BABI NA BAKWAI
Da sauri-sauri zuciyarta ke bugawa, saboda tsabar masifar da ta juyo da shi. Ji tayi tamkar ya watsa mata garwashi lokacin da maganganunsa suka yi dirar mikiya cikin dodon kunnenta.
Ga mamakinta kunnenshi dad'e yake da earpiece, ta san duk maganar da zata yi a banza, dan kuwa ba ji zai yi ba. Lallai yayi sa'a amma da sai ta yarfa mishi bak'ak'en da zasu hana shi bacci a daren yau. Abinda ta rink'a nanatawa a k'asar zuciyarta kenan.
Kamar yadda ta kasa motsa kafafunta, haka ta gagara kyafta idanuwanta a kan shi, ji take duniyar na juyawa mata, dan kuwa tunda take, bata taba cin karo da wulakanci irin wannan ba.
Har a yanzu hankalinsa na kan aikin dake gabansa, ba wai dan bai damu da tsayuwar tata ba, sai dan kawai ya gwada mata bata da wani muhimmancin da zai maida kansa gareta.
Bata iya furta ko kalma daya ba, haka ja kafarta da niyyar barin wurin, kai duban da zata yi gare shi, idanunta suka kulle a tsakiyar nashi.
Murmushin mugunta ya jefe mata, yana mai kanne idonsa, hakan ya jaza mata sabuwar kasala, da saurin saukar da nata idon, ta fara tafiya da sauri, da sauri.
Ya za ayi ta jure irin kallon da yake mata?
A karo guda ya kawar da kanshi, sai dai zuciyarsa dake ta faman sak'a tana warwarewa.
***
Ita kanta ta san bata da hakuri, babu kuma wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya. Babban tashin hankalinta a yanzu, shine yadda ta gagara nuna ko da yatsa ne ga mutumin da ya jefe ta da kalaman da tunda ta mallaki hankalinta, bata ci karo da irinsu ba. Mutumen da ko sunanshi bata sani ba, mutumen da ke kokarin canja mata halayya cikin dan kankanin lokaci.
Har a yanzu da ta shigo gida, bata daina mamakin yadda bakinta ya kulle kanshi ba, bata daina tunanin dalilin da ya dakatar da kwakwalwarta daga nazarin abinda zata gayawa customer care ba, domin kuwa sunan da take ganin ya fi dacewa da shi kenan.
A samar gado ta watsar da kayan hannunta, ta cire mayafin sannan ta zarce kichin, saboda irin yunwar da ke nuk'urk'usarta.
Sai da ta ci ta k'oshi, sannan ta dawo d'aki, bata damu da zuwa ga mahaifiyarta ba, domin ta san dole ta zo nemanta.
Kayan jikinta ta cire tare da d'aura tawul, kamar zata shiga wanka, sai kuma ta koma ta kwanta, ta fara bincika kayan tana neman wayarta.
Kamshin turaren da bata san daga inda yake bugowa bane yake ci gaba da dukan hancinta, hannunta ta kai ga farin hankacif din dake nade da ATM card dinta, ga mamakinta rubutu ta hanga jiki, wanda hakan ya sanya ta warwarewa tana fara dubawa. Lambobin waya ne a jere guda ukku, daga kasa ya kara da
You must call me Jameela, Jay, whatever. I'm just waiting for your call.
Sadam Kazaure
Maimakon ta ji haushi, sai murmushin takaici da ta saki, wanda a zahiri tana mamakin karfin hali irin nashi.
Anya ya san wacece ita kuwa? Ya san maza nawa suke bibiyarta a cikin garin Katsina, ba wai cikin Zenith bank ba kad'ai, tana kuma gara musu kawuna da bango?
Da alama bak'on fuska ne, dan tunda take bata ta6a ganin mai kama da shi ba.
Murmushi ta yi, sai a yanzu take jin, tabbas ita ce zata kawo k'arshen iskanci irin nashi.
A zahiri ta furta
"Sure, I'll call you, sai dai kiran ba zai zama abin alfahari a gare ka ba Kazaure."
Da takaicin shi ta mik'e ta shige wanka, bayan ta loda dukkan lambobin nasa a kan wayarta.
《》《》《》《》
Tun daga lokacin da ta fita yake sakin murmushi wanda ya rasa gane ko na meye, ya tabbatar ma kansa ba soyayya bace, sai dai ya yardar ma kanshi cewar akwai wasu abubuwa da ya gani a tattare da ita, wad'anda zasu taimaka wurin kawar da k'ishin da ke mak'oshin shi. Alal hak'ik'a kuma zai saukar da girma da rawar kan da ya ga tana fama da shi.
"She must call me"
Ya fad'a a bayyane, yana mai kai duba ga wayarsa, sai dai babu alamar kiran da yake shigowa.
Har aka tashi aiki, zuciyarsa fal da tunaninta, haka kuma lokaci zuwa lokaci ya kan kai duba ga wayarsa ko za ayi arashi yaga kiran bak'uwar lamba.
A yau, sa'a yake ji a tattare da shi, dan haka bayan da yayi wanka ya shirya, ya fito zuwa Hotel din da zai taimaka ma yawaitar nishadinshi.
A restaurant d'in dake cikin hotel d'in ya fara tsayawa ya cika tumbinsa tass, sannan ya mik'e.
Yana k'ok'arin fita kira ya shigo masa, la66ansa d'auke da wani makirin murmushi, ya d'aga wayar tare da fad'in
"This is Sadam Kazaure, how may I help you?"
Jay dake kwance tana kallon fankar dake manne da rufin d'akinta, ta lumshe ido tare da k'ank'ame d'an k'aramin filon dake hannunta.
Bata san dalili ba, haka kawai muryarsa tai mata dad'in da baza ta iya misaltawa ba.
Daga bisani ta yi gyaran murya tace
"I know, so you don't have to introduce yourself. Ok?"
"But who are you?"
Ya tambaya ta d'ayan 6angaren lokacin da yake fitowa cikin restaurant d'in.
"That's none of ur business, ina son sanar da kai cewar ka dinga sanin maganar da ya kamata ka fad'a ma customers d'inka, if not wata zata iya yin sanadiyyar aikinka.
Nd by the way, ka gode ma Allah da har na iya d'aga baki na ce maka thank you, domin ba kowa ke samun hakan daga gare ni ba."
Wannan karon murmushin mai sauti ya saki, ita kanta sai da ta jishi, sannan yace
That means I'm special, tunda kin yi mun abinda ba kowa ke samu daga gare ki ba."
Ya bud'a murfin motarsa ya zauna, k'afarsa d'aya a ciki, d'aya kuma a waje sannan ya cigaba.
"Jay right?"
Bata ansa shi ba, shima bai jira hakan ba yace
"just admit it, kinga d'an handsome kina so, kin zo kina wani sneaking. Well, ki gode Allah, Kazaure na jin zai iya taimaka miki 'yan mata."
Bazan taba fahimtar abinda kuke ji dangane da labarin ba matsawar baku ajje ra'ayoyinku ba. It feels like I'm doing this for nothing. So, If that's the case, I'll put the story on hold, till i finish the new one i started.
Y'all shud check HAWAYEN ZUCIYA out.
Regards, Lubbatu.
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro