Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ASHIRIN DA TARA

Sai da suka kwashi dogon lokaci suna abu ɗaya, sannan suka sassauta, hakan ya ba SS damar cigaba da bayaninsa.

  "Tun daga ranar na ɗauki soyayyar duniya na ɗora a kan k'anina abin alfaharina Omar Farouq, kasancewar shi kaɗai ne ɗan uwan da ya rage mun, shine gata na, nine gatanshi, sai kuma mahaifiyarmu.
  A washe garin ranar da na dawo na yi shirina na fita, ban tsaya ko ina ba sai company da Abbana ya ke aiki, cikin ikon Allah na samu Alhaji yana nan, haka na zauna ina jira, har lokacin da mutane suka tsagaita sannan na shiga.
  Zaune yake a tangamemen office ɗin, kan shi a k'asa yana ta 'yan rubuce-rubuce na shigo da sallama k'unshe a bakina.

  K'asar office ɗin na zube ganin mutumen da ban taɓa zato ko tsammani ba, mutumen da ya wulak'anta ni, ya tozarta ni, ya ci mun zarafi, duk da kasancewata ta k'aramin yaro, mai k'arancin shekaru.
  Duk da mamakin ganinshi da nayi, hakan bai hane ni fayyace mishi guzurin da naje da shi ba, na gaya mishi abinda ya faru da Abbana, a k'arshe nace Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu da shi, ban bari yayi magana ba na juya na fita, duk kuwa da irin mamakin da na gani shimfiɗe a kan fuskarsa.

  Tun daga nan muka bar garin Katsina, muka koma Kano da zama wurin wata yayar mahaifiyarmu, a haka nake bin yaran gidan zuwa kasuwa, kuɗin da nake samu da su aka sanya Farouq a makaranta, nima da su ne na samu nayi joining Bayero University, ina zuwa kasuwa, ina kuma karatuna, sai ya zamana Allah ya tallafa mana, tafiya tayi tafiya, sai gashi na buɗe ɗan k'aramin shago na siyar da atamfofi a cikin kantin kwari.
  Haka rayuwarmu ta cigaba, cikin rufin asirin Allah, kuɗin da na tara, na dawo Katsina na siya fili na fara gini, a lokacin kuma ina neman aiki, cikin sa'a na samu a nan Zenith Bank, reshen jahar Katsina, sai muka tattaro muka dawo gida, a haka na haɗu da Aysha marigayiyar matata, wato mahaifiyar Jafar.

   Soyayya mai tsabta muka yi da ita, domin kuwa so na take tsakaninta da Allah ba dan abin hannuna ba. Bayan munyi aure muka cigaba da zama da ita, da mahaifiyarmu sai k'anina abin alfaharina, wanda bana iya rayuwata ba tare da ina jin numfashinsa a kusa da ni ba.
  Muna da shekara ɗaya da aure aka yi mun transfer zuwa Maiduguri, a lokacin kuma Farouq zai shiga jami'a, hakan yasa na yanke shawarar nema mishi admission a UniMaid, domin mun riga mun saba da juna, bama iya yin nesa da junanmu ko alama.
 
Haka muka baro Hajiya a Katsina, bayan na samo mata yarinya da zata na ɗebe mata kewa, muka koma Maid da zama, sai dai kusan duk k'arshen wata zamu zo mu duba ta, mu koma.

  Abu na k'arshe da ya taɓa zuciyata sosai shine mutuwar Aysha. A ranar da ta haifi Jafar, bata ko saka shi a idanunta ba, Allah wanda ya fimu k'aunarta, ya anshe abinshi, haka shima ya tashi maraya, a hannun Hajiyarmu, har sai da yayi shekaru biyu sannan na dawo da shi hannuna, yana samun kulawarmu ni da Farouq.

  A ranar da na haɗu da ke ban san ko wacece ke ba, haka kawai na tsinci zuciyata da son taimaka miki, domin a duniya babu abinda nafi ɗauka da daraja da muhimmanci irin mace, na tsani duk wani wanda zai wulak'anta mace, hakan yasa ni ke jin tsanar aminina Sadam Kazaure.
  Ko da kika bani labarinki, har na fahimci ke ɗiyar Alhaji Kabir ce, banyi mamaki ba, duk da ba wai na ji daɗin abinda ya faru dake bane ba, amma nayi believing da maganar hausawa da suke cewa ALLAH BAYA BARIN HAK'K'IN WANI A KAN WANI."

  Murmushi yake yi, a karo guda yana shafe hawayen da ke kwarara a idonsa, haka ma Jay, haka ma Farouq wanda a yanzu yake jin kiyayyar Baffa, ba kamar juyawar da yayi, ya ganshi tsaye tare da Goggo, da wani dattijo, wanda ya tabbatar shine Mal. Baba, saboda tsabar kamar da ya ga suna yi.
  Mik'ewa SS yayi ya isa gaban Malam ɗin da niyyar gaishe da shi, sai dai ya buɗe mishi hannuwansa, ya faɗa jikinshi, gaba ɗaya wurin ya k'ara kacamewa da kuka.

  Gafara Baffa ya k'ara nema a wurin shi, tare da mik'a mishi wasu fararen takardu, a cewar shi dukiyar mahaifinshi kenan da ya ansa, wacce ya gagara taɓawa tun daga ranar da ya gane cewar shi ne ɗan mutumen da yayi mishi aiki da gaskiya da amana, mutumen da ya haɓaka mishi tattalin arzikinshi a lokacin da yake da rayuwa, wanda da taimakonshi ne ya zama abinda yake a yanzu.

  Dak'yar suka samu SS ya ansa, shima sai da Mal. Baba ya haɗa da wa'azi da nasihohi masu ratsa zuciya, wanda ya cire ma kowa da yake gurin tabbunan da ke k'asar zuciyoyinsu, shekara da shekaru.
  A k'arshe suka mik'e suka musu bankwana, domin kama hanyar Maid, amma dole tasa suka bar Jafar a nan saboda irin borin da ya rink'a yi shi a dole sai an barshi a wurin Mammynshi.

  Jay da ta fito raka su, ta kasa haɗa ido da shi, haka kuma ta rasa da wane baki zata bashi hakuri, sannan kuma tai mishi godiyar abinda yayi mata.
 
"Allah Ya tsare hanya. Ya kai ku lafiya."

Abun da ta iya furtawa kenan, ta juya, ta koma ciki.

***Sadam.

Fuskarshi babu walwala ya fito, jakar da ke hannunsa ya saka a bayan motar, sannan ya juya yana kallon yadda 'yan uwansa suka zagaye wurin tamkar wanda zai yi wata tafiyar da babu dawowa.
  Sa'id ne ya kalle shi, fuskarshi da murmushi.
  "Ka tabbatar ka dawo next weekend ɗin fa, kaga dai yadda rayuwa ta koma mana, bamu da wani mataimaki, mune zamu taimaki kanmu, mu kuma taimaka ma k'ananan k'annenmu. Dan Allah Sadam ka natsu, ka shiga tunanin ka, idan son samu ne ka nemi transfer ka dawo kusa da gida, ka kuma samu mata kayi aure, kai dai kaga ai ba yaro ba ne ba."

  Kallon shi kawai yake, domin kuwa bai son komai game da halayyarshi ba, bai san wanene ainahin mutumen da ke tsaye gabanshi a yanzu ba, bai san yana da aure ba, har ma da albarkar 'ya.
  Ta ɓangarenshi kam, bai san ta ina zai fara faɗi ma danginshi yadda rayuwarsa ke tangal-tangal ba, asali ma shi kanshi bai taɓa gane hakan ba sai a wannan lokacin. 

  "In sha Allahu zanyi bakin k'ok'arina."

  "Masha Allah, ka kiyaye sallolinka a kan lokaci, ka kula da addininka sosai fiye da komai da zaka sa gaba, kana dai ganin yadda rayuwarka ta kasance, ka kuma ji tsoron Allah a duk inda kake, ka kiyaye hak'k'in wani a kanka, domin kuwa Allah yana yafe ma bayinsa kowanne irin laifuka da za su yi, amma baya yafe zaluncin da wani ya yi ma wani. Allah ya bada sa'a, ya tsare ka daga kowanne irin sharri."

  Gabansa ne yayi mummunar faɗuwa. Kalaman yayan nashi sosai, sun taɓa raunatacciyar zuciyarsa, wacce mutuwar mahaifinshi ta gama rugurguza duk wani shiri da yake cikinta. Sai ya rink'a ganin tamkar ya san halin da yake ciki, shi yasa yake yi mishi irin wannan nasihohi.
  Murmushi yayi, wanda iyakacinsa fatar laɓɓansa, yayi musabaha da kowa sannan ya juya da zumar shigewa mota.

  Kiran da ya shigo wayarsa ne ya dakatar da shi, ya fitar da wayar daga aljihunsa ya duba, (Bank Manager) ɗinsu ne, hakan yasa ya ɗaga da sauri, ya ɗora a kunnensa.

  "Alhamdulillah. Mun gode Allah."

  "Yau zan taho in sha Allah, dan har na fito ma."

  "Akwai matsala ne?"

  "Ok to sai na k'araso din."

  Maganganun da yayi kenan, ya kashe wayar ya mayar a aljihu, ya shiga motar tare da ɗaga masu hannu ya fita daga harabar gidan.
  Ya rasa dalilin da ke hana shi samun sukuni a zuciyarsa, duk da ya san mutuwar mahaifinshi ta taɓa shi, amma yana ji a jikinsa akwai wani gagarumin abun da ke addabar zuciya da gangar jikinsa wanda ya gagara gane ko menene shi, haka dai ya rink'a rafsa gudu a titin, sallah kawai ke tsayar da shi, bai isa Maid ba, sai misalin takwas saura na dare.
  Sai da ya tsaya yayi takeaway a wani restaurent, sannan ya kama hanyar zuwa gida.
  Ga mamakinshi yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi, wannan karon gaba ɗaya dabararsa ta gama kwancewa, ya rasa wa zai tunkara da batun ɓatan Jay da tilon 'yarsa? Ya rasa ina ta dosa da take neman jefa mishi kokonta a kasan zuciya, menene dalilinta na guje mishi? Ko ta daina k'aunar shi kamar yadda ta rink'a faɗa a ranar da suka yi karonsu na k'arshe? Wanene ya kuɓutar da ita? Ita ce tambayar da ya fiya nanatawa a k'asar zuciyarsa, amma bai samu ansa ba.
  Buɗe gate ɗin ya fara yi ya shiga da motar, sannan ya fita ya rufe, ya kwashi kayansa daga cikin motar, ya mik'a zuwa ciki.

  Hankalinshi a tashe ya zube kayan da ke hannunsa a kan kujera, ya koma ya zauna shima yana k'are ma yadda gidan yayi wata irin k'ura kallo.
  Bai san ta ina zai fara ba, dan haka ya kwantar da kansa a kujera, zuciyarsa na bugawa fat-fat, idan da wani zai k'unace mishi, to babu dalilin da zai hane shi jin yadda bugun zuciyar tasa ke tsanantawa.
  A daren ranar bai iya tsinana ma kanshi komai ba, haka kuma bai samu wadataccen bacci ba, duk da wannan dama ba sabon abu bane a wurinshi ba, dan rabon da yayi bacci mai kyau, tun ranar da ya kwana a mashayar Grand Pinnacle Hotel.
  Hakan yasa ya ci alwashin matsawar ya kai washe garin gobe, to babu abinda zai yi mishi katanga da zuwa neman ɓatacciyar matarsa.

***

Bakwai da rabi dai-dai na safe ya gama shiryawa.
  Fita yayi ya shiga motar ya fitar da ita, ya rufe gidan, ya koma ya tada motar, ya wuce ya bar harabar wurin baki ɗaya.

  Tsaikon da aka samu na cinkoson ababen hawa, shi yasa ya iso wurin k'arfe takwas saura minti biyar, a hamzarce ya fita ya ɗauki jakar laptop d'insa, a dai-dai lokacin motar SS ta danno kai wurin da suke adana motoci a harabar bank ɗin.
  Sai da ya tsaya ya k'are mishi kallo ya tabbatar da lafiyar shi k'alau babu wani abu da ya same shi, amma ya k'i ya kira yayi mishi ta'aziyyar mahaifinsa, a matsayinsa na mutum mafi kusanci da shi a cikin gaba ɗaya ma'aikatan da suke aiki a wurin, domin kuwa kaf ma'aikatan bankin babu wanda bai kira shi ba, in bayan shi SS ɗin.
  Yana ganin ya gyara parking, yana k'ok'arin fitowa, ya juya da sauri ya wuce zuwa ciki.
  Office ɗin manager ya isa, ya bashi hannu suka gaisa, ya k'ara yi mishi ta'aziyya, sannan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun da ke girke gaban k'aton teburin da ke ɗauke da computer, printer, da sauran muhimman takardu na ma'aikata.
  Mik'ewa manager yayi ya dubo wasu fafaren takardu guda biyu, da suke cike da rubutu a cikin tarin takardu da ke gabansa, sannan ya koma kujerarsa ya zauna.

  "Kazaure ya aka yi haka? Ko ince mai zaka ce game da waɗannan takardun?"

  Ya mik'a ma Sadam, wanda yayi saurin sanya hannu ya ansa yana dubawa.

  "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."

  A zuciyarsa ya so yayi maganar, amma Allah da ikonsa sai ta bayyana a fili, har manager na taya shi k'arasawa.

  "Sanin kanka ne banki baya ɗaukar asara, sanin kanka ne kuma banki baya zama da masu yi masa ha'inci da zagon k'asa. Ya aka yi kayi wannan gagarumin aikin? Ya aka yi haka? Haba Kazaure."

   Zufa ce ta yayyafo a goshinshi, duk kuwa da standard A.C ɗin da ta fuskanto shi tana hura mishi sassanya iska mai fitar da k'anshin airfreshner mai daɗi.

  "Amma kasan wannan cin amana ne ko? Saboda duk wani ma'aikacin banki kafin ya fara dole sai yayi rantsuwa da kula da hak'k'ok'in banki, da kuma kula da dukiyoyin mutane. Haka kuma idan loan kake nema a matsayinka na ma'aikacinmu, kasan baza a taɓa hana ka ba, amma me yasa ka munafurci banki ka ɗaukan mata kuɗi ba tare da sani ba?"

Manager ne me wannan maganar yana kallonsa, amma Sadam ba shi da bakin magana, dan bai taɓa zaton har asirinsa zai tonu kafin ya mayar da kuɗin ba, bai taɓa tunanin caca zata juya mishi baya haka ba, domin kuwa ba zai iya cewa ga abu ɗaya da yayi ba da zunzurutun kuɗi har nera miliyan daya da ya ranta wanda ya wuce masa caca, wanda a lokacin, tunaninsa zai samu abinda ya fisu, sai dai cikin rashin sa'a, a ranar da ya je teburin caca da sauran kuɗin, k'arshe ko takalmi bai dawo da shi ba saboda irin warwas ɗin da akai mishi.

  "Me kayi da kuɗin mutane har haka Kazaure?"

  Maganar manager ta dawo da shi daga kogin tunanin da ya tsunduma.
  Cikakkar sumar da ke kansa ya shafa, yana tunanin irin k'aryar da zai shirya, sannan ya ɗago yana kallonsa.

  "I'm sorry sir. Wallahi bani da wani alternative lokacin da na ari kuɗin nan, kasan Dad ɗina ya sha jinya, to a gaskiya a lokacin ne na ari kuɗin na bada aka fitar da shi waje, to cikin rashin sa'a ma sai gashi bai tashi ba. In sha Allah zanyi k'ok'arin dawo da su tun kafin abin ya fito fili."

  "Amma kai kanka kasan baka kyauta ba ko? Saboda wannan kamar cin amana ne. Amma tunda ka ce haka, zamu yi rubutu a baka daga nan har zuwa k'arshen wata ka fito da kuɗin mutane, idan ba haka ba, banki zai dakatar da albashinka, haka zalika zamu yi gwanjon duk wata kadara da ta kasance mallakinka."

  Bai iya furta komai ba, kanshi a k'asa, haka manager ya gama 'yan rubuce-rubuce, ya sa hannu, sannan ya mik'a mishi shima ya sa hannu, ya tashi ya fita zuwa bakin aikinsa.

  Aikin da ya haye masu shi ya hana shi ganin SS, kasancewar shi yana sama inda yake ansa k'orafe-k'orafen customers, yayin da SS yake kasa, fannin Accountants.
  Lokacin da suka fito lunch yana cikin mota ya kifa kansa jikin steering, yana tunanin inda zai samo makuden kudɗaɗen da ya ranta, ta wani ɓangaren yana tunanin inda Jay ta nufa, a faɗin garin Maiduguri.

  Tsaye SS yayi, yana jifarsa da wani irin wulak'antaccen kallo, zuciyarsa da ta k'untata, take wani irin tafarfasa, a karo guda take bugawa da sauri-sauri.
  Bai ce da shi k'ala ba, ya buɗe gaban motar ya zauna, idanunsa na kallon gabansa yace
  "Ja mu je."
  Dagowa yayi yana dubansa, a lokaci guda yana mamakin canje-canjen da ya ke gani daga aminin nashi.
  Bai yi gardama ba, ya tayar da motar suka fita daga wurin, duk da ba wai ya san ina zasu je ba.

  "Titin bypass zaka ɗauka."

  Yayi maganar fuskarsa babu annuri ko alama, dan kuwa ji yake zai iya illata shi matsawar ya nemi kawo mishi raini a dai-dai lokacin.
  Bai tanka mishi ba, ya canja akalar motar zuwa inda ya buk'ata, sai da suka yi tafiya mai 'yar tazara, sannan suka dakata a k'asar wasu bishoyoyi da ke gefen titi...


Mr. SS me ka zo mana da shi?😂😂😂😂

Ku biyo ni mu ji.

Lubbatu😍✌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro