Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA SHA HUDU

Wayarta ta fitar zata kira Miemie, kiran Goggo ya shigo, ta d'aga ta d'ora wayar a kunnenta tana cewa
"Hello."
"Ina cikin school."
"A'a ban gama ba, ina da lecture 2-4."
"Lafiya kuwa?"
"Ok, gani nan zuwa yanzu."

Da haka ta kashe wayar, ta kira Miemie ta tambayi inda take, bayan ta fad'a mata ne ta cigaba da takawa, zuciyarta duk babu dad'i, ta wani 6angaren maganganun Sadam na kadar mata da gaba, ta wani fannin kuma tana fargabar kiran gaggawar da Goggo tace Baffanta na mata.
Da haka ta iso wurin, ba tare da ta mata dogon bayani ba ta anshi key d'inta, ta shiga ta tayar da motar ta d'auki hanyar gida.
Da sallama ta shigo, ta samu Baffa ya tafka uban tagumi zaune akan kujera mai cin mutum biyu, gabansa plate ne da spoon, a gefe guda kuma babban foodflask d'in abinci ne.
Goggo ce ta fito daga kitchen hannunta d'auke da tray, a tare suka k'araso cikin palon, bayan ta ajje tray d'in ta bud'e foodflask d'in zata fara sa ma Baffa abincin, amma ya d'aga mata hannu tare da cewa
"dakata tukun."
Kujerar da ke kallonsu Jay ta zauna,
"Sannu da hutawa Baffa."
Bai ansa ta ba, illa ajiyar zuciya da ya saki, a karo guda ya sauke hannunsa daga tagumin da yake yace
"Ta so ki dawo nan Mamana."
Mamakin dake kan fuskarta ya kasa 6oyuwa, rabon da ta ji muryar Baffanta haka tun kafin ta tunkare shi da maganar aurensu da Sadam, da haka ta taso ta dawo kusa da shi ta zauna, ya dai-daita zamansa ya fuskance ta sosai, kafin ya kira suna ta.
"JAMEELA."
A hargitse ta d'ago tana dubansa, kasancewar yau ce rana ta farko da ya ta6a kiran sunanta kai tsaye, ba tare da ya sakaya ba.
"Na'am Baffa."
Ta fad'a idonta cikin nasa.
"A watannin da suka gabata, kin zo mun da maganar da ban ta6a tsammaninta daga gare ki ba."
Ya muskuta, sannan ya cigaba.
"A farko, na nuna miki k'in yarda, da rashin amincewata akan abun. Amma daga baya na sauke makaman yak'ina, na kuma sauko daga dokin nak'in da na hau. Bakomai ya jaza hakan ba, illa mahaifina da ya sanya baki a maganar, ya kuma ce inyi yadda yake so. Nayi biyayya a gare shi, nayi abinda ya ce Ba tare da na nemi jin dalilin da zai sa ya tursasani akan abinda banyi niyya ba, ba dan komai ba, sai dan kasancewarsa mahaifina, wanda ya kawo ni duniya, wanda Allah (SWA) yace inyi biyayya a umarninsa matsawar basu sa6a shari'ar musulunci ba.
Abinda yasa na kawo wannan maganar shine, ina so a matsayinki na 'yata, wacce na haifa a cikina, na kuma baki duk wani farinciki da jin dad'in rayuwa da ki cire soyayyar Sadam a zuciyarki, ki hak'ura da shi, ki manta da duk wata alak'a da ta ta6a shiga tsakaninku ba dan komai ba sai dan sakamakon binciken da nayi a kansa, bai dace da kamilar mace irin ki ba Ummi."

A daburce ta d'ago tana kallonsa, wani dodo-dodo take ganin ya koma mata saboda kalmar
'ki rabu da Sadam'
da ya kira mata. Nan da nan idanunta suka ciko da hawaye, bakinta na kyarma ta fara magana.
"Ba zan iya ba Baffa, ba zan ta6a iya rayuwa ba tare da soyayyar Sadam ba, na gwammaci ka ce ka yafe ni, akan kace in rabu da mutumen da nake so fiye da numfashi na. Ina son sa a duk yadda yake, dan haka ba ruwa na da ko me bincikenka ya tabbatar maka, ni nake sonshi, ni kuma zan zauna da shi, to babu ruwan wani da halayyarsa, so far Sadam bashi da wani mugun halin da za'a k'yamata. Ka taimaki rayuwata Baffa, wallahi zan iya mutuwa idan ka hana na aure sa."

Wani matsanancin kuka ta ida fashewa da shi. Goggo dake gefensu itama kukan ta saka, saboda tsananin tausayin halin da 'yar tata ke ciki.
Ta 6angaren Baffa kam, da za'a bud'a zuciyarsa, za'a iya ganin yadda bak'in ciki yayi masa katutu, tare da tokare masa gefen zuciyarsa. Dak'yar ya saita tunaninsa, ya dafa kafad'ar Jay yace
"Ummi, ni mahaifinki ne, kin tabbatar bazan ta6a so miki abinda na san zai cutar da rayuwarki ba. Abinda nake so da ke kiyi hak'uri, ki fawwalawa Allah lamurranki, a sannu zai maki maganin halin da kike ciki. Haka kuma a shirye nake, na aurar da ke ga duk wanda kike so, wanda na aminta da d'abi'u da halayensa, amma ba mashayin giya ba, ba kuma d'an caca ba."

Yana gama fad'ar haka ya mik'e, hannunsa dafe da gefen k'irjinsa na hagu, inda ba dan k'arfin zuciya irin ta namiji ba, shima da kukan zai saki ko dan ya samu sassauci daga rad'ad'i da zafin da yake ji a cikin k'irjinsa.
Cikin zafin nama ta kama bayan rigarsa, kuka take bil hak'k'i, lokaci guda idanunta sun rine, sun k'ara fitowa waje k'ulu-k'ulu.

"Kada muyi haka da kai Baffa, kai fa kace ka amince zaka aurar da ni gareshi, ka taimaki rayuwata dan Allah, haba Baffana, ina kulawa da soyayyar da kake nuna mun a da? Ina tarairaiya da son farincikina da kake yi?"

Ta k'arasa maganar cikin wata azabtacciyar muryar da ta sa zuciyar Baffa tsinkewa, take idanunsa suka yi jajur, a karo guda wata k'walla mai zafi ta sauko masa.
Hannun rigarsa yasa ya d'auke ta, sannan ya duk'a gabanta tare da tallabo ha6arta yace
"ina so ki tuna k'auna da soyayyar da na nuna miki tun tasowarki, ki d'auke ta ta zame maki wani jigo da zaisa kiyi biyayya a gare ni. Domin kuwa ko da zaki rasa ranki, bazan yarda ki auri mashayin giya ba. Wannan itace magana ta k'arshe da zamu yi dake akan shi, daga yau ki warware duk wata alak'a da take tsakaninku."

Yasa hannu ya k'wace rigarsa, ya shige part d'insa, inda ya zube a kujera hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarsa, tamkar wani d'an k'aramin yaro.
Mik'ewar da zata yi da zumar ta bi bayan baffan, amma cikin rashin sa'a ta sulale ta fad'i k'asa a sume.
Kuka mai had'e da salati Goggo ta kwasa tayi kanta, ganin bata numfashi yasa ta warci gorar ruwan da ta kawo ma Baffa ta bud'e ta tuttula a saman fuskarta, cikin d'an k'aramin lokaci ta dawo hayyacinta, tari ta fara yi, daga bisani ta bud'e da wani sabon babin kukan.
Kamar wata mahaukaciya ta mik'e tare da warto jakarta ta zazzage, Goggo banda ido babu abinda take binta da shi, a haka ta d'auki wayarta, ta wuce d'aki da sauri, ta fara kiran number Sadam.
"Babe."
Ya ansa wayar da shi, kukan da ya ji ta fashe masa ne yasa yayi saurin mik'ewa ya fita yana tambayar
"what's wrong with you darling?"
Bata 6oye masa komai ba, cikin kuka ta fayyace mashi yadda sukayi da Baffanta
Duk da ba k'aramin caji kanshi ya d'auka ba, hakan bai hana dabara fad'o masa ba, a karon farko ya saita muryarsa tare da cewa.
"I know you love me, and you're ready to fight for our love, right?"

"Of course, I'll do whatever it takes to prove that."
"Kinyi alk'awarin zaki kasance tare da ni ko da duka duniya sun juya bayansu gare ni. Haka ne?"

"Zan iya rayuwa da kai, ko da kai kad'ai ne mutumen da yayi saura a duniyar da na san mutane da dama."

"Thank you. Now, share hawayenki, ki bani daga nan zuwa gobe, I'll find the solution for all of this. Plans d'in da muka dad'e muna shirya ma kanmu will never go just like that. Trust me babe."

Hawayenta ta shiga sharewa, ko bakomai ta samu k'warin gwiwa daga wurin da take tunanin baza ta samu ba. Tayi zaton ba zai nuna damuwarsa ba, ashe ba haka abin yake ba, ashe soyayyar da Sadam ke mata tafi gaban tunanin dukkan tunaninta!

*

***

Ofishin manaja ya zarce bayan sun gama wayar.
"Sir, zan gama duk abinda nake daga nan zuwa next week, In sha Allah."
"Babu laifi, dama lokacin da aka baka daga nan zuwa end of the month d'in ne."
"Ok, thank you Sir."
"U're most welcome."
Ya bashi hannu suka yi musabaha, sannan ya fito ya zauna a kujerarsa, sai dai zuciya da ruhinsa gaba d'aya sun ta'allak'a ne akan abinda yake shirin aikatawa.
Wani fanni na zuciyarsa na tunatar da shi akan had'arin abun, inda har zuciyarsa kan raya mishi, wane irin hali zai tsinci kanshi, idan aka yi ma 'yarsa abinda yake shirin yi ma 'yar wani?
Wani 6angaren kuma na tunatar da shi akan rashin yiwuwar hakan.
A bayyane ya furta
"That won't happen. I'll never have a child. Jay ta ishe ni rayuwa, babu dalilin da zaisa in k'ara ma kaina nauyi."
Maganganun da ya dinga yi a k'asar zuciyarsa kenan, har aka tashi aiki bai samu wata natsuwar kirki ba, ko da ya fito bai zame ko ina ba sai k'ofar gidansu Jameela.
Bayan ya gyara parking ya cire wayarsa ya kira ta, ba'a d'auki dogon lokaci ba ta fito, idanuwanta sun kumbura suntum, ta ci kuka har ta gode Allah.
Ganin yadda ta koma cikin d'an kankanin lokaci yasa hankalinsa ya tashi, handkerchief ya ciro fari sol, sai k'anshin daddad'an turarensa yake ya mik'a mata, ta sa hannu ta ansa ba tare da gardama ba, ta fara shafe kumburarrun idanunta.
Shiru ne ya ratsa motar na wasu 'yan dakiku, tunanin yadda zai bijiro mata da k'udirinsa yake, sai dai ya rasa hanyar da zai bi domin fallasa mata sirrin da ya matso a k'asar zuciyarsa.
Wannan ne karo na farko, da ya ta6a jin fargabar tunkararta da wani abu tun daga ranar da ya santa.
Dakewa yayi, ya juya ya kama hannayenta duk biyun, cikin wata rarraunar murya ya kira sunanta.
"Jay."
A tsanake ta d'ago kumburarrun idanunta ta sauke a kansa.
"Ba zan iya jure ganinki cikin tashin hankali da bak'in cikin nan ba. Ba zan jure ma kallon yadda kike asarar hawayenki a ko da yaushe ba. Babe me zai hana mu k'aurace ma wannan mummunan tashin hankalin da yake barazana da soyayyarmu? Me zai hana mu canja mazauni, mu koma wata duniya ta daban, duniyarmu mu biyu, mu shimfid'a irin rayuwar da muke mafarkin samu just me and you, no tension, nothing, nothing but love and care."

"How do you think that wud be possible Kazaure? Ka manta k'alubalen da yake gabanmu ne? Ta ya zamu iya samun wannan freedom d'in? Ka gaya mani ta yaya?"
Ta fashe da wani zazzafan kuka, wanda yasa ya dafe kansa, yana jin kukan nata har a cikin zuciyarsa.
"It's possible, matuk'ar zaki amince da shawarar da nazo da ita."
"Sanin kanka ne, ban ta6a k'etare maganarka ba, Dan haka kada ma ka fara tunanin zan bijire ma shawarar da nasan zata zama mabud'in matsalarmu."

"Nayi magana da bank manager d'inmu kafin in fito cewar zan gama duk abinda nake in wuce Maiduguri zuwa next week, dan haka kizo mu tafi tare, mu shimfid'a kyakkyawar sabuwar rayuwa ta soyayya, just the two of us."
Cikin kidimewa ta d'ago manya-manyan idanunta tana kallonsa, fuska ya marairaice, ya d'aga mata kanshi.

"I'll give you everything you need, I'll love you nd you alone Jameela, zamu samu mai d'aura mana aure ba tare da wata matsala ba, zamu k'aurace ma duk wannan tashe-tashen hankulan da muke ciki, zan baki duk wace irin kulawa kike buk'ata, zamu manta da wannan hayaniyar da muka riski kanmu a ciki, zamu yi rayuwarmu yadda muke so, in yaso bayan wasu shekaru sai mu dawo gida, by then, na san dole Baffanki ya hak'ura, tunda dai babu irin biyayyar da baki mishi ba, shine ya kasa gane abinda kike so, ya kuma kasa baki abinda kike so, so ko ina aka je baza a d'ora miki laifi ba."

Kanta ta fara girgizawa, hawaye na bin kumatunta.

"No please, stop it Kazaure, I can't do this to my own parents, ka dai canja wata shawarar, but wannan will never work, kai kanka ka sani."
Baiyi k'asa a gwiwa ba, ya k'ara rik'e hannunta cikin nashi,

"This is the only way out Jay, wannan ce kawai hanyar da zamu iya mallakar junanmu ba tare da mun k'ara cin karo da wani k'alubale a gabanmu ba. Kiyi tunani sosai akan shawarar nan, zan baki daga nan har zuwa kwana ukku, duk hukunci da kika yanke, zanyi amfani da shi, sai dai ina so ki sani, matsawar kika karya alk'awarin da kika d'aukar mun na cewar zaki kasance tare da ni no matter what, to bazan ta6a yafe maki ba, kuma har abada bazan daina yi miki kallon maci amana ba."
Kafin ta bud'a baki, suka tsinkayi muryar Baffa wanda ya fito domin zuwa sallar maghriba a masallacin da ke gaba kadan da gidansu.
"Ummi."
Hakan yasa ta fito daga motar, ta k'arasa inda yake tsaye kanta a k'asa.
"Wuce ki shiga ciki."
Shi kuma ya juya ya kama hanyar inda motar Sadam take. Bata shiga gidan ba ta biyo bayanshi dan gudun kada ya fad'i abinda zai 6ata ran Sadam d'inta.
"Barka da yamma"
Cewar Sadam yana shafe kansa.
Bai damu da ya ansa ba, ya fara maganarsa.
"Dan Allah ina so yau ta zama rana ta k'arshe da zaka k'ara zuwa k'ofar gidan nan, kuma rana ta k'arshe da zan k'ara ganin ka da 'yata. Idan ka yi yadda na ce, zamu zauna lafiya, matsawar ka bijire wa umarnina kuwa, tabbas zaka sha mamakin abinda zai biyo."
"Baffa"
Ya tsinkayi muryar Jay tana yi mashi kallon da yake nuni da bai kyauta ba.
Bai bi ta kanta ba, ya nuna Sadam
"this is last warning."
Kuka ta fashe tana diddira kafa
"Ni wallahi bazan iya rabuwa da shi ba, idan ma ka hana shi zuwa, ni zan taka inje har inda yake in same shi."
Da haka ta shige gida tana wani irin kuka, wanda ya sosa zuciyar Sadam, ya kuma sa ya k'ara zage damtse wajen ganin sun gudu sun je sunyi aurensu, ko dan ya bak'antawa Baffa, shima ya d'and'ani kad'an daga bak'in cikin da ya ke cusawa zuciyoyinsu.

Kallon bak'in ciki Baffa ya bita da shi, abin takaici wai wannan Umminshi ce, 'yar da ya shagwa6a ya sangarta fiye da yadda ko wane uba yake sangarta 'ya'yansa.
Juyawa yayi ya koma cikin gidan shima, nan ya sameta yashe saman carpet sai rusa kuka take yi.
Goggo da abin duniya ya ishe ta, ta saka ta gaba, tana matsar nata hawayen, gashi bata da halin da zata k'etara hukuncin da mijinta ya gindaya, amma ba dan haka ba, da tace ya barta ta auri wanda take son kawai.
Cikin d'aga murya ya nuna ta.
"Ni zaki wulak'anta a gaban wani ko Ummi? Kin manta da cewar nine wanda ya kawo ki duniya wanda yake da alhakin za6a miki mijin ma gaba d'aya. Banga laifinki ba, laifinmu ne da tun wuri bamu yi ma tufk'ar hanci ba, muka barki kara zuba, muka sa miki ido bamu kwa6e ki ba. Sai dai banyi zaton abin zai zo mana a haka ba, banyi tunanin irin wannan ranar zata riske mu ba."

"Haba Baffa, wace irin biyayya ce banyi a gare ka ba? Amma ka kasa cika mini burina, Me sa baza ka gane yadda soyayyar Sadam ke azabtar da ni ba? Ko dan kai baka san zafi da d'acin soyayya ba?"

Ta girgiza kai hawaye na cigaba da kwararowa a fuskarta.
"Kayi hak'uri Baffa, amma bana jin zan iya biyayya a abinda kake so, ba zan cutar da kaina in faranta maka ba, bayan Allah ma ya halatta mun abinda kake shirin haramta mun."

Wani tuk'uk'in bak'in ciki zuciyarsa ta fara fesarwa, nan da nan idanunsa suka kad'a suka yi jajur, gadan-gadan yayi kanta, Goggo tayi azamar shiga tsakaninsu tuni yasa mata hannu, ya isa gaban Jameela, sai da ya daddage, sannan ya d'aga hannu ya wanke ta da wani kyakkyawan mari.
Kafin tayi wani yunk'uri ya kuma kwad'a mata wani, ya sa kafa ya harba ta.
"Ke d'in banza, sai kace ke kika haifi kanki? To tunda abin naki iskanci ne, ba kya jin lallashi, zan bi da ke ta hanyar da zata ladabtar dake, jikinki zai gaya miki, tunda kince baza ki bi abinda nake fad'a miki ba."
Kuka take amma bakinta ya kasa rufuwa,
"Wallahi ko da zaka kashe ni Baffa, ruhina da gangar jikina baza su daina k'aunar Kazaure ba, shine farincikina, abin alfaharina."

Wannan karon a hargitse ya isa gabanta, ya cakumi wuyan rigarta ya shak'e, ya fara k'ok'arin had'a mata kai da bango.

"Na gwammaci in kashe ki, kan ace ina ganin wannan bak'ar ranar da nake fada kina fad'a Ummi. Nayi da-na-sanin irin tarbiyyar da na baki. Ni mahaifinki, ni kika fifita wani D'A NAMIJI a kaina ko? Duniya ce Ummi, zata bi dake yadda kike so a yanzu, amma ina guje miki ranar da zata juya miki ba."

Ganin yana niyyar yin kisan kai yasa Goggo ta taso, dak'yar ta 6an6are hannunsa a wuyan Jay, ta fad'i k'asa sharaf, idanunta sun firfito, sai wani irin tarin wahala da take yi.
"Kije kiyi duk abinda yayi miki, amma ki sani ba zan lamunci irin iskancin da kika zo mun da shi ba, dan haka ki za6a tsakanin NI da d'an iskan NAMIJIN da na tabbata ba k'aunarki yake tsakani da Allah ba."
Daga haka ya wuce part d'inshi masallacin da bai je ba kenan, sai a gida yayi sallar, yana gamawa toilet ya shige ya sakan ma kanshi ruwa saboda yadda zuciyarsa ke k'una, a wani 6angaren har yana nadamar haihuwar Jay a rayuwarsa.

I told you, today is all about SadJay😂😂

Allah Sarki Baffanmu😢😢

Best regards, Lubbatu 😍✌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro