BABI NA TALATIN
"Amma ka san baka cikin jerin mutane masu imani ko?"
SS yayi maganar idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, ya juya yana kallon yadda iska ke kaɗa bishiyoyin wurin cikin kwanciyar hankali, tare da busa musu sassanyar iska mai daɗi.
"Ban fahimce ka ba. Wace irin magana kake yi haka?"
"Baza ka fahimce ni ba dama, tunda ka kasance mutum marar tausayi, marar imani wanda bai san darajar mace ba. Ina tantama idan akwai zuciya a k'irjinka Kazaure. Ashe baka da mutunci ban sani ba? Ashe dama kana da MATA?"
Wani irin bugawa zuciyarsa tayi har yana sa hannu yana dafe wurin, idanunsa a waje ya juya yana kallon shi, sannan ya cigaba.
"Na daɗe ina jin labarin mazaje wanda su kan wulak'anta matayensu ta hanyoyi da dama. Da yawa cikinsu idan aka bibiya, laifin na matayen ne. Amma kai da yake ka kasance butulu, ma ci amana, da ka tashi sai ka wulak'antar da matar da ta baro iyayenta, ta biyo ka a matsayin mutumen da ta fi k'auna a gaba ɗaya duniyarta. Mutumen da ta mutunta, ta bama amanar ruhi da gangar jikinta. Mutumen da ta fawwala ma duk wata soyayya da ke cikin zuciyarta. Amma ka rasa ta wace hanya zaka saka mata, sai ta hanyar nuna k'yama ga abinda ta haifa, wanda ya zama gudan jininta, tsatsonta, abinda ya tsaga jikinta ya fito. Abun bai tsaya a nan ba, sai da ka haɗa mata da duk wani kalar wulak'anci na duniya da ka iya.
Baka da imani Kazaure, haka zalika ina tantamar addininka, anya ma kana tsoron Allah kuwa? Ban san haka kake ba, da tun asali ban buk'aci saninka ba, da ban ɓata lokacina wurin aminta da kai ba. Ina mai shawartar ka da tun muna mu biyu ka bani takardar sakinta, tun mahaifinta bai yi maka mummunan ɗaurin, da igiya zata yi rara ba."
Duk da bugawar da zuciyarsa ke yi, hakan bai hane shi sakin wani makirin murmushi ta gefen bakinsa ba.
"Me kake so ka gaya mun? Wai kana nufin duk neman da nike ma Jay dama tana wurinka? Lallai yau zan ga wanda ya tsaya maka a duk faɗin garin nan, dan sai ka fito mun da mata ko in faffasa maka baki wallahi, domin kuwa zan yakice amincin da ke tsakanina da kai, in yi maka rashin mutuncin da hankali ba zai taɓa ɗauka ba. Ina ka kai mun mata?"
Ya k'arasa maganar cikin wata kakkausar murya, da jajayen idanunsa a waje. A karo guda yasa hannu ya cakumi kwalar rigar SS.
"Get your hands off me, you bloody fool. Sanin kanka ne, bani da lokacin da zan ɓata wurin faɗa da ɗan giya. Ka bani takardarta nace, tun ban canja maka kamanni ba."
Hannuwansa da ya ke k'ok'arin dunk'ulewa SS ya rik'e gam. Kallonsa yake da idanuwansa a waje.
"Don't you dare!"
Ya wurgar da hannun ya faɗi k'asa, sannan ya cigaba.
"Da kake maganar aminci, ai ni na daɗe da yakice ka a cikin jerin mutanen da na sani ma, balle kuma amini. In baka sani ba, ina da-na-sanin, sanin ka a rayuwata Kazaure. Rashin mutunci kuma da kake magana, dama ina za'a samu mutunci wurin ɗan caca, mashayin giya? Ka ɓata wayonka wallahi, ina tausaya ma Rukayya, dan na tabbata wata rana zata yi da-na-sanin kasancewarka mahaifi a gare ta. Sai dai duk ba wannan ba, ka bani takardar sakin Jay, shine kawai buk'atata, akwai wanda zai kula da ita da 'yarka, tunda kai baka san daraja da mutuncinsu ba."
Duk da kasancewarshi ɗan cacan, haka zalika mashayin giya, amma a duk lokacin da wani yayi mishi wannan gorin, to fa sai yayi rashin mutunci ma ko wanene kuwa.
Manya-manyan idanunsa da suka daɗe da canja kala zuwa ja, ya k'ank'ance. Kyawawan jajayen laɓɓansa, ya cije, a karo guda wata 'yar kwalla, ta yayyafo a gefen idonsa na dama, baiyi wata-wata ba, ya dunk'ule hannunsa ya kai ma bakin SS naushi.
"Be careful!"
Ya faɗa yana wani irin huci tamkar mayunwacin zakin da ya ci karo da nama, haka kuma gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa sun tashi, sun fito ruɗu-ruɗu ana ganinsu.
"Ka san abinda bakinka zai faɗa a kaina, dan wallahi da ace ba kai ba ne, da babu abinda zai hana ni shak'e wuyan koma waye in aika shi lahira, in ya so nima sai dai a kashe ni. Kuma kayi gaggawar fito mun da mata, tun ban kai ga yin k'aranka ba."
Hannu SS yasa ya na shafe jinin da ya fara ɗisa daga bakinsa, kallon Sadam yake irin duban da aka fiya yi ma marassa hankali, a lokaci guda yana sakin murmushi.
Handkerchief ya cire ya dafe wurin, bai ce komai ba ya fara k'ok'arin buɗe k'ofar yana shirin fita.
Farɗo shi Sadam yayi ya dawo da shi ciki, a karo guda ya danna central lock a motar.
"Kana tunanin zan bar ka ka fita a wurin nan ba tare da ka sanar mun inda matata take ba? To wallahi baka isa ba."
Bai ce komai ba, ya cire wayarsa ya fara k'ok'arin kiran wata number.
Da sallama aka ɗaga ta wancen ɓangaren, bayan yar gajeruwar gaisawa, ya bukaci mai wayar ya haɗa shi da Jameela.
Sai da ya tabbatar da an bata wayar, sannan ya danna hands free suka fara magana da ita.
Wani wawan ihu Sadam ya saki tare da wartan wayar.
"You can't leave me Jameela. Kinyi gangancin barin gidana. But trust me, I'll find you. Wallahi I'll. Definitely, I'll find you."
Ya wurga ma SS wayar, ya kuma cakumar wuyan rigarsa.
"INA KA KAI MUN MATA?"
Yayi maganar da wata irin lion voice, sai dai ko gezau SS bai yi ba, haka ya sa hannu ya cire hannayensa da ke jikin wuyan rigarsa.
Ganin ba shi da niyyar magana, yasa Sadam ya tada motar a sikwane, ya ɗauki hanyar gidan SS.
Murmushin takaicin da ya fi kuka ciwo SS ke yi, ta wani fannin kuma yana jin kamar ya shak'e wuyan Kazaure ya mutu, kowa ma ya huta.
A haukace ya iso k'ofar gidan ya fara danna horn tamkar zai banka gate ɗin ya shiga. Da gudu mai gadin ya zo ya buɗe k'ofar, kafin ya tura motar ciki, yayi wani wawan parking, ya fita ko rufe k'ofar motar bai yi ba ya shige ciki, sai dai ga mamakinshi, k'ofar palon a rufe take gam da makulli.
Dawowa yayi ya same shi zaune a motar yana danna wayarsa, tamkar bai san abinda Sadam ɗin ke nufi ba.
"Shiga ka fito mun da matata."
"Kai ka ke ɓata ma kanka lokaci Kazaure. Sanin kanka ne a yadda ka ji muryar Jameela, kasan tana cikin kwanciyar hankalin da tasa ta manta da kai da irin bala'in da ka saka ta. Wallahi, ka ji rantsuwar musulmi kenan, ko ka yi shawarar rubuta mun takardar sakinta, ko kuma yanzun nan in saka ka cikin gidan nan in rufe, har sai na shaida ma mahaifinta ya zo da bataliyar police ɗin da zasu kama ka. Haka kuma idan kana tunanin akwai wata soyayyarka da tayi saura a zuciyar matar da ka muzgunawa, to kana yaudarar kanka. Ta daɗe da shafe babinka a littafin rayuwarta. Marar zuciya kawai."
"Naka wasa ne SS. Jay tawa ce. Kai ɗin nan baka isa ka raba soyayyar da muka gina sama da shekaru shidda ba. Baka isa ka raba ni da ita ba, idan ka fasa kiran mahaifinta baka haifu a cikin naka iyayen ba. Idan baka sani ba ka sani, Jay baza ta iya rabuwa da ni ba, in fact, rayuwarta is incomplete without me! Kasa ido kayi kallo, zan nemo ta, zan dawo da ita gare ni, sannan kuma zan gwada maku gaba ɗaya kuskuren da kuka yi na neman raba ni da ita. Fitar mun a mota Dallah Malam."
Kallonshi kawai SS ya ke, a zuciyarsa yana ayyana, anya Sadam bai samu taɓuwar hankali ba?
"Baka isa ba Kazaure, domin kuwa ba ni nace ka kawo ni nan ba, kai kayi niyya ka zo, dan haka baka isa ka ajje ni nan ba, kasan ina da ayyukan yi a wurin aikina ai."
K'ala bai ce ba, ya shiga motar ya ja a hargitse, ya fita gidan.
A k'ofar bankin yayi parking, hakan ya ba SS damar fita, sai dai shi bai fito ba, sai ma reverse da yayi yana k'ok'arin barin wurin.
Waya SS ya ciro a aljihunsa da niyyar kiran Baffa, ko me ya tuna kuma, sai ya maida wayar ya juya ya shige ciki.
**
Gida Sadam ya wuce, ya rufe ko ina ya shige k'uryar ɗaki ya zauna yana wani irin numfashi, bai ankara ba ya ji hawaye na silalowa saman fuskarsa, wanda ya rasa gane ko na menene. Na tafiyar Jay ne, ko ko na halin da yake ciki ne?
Bai sani ba.
Hakan yasa ya fasa wani gagarumin ihun da hatta ɗakin da yake ciki sai da ya ansa.
Kuka ya dinga yi wi-wi, irin kukan da ko da mahaifinsa ya rasu bai yi irinsa ba.
Ya ɗauki a k'alla mintina talatin yana abu ɗaya, k'arshe wata dabara ta faɗo mishi, inda ya yanke shawarar kiran yayanshi Sa'id, ya faɗa mishi bashin da banki ke binshi, in ya so ko a kuɗin gadonshi ne a cire a bashi ya biya.
Har ya fara kiran number sa, sai kuma wata zuciyar ta gargaɗe shi kan yin hakan tamkar ya tona asirin halin da yake ciki ne.
Take ya kashe wayar, ya wurgar da ita, zuciyarsa na bashi shawarar cewar caca ce kawai zata kawo masa kuɗaɗen da ya ke da buk'ata.
Da wannan shawarar ya aminta, a haka kuma bacci mai nauyi yayi awon gaba da shi.
**A week later.
Tun daga waccen ranar, Sadam bai k'ara komawa banki ba, baya zuwa ko ina, kullun yana gida k'unk'ume a k'uryar ɗakinsa, illa idan ya ji bak'in ciki ya ishe shi, maimakon ya dinga kai kukansa ga Allah, kamar yadda Sa'id ya shawarce shi, a'a, sai dai ya fita ya siyo giyarshi, ya sha yayi tatul, har sai ya manta abinda ke yawo a cikin k'walwarsa, sai dai matsala ɗaya, da ke addabarsa ita ce, ko wace irin giya zai sha, dai-dai da rana ɗaya bai taɓa manta fuskar Jay, da yanayinta ba, wanda a yanzu yake ganin tamkar babu wata mace a duniya, da ke da zubi da tsarin surarta.
Fitowa yayi, ya shige motarsa zuwa Hotel. Ba dan komai ba, sai dan saboda irin sa'ar da yake ji a tattare da shi, haka kuma ya gaji da zaman cikin gidan, dole yana buk'atar fresh air.
A harabar Hotel ɗin yayi parking ya fito, ya rufe motar, kafin ya zarce zuwa ciki.
Gefe daya ya samu ya zauna, bayan an kawo masa kwalbar barasa, yana korawa hankalinshi tashe, domin kuwa ya daɗe da yin bankwana da kwanciyar hankali.
A sannu yake duban mutanen da ke zaune saman faffaɗan teburin da ake buga caca.
Cak idonsa ya tsaya kan wani farin inyamurin mutum, mai cikakkar halitta da k'aton tumbi, jikinsa sanye da wani kakkauran leshi ɗinkin fadee, kansa sanye da hula, irin wacce suke lankwasawa ɗin nan.
Ganin yadda kuɗi suka zauna ma mutumen yasa zuciyar Kazaure ta gama raya masa cewar ya samu wurin da zai tatsi kuɗin da zai biya banki bashinsu.
Mik'ewa yayi da kwalbarsa a hannu ya isa wurin manajan da ke kula da wurin, bai yi wata-wata ba, ya ɗora makullin motarshi, kasancewar ita ce kaɗai abu mafi tsada da yayi mishi saura, ya juya ya koma kan teburin ya zauna, yayin da aka biyo shi da cards ɗin buga cacar.
Sai da suka gama wacce ya samu suna yi, sannan ya ɗora na shi suka fara gwabzawa da inyamurin nan.
Cikakkiyar awa ɗaya ba su yi da farawa ba, Sadam ya samu nasarar ciyo zunzurutun kuɗi nera dubu ɗari bakwai a wurin inyamurin, tare da dawowar motarsa da ya ɗora a kai.
Ihu jama'ar wurin ke yi, abun mamaki har da inyamurin da aka cinye, a karo guda ya sa hannu ya daki kafaɗar Sadam.
"What a boy!"
Inyamurin ya faɗa, faffaɗar fuskarsa ɗauke da murmushi mai sauti, a karo guda ya kama hannun Sadam, tare da taimaka masa ya kwashi kuɗinsa suka fito a tare hannuwansu cikin na juna, abinda ya rink'a ba al'ummar wurin mamaki har ma da Kazaure.
Gaban motar Sadam suka isa, ya buɗe ɗayan gefen ya zuba kuɗinsa, sannan ya dawo inda mutumen yake, ya bashi hannu suka gaisa.
"Na daɗe ina neman hazik'in mutum ɗan caca irinka, sai dai ban samu ba."
Murmushi kawai Sadam yayi, hakan ya ba mutumen damar cigaba.
"Zan ɗaga maka darajarka, in ɗaukaka fasaharka zuwa wani mataki da baza kayi tsammani ba."
"Ban fahimce ka ba."
"Zan yi signing ɗinka da wata k'ungiyarmu da mu kan tura matasa irinka zuwa Las Vegas domin gwanancewa a kan wannan sana'ar. Cuz a gaskiya jarumtakarka, ta fi k'arfin ka zubar da basirarka a wannan ɗan k'aramin Hotel ɗin wanda na tabbata duk in ka samu kuɗi da yawa a nan basu wuce miliyan guda."
Mamaki ne sosai shimfiɗe saman fuskar Kazaure, abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa shine, tunanin yadda zai tafi wata k'asa, ba tare da Jay ta dawo gare shi ba, sai dai wata shawara da ta faɗo mishi tasa ya saki murmushi, ya ɗago yana kallon mutumen.
"Ya za'ai in yarda da maganarka?"
Dariya yayi, ya ciro katinsa mai ɗauke da address ɗinsa na New Mexico ya mik'a ma Sadam, ya ansa yana dubawa, sosai ya gamsu da bayaninsa, ɗari bisa ɗari.
"Yi mun cikakken bayani ta yadda zan fahimta mana."
"Kada ka samu damuwa, idan ba ka da wani uzuri yanzu, mu shiga daga ciki, sai muyi magana cikin sirri, kasan komai yana buk'atar sirri."
Kamar bai yarda da mutumen ba, sai dai kuma da ya tuna da cewar yana da buk'atar kuɗi, sai ya juya suka mik'a zuwa ciki.
Bayanai mutumen ya fara yi mishi ɗaya bayan ɗaya, wasu yana ganewa, wasu kam sai a hankali. A k'arshe inyamurin ya mik'e ya shiga toilet kamar mai shirin yin wani abu, sannan ya fito.
Kasancewar barasar da ke jikin Sadam ta fara ɗibar shi, sai bai kula da yanayin da mutumen ya fito ba, gadan-gadan yayi kansa, ya fesa masa wata farar hodar da ke hannunsa, bai yi cikakkun mintina biyu ba ya faɗi a wurin tamkar marar numfashi.
Da sauri ya tura shi cikin restroom din, ya nemi aljihunshi ya lalubo key ɗin motarsa.
Cikin wani irin sauri ya juya ya fita. Wurin motar ta Sadam ya isa, ya buɗe, kuɗaɗen da ya zuba suna nan ajje a gefe, haka zalika gate pass ɗin da akan ba mutum kafin ya shiga ciki, shima yana nan a tsakanin kujerar driver da ta mai zaman banza, haka ya shiga ya tada motar ya isa ya basu abinsu, ya mik'a titin, ya bar wurin baki ɗaya.
Sadam Kazaure...this is just the beginning😂😂😂
Let's party for this chappie. 👏👏
Who's happy?
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro