BABI NA BIYAR
Katsina, 2011
Sanye take da faffad'ar farar riga mai dogon hannun da ta tattare shi zuwa gwiwar hannunta.
Dogon bak'in skinny skirt ta d'ora wanda ya bi jikinta ya lafe, ya kuma hau har saman cikinta (high waist) ta dai-daita jikinta, sannan ta d'auko tattausan farin mayafi karr, ta yane kanta da shi.
A lokaci guda ta duk'a ta sanya bak'ak'en sneakers d'in dake ajje tsakiyar d'akin, ta taka zuwa jikin bags hanger ta ciri jakarta kalar ruwan dorowa mai ratsin bak'i, ta dawo gaban dogon madubin da zata iya hango tun daga kanta har zuwa k'afafunta.
Sai da ta k'are ma kanta kallo tsab, daga bisani ta d'auki ipad d'inta, ta fito.
A tsaye ta samu Goggo da Baffanta, kasancewar haka bafulatanar mahaifiyarta ta horar da ita da kiransu tun tana k'arama. Da alama yayi shirin fita, jikinshi sanye da d'anyar shadda dinkin babbar riga, har ma da hula a kansa.
Tura baki ta fara yi, bata damu da gaishe da iyayen nata ba, tana mai bubbuga k'afa, hakan yada Baffan bud'e hannayensa, ta isa gareshi fuskarta a tur6une .
"Baffa shine zaka fita ba tare da ka ganni ba ko? Kuma kasan fa yau zan fara zuwa school amma shine zaka yi tafiyanka."
Ta k'arasa tana shirin matse hawaye.
Dariya duk suka sanya, har Goggo dake gefe, a hankali ya fara bubbuga bayanta.
"Haba Ummina, ya zanyi in fita ba tare da na ganki ba. Yanzu haka shirin nan da kika ga nayi fitowarki kawai nake jira."
Dariya ta saki itama,
"Ina kwananku?"
"Lafiya lau."
Suka ansa a tare, kafin suka zarce samar dogon teburin da aka wadata shi da abubuwan motsa baki.
A tare suka fito da Baffa bayan sun gama cin abincin, hannunnta cikin nashi, fuskar kowannensu na tattare da annashuwa da annuri mai bayyanar da tsantsar alfaharin da suke da juna.
Wata bak'ar Corolla S taga Baffan da kanshi ya bud'e ya shiga, kafin yayi mata umarnin shiga itama.
Juyawa tayi tana kallonsa bayan ta rufe kofar motar, fuskarta d'auke da murmushi
"Lallai Baffa kana ji da wannan ranan. Rabon da naga kayi driving da kanka idan zan iya tunawa tun 5th birthday na a Kaduna."
Murmushi ya saki mai sauti, hankalinsa na kan titi yace
"Ai dole ne in ji da wannan ranan Ummina, kasancewar ta rana ta farko da burin da na ci alwashi a kanki ya fara cika."
Juyowa yayi ya kalleta, sannan ya cigaba
"Tun ranar da kika zo duniya nake rok'on Allah ya gwada mun ranar da zan ganki kin fito cikin black & white uniform d'in nan, dan na tabbata, za ayi barrister mai adalci, wacce zata taimaki k'asarta, tare da al'ummar da aka zalinta."
Dariya tayi da ta taimaka wurin lobawar gefen kumatunta.
"In sha Allah Baffa na."
Sauran tafiyar tasu ta kasance cikin labarai na nishadi, har suka iso gaban tsangayar horarwa ta lauyoyi dake jami'ar Umaru Musa Yaradua Katsina. Ya juyo da fara'a yana kallon tilon 'yartasa cike da so da kauna
"Yadda na kawo ki makaranta a ranar ki ta farko, ina rok'on Allah ya nuna mun ranar da kika kammala karatun nan lafiya."
Murmushi mai karko Jay tayi,
"Amin Ya Allah Baffana."
"Ga mukullinki nan, ki kula da hanya Mamana. Ina kuma kara tunatar da ke alkawarinmu. Ki rike daraja da mutuncin gidanku."
Cikin tsananin farin ciki da jin dad'i ta ansa, tana mai sunkuyawa ta d'an kama kafad'unsa,
"Allah ya k'ara arzik'i da wadata Baffana. Na gode."
"Allah yi miki albarka Baby, ki maida hankali banda wasa kina ji na?"
"In sha Allah"
Haka rayuwartasu take cike da ababen so da kauna, tamkar ba 'ya da uba ba. Yana tsananin sonta daidai da yadda yake son kanshi. A kullu yaumun, yana son yayi abinda zai faranta zuciyar tilon 'yar tasa, har ya kai ga ta bayyana farin cikin ta a fili ya gani.
Daga haka suka yi sallama ya fito, tare da shigewa bayan motarsa da direba ke biye da su dan karasawa wurin aikinsa.
****
Kwanakinshi biyu kenan a garin na Katsina, sai dai ya kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali kasancewar ya rasa gano wurin baje kolin sana'arsa.
Aiki yake tukuru, amma hankalinsa gaba d'aya ya raja'a a tunanin inda zai ci karo da babbar madaddalarsu ta 'yan caca.
Tunawa yayi da Kano ne, har sai ya za6i inda zai je, amma anan neman wurin zuwan ma yake bai samu ba.
A gurguje ya fito bayan an tashi aiki, dak'yar da taimakon wani mai irin 'yan k'ananan shagunan nan na siyar da sigari ya kwatanta masa wani wuri.
Abinda ya 6ata ran Kazaure bayan isarshi wurin shine ganin yadda suka karya daraja da mutuncin sana'ar da ya daukaka fiye da aikinsa.
Tsaki ya ja mai sauti, wanda yayi sanadin jan hankulan mutane da dama, dan shi a ganinshi da yayi irin wannan cacar, ya gwammace yayi yawon bara, ko da kuwa zai kwana babu abinci
Ya saba da babbar harka, caca da manyan 'yan caca masu kud'i wanda basa jin k'yashin su d'ora nera miliyan daya a take a lokaci guda.
Takaici ya ishe shi yadda mutanen ke ihu, tunawar da yayi hatta motar da yake hawa a caca ya ciwo ta wurin wani bayerabe mutumen Lagos, amma su nan sunzo sun cika mishi kunnuwan kan 'yan kud'ad'en da gaba d'aya basu haura nera dubu goma ba.
Mik'ewa yayi zai fita, cikin sa'a ya ci karo da wani matashi wanda ya sha yayi tatil, cikin dabara ya tambayeshi inda zai gano wani babban hotel a garin, a haka cikin mayensa ya kwatanta mishi, ba dan ya gane ba ya fito, sai dai sunan wurin kawai da ya rik'e, yasan ba zai sha wuya wurin ganowa ba.
Da taimakon wani mai acaba ya iso kofar katafaren otel din da ya amsa sunanshi. Ko da shigar shi wurin take wata natsuwa ta saukan masa, dad'i yake ji har a cikin ranshi, domin kuwa a duniya idan akwai abinda ya fi k'auna, bai wuce yaga ana loda kud'i akan teburin kada caca ba, a kuma samu wani zakaran da ke lashe su cikin d'an k'aramin lokaci.
Wannan ne karo na farko da yayi murmushi mai sauti, tun bayan zuwan shi garin, ganin yadda ake facaka da kud'i da muhimman abubuwa akan k'ayataccen teburin kad'a cacar.
****
Soooooooo.... This is Sadam Kazaure already😄😄😄😄😄
What made the spoilt brat fall for him?
Stay tuned to find out.🤣🤣🤣🤣
Biko, ga wani tauraro nan daga gefen hagu, shi kawai za a danna. Sai ra'ayoyinku da zaku shigar ta akwatin kwament.
Na gode.
Lubbatu😍👌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro