BABI NA HUDU
"Me ke damun ka haka? Naga tunda ka shigo baka da aiki ban da tsaki da yawan tunani. What's the matter?"
A hankali ya d'ago yana kallon shi, kamar zai ce wani abu sai kuma ya share, yana mai juyar da kansa zuwa kallon gefe.
Tsai yayi da idanunsa akan Sadam,
"Definitely, there is something terrible that's tormenting your mind."
Ya fada lokacin da ya karasa gabanshi hannuwansa duk biyun cikin aljihu.
Kallonshi Sadam yayi, kamar ya fad'a masa sirrin da ya dad'e yana 6oyewa, a matsayinshi na babban abokinsa k'waya d'aya tal, a duk fad'in garin na Maiduguri.
Sai dai ina, ba zai iya yin wannan gangancin ba, bai kuma san ta yadda zai fara masa bayani ba, kamar yadda bai san da wace irin fuska zai kalli abun ba. Yanayin murmushin da ya dora a labbansa na dole ne, ya kalle shi da kyau,
"Nothing serious, just a little fever. Zan koma ta gida ne in samu in huta."
"Kar ka manta da ni dai, matsawar kana bukatar wani abun."
"In sha Allah."
Ya fad'a da d'an murmushin da ya fi kama da na kafin hali.
Hannu SS din ya mika masa, ya ansa suka yi musabaha, sannan ya koma cikin bankin, yayin da shi kuma ya tada motar ya bar harabar wurin.
Cikin GRAND PINNACLE HOTEL dake Jimna Road, Pompomari, Maidiguri, ya dakata da motarshi.
Mutane ne cike jingim a babban dakin da za'a iya kira da club, maza ne, da matayen da basu san darajar kansu ba. Karfe hudu ne da yan mintina na yamma, amma hakan bai hana madaddalar tara mutane ba.
Da yawa shaye-shayensu suke yi, k'alilan a cikinsu ke buga wasan karta, wasu na buga whot, wasunsu kuma sunyi dabdala sun zagaye wani babban teburi, suna ihun da ya karade babban dakin mai yawaitar mutane.
Ko da ya shigo kai tsaye gaban teburin ya dosa, hakan yasa hankalin jama'ar ya dawo gare sa, da yawa suna fadin
"Sai Kazaure, sai Kazaure."
Murmushin nan nasa mai tsada ya saki, ta gefen kumatunsa yana mai nannade hannun rigarsa, ya ja kujera domin sama ma kanshi mazauni.
Cikin mintunan da basu haura ashirin da biyar ba, ya gabatar da sana'ar da ya fi kwarewa a kanta, ya kuma samu nasarar kwashe duk wasu kudade da mutanen suka dora.
Da yawan lokuta ba'a cika tashi daga caca cikin dad'in rai ba, yau din ma haka ta kasance, dan kuwa sai da suka kai ruwa rana da mutumen da bai bar ma koda nera biyar ba.
Fad'a sosai ya kaure tsakaninsu, sai da duk suka galabaita, sannan suka saki junan su, yayin da jama'ar wurin suka cigaba da ihu, har sai da Sadam din ya buga musu muguwar tsawar da ta sanya kowannensu shiga taitayinsa.
Cikin jin kai da kwarewa a bariki ya isa ga k'atuwar kwalbar barasar dake kan wani teburi ya d'aga, ya tuttula ma yan hanjinshi, a karshe ya wurgar da kwalbar yana mai fitar da numfashinsa cikin sauri.
****
Shekararshi ta biyu kenan da dawowa aiki garin na Maiduguri, a iya wannan shekarun kuma ya san Sadam, har ya zamo mishi amini, amincin da ya rikida zuwa yan uwantaka. Abinda ya kasa ganewa shine, yadda abokinnasa ke boye duk wani lamari da ya shafe shi, daga ciki kuwa hadda ma adireshinshi, duk da dai ba cika haduwa suka yi ba bayan tashi aiki, idan ma har hakan ta kama, sun fi gane su hadu a wani wurin shakatawa, domin tattauna batutuwan gabansu.
Profile dinsa na ofis ya bincika domin samun adireshin nasa, dan kuwa a shekaru biyun da ya san Kazaure, bai taba ganinshi cikin irin yanayin da ya ganshi a yau ba, uwa uba, ya kira wayarsa ya fi a kirga ba tare da ya daga ba. Tsoronshi daya kada jikinnashi ne ya tsananta.
Titin New GRA ya dauka bayan ya fito, a kofar gida mai lamba 56 ya dakata kamar yadda ya gani a profile din nasa.
Ga mamakinshi katon padlock ne a k'ofar palon, yayin da yake jiyo tashin kukan yarinya k'arama, wacce bai san ko wacece ba, dan kuwa a sanin da ya yi ma abokinnasa, saurayi ne gangariya, wanda bai taba aure ba, balle ayi maganar haihuwa.
A hankali ya ke ci gaba da tura kai cikin gidan, a lokaci gida, kukan na ci gaba da tunkararsa, kasancewar gidan ba wani girma ne da shi ba.
Ta tagar palon ya tura kansa da sallama, da gaggawa Jay dake durk'ushe ta mik'e, ta isa jikin tagar tana mai daga labulen, a sa'a guda idanunta suka fada cikin nashi.
Kallon nata yake shima, sai dai bai san abinda zai ce ba, yayi gyara murya a hankali, da zumar fara magana, sai kuma ya tsinkayi tata muryar cikin sheshshekar kuka
"Dan Allah malam ka taimaka ka fitar da ni a gidan nan, kaga yarinya ta zata mutu da yunwa, tun safe bata sa komai a bakinta ba."
Ido ya fara zarawa yana tunanin anya ya bi adireshin na Sadam dai-dai kuwa?
"Ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka"
Ta katse mishi tunanin da muryarta mai rauni, tana mai tsiyayar da hawaye tamkar ace an bud'e famfo ne.
Take zuciyarsa ta tsinke, yake kuma jin ko da ba gidan Sadam d'in ba ne ba, dole ya taimaki baiwar Allahn nan, domin a duniya babu abinda ya fi d'auka da daraja da kuma muhimmanci irin mace. Cikin k'arfin hali ya dubeta,
"It's okay, I'll help you. Amma ki daina kuka please, kinji?"
Da baya ta koma tana sauke ajiyar zuciya, tana mai share hawayenta, daga waje kam tana jin yadda yake kokarin bige padlock din da yayi musu katanga da daddadar iskar duniya.
*** *** ***
I'm here with my puppy eyes😡😳😳
Biko, show some love with your votes nd comments abeggi😞😞😞
Nd to y'all ghost readers, try nd say something about the story mana. Abaaa😕😕
Bless y'all, nd I love y'all.❤❤❤❤
Lubbatu❤👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro