BABI NA SHA BAKWAI
***Maiduguri.
Misalin k'arfe bakwai na safe ya fito jikinshi sanye da 3quater da armless d'in riga na kayan sport da aka rubuta 53 a gaba da bayan rigar ya wuce gym d'in dake cikin hotel d'in domin ya motsa jinin jikinsa.
Wasan basketball ya samu wasu suna bugawa, nan ya shiga cikinsu aka cigaba da yi tare da shi, wanda a k'alla ya d'auke su kusan mintina arba'in, sannan suka samu damar tsagaitawa tare da zaunawa a bencinan da aka jera a wurin.
Gorar ruwan da ke gefenshi ya d'auka ya sha, sauran ya juye a jikinsa, sannu a hankali yake k'are ma mutanen wurin kallo, daga bisani ya juya tare da mik'a ma mutumen da ke gefenshi hannu.
"Yau kam naga wanda ya fini k'aunar basketball."
Dariya mutumen yayi tare da mik'a masa hannunsa yana cewa
"It's my fav sport, in fact ban iya ko wanne irin wasa idan ba shi ba."
"I see."
Cewar Sadam yana girgiza kansa.
"By the way, I'm Sadam Kazaure."
"Faisal Goni."
Ya fada bayan sun mike tsaye.
A tare suka fito suna takawa da niyyar wucewa d'akunansu, Faisal ke tambayar Sadam abinda ya zo da shi garin na Maiduguri.
"Aiki ya kawo ni. And you?"
"Ni kam gari na ne, nan aka haife ni."
"But mai ya kawo ka nan? Though nasan ba hurumina ba ne."
Yayi maganar tare da 'yar dariya.
"Eh to, amma dai ka share. Abin sirrine."
"Na so?"
"Eh mana. Ko aikin jarida kake ne?"
A tare suka sa dariya,
"No fa."
Ya d'an juya yana kallonsa,
"Ernmmm.. Idan baza ka damu ba zan so inyi maka wata 'yar tambaya please."
"No problem, ina sauraren ka."
Suka koma gefe suka d'an tsagaita da tafiyar, inda Faisal ya mik'a hankalinsa ga abinda Sadam zai fad'a.
"Dan Allah ko zaka iya kwatanta mun wani babban masallaci inda ka san zan samu wani babban Malami haka, ina da issues ne da nake son warwarewa."
Jinjina kai yayi, yana nazarin maganar tasa, daga bisani ya sauke idonsa akan shi.
"Sure, akwai malamai da na sani da dama, sai dai idan babu matsala ina son sanin kad'an daga cikin abinda ke tafe da kai."
"Ka gane ko."
Sai kuma yayi shiru.
"Ehenn, ina saurarenka."
"Ka gane, a yanzu haka maganar da nake yi maka, ina tare da yarinyar da nake son in aura, iyayenta sun rasu, sai k'anin mahaifinta, wanda yake takura mata sosai, at first naje gidansu ina son aurenta, but yayi denying, yace dole sai ta auri wani wanda bata son shi, so shine muka yanke shawarar muzo nan muyi aurenmu, daga baya sai mu koma gida."
Shiru Faisal yayi, yana tunanin dalilin da yasa ake samun yawaitar irin wad'annan matsalolin. Daga k'arshe ya dafa Kafad'ar Sadam,
"Kada ka samu damuwa, I'll help you, I'll take you to my grandfather, babban Malami ne, idan munje sai ka yi mishi bayanin matsalarka, shi kuma zai baka shawarar abinda ya dace."
"Kai, nagode gaskiya, naji dad'i sosai. Yaushe kake ganin ya dace mu je?"
"Barin baka number na, idan ka shirya sai ka yi mun magana, I'm always free."
"Thank You, thank you Mr. Goni. It's very nice meeting you."
"My pleasure."
Ya sanya mishi number, ya mik'a masa wayar, suka k'ara yin musabaha, sannan kowa ya zarce masaukinsa.
D'akin ya wuce, ya yi wanka sannan ya sauka ya samo masu abinci, ya dawo.
A hankali ya fara kiran sunanta yana tsaye bakin k'ofar d'akinta, bata ansa ba sai dai ta taso ta bud'e k'ofar, ta juya da sauri ta koma ciki.
Shigowa yayi shima, ya ajje kayan hannunsa yayi kanta yana tambayar
"How was your night?"
Shirun da ya ji bata ansa shi ba, ta kifa kai sai kuka take, yasa a hankali ya zauna bakin gadon
"Ya kike so inyi ne? Da me kike so inji? Da kukanki ko da abinda ke gabanmu? Babe dan Allah ki daina kukan nan, ya kamata ki gane yanzu wata sabuwar rayuwa zamu shiga, I'm sorry dear, tashi ki ci abinci kinji."
"Ina jin kamar ban yi ma Baffa adalci bane Sadam, guiltness ya hana zuciyata sakewa, duk kuwa yadda naso in yakice abinda nake ji. Ina tsoron kada son zuciyata ya kai Baffana ga kamuwa da wata larurar."
"Oh God! Babe wannan duk wani imaginations ne, ki basar, ki manta komai, ni zan shayar dake jindad'i da farincikin da baki ta6a experiencing irinsa ba. Please tashi kiji, akwai surprise d'in da nazo miki da."
Mik'ewa tayi, a haka yasa mata abincin, ya hau har saman gadon ya mik'a mata, kalamanshi masu matuk'ar tasiri a zuciyarta yake fad'i mata, cikin d'an k'aramin lokaci ya tafiyar da bak'incikin da take ciki.
Bayan sun gama, ya sanar da ita yadda suka yi da Faisal.
"Kinga ko munje wurin kakansa abinda zamu fad'a masa kenan, dan kada muyi baki biyu."
"Amma me sa zamu ce k'anin Babana ne? Me zai hana mu fad'i gaskiya kawai."
"No babe, just listen to me, ki bi abinda nace miki kawai. Kina ji ko 'yan matana."
Murmushi tayi, wanda iyakarshi la66anta,
"Your wish is my command."
"That's my boo. Now ki zama ready, 4:30pm zamu je."
Haka suka cigaba da firar yadda abubuwan zasu kasance, daga k'arshe suka mik'e suka fita wurin swimming pool d'in dake bayan d'akunansu.
*04:50 (PM)
"Babe, fito mana, muna 6ata lokaci fa."
"I'm here, mu tafi kuma, ka wani tsaya kana kallona."
"To ba dole ba, wannan irin kyau da kika yi."
Jujjuyawa tayi,
"ina wani kyau a nan, kana gani ina fama da bak'ar riga kaman 'yar coci."
Dariya ya saki, tare da takawa gabanta, idanuwansa dake rikirkitata ya zuba mata, cikin wata sassanyar murya ya fara magana.
"To me, U're not like those people. U're someone very special, very dear to my heart. U're one of a kind. And everything about you is way too different from others. U're unique, and difficult to find. Cuz people like you, are very rare darling. You look marvelous. Okay?"
K'asa tayi da idanunta, har cikin zuciyarta, tana son yadda Kazaure ke kambata, hakan ke k'ara mata so da k'aunarshi a kowanne lokaci. Girgiza kai tayi, muryanta ciki-ciki tace
"Okay."
"That's my Angel, and kada ki k'ara had'a kanki da 'yan church daga yau, kinji."
Suka fito, suka shige mota, Faisal na gaba suna binshi a baya, suka doshi Bumsa Road da ke cikin unguwar Bolori, Borno, Maiduguri.
Gaban wani babban gida Faisal yayi parking, haka suma suka gyara nasu parking d'in duk suka fito, ya shige gaba suna binsa a baya har zuwa cikin gidan.
Daga gefen gidan, k'aton masallacin juma'a ne, wanda ya mamaye kusan rabin layin gaba d'aya.
Kana shiga gidan, zaka tar da wani part a farkon gidan, inda Faisal ya shigar da su.
Yawan tarin littattafan addini da suka gani, shi ya basu tabbacin part d'in Mal. Goni kakan Faisal ne.
Da sallama dogo, bak'in dattijon ya fito, jikinsa sanye da alkyabba wacce malaman da suka sha karatu suka k'oshi suka fiya amfani da ita, kansa kuma rawani ne na farin zabuni, shima dai rik'ak'k'un malamai ne kawai suka san sirrin yadda suke nad'a shi.
Bayan sun gaisa da shi cikin mutuntawa da karamci, Faisal ya yi mishi bayanin abinda ke tafe da su, inda ya ja gefe, yayin da Sadam ya cigaba da d'ora k'arya da gaskiya wa Mal. Goni.
Girgiza kai yayi, a karo guda ya sauke idanunsa kan Jay, yayin da zuciya da fuskarsa, suka bayyanar da tausayinta cikin d'an k'ank'anin lokaci.
"Faisal."
"Na'am Malam."
"Ku d'an bani wuri, zanyi magana da wannan baiwar Allahn."
"To shikenan."
Da haka suka mik'e suka fita, shi kuma ya maida hankalinsa gare ta.
"Menene sunanki yarinya?"
"Jameela."
"Shin labarin nan da suka zo dashi kin tabbatar gaskiyarshi kenan?"
"Eh haka ne Malam."
"Masha Allah, amma Jameela, me sa baki hak'ura kinyi biyayya ma kawunki ba? Ko mutumen da ya so had'a ki dashi yana da wasu munanan dabi'u da addinin musulunci yayi turr da su?"
Shiru tayi, da kanta a k'asa, kamar baza tayi magana ba, sai kuma ta d'ago
"Bana son shi ne Malam, kuma na kai wanda nake so amma sun k'i su aura mun shi, ni kuma gudun fad'awa tarkon shaid'an, yasa muka yanke shawarar mu gudu muyi aurenmu, daga baya sai mu koma gida, lokacin komai ya zama tarihi."
"Shikenan tunda haka kika fad'a, na fahimci uzurinki, sai dai abinda nake son ki gane shine, komai na duniya da albarkar iyaye ya fi riba, amma tunda kinje musu da batunki, basu kalle shi ba, ni zan d'aura muku aure gudun fad'awa wata hanyar, kamar yadda kika fad'a, sai dai ina rok'onki alfarma, da shekara ta zagayo, ku tattara ku koma gida domin ku samu albarkar mahaifanku."
"To shikenan Malam. In Sha Allah."
Jay ta fad'a, duk da maganar iyakarta fatar bakinta, domin a yanzu babu burin da ya rage mata, irin taga an d'aura aurensu da Kazaurenta
Bayan Malam yasa Jay tayi kiransu kowa ya dawo ya zauna, yayi gyaran murya, tare da kai dubansa ga Sadam
"Nayi magana da Jameela, ta kuma bani k'arin haske akan lamarinku. Abinda nake so shine, ka barta a nan ta kwana, kai ka koma masaukinku, gobe idan Allah Ya kaimu ka taho da sadakinka, ni zan d'aura aurenku bayan mun gama sallar juma'ah."
Wani irin farinciki ne ya bayyana a fuskar Sadam, godiya yai ta zuba ma Malam, lokacin da ya juya yana kallon Jay, itama murmushin ne kwance akan kyakkyawar fuskarta.
Sai dai duk da jin dad'in da take na zata samu cikar burinta, hakan bai hana wani fanni na zuciyarta azabtar da ita ba, haka nan dai take daurewa, tana tursasa zuciyarta, tare da danne abin a duk lokacin da ya bijiro mata.
Mik'ewa Malam yayi, ya gyara zaman alkyabbarsa,
"Idan kun gama, ki shiga daga ciki, zan yi ma mutanen gidan bayaninki."
Daga haka ya wuce, Faisal ya rufa mishi baya aka barsu daga ita sai shi a cikin palon.
Cikin zak'uwa ya fara magana,
"Kinga abinda nake fad'a miki ko? Gashi komai ma yazo mana da sauk'i"
Murmushi kawai tayi, shi kuma ya cigaba.
"Da na fita daga nan, first abinda zanyi shine neman gidan da zamu zauna, zan sama mana wuri mai kyau, irin wanda kike so babe girl."
Har yanzu dai bata ce dashi k'ala ba, shi kawai yake ta surutunshi, hakan yasa ya taso daga inda yake ya dawo daf da ita, yasa hannu ya d'ago kanta dake duk'e.
"What...? Haba babe, wato baza ki daina kukan nan ba ko? Wai jira ma, ko dai har kin gaji da ni tun ba'a je ko ina ba?"
Kai ta girgiza, hawaye na kwarara a idonta.
"Then what? I thought this is what we both want, babe menene abin kukan?"
Share hawayen tayi, ta d'ago tana kallonsa.
"Sure, this is what we want, but na kasa yafe ma kaina gagarumin laifin da na yi, ina jina tamkar wacce tayi kisan kai wallahi, na kasa samun natsuwar zuciyata."
Hannunta ya rik'e, a hankali ya fara magana.
"Babe stop blaming yourself please. Ki tuna this is the only right we've, ya kamata muyi amfani da opportunity d'in da muka samu, one day zamu koma gida, nd trust me, Baffa zai fahimci kuskuren da yayi. Haba amaryan Kazaure, gobe kaman haka fa mun zama married couple. Kina so a kai mun ke da kumburarran fuska ne?"
Girgiza mashi kai tayi,
"A'a mana."
"Then stop this crying, ki sama ranki kamar bamu ta6a barin gida ba, kisa a ranki kamar dama can nan ne duniyar da muka fara shimfid'a rayuwarmu. Okay?"
"Okay."
"That's my bae, now smile for me."
Ya fad'a cikin wata irin muryar da ta sa ta k'yalk'yalewa da dariya ba tare da ta shirya ba.
"Haba ko ke fa, amma kin sa heart d'ina yana boiling, kinsan idan kina kuka har wani extra motsi zuciyana yake yi."
"Sweet mouth nko"
"No be sweet mouth babe, kinsan ina bala'in sonki."
Dariya tayi sosai,
"Ai nima ina mutuwar sonka."
"I know that babe girl, ba sai kin 6ata bakinki ba."
Kiran sallar maghriba da aka kwad'a a babban masallacin da ke gefen gidan shi ya katse su, a gurguje Sadam yayi mata sallama, ya fito, suka had'u da Malam da Faisal suka yi alwala suka wuce masallaci.
Faisal ne ya taimaka masa zuwa wurin wani agent na gidaje, cikin ikon Allah kuma aka dace.
Gida ne irin compound, mai part-part a ciki sun kai guda goma, sai dai kowa da gate d'inshi, ta yiwu ma har ku gama rayuwarku wani bai san wani ba.
Gidan ba laifi self-contained ne, mai d'auke da d'akunan kwana guda biyu, kowanne da toilet a ciki, sai kitchen, da madaidaicin palo, dai-dai ango da amarya.
Ba'a samu matsala ba Sadam ya biya kud'i, aka bashi makullan gida, daga nan ya zarce hotel, zuciyarsa cike da tunanin yadda za'a yi ya samu kud'ad'en da zai sayi kayan da za su saka a cikin gida.
'Dole ya nemi inda zai buga caca da sauran kud'in da suka rage mishi, idan akayi sa'a, zai iya samun abinda ya ninka su, har ya samu biyan buk'atarsa.'
Shawarar da ya yanke kenan, hakan yasa bayan ya isa hotel yayi sallar isha'i, ya fito, a restaurent d'in wurin ya ci abinci, sannan ya wuce bar (mashaya) dake cikin hotel d'in, watak'ila yayi dace da abinda yake nema.
Cikin sa'a ya ci karo da dandazon mutane akan wani faffad'an teburi.
Abinda idanunsa suka hango masa ne yasa annurin fuskarsa k'ara bayyana, ya zarce gaban manajan wurin yasa aka kawo masa kwalbar barasa, ya d'aga ta sama, ya sha kamar rabi, sannan ya cire kud'i ya d'ora, ya zarce teburin da ake buga cacar.
Mutanen da ya samu a wurin, wasu irin hatsabibai ne da suka fishi sanin daraja da mutuncin caca, dan haka ba'a d'auki dogon lokaci ba suka tatike gaba d'aya abinda ke aljihunsa.
Kuka ne kawai Sadam bai yi ba saboda bak'in ciki, wannan wace irin rana ce? Mamakin kansa yake anya shi d'in ne kuwa? Ta wani 6angaren kuma yana mamakin k'wazo irin na mutanen da suka yi wuju-wuju da hazik'in d'an caca irin Kazaure.
Cikin zafin zuciya ya ida kwakwad'e sauran barasarsa ya fito yana wasu irin surutai, ya koma d'akinsa.
(Friday, 01 Feb, 2012.)
Masallacin ya cika sosai yayin da Sheikh Mal. Goni yake gabatar da hud'uba mai ratsa zuciya, wacce gaba d'aya ta ta'allak'a ne akan hak'k'in da 'ya'ya suke da shi akan iyayensu. Yayi hud'uba mai zafi, wacce da yawa mutanen da suke wurin sai da suka zubar da k'walla, daga bisani aka tada sallah aka gama, kafin ya bukaci awwalin Sadam wato Faisal ya matso, shi kuma ya zama na Jameela, jama'ar wurin suka shaida aurensu, akan sadaki nera dubu talatin cif-cif, wanda sai da Sadam ya siyar da agogunanshi guda biyu, sannan ya samu kud'in.
Bayan sun koma cikin gidan Mal. Goni yayi musu kyakkyawar nasihar data ratsa zukatansu, ya kuma k'ara rok'on alfarmar da zaran sun cika shekara, su tattara su koma mahaifarsu, domin kuwa albarkar iyaye ce kawai, zata sa su samu biyan buk'atar komai a cikin rayuwar auren nasu.
Sallama suka yi musu, tare da godiya, sannan suka fito suka shige mota, fuskokinsu d'auke da jin dad'in cikar burinsu da suka samu.
Bayan sun hau titi sosai, Jay ta kalle shi, amma sam hankalinsa baya wurin da alama ya shiga tunani mai zurfi.
"Me ke damunka?"
Ta tambaya tana ta6a kafad'arsa.
Firgit ya juyo yana kallon ta, kamar zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru ya cigaba da tuk'inshi.
"Sadam! What's your problem? You seems not happy at all. Menene?"
Hannunshi ya d'ora akan nata, hankalinshi na kan titi ya fara magana.
"Ina tunanin abubuwan da zamu zuba a gida ne, cuz gaba d'aya kud'in hannuna sun k'are, and hotel ma dak'yar na samu na k'arasa biyan kud'insu, ina jin haushin kaina that I can't provide all your needs, I'm sorry Angel, in sha Allah everything will be just fine. Kinji."
Dariya ma ya bata, a gefe guda kuma ta ji ta d'an tausaya mishi, hakan yasa ta bud'a jakarta, ta ciro ATM card d'inta, ta d'aga mishi.
"We'll buy all we want with this. I've enough money, so have no worries, yau ranan farin cikinmu ce."
A kaikaice ya juya yana kallonta,
"are you serious?"
"Very, so ka d'auki hanyar da zamu samu bank, idan muka cire kud'in sai mu wuce kasuwa."
The billionaire's Daughter.. chaiii😂😂😂😂
Nd let's the journey begins 💃💃
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro