Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

"Na tashi ana kira na Abbakar Sadic Surajo Galadima, duk da a wancen lokacin duka-duka ban wuce shekaru goma zuwa sha ɗaya a duniya ba, domin kuwa ina shirin tafiya aji ɗaya na makarantar secondary.
  Ko da ina da k'uruciya a wancen lokacin, amma bazan manta yadda muka tashi muna rayuwa da iyayena cikin jin daɗi da kwanciyar hankali ba.
  Mahaifina Suraj Galadima haifaffen garin Katsina ne, cikin unguwar Sha'iskawa. Su biyu iyayensu suka haifa daga shi sai k'anenshi Jafar Galadima.
  Kakansu na ukku wanda ya haifi Baban Babansu shine Galadiman Katsina na farko, bayan rasuwarshi sarautar ta koma hannun ɗanshi, ma'ana wanda ya haifi babansu.
  Sun kasance mutane masu rufin asiri da wadatar zuciya tare da neman na kasansu, cikin ikon Allah ba wasu kuɗi ne da su na azo a gani ba, hakan yasa bayan rasuwar Galadima na biyu, sai sarautar ta fita kwata-kwata daga cikin zuri'arsu, abin nufi aka siyar da ita ga masu hannu da shuni, amma hakan bai hana musu cigaba da bearing da sunan Galadiman ba.
  Sana'ar Abbana a wancen lokacin, itace siyar da motoci, domin ba zan manta ba suna da wani company na siyar da motoci mai taken KASAD MOTORS, wanda a kullu yaumun naje wurin sai na tambayi ma'anar abun, sai dai yace idan na girma zai sanar da ni. Haka kuma idan har naga sabuwar mota a wurin nace irinta nake so idan na girma, ina tuna yadda yake kallona da murmushi a fuskarsa yana girgiza kai, wanda sai daga baya na fahimci manufar wannan murmushi nasa, haka zai sa hannu ya shafi sumar da ke kaina, sannan yace

  "Wannan motocin da kake gani Sadic, daga su nike ci nike sha, daga gare su ne nike yi muku duk wata hidima da kai da Mahaifiyarka. Ina nufin ba dukiyata bace ba, dukiyar wani attajiri ce, uban gidana wanda ya yarda da ni, ya bani amanar kayansa. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka, ka sa a ranka cewar zaka girma ka zama mai DOGARO DA KAI."

   A kullu yaumun wannan sune kalamanshi gare ni, sai dai a wancen lokacin ban san ainahin inda maganganun nasa suka dosa ba, ban kuma san wanene mamallakin dukiyar da yake juyawa ba.
  Sunan Sagir S. Tafseer kuwa ya samo asali ne ranar wata bak'ar laraba."

  Jinkirtawa yayi, idanuwansa suka ciko taf da hawaye. Kallon da Farouq ke masa na mamakin yadda ya ji ya kira mahaifinsu Jafar a matsayin k'anen mahaifinshi.
  "Me hakan ke nufi?"
  Farouq ɗin ya tambayi kanshi, sai dai ya san baya da ansar tambayarsa, dole ya gyara zama tare da zura ma SS idanunsa domin warware masa tambayoyin da suke addabar zuciyarsa.

  Handkerchief ya ciro a gaban aljihunshi ya share idonsa, da murmushi ya ɗago yana kallonsu, sannan ya cigaba.

  "Dole nike kiran ta da bak'ar laraba, kasancewar rana ce da na rasa mahaifina, abin tunk'aho na. Rana ce da NA MANTA KOMAI na k'uruciyata, na manta wanene ni, na manta garina, gidana, da ma sunana gabaki ɗaya. Rana ce da bazan taɓa mantawa da ita ba, rana ce ta bak'in ciki, ranar da ta zama silar komai a LABARIN RAYUWATA.

  Tafiya muke da Abbana mun dawo daga Kano kan maganar makarantata.
   A ranar bai yi niyyar zuwa Kanon ba, sai dai sak'on da ya samu daga uban gidanshi da ya tafi k'asar Japan a wancen lokacin, kan yaje ya anso kuɗaɗen da aka tara na company ɗinsu da ke Kano, ya haɗa da na hannunshi ya tura mishi domin zai yo safarar motoci daga can k'asar zuwa nan gida Nigeria. Hakan yasa yace to in shirya muje daga can sai mu biya ayi maganar admission ɗina.

  Kuɗi ne muka taho da su, makuden kuɗaɗe, masu yawan gaske, domin ni kam bazan iya tantance yawansu ba, sai dai na ji Abbana yana cewa a k'alla zasu tasan ma nera miliyan ashirin da biyar, domin kuwa a k'asar boot ɗin motarshi a ka rink'a shirya su, a haka ma sai da wasu suka yi saura.
  La'asar sakaliya, muka kamo hanyar Katsina, gudu sosai Abba ke yi, kasancewar maghriba ta kawo kai, ga shi kuma ana jita-jitar hanya bata da kyau.
   A wani K'auyen da babu yawaitar mutane, haka zalika abubuwan hawa, wani bawan Allah ya tsaya tsakiyar titi yana ɗaga hannu ma Abbana, alamar yana buk'atar taimako.

  Cikin gaggawa Abba ya ja birki tare da yin parking a gefen titi hakan yasa mutumen ya taho da hamzari yana nuna ma Abba wata mota da ke girke a gefe, cewar motarsa ce battery ya bashi matsala.
   Kafin Abba ya buɗe baki yayi magana tuni wasu gardawa majiya k'arfi sun bayyana a kanmu. Abba na ganin haka, ya tura ni bayan motar, ya duk'ar da ni a k'asa, yayin da mutanen suka saita shi da bindiga suna tambayar kuɗi ko kuma ranshi.

    "Kuyi mun rai."

  Furucin Abbana kenan, yana rok'on mutanen, da hannayenshi a sama, idanuwansa sun fara zubar da k'walla.

  "Kada ka ɓata mana lokaci Dallah. Ka bayar da kuɗi ka fanshi ranka."

  "Nera ba ni da ita."

  Fadar Abba, har yanzu ina kallon yadda hawaye ke sintiri akan fuskarsa, wani na bin wani, tamkar an buɗe famfo marar kan gado.

  "Ku bincike mun motarshi."

  Abinda babban su yayi musu umarni kenan, cikin ɗan k'aramin lokaci suka fara bincika motar, inda suka gano kuɗaɗen da aka shirya a k'asar boot ɗin motar Abbana.

  "Wato mu zaka raina ma hankali ko?"

  "Wallahi ba kuɗi na bane ba, kuɗin mutane ne, ku taimaki rayuwata, ku bar ni in isar da amanar da na ɗauko."

  Bai ida rufe bakinsa ba suka saki harsashin bindiga a cikin k'walwarsa, hakan yasa na fasa ihu ni a tunanina suna jina, sai dai ban sani ba ashe basu ma san ina yi ba, a wata duniya ta daban nike ihuna.
  Tun daga nan na silale na kwanta a k'asar motar, ina jin yadda suke maganganu, sai dai na kasa fahimtar komai a maganar tasu, na manta menene ya faru a lokacin, na manta menene ya kawo ni halin da nike ciki a lokacin.
  Biyu a cikinsu, suka shigo motar Abba, sauran suka shiga ɗayar motar da ke gefe, suka dinga tafiya, ban san ina za su je ba, haka kuma ban san ya aka k'are da gawar Abba ba.
  Abinda zan iya tunawa guda ɗaya ne, yadda wani a cikin mutum biyun da ke motar Abbana ya juyo ya ganni duk'unk'une a k'asar motar, yasa dan uwansa ya tsaya, suka fitar da ni suka saita bindiga a kaina zasu harbe, sai dai ɗayan yace ya kyale ni, suka bar ni a nan suka shiga motar suka yi tafiyarsu.

  A bakin titin na kwanta ina kukan da ban san ko na menene ba, domin kuwa NA MANTA KOMAI, ban kuma san ko a ina nike ba.
   Haka na dinga ganin wucewar motoci iri daban-daban, amma ban ko iya motsawa ba, ina kwance a wurin ban san abinda nake buk'ata ba, kuka kawai nike yi, har sai da ya kai idanuwana babu sauran hawaye.

  Wata mota da ta wuce naga ta dawo da baya, inda nike kwance suka tsaya, sannan wani dattijo da ke bayan motar ya buɗe ya fito ya tunkari inda nike kwance.
  Tambaya ta ya fara yi dalilin da ya kwantar da ni a wurin, amma ban sani ba, ya sunana, shima ban sani ba, ina iyayena, duka duk ban sani ba, sai naga yana tofa mun addu'a, a karo guda ya kama hannunna ya mik'ar da ni muka shige motar, ya zaunar da ni a gefensa, ya umarci drivern da ya ja motar muje."

   Wannan karon Jay ce ke zubar da wasu irin zafafan hawaye. Kuka take irin mai tsuma zuciyar nan, Farouq kam idanunsa sun kaɗa sunyi jazir, domin tunda ya zo duniya bai taɓa jin labari mafi muni irin wannan ba, yayin da ta ɓangarenta take tausaya ma rayuwar da SS ya shiga lokacin da yake tsananin buk'atar mataimaki a gefensa.

  Kallon su kawai yake yana girgiza kai, domin kuwa duk lokacin da ya tuna ranar, yana jin ina ma tare da shi ɓarayin suka harbe, ya tabbata da bai gamu da wasu bak'in cikin da suka wanzu a rayuwarsa ba.

Sai da suka tsagaita da kukan, sannan ya cigaba.

  "Kakanki Mal. Baba shine dattijon da ya tsince ni, dattijon arzik'i mai kamala da nasibi na rayuwa, shi ya suturta ni ya 'yanta ni, ya mayar da ni mutum mai gata, ya raɗa mun suna Sagiru, a cewar shi tunda yayi Kabiru, wato Baffanki, kasancewar har a lokacin ban san wanene ni ba.
   Haka na cigaba da zama cikin sabuwar rayuwata mai daɗi, domin kuwa babu abinda nake iya tunawa, sai ya zamana tamkar nan ɗin ne inda na fara rayuwata tun asali.
  Tun daga ranar da na fara zama a gidan, Malam yake faɗin ya sama ma Kabiru ɗa, domin a wancen lokacin na kan ji Iya matarsa na cewa

  "Tabbas ba k'aramin daɗi Kabiru zai ji ba, na samun wannan gagarumar kyauta daga Allah, mutum kusan shekaru bakwai da aure amma bai taɓa haihuwa ba, na tabbata zai ji daɗin wannan abu fiye da kai Malam."

  Sai dai kuma lokacin da Kabirun da suke magana ya zo, Malam ya je mishi da batun, sai ya zamana bana cikin jerin yaran da yake so, k'arshe ma yace ma Malam babu dalilin da zai sa ya ɗauki annoba da hannunsa ya kai gidanshi, dan haka Malam yayi hak'uri, shima ya fitar da ni a gidansa, tun ban girma na ɓata mishi tarbiyyar gida da sunan zuri'a ba.
  Duk da ina k'arami a sannan, amma ban mance furucin Malam ga Baffanki ba.

  "Lallai da sauran ka Kabiru. Wannan ɗan k'aramin yaron ne kake yi ma mugun hasashe? To kai idan baza ka zauna da shi ba, ni baka isa ka hana ni zama da shi ba. Zan kula da shi saboda Allah, in ilmantar da shi domin Allah, har izuwa lokacin da zai samu dawowar tunaninsa, ko kuma lokacin da zai samu damar ganawa da danginsa."

  Tun daga wannan rana sai ya zamana hatta da sauran yaran gidan suna nuna tsangwamarsu gare ni wacce ban san ko ta micece ba, a wurin Mal. Baba da Iya kawai nake samun dama-dama, sai fa 'yar karamar k'anwarsu Nafisa, wacce muke kusan kai ɗaya da ita.
  Malam ne da kanshi ya maida ni makarantar primary nayi aji na karshe, sannan ya kaini FGC Daura na fara karatuna na secondary, ta ɓangaren islamiyya kuwa shi da kanshi yake koyar da ni, haka muka cigaba da zama cikin kwanciyar hankali da sabbin iyayena masu matuk'ar nuna soyayyarsu gare ni fiye da 'ya'yan da suka haifa.
A haka na cigaba da wata irin makauniyar rayuwa, domin kuwa ban san ko wanene ni ba, haka kuma fuskokin mutanen da nake gani ba irin wanda na saba gani bane a baya, hakan ya k'ara taimakawa wurin rashin dawowar tunanina.

  Har lokacin da na fara girma Baffanki bai janye karan tsanar da ya ɗora a kaina ba, haka zalika bai janye k'udurinsa na san fitar da ni daga zuri'ar gidan Mal. Baba ba.
  Babban abinda yayi wanda ya tashi hankalina, shine yadda ya ja k'ima da mutuncina suka zube a idon Malam, har kuma yace ba zai iya cigaba da zama da mai irin halaye na ba. Duk da a wancen lokacin ban san kowa ba, bani da wasu dangi da suka wuce mun su a gaba ɗaya rayuwata, haka Baffan yasa aka kore ni a gidan kan wani dalili marar tushe, marar asali, wanda ko a mafarki aka ce zan aikata haka, ni kaina zan yi gardama da abun."

  Sai a yanzu hawaye suka yayyafo mishi, handkerchief ɗin da ke hannunshi yasa ya toshe bakinsa, kuka yake irin kukan da baya da sauti, sai dai duk wanda ya kalli mai yin irin shi zai tabbatar da ba k'aramar azabtuwa zuciyarsa ke yi ba.

  "A lokacin ban wuce shekaru goma sha takwas ba, domin kuwa gama secondary school ɗina kenan, Malam na fafutukar nema mun admission zuwa jami'a.
  Dakina shine na farko idan ka shigo gidan, ina kwance ina bacci babu riga a jikina, gaba ɗaya gidan babu kowa sai Nafisa, Malam yana k'ofar gida, yayin da Iya ta fita unguwa, sauran 'yan uwanta kuma gaba ɗaya suna gidajensu.
  Ban san me ya shigo da ita ɗakin ba, na farka dai na ganta tsaye a kaina, hakan yasa na mik'e ina tambayar abinda ke faruwa, kafin tayi magana Mal. Baba da Baffanki sun shigo gidan.
Kamar Malam ya manta wani abu a waje, sai ya koma, yayin da Alhajin ya k'arasa shigowa shi kaɗai, gadan-gadan kuma yayo ɗakin nawa, ba tare da munsan wainar da ake toyawa ba, ta duk'a gefen katifa ta tana shirin ɗaukar wani English novel, wanda ɗaukar shi ɗin ne ya shigo da ita ɗakin, a lokacin Alhaji wato Baffanki ya buɗe labulen, ni kuma na mik'e zaune domin in bata damar ɗaukar abin ta fita in cigaba da baccina.

  A ranar nayi bak'in cikin da mutuwar mahaifina kawai ta fi shi bak'antuwa a zuciyata, a ranar nayi kukan da har sai da hawayena suka k'are.
  Ta inda Alhaji yake shiga ba ta nan yake fita ba, har Malam Baba ya dawo ya zayyana mishi a yanayin da ya ganmu, sai dai Malam bai gaskata abun ba, amma Baffanki ya dinga faɗa, har yayi wani furucin da, da wuya in manta da shi.
  "Na faɗi maka yaron nan annoba ne Malam. Ka ganshi a 'yan shekarunsa har ya san ya ɓata maka tarbiyyar 'ya, amma baza ka iya yin komai ba ko? To wallahi yau sai ya bar gidan nan."

  Daga wannan rana na bar gidan, duk da bayanin da yarinyar tayi na k'aryata hasashensa, haka kuma ba da son ran Mal. Baba ba, haka na fito zuciyata k'unshe da bak'in cikin da ya sa nayi alk'awarin bazan kuma komawa gidan ba har abada, na gwammaci cigaba da rayuwa a tasha, kan in koma gidan da ake jifa ta da k'azafin zina.
  Sai dai kuma abinda baki sani ba shine, wannan fitowa ta taimaka mun k'warai wurin dawowar tunanina, kasancewar wata motar masu zuwa Lagos da na bi, domin k'aurace ma garin baki ɗaya, kwatsam a hanya muka k'ara cin karo da ɓarayi masu manyan bindigogi.

  Yadda suka tare mu yasa na fara tunani kamar na taɓa cin karo da irin yanayin, lokacin da na ga sun ɗora bindiga akan drivern motar, sai na fara duk'ewa k'asar wurin da nike, sannu a hankali na fara tunano abinda ya faru shekarun baya, k'arshe na kurma wani gagarumin ihun da ya sa na silale na faɗi k'asa sumamme.

  Lokacin da na farka sai na ganni kwance a asibitin da ban san ko ina ne ba, wata nurse ce take faɗa mun wasu ne suka kawo ni, ganin na daɗe ban farka ba suka ajje mun jaka ta suka k'ara gaba.
  Ita ce ta sanar da ni sunan garin da nike, ita ta bani kuɗin mota, kan in koma gida in nemi iyayena.
   Haka na fito na wuce motor park, na shiga motar Katsina duk kuwa da cewar idan naje can ɗin ma ban san ina zan dosa ba, amma na tabbata ba zan rasa wanda zai taimaka mun ba.
  Cikin dare na isa garin, hakan yasa na kwana anan tasha tare da masu motar da muka zo da su, washe gari na bazama neman dangina.

  K'ofar K'aura na dosa, gidanmu na da kenan, da tambaya na samu wanda suka gane ni, k'arshe aka kaini gidan wata makwafciyarmu k'awar Mahaifiyata, itace ta ɗauke ni zuwa wata unguwa can k'arshe-k'arshen gari, a cewar ta can ne inda Hajiyarmu ke zama.
  Gida ne ɗan karami ginin kasa ɗaki ɗaya ne sai makewayi, sai wani kitchen a gefe da aka zagaye da k'arfen langa-langa.
  Matar da ta fito daga ɗakin, hannunta rik'e da d'an yaron da bai wuce shekaru hudu ba, tabbas fuskar Mahaifiyata gare ta, sai dai na kasa yardar ma kaina ita ɗin ce, domin kuwa ni sanin da na yi ma mahaifiyata mace ce 'yar gayu, mai kyaun surar da duk duniya ita kawai ke birge ni.

  Kuka muka dinga yi tamkar zamu cire idanuwanmu, ta ɓangare na, na sauyin da na gani a tattare da ita ne, yayin da ta ɓangarenta na famin da na yi ma zuciya da gangan jikinta ne.
  Kasa daurewa nayi na fara tambayar ya labarin Abbana, amma sai naga kukan da mahaifiyata ke yi a wancen lokacin ya k'ara tsananta, ta juya ta ce ma yaron da ke gefenta ya koma ciki ya jirata, ba gardama ya wuce ciki, a karo guda ta matse hannuna cikin nata, haka kuma hawayenta basu tsagaita ba, tana kallo na ido cikin ido.

  "Ka bani labarin abinda ya faru da kai da mahaifinka, domin kuwa na daɗe da fitar da raina da ganinku, amma cikin iko na ubangiji sai ga ka ka dawo gare ni, ina Abbanka?"
  Kukan nike nima, a haka na labarta mata gaba ɗaya abinda ya faru, a k'arshe na tambayi yadda akai rayuwa ta sauya mata lokaci guda, da kuma labarin yaron da take tare da shi.
  "Uban gidan Abbanka Alhaji Kabir, mamallakin company KASAD MOTORS shine ya wulak'antar da rayuwarmu, ya fitar da mu daga gatan da muke da shi a da."

   "Ban fahimce ki ba Umma?"

  "Sadic shi ya anshe duk wata kadara da mahaifinka ya tara, a cewar shi Abbanka ya gudan mishi da kuɗaɗen da ya aike shi ansa ne, domin kuwa har yau maganar da nake maka bamu san ya labarin gawar Abbanka ta kasance ba, shi yasa ya k'i yarda kan cewar mutuwa ko kuma wani tsautsayin ne ya faɗa mishi, shi yasa ya k'i yarda da k'addarar da Allah ya jarabce shi da, shi yasa ya bijire ma hukuncin ubangiji. Yanzu haka maganar da nake maka akwai sauran kuɗaɗenshi da bamu k'arasa biya ba."

  Kuka na kuma fasawa, saboda a nawa tunanin abinda Alhajin ya yima Mahaifiyata ba k'aramin cin zali bane. A sama guduwa Abbana yayi, sai na rink'a ganin ai bai dace ace ya huce haushishi akan matar da aka gudu aka bari ba.
   Mik'ewa nayi zuciyata na wani irin k'una, duk da ban san ina zan dosa ba a wancen lokacin.

  "Ina zaka je?"

Ta tambaye ni, hawaye na zuba a idonta, rashin abin cewa yasa na koma na zauna, a haka muka cigaba da kukanmu sai da muka yi mai isarmu muka gama.

   "Ina Uncle Jafar?"

  "Kayi hakuri da abinda zai fito bakina, amma shima Allahn da ya fimu k'aunarsa, ya yi mishi rasuwa."

  Innalillahi wa inna ilaihir raji'un na rink'a nanatawa, a lokacin ji nike tamkar nayi ma Allah wani gagarumin laifi ne, wanda ya rink'a jarabtata ta wadancen ɓangarorin.
  Kasa kukan nayi, saboda hawayena sun gama k'arewa, a galabaice na ɗago ina kallonta

  "Shi kuma wancen yaron fa? Ina kika samo shi?"

  "Amanar Jafar ce Sadic, shi ne kaɗai ɗa guda ɗaya tilo da ya haifa, kuma wurin haihuwarsa mahaifiyarshi ta rasu, hakan yasa ya ɗauke shi ya damk'a mun, ko ranar da zai rasu sai da yace kada in sake in ce ma Farouq ba nice na haife shi ba, dan haka ina rok'on alfarmarka, ko da wasa bana son inji wata magana ta biyo baya a tsakaninka da shi, daga rana irin ta yau, ya zamana kun zama 'yan uwan juna, wanda suke uwa ɗaya, haka ma uba ɗaya."

  K'asar carpet Farouq ya sauko ya zauna dirsham, jajayen idanunsa, sun k'ara fitowa waje, sai dai babu ko ɗigon hawaye, kallon SS yake yi, irin duba na tausayawa, idan ya tuna yadda yayan nashi yayi ɗawainiya da shi, domin kuwa shine cin shi da shan shi, haka kuma shi ya kula da karatunshi baki ɗaya, har izuwa yanzu, ashe ba shak'ik'inshi ne ba, ashe ba uwa ɗaya ta haife su ba kamar yadda ya zata.
  Hakan ya kara masa wata daraja da k'ima a idanunsa, bai san lokacin da ya fashe da kuka ba, ya isa gabanshi, ya sa hannu ya k'ank'ame shi.
  Shima kukan ya saka, itama Jay shi take yi, jin irin tozarcin da Baffanta yayi ma mutumen da ya kuɓutar da ita daga tata rayuwar ha'ula'in.


Soooooo...😢😢😢

Lubbatu😍✌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro