BABI NA SHA TARA
Kuka take mai tsananin zafi, hannayenta duk biyun tasa ta kama shi ta k'ank'ame, sai dai bai ma san tana yi ba, baccinshi ya ke cike da kwanciyar hankali.
Ganin babu abinda kukan zai k'are ta da shi yasa ta tashi ta shiga toilet tayi wanka, tare da alwala ta fito ta kabbara sallar isha'i ta gama, tayi zaune a wurin tana k'are ma Sadam kallo, da alama bashi da sauran damuwa.
Bata tashi a wurin ba sai kusan k'arfe d'aya na dare, shima baccin da ke idonta ne ya ci k'arfinta, a hankali ta ra6a gefenshi ta kwanta, inda ta sa hannu ta rufe masa bakinsa da ya hangame.
*
**
Sannu a hankali ya fara bud'e idanunsa, hasken ranar da ya fara lek'owa ta windon d'akin ne ya haske santaleliyar fuskarsa wanda ya sanya shi d'ora hannu a saman fuskarsa, yana mai juyi zuwa gefenshi.
Zaune ya mik'e yana kallon jikinsa, yanayin da ya samu kansa ne yasa ya fara tunano abinda ya faru a daren jiya, take ya dafe kai, hotonan abinda ya wakana na cigaba da dawo masa, a wani 6angaren na zuciyarsa yana jin haushin irin aika aikar da yayi.
"Its just a cup. Ya Allah!"
Yayi maganar a bayyane.
"Ko dan na dad'e ban sha ba?"
Ya kuma tambayar kansa shima a bayyane. Bai samu ansar ba, alarm d'insa ya fara ruri, dan haka ya mik'e ya wuce toilet yayi wanka tare da alwala ya fito.
Sallah ya kabbara a haka ta shigo ta same shi, har ya gama tana zaune a gefen gado yayi addu'a ya shafa, sannan ya isa gabanta.
"How's my Angel doing?"
Bata ce komai ba ta juyar da kanta, hakan yasa ya tsargu da kansa, a hankali ya matsa ya koma gefenta ya zauna tare da kama hannayenta duk biyun.
"What's wrong with you darling?"
"Me ya faru da kai jiya?"
Ta jefa mishi tambayar tana kallon k'wayar idanunsa.
Tarin sumarsa ya shafa, yayi duban tsanaki zuwa gare ta, bai ce komai ba, ya sake hannunta ya mik'e ya isa gaban mirror ya fara shafa mai.
"Magana nake kayi mun banza."
"Na ji ki, but kada kisa abin a ranki. Pretend like its never happened."
"How can I? Image d'in abun ba zai ta6a gogewa a zuciyata ba. You better tell me the truth, dama kana shaye-shaye?"
A hargitse ya juyo ya watsa mata mayun idanunsa.
"Wane irin magana kike yi haka?"
"Saboda mashayi ne kawai zai iya yin abinda kayi jiya, kuma ka dad'e baka dawo gida ba, and kayi abubuwan da ban ta6a sanin zaka iya su ba."
"Will you just shut up please?"
Ya fada vikin dakakkiyar muryarsa.
Calm down Kazaure
Ya shafa tarin sumarsa, yana mai kankan da murya ya ci gaba
"Me sa baza ki gane ba? Well, an samu matsala ne jiyan nan, so ki basar da maganan kawai."
Hawaye ne suka fara bin kumatunta, ta mik'e ta isa, gabanshi tana kallon yadda ya maida hankali ga abinda yake ba tare da ya juyo ya kalle ta ba.
"Ta ya zan iya mantawa Sadam? Wato hasashena ya zama gaskiya kenan ko?"
Juyowa ya yi cike da jin haushin yadda take magana, a zucoyarsa yana jin kamar ya share ta, sai dai ya daure, ya bud'e hannayensa yana fad'in,
"Come here darling."
Babu gardama ta fad'a jikinsa, domin abinda ta fi buk'ata a dai-dai lokacin kenan. Kanta ya fara shafawa, har sai da ta daina kukan, sannan ya zaunar da ita a stool d'in dake gaban mirror, ya duk'a gabanta ya kama hannayenta yana wasa da su a hankali, daga bisani ya fara magana.
"Babe tsautsayi ne kawai, kin san ba hali na ne ba. Mun je dinner bikin wani christian colleague d'inmu ne suka yi serving d'inmu giya ba tare da mun sani ba, ba ni kad'ai bama almost duk mutanen dake wurin sun sha, but i promise you next time, bazan k'ara shan komai a waje ba. Kinji?"
"Amma ni ai baka sanar da ni zaka je wani dinner ba."
"Yeah, banyi niyyar zuwa ba nima, mutane ne suka yi forcing d'ina. Dan haka kinga maganan nan ya wuce kawai tunda dai na fad'a miki yadda aka yi."
"Na ji, amma dan Allah next time ka tabbatar ka duba komai aka baka kafin ka sha. Kaga kada inje wataran a baka abinda zai kashe mun kai."
"Stop saying that please, Zan kiyaye kinji 'yan matana."
Dariya ta saki tare da shafa gefen fuskarsa.
"That's why I so much love you. Akwai ka akwai jin magana."
"Ba dole na ba. Kinsan bana son abinda zai ta6a kyakkyawan wurin nan."
Yayi maganar tare da dafa setin da zuciyarta take.
"To tashi ka k"arasa shirinka, ka riga ka makara ma."
"Oyaa help me, tun ban k'arasa makara ba."
"Right away."
Ta mik'e tare da ciro masa kayan da zaisa, ta fito masa da takalma, sannan ta wuce kitchen ta had'a masa abinci a lunchbox, ta hado mashi tea a cup, ta dawo d'akin.
Tsaye ta same shi yana gyara necktie d'inshi, cup d'in hannunta ta bashi, sa'adda ta kama necktie d'in ta k'arasa d'aura masa, shi kuma yana kur6ar tea d'in hankalinshi kwance.
Hannuwansu sagale da na juna suka fito zuwa bakin motarsa, ta duk'a tayi pecking d'insa, sannan yayi mata sallama ya tada motar ya tafi.
《》
Kayan da ke hannunta ta zube a saman kujera, sa'adda ta zauna, tare da cire mayafin da ke kanta.
"Woah! Na gaji wallahi, ga wani irin ciwon kai da nake ji, na manta mu siyo magani ma."
K'ofar palon ya rufe, ya k'araso gabanta. Ya ciro roban ice cream ya mik'a mata.
"An shi nan da kinsha ciwon zai bari."
"I don't think so, nafi three days ina yin shi fa, and kusan kullun da fever nake kwana wallahi."
Ta anshi ice cream d'in ta bud'e, tasa spoon ta d'auka ta kai bakinta.
"Amma me sa baki fad'a mun ba, though wani lokacin ina jin jikinki da zafi, but banyi tunanin fever ba ne ba…"
Yunk'urin aman da ta fara yi ne ya katse maganar tasa, da sauri ya isa gabanta
"Hey, what's wrong?"
Kafin yayi wani motsi ta wurgar da roban ta mik'e da gudu ta shige toilet.
Amai ta dinga yi sosai, har sai da ya tausaya mata, shi ya taimaka mata da ruwa ta gyara jikinta, sannan ya kamata suka fito.
Palo suka dawo, ya zaunar da ita a kujera, ya ɗauki gyalenta ya sanya mata, ya juya ya ɗauki makullin mota, sannan ya kamata.
"Tashi muje asibiti Babe."
"Dare ya riga yayi fa, mu bari zuwa safiya kawai. Na ji ma na daina ciwon kan."
"Are you sure?"
"Da gaske fa."
"Alright then. Amma me kike tunanin ya saka ki amai har haka?"
"I can't say gaskiya. Kaman ice cream ɗin nan ne."
"Ke fa kike ta cewa zaki sha, kuma ni tunda nake ban taɓa ganin ya saka ki amai ba. Bakya tunanin wani abun?"
"Bakomai, kai dai kada ka wani damu fa."
"No, seriously hankalina a tashe yake. Gaskiya ki tashi muje asibiti."
"Ba fa inda zamuje cikin daren nan, kayi hak'uri zuwa safe."
Ba wai dan Sadam ya so ba haka kawai ya hak'ura duk kuwa da dukan tara-tara da zuciyarsa ke yi, tare da addu'ar kada Allah yasa hasashensa ya zama gaskiya.
A daren ranar haka ta kwana da wani irin zazzaɓi mai zafi, hakan yasa Sadam ya k'ara sarewa. Duk da ba sanin alamomin masu ciki yayi ba, amma zuciyarsa ta kasa natsuwa, haka kuma a lokuta da dama ya kan ji ance mata suna amai da zazzabi mai mugun zafi a farko-farkon samuwar cikinsu. Sai dai ta wani ɓangaren ya kan ɗan samu kwanciyar hankali idan ya tuna da ta na shan contraceptive pills din da yake bata (maganin hana ɗaukar ciki).
Amma kuma bugun zuciyarsa ya kan tsananta idan ya tuna ranar da ya je mata yana cikin maye.
Da wannan tunanin ya kwana, hakan yasa yana tashi da safe bai yi maganar kaita asibiti ba, ya fito ya wuce wani chemist mafi kusa da su ya anso PT strips (pregnancy test strips) ya fito.
Ko da ya koma a duk'unk'une ya same ta kyarma kawai take yi, saboda azababben sanyin da take ji, duk kuwa da zafi irin na garin Maiduguri.
Gaban gadon ya isa ya ɗan ɗaga bargon da ta lulluɓa da shi, yasa hannu ya taɓa wuyanta, zafin da ya kai mashi bak'unci ne yasa shi sauke hannun cikin gaggawa.
"Sorry Babe. Daure ki tashi kiga"
"Ya kamata muje asibiti Sadam, ina jin jikin nan sosai wallahi."
"Zamu je ai, now tashi kiyi amfani da abin nan, daga nan sai kiyi wanka muje asibitin."
Da haka ya taimaka mata ta mik'e, ya ɗauko towel ya mik'a mata, ta ansa ta ɗaura, ya kama hannunta suka wuce toilet ɗin.
Abun ya fitar ya bata, yace ta karanta taga yadda ake amfani da shi, ta ansa ta duba anan ta gane amfaninsa. Murmushi tayi, tare da girgiza kai. Process din ta bi tayi amfani da shi, kafin tayi wankan ta dawo.
Zaune ta same shi ya buga uban tagumi da alama ya faɗa kogin tunani, domin ko fitowarta bai ma ji ba.
Gabanshi ta isa, ta sa hannu ta dafa kafaɗarsa
"are you ok?"
Firgit ya ɗago,
"Ina abun yake?"
"Yana ciki."
Bai ce komai ba ya tashi ya shige toilet ɗin, strips ɗin ya ɗauka wanda dama a k'alla ana son a barshi yayi kamar minti biyar, ta yadda za'a gane ainahin gaskiyar gwajin da aka yi.
Abinda idon Sadam ya gani ne yasa shi dafe kai, hannunsa dafe da kirji yayi baya tare da jinginewa jikin bango.
"Positive?"
Yayi maganar da k'arfi, wanda hakan yasa ta faɗo toilet ɗinn cikin sauri, tana tambayar abinda ke faruwa.
Bai bata ansa ba ya cigaba da girgiza kai.
"No, no.. This can't be."
"What?"
Ta tambaya lokacin da ta sa hannu ta anshe strips ɗin ta na dubawa.
Abinda ta gani, wanda ya tabbatar mata positive kenan, yasa ta washe baki, ta isa da sauri tana kokarin rungume shi, amma ya sa mata hannu.
"Wait please. Don't tell me you're happy with this?"
"Of course I am, wannan ai abun farinciki ne. Nan ba da jimawa ba zamu zama parents, ya kamata muyi farinciki mana."
"Dallah dakata mana"
Yayi kanta da sauri, ko me ya tuna kuma, sai kawai ya juya, yasa hannu ya shafi tarin sumarsa, ɗayan hannun rik'e da kugunsa, ya ma rasa menene abinda ya kamata yayi.
"What? Ban gane me kake nufi ba."
"Well, fito muje asibiti. Ban yarda da abin nan ba. Jira ma tukun, wai kina shan maganin nan da nake baki ko kuma kina fakar idona ne ki watsar?"
"Ka ji ka da wani magana, abinda a gabanka nake sha, kai fa kake bani da hannunka. And me ma ya kawo maganar maganj?"
"Ya Allah! Kinga shiga kisa kayanki ki fito muje asibiti kawai."
Daga haka ya wuce ya fita, gaban mota ya buɗe ya shiga, kasa yayi sosai da seat ɗin ya shingiɗa, tunanin yadda abin nan ya kasance kawai yake yi, inda ya gama yanke shawara abinda zai yi, matsawar suka je asibiti aka kuma tabbatar da gaskiyar lamarin.
A haka ta fito ta same shi, ya haɗa zufa idanunsa a rufe, bai ma san da isowarta ba.
"Sadam."
Ta kira shi a hankali, dan ta rasa dalilin da ya sa shi rasa natsuwarsa cikin ɗan kankanin lokaci.
Bai tanka ta ba ya tashi zaune, ya gyara zaman kujerarsa, sannan ya tada motar, hakan ya bata damar shiga ta zauna, zuciyarta duk a cunkushe duk kuwa da farincikin k'aruwar da suka samu da take yi.
Shiru ne ya ratsa motar, babu wanda ke ce ma ɗan uwansa komai, har suka iso asibitin, kasancewar private ne, sai basu sha wahala wurin ganin likita ba.
Bayani likitan ya bukaci Jay ta masa na abubuwan da take ji, a take ta zayyana mishi komai, hakan yasa yace su biyo shi zuwa ɗakin scanning.
Idon Sadam kyar akan allon na'urar, sai dai ya kasa fahimtar komai, cikin ɗimuwa ya kai duba ga likitan ganin yace Jay ta mik'e ta gyara jikinta.
"She's four weeks, four days pregnant. Congratulations Mr. Kazaure."
Ya mika masa hannu, amma Sadam ya bige hannun ya mik'e.
"What the f*ck! Pregnant?"
"Sure. Are you alright?"
Likitan ya tambaya yana kallonsa, fuskarshi cike da alamar tambaya.
"I'm not!"
Sadam yayi maganar a tsawace, kan shi tsaye ba tare da ya damu da kallon da likitan ke masa ba.
"Whats your problem?"
Jay da ta k'araso gabansa ta tambaya, tana kokarin kama hannunsa. Ganin hakan yasa likitan ficewa yana faɗin
"ku same ni a office."
Hannunta Sadam ya kama, fuskarsa ta gama bayyana halin da zuciyarsa ke ciki, juyo da ita yayi, ya zaunar ta a kujerar da ya tashi, sannan ya duk'a gabanta, yasa hannu yana shafar kumatunta.
"Babe me kike ganin ya dace ayi da cikin nan, dan gaskiya is too early ace mun fara haihuwa. Duka-duka wata nawa ne da aurenmu, amma ace har zamu fara tara yara? Bazan lamunta ba gaskiya."
"Me kake nufi kenan? Kana tunanin a zubar da cikin ko me?"
"Kwarai ma kuwa, in ba haka ba kema zaki tsufa da wuri, kizo ki tara ya'ya, kinga daga nan zaki gundire ni, har kiga na fara neman wata a waje, ni kuma abinda bana son ya faru kenan, saboda ina son ki sosai, and bana son na haɗa soyayyarki da ta kowa."
"Wannan ba hujja ba ne Kazaure. Cikin nan fa ba shege ba ne, ka tuna da aure muka same shi, gaskiya ni ba zan iya zubar da shi ba."
"Dole a zubar da shi Jay, cuz I'm not f*cking ready to be a father yet! Tashi muje."
"No Sadam, I can't do such evil, ba zan kashe kyautar da Allah yayi mun ba. Ina son baby na tun daga lokacin da na gane ina ɗauke da shi."
Hannunta ya k'ank'ame,
"Zamu samu wasu babe, but this one, dole a zubar da shi, ki tuna ta yadda akai muka yi auren mana, yanzu haka kawai sai ki ɗauki yaro ki koma ma su Baffa da shi idan mun tashi komawa? Haba Baby na, think over it mana, ki tuna yanzu muka fara rayuwarmu, muna jin daɗinmu, muna more kuruciyarmu, haka kawai sai mu wani fara haihuwa ko amarcinmu bamu gama ci ba?. Babe kinsan ina son ki, kuma ba zan so abinda zai cutar da ke ba, so ki tashi kawai muje in yi ma Dr bayani, cuz dama an faɗa mun asibitin nan suna irin aikin nan a ɓoye, kinga baza mu sha wani wahala ba. Please baby na."
Ya kama fuskarta da duk hannayensa guda biyun, yana aika mata da wani sakon kallo wanda a duk lokacin da ya yi mata shi take daburcewa, ta manta tunaninta, ta kuma bi duk abinda yace mata tayi.
Take huɗubarshi ta ratsa ta, zuciya da gangar jikinta suka aminta da gadar zaran da Sadam ya kulla mata.
"Na ji, amma ka yi mun alk'awarin this is the first and also the last."
"I promise you babe, wannan ma dan kawai mu samu lokacinmu mu ci amarcinmu, mu kuma morewa kuruciyarmu. Kin gane ai?"
Ya wani ja girarsa sama, ya sakan mata makirin murmushinsa ta gefen kumatu.
Murmushin ta saki itama, ta mik'e suka wuce office ɗin likitan, Sadam yayi mishi bayanin shawarar da suka yanke.
Shiru likitan yayi, daga bisani ya ɗago ya kalle shi,
"Tabbas muna yin wannan aikin, amma ba kowa ya sani ba, saboda aiki ne mai haɗari, haka kuma akwai buk'atar kuɗaɗe masu ɗan nauyi."
"Kada ka damu Dr, wannan duk ba matsala bane, in dai za'a samu biyan buk'ata."
A take a wurin Sadam ya saka hannu, likita tare da masu taimaka mashi suka wuce da Jay ɗakin da za'a murje cikin da ke jikinta.
Yaaaa Ilahiii!😭😭😭
Our innocent baby is at risk, do help us with your prayers please....
Best regards, Lubbatu_Maitafsir 😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro