BABI NA SHA BIYU
Fitowarshi kenan daga taron da sukan yi a duk k'arshen wata da manajojinsa na sauran rassan kamfanoninsa da ke garuruwa daban-daban a arewacin Nigeria wayar Mal. Baba ta shigo masa. Gefe ya matsa, ya ansa wayar da sallama, ya gaishe da mahaifin nasa cikin dattako da girmamawa.
Sama-sama Malam ya ansa shi, ya d'ora da cewa
"Ba wannan ne dalilin kiran ba, ina so ka baro duk abinda kake kazo Daura ka same ni yau d'in nan, ba wai sai gobe ba."
"Lafiya Malam? Ko akwai wata matsala ne?"
Baffa ya tambaya lokacin da ya k'arasa fitowa daga d'akin da suka gabatar da taron.
"Babba ma kuwa Kabiru, domin kayi abinda ban ta6a tsammani daga gare ka ba, duk da dai ba abin mamaki bane, idan nayi duba da yadda son zuciya yasa kayi watsi da iliminka na addini, kayi aron wasu al'adu da ak'idu na nasara ka yafa ma kanka tuntuni. Idan ka iso zaka ji sauran bayani."
Daga haka ya kashe wayar, ya cigaba da jijjiga kai, yana mamakin rayuwa irin ta mutanen yanzu. Daga bisani ya kai duba ga Iya, yace
"ku shiga ciki ko fura ki sama mata tasha kafin shi kuma yazo ya bani dalilinsa na son hana yarinya raya sunnar ma'aiki."
"Sallallahu alaihi wa sallam"
Iya ta k'arasa masa, suka mik'e gaba d'aya, shi yayi k'ofar gida, su kuma suka kama hanyar shiga ciki.
Duk iya tunanin duniya, babu kalar wanda Baffa bai yi ba, sai dai ya kasa gano dalilin kiran gaggawar da Malam ya masa.
A haka ya fito ya samu direbansa "shiga mu tafi, Daura zamu je yanzun nan."
A tare suka shige motar, zuciyar Baffa fal da tambayoyin da ya gagara ansawa.
Cikin ikon Allah tafiyar awa d'aya da minti goma cif-cif, ta kawo su k'ofar gidan Mal. Baba. Babban abinda ya d'aure kanshi kuwa, shine motar Jaay da ya gani, ajje a k'ofar gidan, duk da bashi da tabbacin ita d'in ce, ko a a, domin kuwa wata zuciyar na gaya masa babu abinda zai kawo ta Daura.
Bai ida gaskata zarginsa ba, har sai da ya sa kai cikin gidan, ya ko ci karo da ita zaune a palo ta takure wuri guda, sai faman danna waya take yi.
Gyaran murya yayi, ya had'a da sallama ya shige ciki, idanunsa akanta, ta dago tana dubanshi, bata ce da shi komai ba, sai dai ta 6angarensa sosai yake mamakin canjawar halayenta cikin d'an k'ank'anin lokaci.
"Ba dai k'arata ta kawo ba?"
Tambayar da ya yi ma kansa kenan, da haka Malam ya fito yana ansa sallamar, Iya na biye da shi, duk suka nema ma kansu mazauni a cikin palon.
Bayan sun gaisa, Malam yayi gyaran murya, ya kalli Baffa wanda har yanzu bai daina mamakin ganin Jay ba, yace "Kabiru."
"Na'am Malam."
Baffa ya ansa shi, lokacin da ya maida kallonsa gare shi.
Har ya bud'a baki zai fara magana, sai kuma ya dubi Jameela tare da cewa
"shiga ciki ki jira mu."
Ba dan ta so ba ta mik'e ta shige, duk da haka ta la6e bakin k'ofa tana saurarensu, tana mai ayyanawa ranta matsawar Baffa bai amince ba, to baza ta koma gida ba, har sai Mal. Baba ya d'aura masu aure da Sadam d'inta.
A palo kuwa Malam gyara zama yayi,
"Ummi ta zo da batun da ya girgiza tunanina, nasan kasan komai ba sai na maimaita maka ba."
"Haka ne Malam."
Baffa ya fad'a tare da girgiza kansa.
"Ina so in san menene dalilinka na cewa baza ka aurar da ita ba har sai ta gama karatu? Shin rayuwarta a hannunka take, ko kai ke da lokacin da zata gama karatun? Bayan kuma ta fad'a maka cewar yaron ya amince zata cigaba da karatun agidansa."
Sai da ya d'an tsagaita, sannan ya cigaba
"Haba Kabiru, da saninka da komai, ya kake neman ka haramta abinda Allah (SWA) ya halatta da kanshi? Me zaka ce ma Allah a ranar gobe k'iyama idan taje ta d'auko maka magana? Bayan kuma yarinya ta fito ta kwatanta abinda take so, kai kuma son zuciya, da al'adun nasara da suka ratsa ka sun sa ka toshe kunnuwanka, ba tare da ka fahimci girman abinda ta zo da shi ba.
To ina so ka saurare ni da kyau ka kuma ji abinda zan fad'a maka, tun wuri ka janye wannan mummunan k'udirin da ka cusa a ranka, ka bar yarinya ta auri wanda take so, tun baka gamu da fushi na ba."
Duk da tashin hankalin da Baffa yake ciki, amma haka ya daure ya cije, ya ansa umarnin mahaifin nasa, ya kuma k'ara da cewar
"Za ayi yadda kace in sha Allah, yau d'in nan zan nemi ganawa da yaron, daga baya sai muyi magana da magabatanshi. Zan aurar masa da ita, matsawar ya cika sharud'd'an da musulunci ya gindaya akan miji nagari."
"Masha Allah, Allah yayi albarka, ya kuma sa a dace."
"Amin"
Cewar Baffa, da haka suka mik'e domin fita sallar azuhr da ake ta kira a masallacin dake k'ofar gidan.
***
A gigice ya farka yana mik'a, toilet ya wuce yayi wanka had'e da alwala, ya fito ya zira jallabiya, ya gabatar da sallar asuba tare da zuhr, yayin da cikinsa ke ta faman k'ugi, saboda azabar yunwar dake nuk'urk'usarsa.
Key d'in motarsa ya fara nema bai gani ba, hakan yasa ya d'auko wayarsa da niyyar ficewa, anan ya ga missed calls d'in Jau da suka tasan ma guda talatin.
Hankali kwance ya fito, ba tare da wata damuwa ba, a karo guda ya danna number ya fara kiranta.
Tsaye suke a k'ofar gidan Malam sun fito da niyyar tafiya har Baffa, wayarshi ta shigo mata, bata damu da mutanen da ke gabanta ba tayi saurin komawa gefe, ta ansa wayar cikin zak'uwa, ta kara a kunnenta tana cewa
"Haba Sadam, me nayi da kake punishing d'ina haka? Ka san irin tashin hankalin da na shiga kuwa?"
"Hey I'm sorry."
Ya fad'a cikin wata irin murya mai rauni.
"Wallahi babe dak'yar na koma gida bayan na sauke ki, hankalina ya tashi gaba d'aya, zuciyana ya kasa kwanciya, tunanina zan iya loosing d'inki any moment from now, matsawar bamu samu cikar burinmu ba, wad'annan abubuwan ne suka sanya ni rasa natsuwata, sune kuma suka sa na kamu da rashin lafiya mai tsanani wacce tayi sanadiyyar kwantar da ni tun daren jiya."
Fuskarta tamkar mai shirin yin kuka, tace
"Oh my God! I'm so sorry dear, shi yasa na nemi natsuwata gaba d'aya na rasa, jikina ya bani kana cikin wani yanayi, amma ka kwantar da hankalinka, yanzu haka ina Daura na kawo k'arar Baffa, kuma munyi nasara Mal. Baba ya tursasa masa dole ya amince."
"Babe? No, no, you must be kidding, right?"
"I'm not sweedy. Yanzu dai ka gane ko, I'll be on my way right back to Katsina, so zan kira immediately da na shigo."
Da haka ta datse wayar, kasancewar Malam da ya fara k'wala mata kira.
Gabansu ta isa, daga nan suka yi masu sallama suka shige motar Baffa, yayin da driver ya shiga tata suka d'au hanyar ta Dikko d'akin kara.
Tunda suka tafi babu wanda yace ma kowa komai, sa6anin da, da har so suke suyi tafiya tare domin su samu lokacin fayyace ma juna labaran da ke zukatansu.
A haka wayar Goggo ta shigo ma Baffa, hankalinta a tashe take shaida mashi cewar Ummi bata gida.
"Ga ta nan zaune."
Ya bata ansa hankalinsa na kan titi, ya k'ara da cewar
"ki kwantar da hankalinki, gamu nan a hanyar gida."
Ya kashe wayar, ya ajje, inda ya saita hankalinsa sosai a titi, sai dai zuciyarsa ta gagara natsuwa, ba tare da ya kalleta ba yace
"meye sunan sa?"
Da mamaki ta d'ago tana kallon Baffan, murmushi ta saki tare da cewa
"Sadam."
A tak'aice.
"Ki ce da shi ya zo ya same ni a gida k'arfe bakwai na daren yau."
Wannan karon ta kasa 6oye farin cikinta, hannun Baffan da yake tuk'i da shi ta dafa tana cewa "nagode, nagode Baffana. Zan sanar da shi in sha Allah."
Bai ce komai ba, haka kuma bai kalleta ba, murmushin takaici kawai ya saki, inda ya cigaba da tuk'insa, ita kuma dan rashin kunya ta fara k'ok'arin jan shi da surutu, sai dai bai ce k'ala ba, har ta gaji taja bakinta tayi shiru itama.
Koda suka je gida da sauri ta shige ciki, ta bar Baffa yana gyara parking, inda ta samu Goggo zaune a palon ta rafka uban tagumi, fuskarta babu alamar walwala.
Da sauri ta taso ta tare ta,
"Ina kika je haka Baby? Wai me yake shirin faruwa da ke? Yanzu ace zaki fita, kuma ina cikin gidan nan, amma baza ki iya sanar da ni ba, sai dai in fito kawai in neme ki in rasa? Wace irin rayuwa kike shirin jefa kanki?"
A haka Baffa ya shigo da sallama, da sauri ta sake ta tayi kansa ta anshi babbar riga da hularsa, tare da jakarsa a hannun drivern dake binshi a baya, ta dawo cikin palon inda Baffa ya samu wuri ya zauna, ya had'a hannuwansa duk biyun ya dunk'ule ya tallabe ha6arsa, sai faman cika bakinsa yake da iska yana furzarwa.
"Sannunku"
ta ce da shi lokacin da ta ajje kayan dake hannunta a gefensa.
"Yawwa dai, bani ruwa da Allah."
Bata 6ata lokaci ba ta wuce kitchen domin kawo masa ruwan, yayin da Jay ta dawo gefensa ta zauna hankalinta na kan waya da alama text take rubutawa.
Bayan Goggo ta aje tray d'in da ke hannunta mai d'auke da gorar ruwa, cup, tare da jug mai cike da pineapple & coconut squash.
Tsiyaya lemun ta yi ta mik'a masa tana tambayar
"lafiya dai ko? Naga ka dawo da wuri. Ya akai na ganku tare da Ummi kuma?"
Ansar lemun yayi ya kafa a baki ya kwankwad'e tass, take yaji zuciyarsa ta d'an sassauta masa, sannan ya aje cup d'in yace
"A Daura muka had'u."
"Daura?"
Goggo ta tambaya idanunta a waje.
Girgiza kai Baffa yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya tashi ya wuce d'aki dan muddin ya cigaba da zama kusa da Ummi, ba zai samu natsuwar zuciyarsa ba, dan a yanzu haka ma azalzalarsa kawai take, abinda bai ta6a ji ba dangane da ita tun bayan zuwanta duniya.
Kallonta Goggo take tana tambayar
"me ya kai ki Daura Ummi? Ba dai kan maganar da Baffanki yace kar ki kuma tadawa ba?"
"Kanta mana."
Ta fad'a kai tsaye.
"Haba Ummi, wai me yake yawo a kanki? Duka-duka kwananki nawa da sanin mutumin nan da har zai sa ki manta da k'auna da soyayyar da muke nuna miki tunda kika taso a cikin gidan nan? Kinsan yadda Baffanki baya son 6acin ranki, na tabbata da kika bari aka bi komai a hankali, da zai hak'ura har ma ya sauko daga dokin nak'in da ya hau. Amma da yake ke d'an Adam ce butulu, shine kika tafi kika kai k'ararsa wurin Malam ko? Dan kinsan shi ba zai iya bijirewa maganar mahaifinsa ba ko? Kinyi dai-dai. Sai dai ina so dake ki bi sannu, kada son zuciya ya kai ki ya baro ki."
"To meye laifi na anan?"
Ta fad'a tana kallon Goggon.
"Haka kawai sai in bari a danne mun 'yancina, bayan kuma bashi da wasu reasons masu k'wari. Ni banga wani rashin kyautawa ta ba, kuma ko Mal. Baba da na fad'a mai, haka yace nayi dai-dai da nayi wayon sanar da shi."
Daga haka ta wuce d'aki ta bar Goggo cikin jimami, da tashin hankalin irin tarbiyyar da sukai mata, da kuma rashin nusar da ita muhimmancinsu a rayuwar ta. Gashi nan yanzu reshe yana neman juyewa da mujiya.
Girgiza kanta tayi, daga haka ta wuce d'akin Baffa, dan ta san yana buk'atar wanda zai yi magana da shi.
Tunda ta taso a rayuwarta yau ce rana ta farko da ta ta6a yin abun da Goggo tace bata kyauta ba, duk kuwa da ta6argazar da take tafkawa, wanda ita kanta wani lokacin idan tayi wani abun tana jin bata kyauta ba, amma son kai da son zuciya irin na iyayenta bai ta6a bari sun tsawatar mata ba, hakan yasa ta mik'e a haka, gaba d'aya rayuwarta bata san akwai wata kalmar baki kyauta ba.
Kan gadonta ta fad'a hankalinta kwance, ta fara kiran number Sadam, bugu biyu zuwa na ukku ya d'aga tare da cewa
"how's my baby doing?"
"Great"
ta bashi ansa, inda damuwa da fushin da ta shigo da shi, ta neme su sama-ko-k'asa ta rasa, sai wani farin ciki da jin dad'i da suka maye gurbinsu.
Muryarsa ce ta katse mata tunani inda yake cewa
"me kika samo mana a Daura? I'm eager to hear the result."
Murmushi ta saki, sannan ta tura hannunta a baki tana tsotsa a hankali tace
"zan fad'a maka, but what wud I get in return?"
Jim ya d'anyi, daga bisani yace
"I'll love you, & stay by your side for the rest of my life."
Wani murmushin ta kuma saki, wannan karon mai d'an sauti tace "promise?"
"You know I mean my words, just trust me."
"I trust my bae."
Ta k'arasa tana dariya.
"Now, I'm all ears."
Ya fad'a ta d'ayan 6angaren.
A haka ta labarta masa duk abinda ya faru, daga k'arshe ta sanar da shi kiran da Baffa yake masa.
Wani mugun farin ciki ne ya lullu6e Sadam, yayin da a zuciyarsa yake jin hak'onsa ya kusan cimma ruwa. Daga nan suka yi bankwana ta kashe wayar ta juya tayi kwanciyarta, tana jin wata sabuwar soyayyar Sadam na yawo a gaba d'aya jinin da ke gudanyawa a cikin jikinta.
**7:00 (PM)
Jikinshi sanye da lallausan bak'in yadin filtex wanda ya ji lafiyayyen aikin hannu da zare kalar ruwan gwal mai sheki. An kuma k'awata shi da d'inki irin na samarin zamani wad'anda suka ci suka k'oshi, suke kuma ji da gayu da k'uruciyarsu.
A k'afarshi rufaffen bakin takalmi ne na Rockport, ya dora hular zanna bukar da tayi matching da kwalliyyarsa.
Yadda yayi karin hular ya fito da asalin zati da haibar da Allah (SWA) ya masa, fuskarshi ta fito tas-tas, manya-manyan idanunsa suka kuma fesowa, in banda jajayen la66ansa da suka fara canja kala zuwa bak'i-bak'i.
Hannu yasa ya shafe fuskarsa, sannan ya d'aura bak'ar agogon fata a tsintsiyar hannunsa, ya mak'ala cuplinks a hannuwan rigarsa, ya k'ara gyara zaman hularsa sannan ya fito, hannunsa rik'e da makullin mota, yana cigaba da basarwa yana bada feelings ma duk wanda yayi katarin kallonsa, har zuwa lokacin da ya iso gaban motarshi.
Titin GRA ya d'auka, a gefe guda wak'ar Good Enough ta Jussie Smolett tana tashi a hankali, yayin da yake jin kanshi a wata duniya ta daban, tamkar yana yawo a sararin samaniya.
Tafiyar minti sha biyar ta kawo shi k'ofar gidan, wannan karon oda ya rink'a yi, mai gadi ya fito ya bud'e masa gate, ba tare da 6ata lokaci ba ya tura motar ciki, ya sama ma kansa wuri yayi parking, sannan ya fito ya jingine da jikin motar, ya ciro wayarsa ya fara kiran number Jay.
🤗🤗🤗🤗👏
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro