BABI NA SHA TAKWAS
***Katsina.
Sannu a hankali yake takawa tare da taimakon Goggo da ta kama hannunsa zuwa cikin gidan.
"Sannu Alhaji."
"Yawwa. Taimaka mun da wayar can dake k'ara da Allah."
Ba tare da tace komai ba, ta juya domin d'auko wayarsa da ke neman agaji wacce ya bari a cikin mota. Shi kuma ya k'arasa shiga ciki ya zauna a d'aya daga kujerun da ke girke a palon.
"Ga shi na d'aga, Malam ne yana kan layi."
Ansa yayi ya kara wayar a kunnensa.
"Assalamu alaikum. Barka da Juma'ah Malam."
"Wa alaikumus Salam. Barka dai Kabiru, ya k'arfin jikin?"
"Alhamdulillah, gamu nan ma yanzu muka dawo daga asibitin."
"Ahh, to madalla, ai na kira wayar Ummi d'azu da na kira ka baka d'aga ba sai na ji ta a rufe, ina ta tunanin ko jikin naka ne yayi tsanani."
"A'a da sauk'i ma kam. Alhamdulillah."
"Haka ake so ai. Ina ita Ummin take ne?"
Shiru Baffa yayi, yana tunanin abinda zai fad'a mashi, can ya tsinkayi muryarsa.
"Kana ji na kuwa? Ba ni ita inyi magana da ita."
"Malam Ummi bata nan."
"Ina ta je ne? Taimaka ka had'a ni da ita, akwai maganar da zanyi da ita."
Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma zuciyarsa ta fara bugawa da sauri-sauri, yasa hannu ya dafe wurin, tare da cije la66ansa na k'asa, da alama yana jin jiki ba kad'an ba.
Ganin haka yasa Goggo tayi saurin anshe wayar ta d'ora a kunnenta, ta gaishe da Mal. Baban.
"Maryama ba dai jikin nashi ne ya motsa ba?"
"Shi ne fa wallahi Malam."
"Subhanallah. Kinga, kula da shi, bani Ummi inyi magana da ita, nima ina nan na shirya driver kawai nake jira mu taho."
Kuka Goggo ta fashe da shi, hawaye na tsiyaya a idanunta, ta labartawa Mal. Baba abinda ke faruwa.
Salati kawai ya d'auka, tare da kashe wayar, ita kuma ta duk'e a wurin ta cigaba da gunjin kuka.
Kallonta Baffa yayi kamar ba zai ce komai ba, ya daure yace
"haba Maryama. Menene zaki tsaya kina asarar hawayenki ga 'yar da bata damu da farinciki ko bak'incikinki ba? Tun wuri gara ki mance da kin ta6a haihuwar wata mai suna Ummi, in ba haka ba kina gab da kamuwa da ciwon zuciya kamar yadda na kamu da shi."
Bai jira ansarta ba ya mik'e ya wuce part d'insa, yana shiga ya maida k'ofar ya rufe
0 da makulli, ya duk'e a wurin yana wani irin kuka marar sauti sai wasu zafafan hawayen da suke kwarara a saman dattijuwar fuskarsa.
K'auna da son ganin fuskar 'yar tasa suka bijiro masa, duk kuwa da fushin da yake da ita, amma hakan bai hana zuciyarsa shiga tararrabin halin k'uncin da 'yarsa zata kasance ba tare da mataimaki ba, domin kuwa yana da yak'inin cewar Sadam ba soyayyar gaskiya yake yi mata ba.
Wayoyinta da ya k'wace ya tashi ya d'auko ya kunna, kyakkyawar fuskarta ce ta bayyana lokaci guda akan tangamemen screen d'in da ke shimfid'e jikin wayar.
Fuskarta ya fara shafawa, tare da tunanin yadda rayuwa zata kasance ma 'yar yarinya kamar ta, ba tare da iyaye ba.
Text message d'in da ya shigo wayar ne ya katse mashi tunani, a karo guda ya sa hannu ya bud'e ya fara dubawa.
Withdrawal alert ne daga ZenithBank suka dinga shigowa sun kai guda biyar, a na k'arshen ya tsaida idanunsa inda yaga an cire kud'in ne a First Bank dake kan titin Sir K. Ibrahim, Borno, Maiduguri Branch.
"Maiduguri Ummi?"
Yayi maganar cikin d'aga murya, zuciyarsa dake bugawa fat-fat, itace ta hana shi k'arasa fad'ar abinda ya so fad'a, ya saki wayar ya mik'e da sauri domin d'aukar maganinsa.
**Maiduguri.
Komai da zasu buk'ata, babu abinda basu siyo ba. Haka suka dawo suka fara shirya gidan, da taimakon masu babbar motar da suka d'auko masu kaya.
Basu samu kansu ba sai wurin k'arfe taran dare, duk da haka ma ba komai suka gama ba. Girki ne abu na k'arshe da suka yi, sannan suka wuce wanka.
Jay ce ta fara fitowa, ta bincika kayan da suka siyo ta fito masu da wasu kyawawan couple's pjs nata pink masu vest da bumshort, nashi kuma blue masu 3quatern wando da armless d'in riga.
Lokacin da ya fito ta gama had'ewa, kallonta yake kamar yau ne rana ta farko da ya fara ganinta, kasancewar yau d'in ce rana ta farko da ya ta6a ganinta a irin wannan shigar.
Zuciyarsa ce ta buga da k'arfi, alal hak'ika yarinyar tana da abubuwan da ba kowacce mace ce ke da su ba.
Ashe da ya rasa ta ba k'aramar asara zaiyi ba a rayuwa.
Abinda ya dinga sak'awa a k'asar zuciyarsa kenan.
A hankali ya fara takawa zuwa gabanta, k'ugunshi d'aure da towel, hannuwansa sun k'ara bud'awa, haka faffad'an k'irjinsa ya k'ara masa kwarjini, ba kamar yadda d'igo-d'igon ruwa yayi ma kyakkyawar fatar jikinshi ado.
Ganin yadda ya tsaya ya k'ura ma halittarta ido yasa tayi saurin wartan abayan dake gefenta tana k'ok'arin d'orawa a saman kayan jikinta.
Murmushi ya saki ta gefen kumatunsa, ya k'arasa inda take, yasa hannu ya fincike abayan.
"Me kike 6oyewa?"
"Dan Allah ka bani Sadam, kaga dai ba kyau ai."
Dariya yayi sosai, hadda buga k'afa.
"Ba kyau? Indeed."
"Eh mana ai ka sani. Ka bani please."
Gefen fuskarta ya shafa, ya saita idanunsa cikin nata, yana yi mata wani kallo na goggun 'yan duniya.
"That was then Babe. Its now officially, Mr.&Mrs. Sadam Baffa Kazaure. So feel free, and have no worries. Okay?"
Ya k'arasa maganar da wani makirin murmushi a saman la66ansa, ya d'age girarsa, yana cigaba da aika mata wani mayunwacin kallon da yasa dole tayi k'asa da kanta, kafin ya wuce gaban mirror ya fara taje sumarsa.
Tsaye tayi ta kasa motsa ko d'an yatsan kafarta, a zuciyarta tana ayyana cewar a kullu yaumun al'amurran Kazaure na kasheta, tare da sanyata ta mance duniyar da take ciki.
Yana lura da yanayinta, hakan ya bashi damar matsawa kusa da ita, yana k'ok'arin cire towel d'in jikinsa domin sanya kayan da ta ciro masa.
Da sauri ta juya ta fita, shi kuma ya saki dariya mai sauti, ya cigaba da abinda yake yi.
Kitchen ta wuce ta fito da warmers d'in abincin da suka yi, ta jera a tsakiyar palon, ta koma ta d'auko plates da spoons ta fito da su a hannunta, a dai-dai lokacin ya fito, yayi saurin isa wurin yasa hannu ya anshe daga hannunta.
"Kai. Wane ni in bar amarya da wannan aikin. Me sa kika ba kanki wahala haka? Wannan ai duk aikin ango ne."
"Hmmmm, ashe ma aikinka. Kai da ko ruwan zafi baka iya had'awa ba kana nan kana wani cika baki, wai aikinka."
"Yes durl, it's my duty. Now, bani plates d'in nan kiga yadda zanyi serving d'inki."
Bata ce komai ba ta mik'a masa, ya juya ta biyo bayanshi suka dawo tsakiyar palon.
Shi yayi serving dinsu a wahalce, dan bai iya komai ba. Suna cin abincin yana yi mata labaru masu dad'i, cikin farin ciki da jin dad'i suka yi suka gama, babu wata sauran damuwa a zuciyarta, ta san ta 6angaren Sadam bata da wata matsala, haka kuma bata tunanin akwai wani lokaci da zai zo wanda zasu samu matsala da junansu.
Bayan sun gama cin abincin ma shi ya gyara wurin ya kwashe kwanukan, ya kuma taimaka mata suka wanke su, sannan suka wuce d'aki.
Toilet ta shiga tayi brush, ta fito amma bata ganshi ba, hakan ya bata damar k'ara gyara gadon, tare da kashe fitila ta koma ta kwanta.
Shigowa yayi da ruwa a cikin cup, ya kunna fitilar ya d'ora cup din saman mirror, sannan ya bud'a jakarsa ya fito da wasu pills ya 6alla guda d'aya, ya d'auki ruwan ya hau samar gadon ya mik'a mata.
"Open your mouth Baby."
"What's that?"
"Ki bud'e bakinki ki sha mana. Zan cutar da ke ne?"
"A'a fa, but ka fad'a mun 1st."
Ruwan ya ajje a gefe, ya juya tare da kashe lumsassun idanunsa, yasa hannu ya kama hannuwanta, sannan ya fara magana.
"Babe kin san ina k'aunarki, kin san kuma bazan ta6a yin abinda zai cutar da ke ba.?"
"I know Kazaure, but ina ganin ba komai ba ne dan na tambaye ka ko?"
"Yeah, its nothing, but from now on, bana so kina questioning actions d'ina, be a good wife, and do whatever I ask you to do please."
"But Sadam.."
"Shhhh.. just do as I said. Please."
Yayi maganar lokacin da ya d'ora yatsansa akan bakinta, ya karkata kai tamkar mai shirin yin kuka.
Hannu tasa ta cire yatsan nasa, ta sakan mishi lallausan murmushi, a zuciyarta, ta rasa me yasa bata ta6a jin haushin duk abinda zaiyi ba, haka kuma bata tsammanin akwai ranar da zata zo wacce zata ji haushinsa.
Hannunta ta dora a kan fuskarsa, a hankali tana kallonsa, tasa babban yatsanta ta shafi cikakkar girarsa,
"It's Okay Hunnay, I'll try my best, and I'll be the perfect wife ever."
Hannunshi dake cikin nata ta k'ara k'ank'amewa sannan ta cigaba
"Trust me, you won't regret having me as a wife, cuz I love you so so very much."
"I won't for sure, cuz U're a blessing to me. I love you so very much too Angel."
Ya d'auko ruwan tare da mik'a mata maganin, tasa hannu ta ansa, ta saka a bakinta, ta bi da ruwan ta had'iye, sannan ta mik'a masa cup d'in.
"That's my boo. Kinga every night zaki na shan maganin nan, so ko da na manta please ki tuna mun kinji, dan ba'a so ayi skipping d'inshi ko sau d'aya. May be zan baki shi ki ajje a hannunki, amma ba yanzu ba."
"Na ji, but promise me, akwai lokacin da zaka fad'a mun ko na menene."
Dariya ya saki, lokacin da ya mik'e da cup a hannunsa, sai da ya je bakin k'ofa sannan ya juyo,
"zanyi deciding, amma ba yanzu ba."
"Please.."
Tuni ya wuce yana girgiza kansa, ya mayar da cup d'in kitchen ya dawo, ya kashe fitilar sannan ya koma kusa da ita ya kwanta.
A hankali ya raba ta da jikinshi, duniya yake jin tana juya masa, taushin fatarta mai kamar audiga, ya jefa shi a wani na daban, har bai san yadda zai fassara soyayyarta ba.
Wani bakon lamari take ji a tare da ita, sosai ta lafe a cikin rikonsa, a hankali kwakwalwarta ta gagara ansa sakon da yake aika mata a yanzu.
"Sadaam please.."
"Shhh.. let us be please.."
Ya ja duvet din da ke gefe ya lullube su, suka ansa bakuncin wata duniya, mai wahalar fitowa.
"I love you"
Shine kawai abinda zaka iya ji daga bakin Kazaure.
***
Washe gari ma tare suka gabatar da duk wani abu da yayi musu saura, zallan soyayya mai asalin aji da tsabta Sadam d'inta ke nuna mata, ko nan da can baya barinta ta matsa, yana mak'ale da ita, yana tunatar da ita muhimmancin da take da shi a rayuwarsa, da yadda zai kula da ita har izuwa numfashinsa na k'arshe.
**Katsina.
Maganinsa ya d'auko ya dawo palo ya d'auki ruwa ya sha, ya koma kan kujera yana mai cigaba da al'ajabin yadda Ummi ta wulak'anta mutuncinta, da gatan da ya yi mata a rayuwa.
Shigowar Goggo ce ta katse tunaninshi,
"Alhaji su Malam ne suka iso."
D'agowa yayi yana kallonta, bai ce komai ba ya mik'e ya fara tafiya, ta rufa masa baya zuwa inda ta baro su.
"Sannunku Malam. Ya hanya?"
"Yawwa, Alhamdulillah. Ya jikin naka?"
"Jiki Masha Allah, ana samun cigaba."
"To madallah. Allah ya k'ara sauk'i."
"Amin."
Baffa ya ansa da shi, shiru na wani d'an lokaci ya ratsa wurin, a haka Goggo ta shigo d'auke da tray a hannunta, ta ajje kan centre table ta samu gefe ta zauna.
Kan Mal. Baba a k'asa, ya had'a hannayensa wuri guda yana jinjina kai, daga bisani ya d'ago yana kallon Baffa.
"Kabiru menene gaskiyar abinda Maryama ta sanar da ni a waya? Ina Ummi ta nufa kuma wane mataki kuka d'auka? Kuma me ya hana ku sanar da ni tun farko?"
"Malam abin ne ba dad'in ji. Ban san ta ya zan fara fad'ar irin wannan mugun abu ba."
"Tunda ka sa k'afa ka shure maganata, ai dole fad'ar irin wannan yayi ma bakinka nauyi Kabiru."
"Ba haka bane Malam. Al'amarin ne Allah kad'ai ya san dalilin faruwarsa."
"Rufe mun bakinka kawai."
Yayi maganar yana d'aga masa hannu, sannan ya cigaba.
"Nan na kira ka, na ce ka aurar da yarinyar nan, amma kayi biriss da zancen, ba komai yasa nace ka aurar da ita ba, sai dan saboda gudun irin abin nan da ya faru. Shi na gujewa tun farko Kabiru, shi yasa nace ka aurar da ita ga wanda take so, amma da yake kai kunnen k'ashi ne da kai, baka d'auke ni da daraja ba, shine kayi watsi da maganar. Ai yanzu kaga sakamakon taurin kai. Yanzu ka fad'a mun wa gari ya waya a irin wannan aika-aika da aka tafka?"
"A'a, wallahi Malam ba laifi na bane, ga Maryama nan ita shaida ce, na yi bincike a halayyar yaron na gano yana da d'abi'un da bai dace ace na d'auki 'ya na bashi ba. Bincike na ya tabbatar mun Sadam mashayin giya ne, kuma d'an caca. A yadda na samu labari daga garinsu ma hatta mahaifinshi bai d'auke shi da wata daraja ba, yanzu Malam ta ya zan d'auki 'ya in ba mai irin wannan halayyar? Kuma sai da na kira Ummi, na zaunar da ita na zayyane mata abinda ke faruwa, nace ni ta kawo wani ma, amma da yake Ummi bata d'auke ni a bakin komai ba, ta sa k'afa ta shure maganata. Dan k'arfin hali har da bar mun wasikar cewar kada in sha wahalar nemanta, wane mataki kuma ya rage in d'auka fisabilillah?"
"Wannan yasa a kullun nike takaicin irin tarbiyyar da kuka bata. Kuma sanin kanka ne, babu ranar banza da bana tunatar da kai cewar 'ya'ya amana ce ta Allah ya damk'a a hannun iyayensu, amma da yake al'adun nasara sun gama ratsa k'wanyarka, baka ta6a d'aukar maganata da muhimmanci ba, kun bar yarinya sakaka, baku san ku nuna mata dai-dai ba tun asali, ta ya yanzu da girmanta, ta kai wani munzali na sanin abinda take so kake tunanin zata yi maka biyayya? Kaima ka san abinda ba zai ta6a yiwuwa ba ne Kabiru."
"Amma duk da haka Malam ai ya kamata Ummi ta san mutuncimu a matsayinmu na iyayenta."
"Rufe mun baki da Allah, tunda kuke kun ta6a nusar da ita muhimmancin naku ne? Yanzu wannan abu da me yayi kama? Allah ya gani baku kyauta mun ba wallahi, wannan abun kunya har ina? A cikin zuri'a ta?"
"Malam abinda abinda ya faru ya riga ya faru, mun kuma tabbatar da hannunmu a tafiyar Ummi, ban k'i ace duka laifin na mu ne ba, amma ayi hak'uri. A fara tunanin hanyar da za'a bi a ganota."
Cewar Goggo da ke zaune gefe, kanta a k'asa da alama hawaye take zubarwa.
A fusace Baffa ya d'ago,
"Ba da yawu na ba. Kuma ban bada izinin a nemi Ummi ba har abada."
"Kabiru? Kana cikin hankalinka kuwa?"
"A hankali na nake Malam, amma na dad'e da mantawa da na ta6a haihuwar wata mai suna Ummi a rayuwata."
"To baka isa ba, dole ka tashi muje gidan talabijin da na rediyo mu bada cigiyarta. Kuma dole ka sanya kud'i ga duk wanda ya samo ta. Tashi wuce ka shirya ka fito mu tafi."
Kukan da Goggo ta fara yi ne ya ta6a zuciyar Baffa, tausayinta sosai ya tsirga raunatacciyar zuciyarsa, kamar ya tafi Maiduguri neman Ummi, sai dai kuma ya riga ya sanya ma zuciyarsa dangana, ya kuma shafe babin Ummi a matsayin d'iyar da ya ta6a haifa a doron k'asa.
K'asa yayi da kanshi, hawaye na kwarara a idon babban mutum kamarsa, murya na karkarwa yace,
"Kayi hak'uri da abinda zan fad'a Malam. Wallahi ba zan ta6a asarar lafiyata wurin neman Ummi ba, ba kuma zan ta6a fita neman 'yar da ta fifita wani k'ato akan mahaifanta ba. Ka gafarce ni dan Allah."
Yadda Baffa yayi maganar, ya tabbatar ma Mal. Baba iya gaskiyarsa kenan, sai dai kuma yana tausaya ma d'an nashi, saboda ya san irin k'auna da shak'uwar da ke tsakaninshi da tilon 'yar tasa.
Shiru na wasu dak'ik'u ya cigaba da wanzuwa a tangamemen palon, in banda sheshshekar kukan Goggo, ba'a jin komai, yayin da kan Baffa har yanzu yana k'asa, ya kasa had'a ido da mahaifin nasa, kasancewar yau rana ta farko da ya ta6a yi masa umarni ba tare da ya cika ba.
**Maiduguri.
Rik'e take da jakar Laptop d'inshi, yayin da shi kuma yake tsaye gaban madubi, yana taje sumar kansa, sosai take kare mishi kallo daga cikin madubin,
"Please, gayun nan ya isa haka, sai kace wanda zai je wani gagarumin taro."
Comb d'in da ke hannunsa ya tura a aljihu ya taka zuwa gabanta, a lokaci guda yana gyara collar rigarsa.
"First day in office, I've to look extraordinary, dan su san Kazaure ba sa'an yin su bane. Kin gane ai."
Ya k'arasa maganar yana d'aga girarsa tare da shafar gefen fuskarta.
"Duk wanda ya ganka ai ya san kai d'in na daban ne, I'm just scared kada 'yan matan Borno su fara eyeing mun kai."
"Ke d'aya ce Baby na, baki da number two. Now gimme a peck."
Ya tura mata gefen fuskarsa, tayi pecking, sannan ya ansa jakarsa suka fito hannunsa cikin nata har zuwa bakin k'ofa.
"Sai na dawo ko?"
"You take care of yourself for me please."
"I'll Hunnay. You do the same."
Ya raba ta da jikinsa, shiru na dogon lokaci ya ratsa tsakaninsu,suna jin yadda zukatansu ke bugawa da soyayyar junansu.
"I love you Mrs. Kazaure."
Ya yi kargin halin fada lokacin da ya dago ta, ya sumbaci saman goshinta, ya juya ya fara tafiya.
"I love you too Mr. Kazaure."
Ta fada tana daga mishi hannu.
Da haka ya tada motar ya wuce, ita kuma ta koma ciki.
Haka rayuwar tasu take tafiya, cike da soyayya, shak'uwa da jin dad'i.
《》BAYAN WATA BIYU《》
Sanye take da bak'in skinny jeans tare baby pink d'in T-shirt da ta kama ta sosai, mai gajeran hannu an rubuta Be My Baby, tare da zanen k'atuwar rose flower a gaban rigar.
Ta takure kanta wuri guda a cikin kujera mai cin mutum daya, k'afafuwanta da hannayenta, ta had'a su wuri guda tana tunanin ina Sadam ya shiga, kasancewar har yanzu bai dawo daga aiki ba, bai kuma ta6a kai irin wannan lokacin basa tare ba.
A hankali ta d'aga kanta, ta sauke idonta jikin agogon dake mak'ale a bangon palon, k'arfe bakwai da mintina hamsin da biyu cif-cif, ta san duk wani magidancin arzik'i indai baya masallaci, to yana gidansa a irin wannan lokacin tare da iyalinsa.
Tsoronta d'aya kada taje ko wani abun ya same shi, ga shi ita ba waya ba, balle ta nemi sanin halin da yake ciki, domin kuwa tun da yake bai ta6a kai irin wannan lokacin a waje ba, duk da yawan traffic jam na garin, bai ta6a kai k'arfe bakwai bai dawo gida ba.
Hawaye ne suka fara sintiri akan fuskarta, addu'a ta fara yi Allah ya ku6utar da mijin nata a kowanne irin hali yake ciki.
K'arfe tara da rabi na dare ya shigo gidan, ta ci kukanta ta gaji, har bacci ya d'auke ta a wurin.
K'aran bud'e k'ofar palon ne yasa ta mik'e a firgice, ta sauke idanunta a kansa.
Da sauri ta tashi ta isa inda yake, jikinsa ta fara duddubawa ko wani abun ya same shi, amma bata ga alamar hakan ba, yayin da ta 6angarensa biyu-biyu ya ke ganinta, a karo guda zuciyarsa ce ke k'awata mashi kyakkyawar surarta fiye da yadda yake ganinta a baya.
Bai damu da yadda take kallonsa ba, gadan-gadan ya nufe ta yana k'ok'arin d'aga ta sama.
"Are you ok?"
Sai a lokacin ya fara tunanin dai-daita natsuwarsa.
"I'm fine dear. Me ya faru ne?"
"No U're not fine Sadam. Kalla fa idanunka. Me ke damunka dan Allah?"
Ta matsa gabanshi, ta yadda har zasu iya jin numfashin juna.
Wani mugun wari da taji yana fita a jikinshi, wanda bata san d'an gayun kazaurenta da shi ba.
Ido ta k'walo waje
"Sadam warin me haka? Ina ka tsaya? Me yake damunka?"
"Hey nothing fa. Muje ciki, I wanna take a shower"
"Ba inda zamu je sai ka fad'a mun inda ka samo warin nan."
"Babe ba komai fa, muje inyi wanka I'll explain."
Ya matsa gabanta yana k'ok'arin had'a ta da jikinshi a karo na biyu, amma tayi saurin ja da baya, ta fashe da wani irin kuka tana toshe bakinta, tana yin da baya, da baya yayin da shi kuma ya cigaba da takawa yana binta, domin tunda yake bai ta6a ganin tayi mashi kyau irin haka ba, barasar da ke kanshi ta cigaba da k'awata mishi ita, a haka har ta had'e da jikin kujera, shi kuma ya isa daf da ita, ya sa hannu ya fisgeta suka wuce ciki.
Allah ne ya taimaketa da yamma tayi wankan tsarki, amma da a haka Sadam zai fad'a mata ba tare da hankalinshi na jikinshi ba.
Haka kuma bai damu da bata magani kamar yadda ya saba a ko wacce rana ba.
Anya wannan Sadam d'inta ne? Mutumen da ke riritata yana lalla6a tamkar jaririya yau shine ya zo mata a haka? Addu'a ta fara yi a k'asar zuciyarta,
'Ya Allah kada kasa maganar Baffa ta kasance gaskiya.'
The love birds are turning upside down. Chaaai😂😂😂
Let's rock this hayaties😍
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro