BABI NA ASHIRIN DA HUDU
"Kada ki biye ma son zuciya, ki hana kanki amfani da damar da kika samu. A yadda na fahimta, labarinki na cike da wasu al'amurra wanda tunanina kaɗai ba zai iya fassara su ba har sai kin taimaka wurin sanar da ni. Idan kika yi haka Jameela, zan zame maki wata katanga da zaki jingina jikinta domin samuwar maganin matsalolin da kike ciki. Ki daure ki sanar da ni. Dan Allah."
"Kayi hak'uri, amma mutane irina basu dace da wata katangar da zata jiyar da su daɗi ba, face in cigaba da yawo a cikin duniya har izuwa lokacin da Allah zai anshi rayuwata."
Cikin wani matsanancin kuka take maganar, hakan kuma ya k'ara dagula lissafi da tunaninshi, sai dai bai yi k'asa a gwiwa ba, ya cigaba da rok'onta yana haɗa ta da Allah da ma'aikinsa, har sai da ta ji ita kanta tana son sanar da shi labarin da bata taɓa sanar da kowa ba, labarin da take kwana da shi ta tashi da shi, wanda yake sanya bugun zuciyarta k'aruwa a duk lokacin da ta tuna gingimemen giɓin da ta yi ma k'uruciya, da rayuwarta baki ɗaya.
Bata ce komai ba, ta juya ta koma cikin palon ta zauna, hakan ya bashi damar dawowa ya zauna shima ya zuba mata idanu yana kallonta.
"Nayi kuskuren wulak'anta iyayena akan namijin da bai san daraja ko mutuncina ba. Mutumen da ya raba ni da farincikina, ya raba ni da iyayena, ya kuma sa na wulak'anta babbar aminiyata. Mutumen da bai san k'ima ko daɗin kyautar da Allah mahalicci yake yi ma bayinsa ta 'ya'ya ba. Mutumen da ya ɗaukaka sana'arsa ta caca da shan giya fiye da 'yarsa da matar da yake aure. Malam ina mai tabbatar maka cewar a duk faɗin duniyar nan ban taɓa cin karo da mugun mutum, azzalimi, maha'inci, marar tausayi, wanda bashi da imani, marar tsoron Allah kamar mijina Sadam Kazaure ba."
Wayar SS da ke rik'e a tsakanin hannuwansa biyu da ya haɗa wuri ɗaya ce ta sunɓule ta faɗi k'asa, idonsa a waje ya ɗago yana kallonta.
"Sadam Kazaure?"
"Sunanshi kenan. Shine mutumen da ya wulak'anta mun rayuwa ya mayar da ni ba kowan kowa ba, duk kuwa da irin gata da soyayyar da iyayena suka nuna mun."
"Dakata tukun. Kina nufin gidan da na same ki shine gidan da naje nema na aminina, abokin aiki na Sadam Kazaure?"
"Shakka babu. Nan ne gidanshi."
K'asan carpet ya sauko ya zauna, zuciyarsa na wani irin k'una, a karo guda ya tank'washe k'afafunsa yana kallon Jay, dak'yar yayi k'arfin halin ɗaga bakinsa
"Ki cigaba ina sauraren ki."
Zamanta ta gyara itama, tare da share hawayen da suka ɓata mata fuska, ta fara bashi tarihin soyayyarsu da Kazaure, tun daga ranar da suka fara haɗuwa har izuwa ranar da ya taimaka ya fitar da ita daga uk'ubar da take ciki, ba tare da ta rage komai ba, daga rayuwar rashin 'yancin da tayi a gidan Sadam Baffa Kazaure.
Shiru na dogon lokaci ne ya cigaba da wanzuwa a cikin palon, yayin da Jay ke share hawayenta, tana wata irin sheshshekar kuka mai cike da nadama da da-na-sanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki.
"Alal hak'ik'a labarinki ya fi gaban tunanina Jameela. Sai dai ba wannan ba ne zai sa ki yanke k'auna daga rahamar Allah ba, wanda na tabbata wannan yana cikin k'addarar rayuwarki. Na tabbata wannan itace ishara da Allah ya ke son nunawa iyayen da basu damu da tarbiyyar yaransu ba, kuma ki ɗauka cewar wannan wata jarabawa ce da Allah yayi miki, wacce mutum mai k'arfin imani ne kawai zai iya cinye ta. Ki yi hak'uri ki share hawayenki, da izinin Allah zan taimaka miki, zan sada ki da iyayenki domin ki samu damar neman yafiya a gare su."
Kuka take tana girgiza kanta. Idanunta sun rine, sun fita daga ainahin kamaninsu, hancinta yayi ja sosai abinka ga farar fata.
"Bana tunanin Baffa na zai iya yafe mun. Haka dangina baki ɗaya. Na kasance mutum ta farko data fara ɓata sunan zuri'armu, haka kuma nice mutum ta farko wacce ta bijirewa umarnin mahaifinta a kaf faɗin zuri'armu. Ka gaya mun da wane ido zan kalli iyaye na? Kana tunanin ina da bakin da zan nemi gafararsu? Ta yaya zasu gafarta ma 'yar da ta ɗaukaka farincikin wani k'ato akan farincikinsu? Ba zan taɓa komawa gida ba, na gwammaci na k'are rayuwata a haka har izuwa lokacin mutuwa ta."
"Wannan wata magana ce wacce bata da tushe kike yi. Ki cire wannan a zuciyarki, ki rungumi k'addarar da Allah ya ɗora miki, domin na tabbatar a yanzu kinsan minene rayuwa, kin kuma san wanene namiji. Dan haka ki manta da komai, ki fara tunanin dai-daita rayuwarki, da yadda zaki kula da tarbiyya da rayuwar yarinyarki. Ni kuma na miki alk'awarin in sha Allahu jibi idan Allah ya kaimu Juma'ah, zan kai ki har cikin gidanku domin sada ki da Goggo da Baffanki. Ki shiga ki kwanta, zamu k'arasa magana idan Allah ya kaimu."
Bai jira ansarta ba ya mik'e ya fita harabar gidan, zuciyarsa har wani bugawa take da k'arfi saboda yadda yake jin da zai ga Kazaure a yanzu, da babu dalilin da zai hana shi shak'e masa wuya ya aika shi barzahu.
Agogon hannunsa ya kalla k'arfe goma har da wasu mintina na dare, hakan yasa ya hak'ura ya koma cikin gida, ya tabbatar zasu haɗu a banki da safe.
**Sadam.
Babu kalar tunanin da Sadam bai yi ba, amma ya kasa gano inda Jay zata nufa a duk faɗin garin maiduguri.
Takaicinsa ba wai na rashin ganinta ba ne, na tunanin yadda zai zauna ba tare da ya cigaba da takura ma rayuwarta ba, har ta fahimci kuskuren da tayi na haihuwa da shi, domin ya lura duk abinda yake mata bai sa tayi nadamar haihuwar da tayi ba. Sai dai ya ci alwashin zai nemo ta a duk inda ta shiga, domin kuwa tunda ta zaɓi zama da shi, to kuwa bata isa ta suɓuce masa ba a kowanne irin yanayi zata tsinci kanta.
Mik'ewa yayi da sauri, ya zari makullin motarsa ya fita, kai tsaye titin da zai sada shi da Grand Pinnacle Hotel ya ɗauka, domin kuwa yadda yake jin kansa na gab da bugawa, barasa ce kawai zata taimaka masa wurin samun natsuwar k'wak'walwarsa.
Mintina goma sha biyar suka kawo shi bakin hotel ɗin, bayan ya shiga yayi parking yana k'ok'arin fitowa wayarsa dake ajje gefe ta fara ruri, hakan ya dakatar da shi, ya buɗe k'ofar motar tare da fitar da k'afarsa ɗaya waje, ya ɗaga wayar ya sanya a hands free, sannan ya k'arasa fitowa, yana k'ok'arin rufe motar.
"Ya aka yi kake kira na yanzu?
Saboda kasan anyi albashi ko? To dakata ka ji in gaya maka, idan kana tashi ka nemi na kanka gara tun wuri ka mik'e ka nemi naka, dan ni ba a wurinku zan lalace ba, nima babu wanda ya taimaka mun lokacin da nake nawa karatun."
"Ba wannan bane yasa na kira ka ba ma wallahi, Baba ne bashi da lafiya sosai muna nan Kano asibiti, kuka kawai yake yana kiran sunanka, bai ma san ina da number ka ba, nine nayi tunanin in sanar da kai, dan Allah Yaya kayi gaggawar tahowa idan ba haka ba komai na iya faruwa wallahi."
Tsayuwarsa ya gyara, a lokaci guda idanunsa suka juya, duk da fuskarsa dama babu annurin, amma maganar wanda ya kira shi ta k'ara tsananta bak'incikin da yake ciki.
"Ya kira sunana yace mun me? Ko ya manta abinda yace da ni? Ka gaya mun wanda aka yi ma abinda akai mun ta yaya zai kuma kallon inda mutumen nan yake? To ka buɗe kunnuwanka da kyau ka saurari abinda zan faɗa maka, ko mutuwa mutumen nan yayi, kada ka sake ka kira ni. Ka dai ji abinda na faɗa maka."
Ya ja wani mugun tsaki, yana k'ok'arin kashe wayar, ta ɗayan ɓangaren aka cigaba
"Haba Yaya Sadam, duk fa abinda zaka faɗa baza ka taɓa canja shi a matsayin mahaifinka ba, kuma koma me ya maka ya kamata kayi hak'uri ko dan darajar kawo ka duniya da yayi, ka daure ka zo ka saurari abinda zai faɗa dan Allah, watak'ila abu ne da zai amfani rayuwarka gaba ɗaya, dan Allah Yaya ba dan abinda yayi maka ba."
"Kai Dallah rufa mun baki, an gaya maka ni sokon mutum ne? Ko an gaya maka ina da lokacin ɓatawa? Ko kuma kana tunanin kare ya cinye mun zuciya ne? Ina so ka sani matsawar mutumen nan yana numfashi, to har abada bazan kuma taka k'afata garin nan ba, tunda dama ba kowa na ajje a garin ba."
Yana gama faɗar haka ya kashe wayar ma gaba ɗaya, ya juya ya fara tafiya, yana tunanin da mai zai ji, da bak'incikin Jay, ko ko da bak'incikin kiran da k'aninsa ya mishi?
Zuciyarsa a daburce ya shige ciki, tashin farko kwalbar barasa guda ya ɗaga ya zazzage a cikinsa, sannan ya k'ara buɗe ta biyu, har sai da ya kai ga ya kasa gane komai saboda irin giyar da ya tuttula ma cikinsa k'arshe ya rink'a jin kamar numfashinsa na ɗaukewa saboda azabar tashin hankalin da ke damunsa.
Bai iya motsa ko da yatsar hannunsa ba, asali ma bai san abinda yake faruwa ba har sai da misalin k'arfe goma sha ɗaya na washe garin ranar.
**Jay.
K'arfe bakwai dai-dai na safiyar ranar alhamis SS ya fito da shirinshi tsab-tsab cikin bak'ak'en suit da farar riga daga ciki, k'afarsa dake ɓoye ciki rufaffen bak'in takalmin Alfani, ita ce ta fara yi ma Jay dake duk'e tana gyaran pillows ɗin kujera sallama, hakan yasa ta ɗago tare da gyara hijab ɗin jikinta tana k'are mashi kallo.
K'anshin da ta shak'a na turaren Mediterranean (Elizabeth Arden) ɗinsa shi ya bata damar tuno da ɗan gayun Kazaurenta, wanda a kullu yaumun yake cikin daddaɗan k'anshin da ke kashe zuciyar mai shak'ar shi.
"Ina kwana."
Muryarsa ta doki dodon kunnenta, hakan ne kuma ya katse ta a tunanin da take.
"Ina kwana. An tashi lafiya?"
"Alhamdulillah, ba dai shara kike tunda safe haka ba? Da kin bari Farouq ya dawo school duk shi yake aikin gidan ma."
"Ba komai ai."
Tayi maganar muryarta a sanyaye. A haka Farouq da Jafar suka fito da shirinsu, da sauri Jafar ya isa ya kama hannunta yana washe hak'ora.
"Ina kwana Mammy."
"Ka tashi lafiya?"
"Lafiya lau. Ina Rukayya?"
"Bacci take yi. Ina zaka je haka?"
"Daddy zai kaimu school ɗin su Uncle Farouq, shi kuma ya tafi wurin aiki ko Daddy? Kuma kullun haka muke yi."
Yayi maganar yana kallon Babanshi.
"Ni bazan ansa ka ba, tunda ka fito ko gaishe ni baka yi ba."
Dariya yayi, ya koma gabansa yana cewa.
"Na manta ne Daddy, barin gaishe ka yanzu. Ina kwana?"
Dariya duk suka sanya, in banda Jay, a haka ya juya yana kallonta.
"Zan je wurin aiki, akwai komai da zaku buk'ata a store. Jafar ka zauna kuyi wasa da Rukayya mana, kaga yau ba sai ka bi Uncle Farouq school ba ko?"
"Daddy da gaske?"
"Sosai mana. Ga Mammy zata dafa muku abinci mai daɗi."
Da murnarshi ya juya da gudu ya shige ɗakin da Rukayya take, yayin da Farouq ya matso yana dariya.
"Aunty ina kwana."
Kunya ce ta lulluɓe ta yadda k'aton saurayi ke kiranta aunty, haka dai ta maze ta ansa shi da
"Ka tashi lafiya?"
"Alhamdulillah."
Har sun sa kai zasu fita, sai kuma ya dawo da baya
"Yawwa, aunty da Allah idan za ki girkin nan ki ɗan sa da ni."
"Wuce muje ni kada ka makarar da ni."
Cewar SS suna dariya gaba ɗaya, a haka suka fita suka barsu a gidan.
Wani irin yanayi take ji a tattare da ita, rabon da ta samu sakewa irin haka har ta manta, amma duk da haka tana tunanin halin da Sadam zai shiga, ba tare da ya san inda ta dosa ba, ta wani fannin kuma tana tunanin ba zai wani damu ba tunda dama ba k'aunarta yake yi ba. Sai dai ita ta kasa yakice tunaninsa a k'asan zuciyarta.
**Sadam.
Idanunsa ya fara buɗewa a hankali, sai dai ya kasa gane shin rana ce ko dare, kasancewar mashaya 'yan uwansa da ke zube a wurin suna ta kwasar baccinsu bil hak'k'i da gaskiya.
Hannunsa ya duba da zumar gane lokaci a agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun, sai dai ga mamakinsa babu agogon kamar yadda ya tabbatar ya shigo wurin da ita.
Bakinsa ya cika da iska ya furzar, kansa na wani irin sarawar da ya sanya shi saka hannu ya dafe kan, ya mik'e zaune.
Wayarsa dake cikin aljihu ya fitar ya kunna, k'arfe goma sha ɗaya da mintina ashirin da biyu, hakan yasa shi mik'ewa tsaye da sauri, sai dai sauran barasar da ke jikinsa ta k'ara mayar da shi ya faɗi k'asa sharaf.
Mik'ewa ya kuma yi a karo na biyu, ya fara bin bango ya fito wurin motarsa.
Shigarsa ke da wuya wayarsa ta fara ruri, amma bai ɗaga ba, har sai da ya juya motar ya fita a hotel ɗin, sannan aka kuma kiran wayar a karo na biyu.
A kasalance ya ɗaga yana tsaki, ya sanya ta tsakankanin kafaɗarsa da wuyansa, yayin da ya cigaba da tuk'i da hannuwansa duk biyun.
"Saheeb ba nace kada ka k'ara kira na akan maganar nan ba? Ka bar ni inji da abinda ke damuna da Allah."
"Yaya wallahi Baba na gab da mutuwa matsawar baka zo kun sadu da shi ba yanzu, watak'ila sai dai ku haɗu a lahira, tsakanin jiya da yau ya suma ya kai sau biyar, kuma duk farkawar da zaiyi sunanka ne kawai a bakinsa. Dan Allah Yaya ka sassauta zuciyarka, yanzu wannan ko ba mahaifinka bane ai ya kamata ace ka tausaya mishi, duk wani fushi da kake da shi a banza in har ya mutu da bak'incikinka. Dan Allah ka zo ka ji abinda yake son sanar da kai."
"Maganar banza kenan. Me ya hana lokacin da ya wulak'anta ni baka yi masa wannan wa'azin ba? Ko sai ni da ka raina ma wayo? Idan ka kuma kira na akan maganar nan sai na sassaɓa maka kamanni wallahi."
Ya kashe wayar ya wurgar, ya cigaba da rafsa gudu har ya isa gida, lokacin k'arfe sha biyu na rana, bai san ta ina zai fara bayani idan yaje banki ba.
Wanka ya fara yi ya shirya, a haka wayar Saheeb ta kuma shigowa, a masifance ya ɗaga ya kara a kunnensa.
"Zan ci u…"
Maganar shi ce ta mak'ale jin muryar mahaifinshi cikin tsananin tashin hankalin da ya tabbatar masa ciwo na galabaitar da shi.
Shiru yayi yana saurarensa, ya kasa cewa komai, har ya gama, a k'arshe ya kashe wayar ya zube a kujera, fuskarsa na bayyanar da alhini da tashin hankalin da yake ciki, bai ankara ba hawaye suka fara bin kumatunsa, shekara shidda cif-cif rabon da ya ji murya ko ya sa mahaifin nasa a idanuwansa.
Haka kawai ya ji yana son ganin shi, duk kuwa da haushinsa da yake ji, ta wani ɓangaren kuma yana tunanin barin Maiduguri ba tare da ya san ina Jay take ba.
"Zan dawo gare ta."
Ya faɗa a bayyane, a karo guda ya mik'e ya fara haɗa jakarsa, ya fito ya wurga ta a bayan boot, ya rufe gidan sannan ya yi tunanin zuwa banki ya sanar da su, kafin ya wuce.
Ganin har sun fito lunch, amma Kazaure bai zo aiki ba yasa SS fitowa, ya wuce inda yayi parking ya shige mota da niyyar zuwa gidanshi ko Allah zai sa ya ci karo da shi, ta yadda zai samu damar faffasa bakin mugu marar tausayi irinshi.
Cikin rashin sa'a yana fitowa ya mik'a titi domin ya juya ya ɗauki hanyar gidan Sadam, a dai-dai lokacin shi kuma motarsa ta iso bakin bankin, a waje yayi parking ya fita da sauri ya shige ciki.
Ba'a fi minti goma ba ya fito, ya kama hanyar ta dabo tumbin giwa, cikin tsananin fargaba da tunanin abinda zai tarar, duk kuwa da wani irin k'una da zuciyarsa ke yi.
**
Ko da ya isa a kulle ya samu gate ɗin gidan, ya duba ko ina amma bai samu wanda zai tambaya labarin Kazaure ba, haka ya shiga mota ya koma, zuciyarsa a dagule tare da tsinewa maza masu halaye irin na Kazaure.
Har aka tashi aiki bai samu daidaituwar tunaninsa ba, al'amarin Sadam ya gama ɗaure duk wasu jijiyoyin jikinsa, k'arfe shidda da rabi na yamma ya isa gida a gajiye, rigarsa ta sama tare da jakar laptop ɗinshi sagale a hannunsa na dama, ya shigo gidan da sallama.
A palo ya same su zaune, Jafar da Rukayya na wasa, Jay na zaune a gefensu. Jafar na ganinshi ya tashi da gudu ya isa ya k'ank'ame shi yana dariya.
"Sannu da zuwa Daddy."
"Yawwa yaro na. Ina Rukayya?"
Yayi maganar yana murmushi yayin da ya mik'a mata hannu yana mata nuni da ta taho, amma ta mak'ale kafaɗa alamar ta ki, k'arshe ma tashi tayi ta koma jikin mamanta ta kwanta, tana kallonsa a tsorace.
Girgiza kai yayi, sa'adda ya k'ara jin wata k'iyayyar Kazaure, wanda ya wulak'antar da kyautar da Allah ya mishi, ga shi nan ta sanadiyyarsa har ya sa yarinyar tana tsoron mutane.
A tausashe ya d'ago yana kallon yadda Jay tayi k'asa da kanta, tausayinta sosai yake ji, har yana ganin ta kamar k'anwarsa ta jini.
"Jameela."
"Na'am"
Ta ɗago dara-daran idanunta, cikin rashin sa'a ta sauke su cikin nashi.
"A'uzubillah."
Ya faɗa a cikin zuciyarsa, kasancewar wata kibiya da tayi mishi suka a k'ahon zuciya.
Dak'yar ya dai-daita kansa, duk kuwa da bai san menene dalilin da yasa yake rasa natsuwarsa a duk lokacin da ya kalleta ba, a matsayinta na matar aure, matar amininsa.
"Tunda na fita nake neman Kazaure, sai dai har yanzu bamu haɗu ba, naje har gida amma ban same shi ba, cuz yau ko wurin aiki bai je ba. So wannan ba matsala ba ce, gobe zamu tafi in sha Allah, daga baya idan na dawo zan san duk yadda nayi na gana da shi"
A firgice ta k'ara dagowa tana kallonshi, sai dai idanunsa na kan tv, bata iya furta komai ba, illa wasu ZAFAFAN HAWAYE da suka wanke mata fuska.
Bai lura da halin da take ciki ba, ya mik'a mata ledan abincin da ya shigo da shi, ya kai dubansa ga Jafar
"Ina Farouq ya kawo maku plates. Na san k'ila baku ci abinci ba ko?"
"Mun ci abinci Daddy. Kaima ga naka can kan table Mammy ta dafa mana mai daɗi."
"Chap, Yaya yau waye zai ci abincin waje? In gaya maka Aunty Jay ta mana wani girki mai daɗi da na ci kunnena har motsi ya dinga yi."
Farouq ya yi maganar lokacin da ya k'araso cikin palon ya zauna, yana yi ma yayan nashi sannu da zuwa.
"Kai ga ka ba gwanin cin abincin waje ba dama, dole kunnenka yake motsi."
"Ai wallahi dan dole nake zaune garin nan, na matsu muyi hutu ko na tattara in koma gaban Hajiya in cigaba da cin abincinta mai daɗi."
Dariya suka sanya a tare, SS ya kalle shi,
"Ka ko ga gobe in sha Allahu zamu tafi, idan kana da sak'o ka bayar in kai mata."
"Da gaske Yaya? Me zaka je yi Katsina gobe?"
"Jameela zan kai gida."
"Ai ko k'afarku k'afata, tunda dai ka ga weekend ne nasan kuma duk inda Sunday tayi kaima dole ka dawo."
"Ka zauna kayi karatu. Ba ka ce mun exams zaka fara ba?"
"Haba ai da saura Yaya. Allah nayi missing Hajiya ne."
Jay dai saurarensu kawai take yi, bata tsoma bakinta ba har suka gama, sai da SS ya shiga ciki sannan ta kalli Farouq
"Dama ba nan ne asalin garinku ba?"
Dariya yayi ya ɗauki remote ya fara latsawa.
"Haba aunty, ki ganni fari tas kice da ni yaron Maiduguri? Bari mana ai bana ma kama da bak'ak'en mutanen nan."
Dariya ya bata sosai, hakan yasa ta murmusa tace
"Ya suke ne su 'yan Maidugurin? Kuma ma na sani ko shuwa ne kai."
"Bari mana aunty. Wannan Kt bobo ne."
"Da gaske Katsina kuke?"
"Eh wallahi."
"To ya kuke da mai gidan nan?"
"Yaya na ne same Mother same Father."
Har ta buɗe baki zata kuma yin wata tambayar, sai gashi ya fito, hakan yasa tayi gum da bakinta, ta maida hankalinta a tv, k'arshe da taga bata ganewa ta mik'e ta koma ɗaki.
Will she be able to leave her soul mate behind?
Lets find that out👏👏
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro