka fita zuwa harabar gidan.
Yana ganin kowa ya fita, ya rage palon daga shi sai ita, sai kuma Rukayya da tayi bacci a jikinta, ya mik'e ya tako zuwa inda take, a gabanta ya duk'a, tare da k'ura mata mayun idanunsa.
"How have you been?"
Banza tayi kamar baza ta ansa ba, haka ta rink'a jin muryarsa na ansa kuwwa a cikin zuciyarta.
"Good, I can see. Kin canja gaba ɗayanki, kin k'ara kyau abinki."
Wato mai hali baya fasa halinshi kenan, ta innata a cikin zuciyarta, sai dai ta kasa furta komai, kamar yadda ta gagara ɗora idanuwanta a kanshi.
"Kinga yadda Rukayya take gudu na ko? Me sa baki bata hak'uri on my behalf ba? Na ji kunya sosai yadda naga tana kuka lokacin da ta ganni. Please I'm so sorry for everything babe, please."
Sai a lokacin ta juyo ta kalle shi, a take ta dake zuciyarta, ji tayi ta samu wani confidence da yasa ta watsa mishi kallon raini.
"Ashe kana da kunya Sadam? Ashe akwai ranar da zata zo wacce har zaka ji kunyar abinda kai ma yarinyar da bata ji ko ta gani ba? Please idan wannan labarin ne ya zo da kai, ka tashi ka tafi dan bani da lokacin da zan ɓata wurin saurarenshi."
"Babe kiyi hak'uri mana, na zo dan in nemi gafararku, ki yafe mun ki dawo ɗakinki mu cigaba da zaman mu."
Kafin ta buɗe baki tayi magana, wayarta da ke rik'e a hannunta tayi beeping alamar text ya shigo, bata damu ba ta kai dubanta gare shi.
"In dan wannan ne, da baka ba kanka wahalar zuwa ba, dan na riga na yafe maka na kuma manta da kai da duk rayuwar bak'in cikin da nayi tare da kai. Dan haka ka sani, har abada ba zan k'ara zama k'ark'ashin inuwa d'aya tare da kai ba Sadam, babu wata soyayyarka da tayi saura a cikin zuciyata."
Text ɗin da ya k'ara shigo mata ne yasa tayi saurin buɗewa, ta fara karantawa.
'Ga ni a cikin gidan ku, 'll like to see to soon. SS'
'Ka same ni a guest room.'
Bata san lokacin da tayi rubutun ba har kuma ta tura, abu ɗaya da ta sani shine tana son bak'anta zuciyar Kazaure, watak'ila hakan zai sa ya fita a harkarta.
"You're lying."
Muryarshi ta dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa.
"I can see the love you've for me in your eyes. You love me and nothing can change that. Kiyi hak'uri ki yafe mun, ki zo mu zauna mu fara sabuwar rayuwa mai inganci. I promise to shower you with love and care. I love you Jay, so very much. I cant live without you."
Murmushin takaici ta saki, a karo guda tana jin kalamanshi na bugun zuciyarta, sai dai bata da wani option, and this is the best for both of them, zata tursasa zuciyarta ta hak'ura da son mutumen da ba za su taɓa k'ara kasancewa tare ba har abada.
Kallon shi tayi ido cikin ido, a karo guda ta girgiza kanta.
"That was then Sadam, A da na so ka, son da nike tunanin bazan taɓa iya fitar da shi daga zuciyata ba.
As for now, my heart is already giving to someone. Someone who will take care of me and the baby you live your life hating.
Idan da zaka ji shawara da ka daina nuna fuskarka a gaba na da sunan kana neman soyayyata, saboda na riga na shafe babinka a zuciyata, na manta da kai, da rayuwar da nayi tare da kai, na kuma riga da na damk'a zuciyata ma wanda ya cancanta."
"This is insane."
Ya fada yana kauda kai daga dubanta.
"You belong to me Babe, and me alone. Wallahi ba wanda ya isa ya raba ni da ke I love you, look into my eyes babe, zaki gane son da nike miki babu k'arya ko yaudara a ciki, i love you with all my body and soul."
Ya sassauta muryarshi, a karo guda hawaye suka sauka a kuncinshi, bai damu da yadda suka wanke mishi fuska ba, burinshi ɗaya Jay ta fahimci zazzafar k'aunar da ke harbin mishi zuciya.
"Babe please, you deserve no one, but me. Nine fa. Your Sadam. The man you love, you care for. Please dont do this to me i beg you."
"I did already Sadam. There come the man I'll spend the rest of my life with."
A dai-dai lokacin SS ya tura k'ofar palon ya shiga.
Juyawa yayi da sauri yana kallon k'ofar. Ganin mutumen da ya shigo ya sanya shi sakin wata dariyar da bai san ko ta mecece ba.
"But this is SS. My very good friend."
"Of course. And he's the man I choose to be with. Will you excuse me now please?"
Ta mik'e da shirin takawa zuwa inda SS ke tsaye, wanda ke son ya fahimci abinda ke faruwa.
Dariya sosai Sadam ya yi, daga bisani ya tak'aita, ya d'ago da idanunsa da suka canja color tuntuni. Cikakken sumar kanshi ya shafa, a karo guda ya juyar da kai yana kallon yadda suka tsaya.
Ganin perfect match din da suka bayar ya sanya shi sakin wani razanannen k'ara tun k'arfi, da alama bai san lokacin da ya sake shi ba.
"Bull sh*t! This totally bullbsh*t! You hear me?"
Ya tafi da sauri da shirin jacking din SS, idanunshi a waje domin yadda ya ke jin zuciyarsa, zai iya yin ajalinshi.
Cikin zafin nama Jay tayi gaggawar shiga tsakaninsu tana fad'in
"What's your damn problem with my decision? Ka kama gabanka Malam, we're done here."
"What's going on?"
SS ya tambaya yana kallon Jay, ya juya ya kalli Kazaure, kanshi ya gama kullewa, ya kasa fahimtar abinda ke faruwa.
Juyar da kai Sadam yayi, labbansa na k'asa ya tura cikin baki, ya kama waist dinshi da hannu daya, dayan yasa ya shafi tarin sumarshi, juyowar da zaiyi hawaye suka wanke kyakkyawar fuskarshi da ta fara fita daga hayyacinta.
"Tell me you're kidding please."
Yayi maganar da hawaye taf a idonshi.
"I'm not Kazaure, I love him, and I'll soon marry him."
Sosai kan SS ya kusa ya buga jin abinda Jay ta fada. Ta wani bangaren ya kasa gaskata kunnenshi, yayin da ta wani bangaren yake tunanin abinda ta ke shirin yi, a matsayinta na wacce yake neman soyayyarta, amma ta k'i amincewa.
"Enough of this bull sh*t!"
Sadam ya fada tun k'arfi cikin wata irin lion voice din da ta ansa kuwwa a gaba daya wurin.
Palon ya fara zagayawa, zuciyarsa na cikin tashin hankalin da bai san ta ina zai fara maganinsa ba.
Kallonshi Jay ta ke zuciyarta a k'ek'ashe, domin ta gama yanke ma kanta hukuncin rabuwa da shi ko ta wane irin hali.
"So this is what you're up to?"
Ya juya yana kallon SS, sannan ya cigaba.
"But we're friends Tafseer. Ain't we?"
Yayi maganar da lallausar murya, irin ta mai neman sulhu.
Duk da fahimtar manufar Jay da SS yayi, hakan bai hana shi jifar Sadam da kalaman da suka fito bakinshi ba.
"Of course we're. But banga abin tashin hankali a ciki ba. Ka saki mata zan aura, there's nothing wrong with it."
"Owwh really? There's nothing wrong with it? Alright then, but wallahi. Ka ji na rantse? Baka isa ba Tafseer. Jay is mine. She's a mother of my kid, so to me she belongs, and no one else. Kuma zan gwada maka kai baka isa ba, mayaudari kawai."
"Please out of this room Kazaure."
Jay tayi maganar idanuwanta a kasa, muryarta na wani irin rawa.
"Amma..."
"Now. Please!"
Ta katse shi cikin kakkausar muryar da ta razanar da Rukayya har ta farka a baccinta.
Idanuwansa ne suka k'ank'ance, a take zuciyarsa ta karye, ya rasa me ke masa dad'i a gaba daya rayuwarsa. Murya k'asa-k'asa ya fara magana.
"Babe idan zaki hukunta ni, ki hukunta ni ta kowanne hanya, but please don't do it this way. He's my friend. I can't bear to see you guys falling in love with each other. Please I'm begging you."
"Kana bata ma kanka lokaci Sadam. Idan baka sani ba then lemme tell you, wallahi ko kai daya ne namiji da yayi saura a wannan duniyar na hak'ura da kai, ba kuma zan iya cigaba da zama da kai ba. Ka nemi gafara na, na yafe maka. Then what else do you want from me? The remaining pieces of my broken heart?"
Murmushi tayi irin na takaici mai zafi a cikin zuciya, ta girgiza kanta, a karo guda hawaye suka silalo mata sannan ta cigaba.
"That's impossible Kazaure, bazan taba k'ara yin wannan gangancin ba. Never!"
Ta juya da sauri ta wuce ciki saboda kukan da Rukayya ta fara yi.
"Jay. Jay please..."
Sadam ya rink'a kiranta, amma ko kallon inda yake bata yi ba, ta shige ciki da saurinta.
Juyawa yayi gadan-gadan ya doshi inda SS ke tsaye, collar rigarsa ya damk'a, yana kokarin hade shi da bangon, sai dai a lokaci guda yasa hannu ya cire hannunsa da ke jikin collar tasa, ya daddage, ya wurgar da shi.
"Be careful Mr. Kazaure. Kayi sa'a I'm not as stupid as U're, amma yau da sai ka gane baka da wayo wallahi."
"Baka isa ba Tafseer. Me sa zaka yaudare ni? Me sa zaka ci amanata? I trusted you with all my life amma ka rasa ta ina zaka saka mun sai ta wannan hanyar ko? Zaka yi da-na-sani SS, ni Sadam Kazaure sai na baka mamaki wallahi."
A dai-dai nan Sa'id ya leko yana kiran Sadam tare da fad'in
"Kai muke jira Malam. Ka zo mu tafi."
Juyawa yayi yana nuna SS da hannu, daga bisani yayi k'wafa, ya girgiza kai ya juya ya fita.
Shi kam k'arasawa yayi cikin palon yana gyara wuyan rigarsa da ya fara squeezing, ya zauna a daya daga kujerun da ke wurin, ya dora kafarshi daya kan d'aya, yayi balancing hannuwanshi, a karo guda ya fara tunanin abinda ya wakana.
"So she used me."
Yayi concluding, yayin da ya gamsu da abinda zuciyarsa ta ayyana 100%.
Wayarsa ya cire ya typing mata text
'Let's talk, he's gone.'
'Okay.'
Tayi replying mishi.
Ba'a dade ba, ta fito kanta a k'asa, domin ta kasa gaskata abinda ta yi.
Bayan ta zauna ya d'ago yana dubanta, har yanzu kanta na kasa, ta gagara hada ido da shi.
"What's all this about?"
Ya tambaya cikin natsuwa, ya kuma gagara sauke idanuwansa a kanta, duk kuwa da yadda yake jin zafin abinda tayi.
"I'm sorry please. I just wanted to.. to get rid of him. Kayi hakuri dan Allah."
"Is that why you used me? Saboda I'm nothing to you, cuz he's the one only one da kike gani a matsayin namiji ko? You did good Jay, and thank you very much for that."
Ya mike da sauri, yana shirin barin palon.
Duk da kasancewarshi ba gwanin zafin zuciya ba, abin nan ya taba shi sosai, har yana ganin he's less important a wajenta.
"Ba haka ba ne fa."
Ya tsinkayi muryarta lokacin da ya kai k'ofar fita, wacce ya tabbatar da kuka take kasancewar yadda maganar ta rink'a rawa, dakyar ta iya furtata.
Chak ya tsaya, kamar zai juyo, domin a duniya idan akwai abinda ya tsana bai wuce kukan ta ba, amma ina irin kishin da ke nukurkusarshi ba zai taba barin shi ba, haka ya sa kai ya fita ya barta zaune a wurin.
Here come another chapter🙌🙌🙌
Lubbatu 😍👏
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro