Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA BIYU

A wurin ta duk'e tana wani irin kuka mai ta6a zuciya, sai dai da yake k'irjin Sadam babu zuciyar kamar yadda ta fad'a, haka ya wuce ta bayan ya dawo daga d'auko abinda yayi niyya ya shige d'aki, yana mai buga k'ofar da duk iya k'arfinsa.

Hakan yayi dai-dai da haskowar walk'iya mai ban tsoro, tare da tashin wata gagarumar tsawa, daga nan aka tsuge da ruwan sama tamkar da bakin k'warya.

Idan da sabo ya ci ace ta saba da azabar da take sha kullu yaumun daga wurin mijinta, abin alfaharinta, mutumen da take so fiye da numfashinta, sai dai kuma bata da idon da zata kalli wani da matsalarta, domin idan akwai wani mai laifi, to ba Sadam bane, illa ita, wacce tayi sanadiyyar jefa kanta a kurkutun azabarsa.

Ta kwashi kusan minti ashirin duk'e a wurin tana kuka, sa'ili da 'yan yatsunta ke mata tsatstsauran zinga, har tana jin tamkar zasu bar gangar jikinta ne.
A daddafe ta mik'e zuwa d'aki, jin kukan Rukayya wacce da alamu ta motsa ne ba tare da ta ji mamantata ba.

Yarinyar ta dauka ta rungume tsam a k'irjinta, wani kukan ta kuma fashewa da shi, itama Rukayyar kukan take tana fadin

"Maami abinci"
Cikin muryarta ta 'yan yaran da basu ida k'warewa da maganar ba.
Ruwa ta bata ta sha, ta kuma maida ta jikinta ta rungume tana shafa kanta har sai da wani baccin yayi awon gaba da ita.

'Baza ta iya jure zaman cin kashin nan ba.'
Tayi furucin a kasar zuciyarta, inda ta fara sak'a hanyar da ya dace ta bi domin k'watar ma kanta 'yanci, duk da ta san bata da shi a gidan SADAM.
Amma ya zama dole ta jajirce, ko dan gudun rayuwar da yarinyarta zata taso a ciki.
Duk da kasancewar bata da wani wanda zai tsaya mata tsayin daka, wurin samuwar 'yancin nata a matsayinta na mace, halittar da Allah ya fifita fiye da dukkan halittunsa.

****
Washe gari da sassafe ya fito cikin shirinsa na bak'in wandon chinos, da rigarshi kalar sararin samaniya, necktie d'inshi ma kalar ruwan bula ne mai turuwa, yayi zanzaro irin na matasan da suke ji da tashen kuruciyarsu, belt dinsa kirar Versace, ya taimaka sosai wurin kara fito da kwalliyar tasa.
Cikin isa da jin kai ya fito, da alama shirin aiki ne yayi, gefen kafad'arsa ta dama sagale da jakar kwamfutarsa, sai tashin wani dadd'an k'anshi mai tsada yake yi.
Nera d'ari biyar ya fitar a aljihunsa, ya d'ora samar teburin tsakiyar palon, bai jira komai ba, ya doshi hanyar da zata sada shi da waje.

Da sauri ta fito har tana karo da bango, bata damu da gaishe da shi ba, domin ya sha yi mata kashedi a kan hakan, kai tsaye ta sha gabansa ta fara magana cikin kwarin gwiwar da bata san ina ta samo shi.

"Ni kam Allah Ya na gani na gaji da zaman uk'ubar da kake mun Kazaure. Dan Allah ka taimaka ka bani takardata ko dan ka hutar da ni da kai duk gaba daya."

Duk wanda ya ga yadda tayi maganar, zai tabbatar ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi kafin ta iya hada kalmomin da ta furta ba.

"Matsa mun a nan malama."
Ya fad'a a tak'aice, tare da d'aurewar fuska.

"Babu inda zanje sai ka bani takarda ta."
Ta fad'a yayin da take kallon gefe.
Daf da ita ya matsa, har ta kan iya jin saukar numfashinsa mai zafi saman fuskarta, yana jifarta da wani wulak'antaccen kallo, daga bisani ya kama doguwar habarta, ya saita idanunsa cikin nata, kafin ya fara magana.
"Sanin kanki ne tsakani na dake babu saki, kin fi kowa sanin idan ma na sake ki baki da inda zaki je, watak'ila ki karaci rayuwarki cikin tasha."
Yayi murmushin raini mai kona zuciyar wanda duk ya ci karo da shi, sannan ya kara da fadar
"Ni kuma abinda ba zan iya jure gani ba kenan."
Tsai yayi da idanunsa a kanta, tamkar mai karantar yanayinta, a karshe ya sake mata fuska, har kuma yanzu murmushin na nan makale da labbansa.
"Ba ni hanya in wuce Jameela Kasad."

Hawayen da take mak'alewa ne suka gangaro, haka kuma bakinta ya kasa furta komai, 'wannan wace irin kaddara ce?' Ta jefi zuciyarta da tambayar, sai dai bata sani ba. Abu daya da zata iya tantancewa shine, ita ce silar komai, ita kuma ta jefa kanta a koma wane irin hali ta tsinci kanta, ta kuma tabbatar da wannan ne dalilin da yasa tayi bankwana farin ciki a gaba d'aya rayuwar gidan aurenta.
Sama da shekaru hud'u kenan, tunda ta auri Sadam masoyinta, take fuskantar tasku da bala'i kala-kala a 'yar gajeruwar rayuwar da tayi a duniyarta.
Bata ankara ba ya hankad'ar da ita, a karo guda ya gyara zaman jakar dake kafad'arsa, ya wuce yana mai kakka6e jiki tamkar wanda ya taba wani abun kyama. Motarsa, ya shige, ya bar harabar gidan.

Kuka ne ya kuma k'wace mata, tunawar da tayi ita d'in yadda take a baya.
Rukayya dake la6e a k'ofar d'akin maman tata ta k'arasa fitowa ganin dodon da take tsoro ya fita, dan kuwa a haka take ganin mahaifin nata, hakan yasa Jameela tayi saurin shafe hawayenta, ta mik'e ta kama hannunta tare da k'ak'alo murmushin dole suka koma ciki, domin yi mata wanka.

Yes.. yes.. yes! There we go again👌😃

Any guesses yet?

Me ya jefa Jameela Kasad a irin wannan tasku na da namiji?

What do you think of Sadam Kazaure?

Looking forward to hear yo tantalizing comments hayatiess😃🖤🖤🖤

One more thing, Kar a manta a danna tauraron nan dake gefe kadan da hannun mutum na hagu, a kuma shiga ta akwatin kwament domin ajje ra'ayoyi.😍😍😍

Abinda kuke ji dangane da labarin shi zai sa ni zage damtse in tabbatar da na gamsar da ra'ayoyinku😃😃👌👌

Na gode da kaunarku.

Lubbatu😍👌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro