BABI NA ASHIRIN DA UKKU
Rayuwa a gidan Sadam Baffa Kazaure rayuwa ce mai cike da tsantsan tashin hankali, rashin wadata, rashin gata, da rashin daraja a matsayin Jameela Kasad na mace mai isa da iko, wacce ta tashi cikin gata, soyayya, da tattali na iyayenta.
A haka zaman na su ya cigaba da wanzuwa cikin tsananin matsi da takura tamkar ba masoyan da suka yi k'aura domin cimma burin soyayyarsu ba.
Sun kasance tamkar wasu gagaruman mak'iyan da aka yi ma auren dole, aka tura su wata duniya ta daban.
Duk wasu kalaman yaudara da Sadam yayi amfani da su wurin saye zuciyar Jay, yanzu sun tashi a tutar babu, sai ya zamana tamkar babu wata kalmar so da ta taba gittawa tsakanin masoyan guda biyu. Zama dai kawai suke yi da juna na dole, na babu yadda wani zaiyi da dan uwansa, yayin da ta bangare Jay, tana zaune da Sadam saboda rashin inda zata dosa, dan ta san ko tasha giyar wake, bata isa ta tunkari iyayenta a halin da take ciki ba.
Har zuwa lokacin da aka yaye Rukayya Sadam bai daina k'untata ma rayuwar Jay da 'yartasa ba, har ya kai ga yarinyar ta fara gane irin karan tsanar da ya dauka ya dora musu, ta yadda bai taba damuwa da ita ko abinda ya shafe ta ba, haka zalika idan ta tunkari inda yake ba zai duba k'ank'antarta ba, zai daka mata tsawar da zata razana ta, ya zara mata manyan idanunsa dake daburta hankalinta, wani lokacin yasa k'afa ya dungure ta tamkar bai taba sanin inda yarinyar ta fito ba.
Wannan ne yasa take masifar tsoronsa, matsawar yana wuri to bata iya motsi mai k'arfi har sai ta tabbatar da ya bar wurin.
**Jan 30th, 2016
K'arfe goma sha biyu dai-dai na dare ya fito harabar Grand Pinnacle Hotel, hannuwan rigarsa a nannade zuwa gwiwar hannun, k'afarsa babu ko takalmi, tafiya kawai yake tamkar mahaukacin da ya fara hauka a ranar.
Kai tsaye wurin da yayi parking motarsa ya dumfara, zuciyarsa a hargitse kasancewar yadda wani hazik'in dan caca yayi mishi warwas, ya tatike duk wani abu da ya shiga wurin da shi tun daga kan kudadensa, agogon da ke hannunsa, har zuwa takalman da ke sanye a k'afarsa bai bar masa.
Motar ya shiga, a sikwane ya fita a hotel din cikin kunar zuciya ya dinga rafsa gudu tamkar wanda zai tashi sama.
Cikin sa'a babu yawaitar abun hawa a titi nan, kasancewar dare ya riga yi, duk wani mutumen arzik'i yana gaban iyalinsa a dai-dai wannan lokaci.
Zuciyarsa a dagule ya kawo kofar gidan, ya fita ya bude gate ya shige da motarsa yayi parking, ya fito ya tunkari k'ofar shiga palon fuskarsa a murtuke kamar kowacce rana, sai dai bakin cikin da yake ji a yau ya fi na sauran kwanakin.
Ga mamakinsa k'ofar a bude ya sameta, sabanin kullun da sai yayi ta faman bugawa kafin yake samu Jay ta bude mishi.
Hannun k'ofar ya murd'a ya shiga, ya maida k'ofar ya rufe, ya juyo da zumar k'arasawa ciki, sai dai ya kasa d'auke idanunsa da suka yi kicibis da kyakkyawar surarta dake kwance tana bacci saman doguwar kujera, Rukayya na a k'asar carpet din dake shimfid'e tsakiyar palon.
Zafin da ake yi a garin ne ya sanya ta cire rigarta, ta tsaya daga ita sai half vest, da wani dogon budadden purple skirt, wanda shima rabinshi ya tattare, hakan ya kara bayyanar da kyawawan surorinta muraran, a waje ana kallo.
Idanuwansa da ya shigo dasu kunshe da masifa ne suka fara washewa, ya gagara sauke dubansa a kanta, yana yi mata wani mayen kallon da ba zai iya tuna lokacin da yayi mata irin shi ba domin kuwa tunda ya gane tana d'auke da cikin Rukayya bai k'ara jin yana sha'awar kusantarta ba sai fa a wannan lokacin da yake ganin tamkar an k'ara k'awata surar jikin nata ne.
Kanshi ya girgiza ya shafe idonsa, a zuciyarsa yana ayyana barasar da ke kansa ce take dibarsa, har ma take k'awata masa surorinnata, dan kuwa a ganinshi Jay bata da sauran wani abu da zai gani har ma yayi sha'awa a wannan lokacin.
Da wannan tunanin ya juya a hankali ya fara tafiya zuwa d'akinsa, sai dai kuma mayun idanunsa sun gagara kauda kansu akan k'irjinta da ya cika sosai tamkar bata taba shayarwa ba.
Dawowa yayi cikin sand'a kamar wani barawo ya isa gaban kujerar yana cigaba da kallonta, baccinta take sosai hakan ya bashi damar duk'awa gabanta passionately ya fara shafa gefen fuskarta.
A hankali ta fara bud'e ido, a k'arshe ta sauke su a kan mutumen da ke tsugunne gabanta, wanda yayi nisa sosai a abinda yasa gaba.
Da sauri ta mike a firgice tana tambayar
"Me he haka kuma?"
Bai bata ansa ba ya mik'e cikin borin kunya ya tura hannuwansa cikin aljihu ya fara tafiya, daga bisani ya juyo yana kallonta
"Ki same ni a dakina."
Bata ce komai ba, ta mik'e tana k'ok'arin d'auke Rukayya, sai a lokacin ta lura da yanayin da jikinta ke ciki.
Da sauri ta zira rigar ta, ta dauketa ta kaita d'aki, sannan ta fito ta doshi d'akin Sadam.
"Shigo mana."
"Yau kuma? Ka manta ka bige mun warning akan shigowa d'akinka ne?"
"Kinga, ba dogon zance nake so ba. Nace ki shigo."
Bata k'ara cewa komai ba ta tura kanta ciki, ta samu gefe ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Gabanta ya iso da (contraceptive pilss) da ya ballo a hannunsa ya mik'a mata, ya d'auko wata gorar ruwa dake ajje a gefe, ya mik'a mata.
"Sha kizo nan ki same ni."
Ya koma bakin gado ya harde k'afafunsa.
"Maganin me haka?"
"Ki sha nace. Bana son dogon bayani."
"Ba zan sha ba sai ka fad'i ko na meye."
"Na planning ne, dan bazan kuma yin sakacin da nayi a baya ba."
Tsayuwarta ta gyara, mamakin dake zuciyarta bayyane sosai akan fuskarta, 'wato dama maganin da ya rink'a bata kenan?' Kawar da tunanin tayi duk kuwa da kasancewarta cikin alhini, ta had'e fuska tana dubansa.
"To kai me ruwanka da bani maganin planning kuma? Ko har ka manta da ka daina hada gado da me ciki ne?"
"Hak'k'i na nake buk'ata, so ki sha maganin nan tun muna cikin laluma, ki zo nan ki same ni."
'Lallai wannan shi ake kira da SABON SALON D'A NAMIJI.'
Abinda ta fada a kasar zuciyarta kenan, a fili kuma ta kalle shi tace
"Amma baka tsoron Allahn ka Sadam. Kai yanzu banda rashin kunya har kana da bakin da zaka daga kace kana neman hak'k"inka a wuri na? Kai yaushe rabon da ka sauke nawa hak'k'in da ya rataya a wuyanka?"
Labbansa na k'asa ya cije, ya rasa abinda zai fada, kawai ya mik'e a fusace ya isa gabanta ya warce maganin ya fara k'ok'arin tura shi a bakinta.
A karo guda itama ta fara kiciniyar k'watar kanta, sai dai k'arfinsu ba daya ba, tuni ya kai ta k'asa, sannan ya fara kiciniyar matse mata baki.
Ganin yana shirin illatata yasa ta bude bakin, ya tura maganin, tare da warto gorar ruwan da ta fadi gefe ya bude ya tsiyaya mata, bai jira komai ba ya fara cire kayan jikinsa.
Hannayenta ta hade, ta mak'alkale zuwa k'irjinta, zuwa yanzu, idanuwanta sun fara fara kawo ruwa.
Bai bi ta kanta ba ya fara k'ok'arin cire mata kaya itama, sai dai tasa hannu ta rik'e skirt dinta gam-gam, hawaye na kwarara a idanunta.
"Ki rufa ma kanki asiri ki bar ni nayi abinda nayi niyya. Idan ba haka ba ke zaki wahala a banza a wofi, wallahi, domin kukan ki ba zai hana ni aiwatar da abinda nayi niyya ba."
"Me zai hana ka kashe ni kawai in huta da wannan azabar da kake mun Sadam. Na gaji. Na gaji da halin k'asak'anci, da bak'incikin da kake cusa ma zuciyata."
Tayi maganar tana dukan gaban k'irjinsa da ya matso daf da ita yana k'ok'arin had'a jikinsu.
Bai bi ta kan maganar ta ba, haka kuma bai damu da yadda take bugunshi ba, yasa k'arfi ya farka rigar dake jikinta, kasancewar hankalinsa gaba d'aya baya tare da shi ko alama.
Kuka ta saka mai k'arfi, tare da toshe idanunta da duk hannuwanta biyu, hakan ya ba shi damar aiwatar da abinda yayi niyya cike da mugunta da rashin tausayi, sannan ya mik'e ya shige toilet ya barta tana cigaba da zubar da wasu zafafan hawaye.
Har ya gama abinda yake ya fito, amma tana wurin a kwance, sai da ya ji tausayinta kadan ya tsirga zuciyarsa a daidai lokacin, hakan yasa ya taka zuwa gabanta yasa hannu da niyyar ya tayar da ita, amma ta buge hannun ta mik'e a bala'ince ta tofa masa yawun da ya cika mata baki.
"Mugu azzalimi. Bazan taba yafe maka ba Sadam. Ka ci amana ta. Allah sai ya saka mun wallahi. Da izinin Allah zaka ga sakamakon cutar da ni da kake yi."
Towel din jikinsa yasa ya share yawun da ta tofa masa ya mik'e zuciyarsa na wani irin tafasa.
Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya dawo da baya ya d'auke ta da wani wawan marin da ya sa ta hango taurarin da suke yawo a sararin samaniya.
"Be careful, you bloody fool."
Yasa hannu ya warce ta ya fitar waje, sannan ya dawo ya mayar da k'ofar ya rufe, ya zauna bakin gado yana mayar da numfashi.
Mik'ewa tayi dafe da kuncinta ta wuce d'aki tana zubar da hawaye ta gyara jikinta, ta fito ta canja riga ta kwanta a gefen Rukayya ta k'ank'ame ta tana wani irin kuka a hankali wanda ke taba zuciyar dukkan wani mai saurarenta.
Da tunanin abinda ya wakana Sadam ya kwanta, hakan yasa washe gari tun kafin su tashi ya fita ya bar garin ma kwata-kwata, duk kuwa da ya san basu da isasshen abincin da zai wadacesu su ci a iya kwanaki biyar din da zai yi na tafiyarsa.
Haka suka cigaba da zama a wahalce, cikin tsananin matsi har zuwa ranar da ya dawo.
CIGABAN LABARI
**Sadam
A waje yayi parking ya fita ya shige cikin gidan da niyyar ya kai masu abincin da ya siyo, ya fito ya kama gabansa.
Mamaki ne sosai shimfiɗe a kan fuskarsa, ta yadda ya hango k'ofar palon a wangame. Bai yi k'asa a gwiwa ba ya cigaba da tunkarar wurin, har ya isa bakin k'ofar yasa hannu yana shafa wurin da aka bige yana tunanin wanda yayi wannan gagarumin aikin.
Cikin ɗan lokaci zuciyarsa ta motsa, wani irin tururin tashin hankali ya fara tashi, ya mike, ya wuce ciki ya fara duba kaf ɗakuna da kitchen, har ma da toilets ɗin gidan, amma wayam, babu kowa sai k'aran fans ɗin dake wulwulawa a ɗakuna da palon gidan.
A hargitse ya fito, k'irjinsa sai dukan tara-tara ya ke yi, hankalinsa gaba ɗaya baya jikinsa, ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana tunanin inda Jay ta dosa a cikin halin da ya barta. Ta wani ɓangaren kuma yana tunanin wanda ya fitar da ita, kasancewar ya san ko mak'wabtansu babu wanda suke mutunci da shi, babu wanda ya taɓa shiga gidansu, kamar yadda suma basu taɓa shiga gidan kowa ba.
"Faisal Goni."
Abinda ya faɗa a bayyane kenan, domin kuwa kaf mutanen da yake hulɗa da su cikin garin Maiduguri babu wanda ya san gidansa bayan Faisal Goni.
"Zai gane ba shi da wayo. Sai na yi mishi rashin mutuncin da sai ya ji dama bai taɓa sani na ba a rayuwa."
A haukace ya fito gidan, bai tsaya kullewa ba ya shiga ya figi motar ya ɗauki hanyar gidan Mal. Goni.
Tun a hanya ya fara kiran wayar Faisal, da sallama ya ɗaga yana faɗin
"Kazaure sarkin kirki. Ashe har yanzu kana ajiyar number ta."
"Sosai kuwa, saboda irin wannan ranar. Ina matar mutane?"
"Matar wa kenan?"
"Kada ka raina mun hankali Malam. Ina matata?"
Dariya Faisal yayi,
"I don't know what you're talking about. I'm sorry."
"Zaka sani idan na zo na same ka. Wallahi sai kayi da-na-sanin sani na a rayuwarka. In banda rainin hankali, ya zaka zo har gidana ka ɓalla mun k'ofa ka fitar mun da mata, kuma in kira ka kana cewa baka ma san zancen ba. Zaka sani idan na faffasa maka baki."
"Hey. Take it easy mana. Ni tunda na sanka ma ban taɓa taka hanyar gidanka ba. And ka faɗa mun idan na ɗauki matarka ina zan kaita? Ni me ma yayi haɗi na da wata matarka? Kawai dai kana k'untata ma yarinya ta gudu ta kama gabanta, kai kuma ka zo nan kana tada jijiyoyin wuya. Shawarata gare ka tun dare bai yi maka ba ka san inda zaka nemi matarka, cuz ni rabona da Maiduguri ma yau wata guda kenan. Ina Lagos wurin aikina."
Ya kashe wayar, ya bar Sadam yana banbami, bakinsa har kumfa yake saboda masifa, haka kuma bai daina tunkarar gidan Mal. Gonin ba.
A k'ofar gidan yayi parking ya fito, ya jingine jikin mota, kasancewar sallah da ya ga ana yi a masallacin da ke jikin gidan, wanda ya tabbatar Malam ne limamin da ke jan al'ummar wurin.
Sai da suka gama, a kan idonsa kowa ya gama fitowa amma babu mai kama da Faisal a ciki, a haka Malam ya fito shima, yayi saurin shan gabansa, ya bashi hannu suka gaisa, sannan suka shige ciki.
A palo suka zauna, shiru na ɗan lokaci ya ratsa tsakaninsu har sai da Malam yayi gyaran murya, ya na mai duban Sadam, fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Sadam lafiya kuwa? Yau kaine a gidan namu."
Kamar yana jira, ya ɗago da manya-manyan idanunsa da suka yi jajir yana kallon Malam.
"Babu lafiya Malam, Faisal ya je har gida ya ɓalle mun k'ofa ya fitar da Jameela."
"Faisal? Wane Faisal ɗin ma wai tukunna?"
"Faisal nawa ka sani ne?"
Yayi maganar yana wani juya kai, irin na marassa ɗa'a.
"In dai Faisal nawa ne yaushe ma ya zo garin? Kuma me ye alak'arshi da matarka?"
"Ina zan sani ni? Ka dai mishi magana kawai ya fito mun da mata tun muna mu biyu."
"Dakata da Allah, abin duk bai kai na haka ba. Barin kira shi muji."
Ya fitar da wayarsa ya lalubo number Faisal ya danna kira, bugu biyu zuwa ukku ya ɗaga tare da sallama.
Hands free Malam ya saka, ya ajje wayar a k'asa ta yadda kowa zai iya jin maganar da za su yi.
"Me yayi haɗinka da matar Sadam Faisal? Yaushe ma ka zo garin ban sani ba?"
"Ya Salam. Ba dai wurin ka mutumin nan ya zo ba? Ya kira ni fa, na faɗa mishi ni rabona ma da Maiduguri yau wata ɗaya cif-cif, amma dan ya raina hankalin mutane shine zai zo maka. To wai ni me ye haɗina da wata matarshi can?"
"Ka saurare ni da kyau. Kana jina?"
"Ina ji."
"Idan kana da masaniyar inda matarshi take ka sanar da ni tun muna mu biyu."
"Malam wai baka yarda da ni bane? Wallahi ban sani ba. Mutumen nan bashi da kirki wallahi, watak'ila takurar da yake yi ma yarinyar ne yayi mata yawa ta gudu, dan naji ance bashi da hankali kuma mashayin giya ne."
A take idanun Sadam suka k'ara juyewa, dan masifa har wani yellow-yellow yake yi, a hargitse ya sa hannu ya warci wayar kamar Faisal na kallonsa ya fara nuna wayar.
"Zaka gane hauka na idan muka haɗu da kai, wallahi sai na illata ka, sai na zubar maka da hak'ora idan baka fito mun da matata ba. Babu wanda ya san gidana a duk faɗin garin nan bayan kai."
Ya wurgar da wayar, ya mik'e a fusace ya fita.
"Sadam. Sadam. Sadam.."
Mal. Goni ya dinga kiransa, amma yayi kunnen uwar shegu da shi, ya fita ya buga mishi k'ofa, yayin da shi kuma ya bi bayansa da kallo yana girgiza kai, a zuciyarsa yana addu'ar 'Allah ya kyauta.'
**Jay.
Har suka bar unguwar bata daina zubar da hawaye ba, sai da taga mutumen yayi parking gaban wani restaurant, bai ce mata komai ba ya fita ya anso masu abinci, sannan ya dawo ya shiga ya tada motar suka cigaba da tafiya.
"Ka sauke ni a nan ma ya isa, nagode da taimakonka."
Bai ko kalle ta ba, balle ta sa ran samun ansarshi, domin kuwa zuciyarsa ta gama karyewa a irin yanayin da ya same ta a ciki, haka kawai ya ji yana buk'atar taimaka mata, idan da hali ma yana son sanin ainahin labarin rayuwarta.
Gidanshi da ke Old GRA suka dosa, gida ne tsararre ginin zamani, ya shiga ya samu wuri yayi parking, a dai-dai lokacin wani matashin da bai wuce shekaru ashirin da biyar ba ya fito hannunsa rik'e da na wani yaro wanda a k'alla zaiyi shekara ukku zuwa hudu.
Ganin sunyi parking yasa yaron ya k'wace hannunsa, ya ruga da gudu ya isa inda suke, a lokacin SS ya buɗe motar ya fito, tare da ɗaga yaron sama yana dariya.
Dariya yake yi sosai shima, a haka ya zagaya ya buɗe ma Jay k'ofa, ya ɗauko ledar abincin da ya siyo yayi gaba zuwa cikin gidan.
Duk da bai ce mata komai ba, buɗe k'ofar da yayi ya tabbatar mata yana nufin ta fito ta shigo, hakan yasa ta ziro k'afafunta a hankali ta fito Rukayya saɓe a kafadarta, ta tunkari k'ofar da ta ga sun shiga.
Babu kowa a palon, sai tv da ke ta faman aiki, sai wani sanyin AC mai haɗe da k'anshi mai daɗi, da ya daki hancinta a lokaci guda.
Gefe ta zauna, sannan ta kwantar da Rukayya wacce har yanzu baccinta take yi, a haka ya fito yana kiran Farouq.
Wannan matashin ne ya fito daga wani ɗaki ya iso gabansa yana faɗin
"Sannu da zuwa Yaya."
"Yawwa, taimaka mun da plates da cups da abin sha da Allah."
"Okay."
Ya juya zuwa kitchen, shi kuma ya isa wurin da ya ajje ledar abincin da ya shigo da ita, ya ɗauko ya kawo gaban Jay, a lokacin yaron ya fito daga ɗakin da SS ya fito ya rugo ya haye bayansa.
"Haba Jafar. Yanzu fa ka girma ya kamata ka daina hawa na haka nan. Kalla nan, kaga ga sister nan na kawo maka ku dinga wasa, amma banda cin zali kana ji na?"
Dariya Jafar yayi, lokacin da ya sake shi ya ruga wurin Rukayya yana taɓa fuskarta, ya kalle shi yace
"Daddy da gaske zata zauna a wuri na? Wannan kuma ai dai Mammy ce ko?"
"Sosai kuwa. A nan zata zauna ku rink'a zuwa school din su Uncle Farouq, kuna yin wasa tare."
Hannunta ya fara jijjigawa yana dariya, hakan yasa ta tashi a baccin, yadda yake mata wasa ita ma sai ta washe ta dinga k'yalk'yala dariya, duk kuwa da cewar a rayuwarta bata san kowa ba bayan mahaifiyarta.
A haka Farouq ya iso da tray ɗauke da plates, spoons, da cups ya ajje a k'asa ya koma ya kawo masu abin sha, sannan SS ya kalle ta,
"Sauko ki sa mata abinci."
Bata yi gardama ba ta sauka ta sa masu abincin, a tare suka rink'a ci ita da Rukayya da Jafar wanda suke ta wasansu tamkar sun daɗe da sanin juna.
Abincin ya ɗauka shima ya ɗauki plate da spoon ya juye ya koma kan table yana ci, sai dai hankalinsa gaba ɗaya yana kan su, tausayin matar da bai san ko wacece ba ya dabaibaiye dukkan jijiyoyin jikinsa.
Bayan sun gama cin abincin ne ta tashi ta tattara wurin, ta haɗa plates ɗin wuri ɗaya, tana shirin ɗaukewa ta tsinkayi maganarsa.
"Ki bar shi Farouq zai ɗauke. Jafar kaje ka nuna ma Mammy ɗakinta tayi wanka ta huta ka ji."
Ya k'arasa maganar yana kallon ɗan kyakkyawan yaron da ke gabansa.
Da sauri ya mik'e ya kama hannunta ya fara ja, hakan yasa ta saki murmushi mai haɗe da wasu zafafan hawaye, ta kama hannun Rukayya suka doshi hanyar da Jafar yayi.
Ga mamakinta ɗaki ne lafiya lau na mace, ta yadda taga takalma da jakunkunan mata a jere, tsab-tsab.
A bakin gado ta zauna tana k'are ma ɗakin kallo, a zuciyarta kam ta rasa tantance yanayin da take ciki, shin farincikin rabuwa da Sadam take ko ko bak'inciki? Ta wani ɓangaren kuma tana tunanin inda zata dosa daga nan.
A k'arshe dai mik'ewa tayi ta shiga toilet tayi wanka, ta yi ma Rukayya, amma yadda Jafar yasa rigima shima sai anyi mishi, dole ta fara yi musu, sannan tayi ta fito
Cikin ɗan k'ank'anin lokaci ta ji yaron ya shiga ranta, ganin yadda tunda suka zo gidan ya kasa matsawa ko ina yana mak'ale da ita yana kiranta Mammy, yana wasa da Rukayya. Hakan yasa ta fara tunanin ko ina ta shi Mammyn ta nufa?
Sai da ta shirya yaran, sannan tayi sallolin da ke kanta, gamawarta kenan, ta mik'e tana ninke sallayar SS yayi sallama a bakin k'ofar ɗakin.
Bayan ta ansa shi, ta k'arasa ninke sallayar, ta fita ta same shi tsaye gefen k'ofar hannunwansa cikin aljihun farar jallabiyar dake jikinshi.
"Idan babu damuwa ina son muyi magana da ke."
"Babu komai."
Ta faɗa lokacin da ta fito a ɗakin, yayi gaba ta rufa masa baya suka koma palon.
Shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara, a k'arshe ya kai duba gareta, a nan ya fahimci ba k'aramin kyau Allah yayi mata ba, sai dai da alama wahala ce ta dafar da ita.
"Astagfirillah."
Ya faɗa a k'asar zuciyarsa, kasancewar yau ce rana ta farko da ya taba yi ma wata mace irin wannan kallon tun bayan rasuwar matarsa, abar kaunarsa.
"Baiwar Allah, menene sunanki?"
"Jameela."
Tayi maganar muryarta a sanyaye.
Shiru yayi sannan ya tsaida idonsa akan tv, ya cigaba da magana.
"Naje neman gidan wani colleague ɗina ne a unguwarku, kwatsam sai na ci karo da case ɗinki. Idan bazan takura ki ba, zan so inji ainahin labarinki, da dalilin da yasa kika samu kanki kulle a cikin gida babu mataimaki."
Tun bai kai k'arshe ba hawaye suka fara ambaliya akan kumatunta, kuka sosai ta fara rerawa hadda sheshsheka, yayin da ta ke girgiza kanta, hakan ya k'ara haifar da tausayinta da son taimaka mata a zuciyarsa.
"Babu komai a labarina face tur ga masu ɗabi'a da halaye irin nawa. Babu komai a labarina face da-na-sani, da takaici a wurin iyayen da suka haifi 'ya mai irin halayena. Malam kayi hakuri, amma labarina baya tattare da komai illa tashin hankali, nadama da kuma da-na-sani wanda watak'ila har k'arshen rayuwata bazan daina yinsu ba."
Ta k'ara fashewa da wani irin kukan da ya rink'a taɓa zuciyar SS Tafseer, ya kuma k'ara masa kwaɗayin son sanin labarin nata domin yana ji a jikinshi shi ne zai zama silar warwarewar matsalolinta.
"Kada ki damu Jameela. Kada kuma kisa wannan a ranki, ki daure ki sanar da ni, ta yadda zan taimaka miki, in fitar dake daga halin k'uncin da zuciyarki ke ciki."
"Kayi hak'uri bawan Allah, amma bana tunanin akwai wani taimako da zaka mun bayan wanda ka riga ka mun. Nagode da wannan, amma ba zan iya sanar da kai babban kuskuren da na tafka a rayuwata ba."
"No please. Kada muyi haka da ke mana. Naga neman taimako bayyane a cikin idanunki Jameela, please, I beg of you to lemme help you. Kiyi hak'uri ki sanar da ni mana."
Girgiza kai ta cigaba da yi, a k'arshe ta mik'e da sauri ta kama hanyar ɗakin data fito, a haka shima yayi saurin mik'ewa ya sha gabanta.
Nd let's the journey continue 💃💃💃💃
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro