Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA SHIDDA


***

ATM card d'inta yayi expired kwana biyu da suka wuce, tun jiya taso ta shiga ta canja sabo, yanayin lectures dinta bai bata dama ba.
Dole ta san abin yi, domin tana da buk'atar cire kud'i.

Tsaye take a traffic jam na k'ofar k'waya, cunkoson ababen hawa a daidai wannan lokacin ya kan bakanta zuciyar mai jiran tsammani. Idanunta ta sauke kan agogon da ke daure a hannunta, ganin lokaci na shirin rugawa ya sanya ta dukan sitiyari, tana mai danna oda da duk karfinta.

A duk sa'ar da ta iso gaban Zenith Bank, abu na farko da kan fado zuciyarta shine sunan Jameel sarkin naci. Jameel masoyin Jay ne na a mutu, ma'aikaci kuma a bankin da take ajiyar kud'i.
Wulak'anci na gidan duniya babu kalar wanda bata yi ma Jameel, amma ya kasa gane cewar ita d'in ba tsarar irin shi bace.
Da wannan tunanin ta gyara parking, ta ciro bak'in tabarau kirar Versace ta mak'ala a idanunta, ta fito cikin zubinta mai tsantsan kwarjini da haiba, ta taka cikin tsanaki zuwa k'ofar shiga.

Wurin da aka rubuta customer care ta karasa ta zauna a kujerar da ke fuskantar ma'aikacin da ko kallon inda take bai yi ba.

"Errnmmm"
Ta fara gyaran murya a hankali.

A zahiri bashi da niyyar motsawa, sai dai a wannan karon ya d'ago manya-manyan idanunsa masu haske, yana satar kallonta.

"Ran gimbiya Jay ya dade."

Muryar Jameel ta ratsa shirun da ya shiga tsakaninsu.
'Ya Allah!'
Tayi furucin a kasarzuciyarta. A zahirance, ta dago tana mai sauke wulak'ance duba gare shi. Kamar baza tayi magana ba, cikin murya marar karfin amo ta furta

"Sannu fa."

Baki bud'e ya zauna a kujerar gefenta, yana kallonta da mamaki, domin kuwa tun ranar da ya santa, bai ta6a jin kalma mai dad'i irin wannan ta fito a bakinta ba.

"Akwai matsala ne?"

Ya tambaya yana k'are mata kallo, a zuciyarsa yana jin akwai ranar da zata zo, wacce Jay zata sassauta wulak'ancin da ta kan mishi, har ma su samu damar dai-daita kansu.
Hankalinta na kan waya ta ansa da,
"Zanyi renewing ATM card d'ina ne, sai dai naga alamar wanda ke kan aikin kaman bai san darajar customers ba."

Dariya Jameel ya saki mai dan sauti, ya kai hannu ya shafo gashin da ya taru a gefen fuskarshi,

"In dan wannan ai da kin kira ni nasa anyi miki, in je har gida in kai miki. Ina da wani amfani ne da ya wuce wannan?"

Kallon da take mishi yanzu irin kallon tausayi ne, irin kallon da ke nuni da cewar tabbas yana tare da ta6in hankali.
Sai da ta ja ajiyar zuciya, fuskarta da alamun kosawa, ta kafe shi da idanu

"Kana tunanin akwai irin ka a jerin mutanen da nake adana numbers d'in su cikin wayata? Dan Allah ka koma bakin aikinka, wallahi bani da lokacin batawa."

Cikin zafin rai ta maida dubanta ga Kazaure,

"Malam zaka ajje abin nan kayi attending customer d'inka ko kuwa?"

A tsanake ya d'ago ya k'are mata kallo, bai ce uffan ba, ya mayar da kallonshi ga kwamfutar dake gabansa. A daidai lokacin Jameel ya mik'e yana fadin
"Please attends my wife to be Kazaure."

"God forbid."

Ta fad'a cikin k'unar zuciya. Bai ce komai ba sai murmushi tare da shafar sumar kansa, ya wuce da hannayensa duk biyun zube cikin aljihu.
Abinda ya ke ya bari, ya juyo da kallonsa gare ta, ta dago cikin rashin sa'a ta sauke idanunta cikin nasa. Cikin dakushewar murya, mai hade da sanyin jiki ta furta

"Ina son form zanyi renewing ATM card d'ina."

Bai ce k'ala ba, ya d'auko form ya mik'a mata, ya kuma maida kansa a aikin da yake, amma lokaci zuwa lokaci ya kan saci kallonta, inda a zuciyarsa yake yaba tsarin halittarta, wacce ya tabbatar ba ta dace da mazaje irin su Jameel ba.
Bayan ta cika ta mik'a masa ya ansa ba tare da ya kalleta ba.

Yadda yake abubuwan shi cikin jan ajin da bata san ko yanayinsa bane, ko kuwa yayi hakan dan ya birgeta ne, yasa taji zuciyarta ta cure a wuri guda, haushinsa na ba gaira ba dalili ya darsu a kirjinta, har tana jin kamar ta wanke shi da marin da zai dawo da shi hayyacinsa.
Wani abu da bata fahimta ba shine yadda ta kasa dauke idanunta a kansa, tana mai lura da dukkan motsinshi, tana kuma kallon yadda yake shigar da abinda ta bashi cikin na'ura mai kwakwalwa, cike da sanin makamar aikinsa.
Ya gama tsab, ya d'auko ATM d'in ya saka yace tayi activating pin d'in ta.

Sai da ta gama tsab, ya dago da murmushin da ta kasa fahimtar manufarshi ta gefen kumatunsa, ya damka ATM din da ya nannade da farin hankacif dinshi gare ta.

"Thank you."

Ta tsinkayi muryarta da fadi, labbanta kunshe da murmushin birgewa.
Murmushin san nan har yanzu kunshe da bakinsa, a wannan karon yana mai bayyana jerin fararen hak'oransa na sama.
Muryarsa mai zurfi ya kaikaita,  k'asa-k'asa ya furta

"Gaisuwa ya kamata ki fara koyowa, kafin ki dawo kiyi godiya."

Tsaye tayi tamkar kasa ta bude ta shige tsakaninta, cikin karfin hali irin nata ta juya tana kallonsa.

Kamar ba shi yayi maganar ba, idanunsa na kan allon kwamfutar gabansa ya ci gaba

"There is my number, ina jiran godiyarki idan kin dawo daga makarantar koyon sallama tare da gaishe da mutane."

Bai kara komai ba daga haka, yaja earpiece d'in dake jone da kwamfutarsa, ya mak'ala a kunnuwansa, bakinsa na kara fadada zurfin murmushinsa.

Watchaaa say bout this?😂😂😂😂

Just one word for Sadam Kazaure.🔥

A word for Mr. Jameel🤣🤣

What's happening to the spoilt brat? Will she call the amiable Mr. Gutsy?😎😎😉😉

Drop yo comments biko, i promise to read every single one of it.

Nd don't forget to vote nd share with loved ones. 💃💃💃

I heart y'all💖💖

Best regards, Lubbatu🖤

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro