Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Gudu ya dinga rafsawa, hakan yasa ya isa gidan cikin ɗan k'aramin lokaci, zuciyarsa a hargitse yayi parking ya fito, kai tsaye part ɗin Mal. Goni ya dosa da sallama, sannan ya tura kansa ciki.
"Wa alaikumus Salam. A'aha, wannan kamar Sadam ai. Shigo mana."
"Nine Malam."
Ya faɗa lokacin da ya cire takalmansa, sannan ya shiga ya zauna tare da tank'washe k'afafunsa ya k'ura ma zanen carpet ɗin dake shimfiɗe k'asar palon ido.
"Malam Barka da aiki, da fatan mun same ku lafiya.?"
"Lafiya lau. Alhamdulillah. Har ka dawo kenan?"
Ya buɗe baki zai tambaya daga ina? Sai kuma Malam ya cigaba.
"Ai a ranar da ta zo take ce mun an tura ka aiki Lagos da kwana biyu ita kuma ta haihu. Nace lallai kunyi dabara da kuka yi tunanin kawo ta nan, da a gida zata haihu baka nan."
Dariyar yak'e Sadam yayi, yana sosa kai, zuciyarsa na harbawa, ya daure yace
"Eh wlh, yanzu ma ita nazo ɗauka ai."
"Kai haba dai? Ba za ka barta ta ɗan k'ara kwana biyu ba? Kasan jikin mai haihuwa yana buk'atar taimako."

"Haka ne, ai akwai wata da zata cigaba da taimaka mata a can ɗin."

"To Masha Allah. Barin sanar da ita ta fito."

Ya mik'e ya shiga ciki, lokaci zuwa lokaci ya kan kalli agogonsa, a zuciyarsa ya dinga addu'ar kada Allah ya kawo Faisal har sai sun bar gidan.
A cikin gida kam artabu aka sha da Jay kan baza ta koma ba, hakan yasa Malam ya gyara zama yana tambayar
"ko kuna da matsala ne?"
Kamar ta faɗi masa ainahin yadda zaman nasu ya kaya, sai kuma ta tuna k'aryar da ta masa ranar da ta zo gidan, hakan yasa ta fashe da kuka ta k'ank'ame hannun Hajiya Malaa.

"Bana son in rabu da Hajiya ne wallahi. Kuma idan na koma gida ban san wa zai cigaba da kula da ni kamar yadda take man ba."

"Allah sarki."

Cewar Hajiya Malaa.

"Wannan ba wani abu bane Jameela. Kar ki damu, akwai abubuwa da zan baki da zaki cigaba da amfani da su, sannan kuma ki cigaba da kula da kanki, kamar yadda nake miki da ikon Allah zaki dawo jikinki na ainahi. Tsabta, abinci mai kyau, duk za su taimaka miki. Dan haka kada ki damu, idan kin samu lokaci kuma ai zaki dinga lek'o mu. Tashi maza ki shirya kayanki."

"Nagode maku Hajiya, nagode, Allah ya k'ara rufa mana asiri baki ɗaya."

"Amin Amin."

Suka ansa gaba ɗaya har Malam da ya mik'e ya sa hannu ya ɗauki jaririyar dake cikin lallausan farin shawul ɗin da ya siya mata, sai kanshi take, ya juya ya fita, ita kuma Hajiya ta cigaba da taimaka mata tana haɗa kayanta.
Har yanzu Sadam na zaune sai mazurai yake, da alama akwai rashin gaskiya a tattare da shi, a haka Malam ya shigo, gadan-gadan yayi kanshi ya mik'a masa jaririyar.

"Kai mata addu'o'i, sai ka yi mata huɗuba dan bamu san sunan da kake son kiranta ba."

What? Ni in ɗauki wannan abar? No it can't be.

A zuciyarsa yake sak'e-sak'en nan, a fili kuma ya saki wata dariya dak'yar, yana duban Malam.

"Wallahi ban iya ɗaukan yara ba Malam. Akwai wata rana da na ɗauki wani yaron k'anwata sai da na yi masa targaɗe saboda irin rik'on da na yi mishi. Sai sunyi k'wari tukun."

"Subhanallah, a'a ni kam ba zaka karya mun mata ba, barin rik'e abata, idan Jameela ta fito ta anshe ta."

Ya juya ya zauna da yarinyar yana k'are mata kallo, tare da tofe ta da addu'a, daga bisani ya ɗago yana kallon Sadam wanda ya tsura ma k'ofar shigowa ido, kamar mai jiran wani.
"Ya kamata ayi mata huɗuba fa. Matso nan kayi mata a hannuna."

Wata makirar dariya yayi wacce iyakacinta laɓɓansa.

"Malam ai duk ɗaya ne, ka yi mata da duk sunan da ya kwanta maka."

"Kai haba da Allah?"

Malam ya tambaya fuskarsa cike da annuri, a zuciyarsa yana yaba alkunya irin ta Sadam Kazaure.

"Sosai ma kuwa, ai ba wani abu bane."

Cikin jin daɗi Malam yayi ma yarinyar huɗuba, ya ɗago da murmushinsa,

"Gata nan an samu Rukayya. Sunan mahaifiyata ne. Allah yasa ta biyo ɗabi'u da halayenta."

Sadam bai ce komai ba sai murmushin takaicin da ya fi kuka ciwo. A haka Jameela da Hajiya Malaa suka shigo, a gaggauce ya gaishe da Hajiyar, ya rink'a watsa ma Jay wani kallo mai nuni da 'zaki sani idan na kama ki.'
Ya tashi yayi ma Malam sallama da wata godiyar munafunci ya fita ya shige mota.
Jay kam kuka ta dinga yi, dak'yar ta anshi Rukayya suka fita, Hajiya ta fito da kudi ta damk'a mata, Malam ɗauke da kayansu, ya saka masu a motar itama ta buɗe gidan gaba ta shiga, Sadam ya figi motar a sikwane suka bar unguwar.

Suna fita layin ya ja gefe yayi parking, hannu yasa ya toshe hancinshi, yana yi mata wani wulak'antaccen kallo.

"Warin me haka nake ji kamar turaren 'yan bori?"

Kallonshi take fuskarta cike da mamaki, me yake nufi? Ba dai haɗaɗɗiyar khumra da Hajiya Malaa ke mata wanka bace yake nufin tana warin 'yan borin?

"Ke Dallah kwashi kayanki ki koma baya, ina magana kin tsare ni da idanunki masu kamar an shak'e mujiya."

"Ba inda zan je. In kuwa na fita, sai dai ka maida wata gidanka ba dai Jameela ba."

Steering ya saki, yasa hannu ɗaya ya tallabi k'irjinsa, ɗayan kuma ya tallabe haɓarsa kamar wata mace, yana jinjina kai yana kallonta.

"Lallai kin ci abinci. Ni kike gaya ma magana haka? Bari kiga abinda zan miki."

Ya fita ya zagaya ya buɗe k'ofar, sannan ya fincike ta, yana k'ok'arin fitar da ita.
Ganin bai ko damu da Rukayya da ke kan cinyarta ba, asali ma k'ok'arin fitar da ita ya cigaba da yi, yasa ta fashe da kuka tana daka masa wata gigitacciyar tsawa.

"Da Allah Malam ka saurara ma rayuwata. Kai wane irin mutum ne marar tausayi? Haba Sadam. Ka dubi yarinyar da ke jikina ka mutunta ni ta dalilinta mana."

Dariyar 'yan bariki ya saki, ya ɗago da kanta yana kare ma yadda take kukan kallo, daga bisani ya sake mata fuska ya fara magana.

"Ni me ruwa na da yarinyar dake jikinki wanda har zai sa in tausaya mata? Kinga da Allah malama fito mun a gaban mota ki koma baya in taimaka in kaiku gida in ba haka ba kuma idan kina da kudi fita ki samu acaɓa ya k'arasa da ke, cuz I've a lot to do na saki na taho wurinki."

Hawayen idonta basu tsaya ba, ta ɗago su ta saita idanunta a kanshi tana girgiza kai.

"Ko da ruwanka ko babu, baza dai a taɓa canja ma tuwo suna ba, 'ya dai 'yarka ce, komai zaka faɗa ba zai taba canja hakan ba. Sake mun hannu in fitar maka a motar da kai kanka kasan na fi k'arfin ka wulak'anta ni saboda ita."

Sakinta yayi ya ja gefe yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ta gefen kumatunsa, ya matsa yasa k'afa ya murje yatsun k'afarta da ta ziro waje tana shirin fitowa.

"Wannan motar da kike gani, a yanzu ko duka danginki zasu taru baza ki taɓa maganin kamar ta ba. Dan haka ki iya bakinki, tun ban faffasa shi a bakin titin nan ba."

K'ara ta saka, tana kiciniyar k'wace k'afarta, sai da ya murje ta da takalmanshi, sannan ya ɗaga ya matsa gefe yana jiran ta fito.
Bayan ta fito tana ɗan ɗingisa kafar, kamar zata shiga motar, sai kuma tayi gaba tana cewa

"Mugu kawai, Allah ya isa."

Tuni ya cafko ta ya buɗe bayan motar ya tura ta.

"Ina kike tunanin zaki je? Ni da ke ai mutuwa kawai zata raba mu, dan haka babu inda zaki tafi. Ke ko kin tafi ma sai na nemo ki na cigaba da gana miki azaba. Kin manta zaɓata kika yi a kan iyayenki, ta ya ni kuma zan bari ki suɓuce mun? Shiga muje akwai horo mai tsanani wanda ya dace da masu taurin kai irinki, sannan kuma ki gaya mun wanda ya baki izini kika tafi gidan Mal. Goni."

Rukayya ta matse gam a k'irjinta, tana kuka, har sai da irin rik'on da ta yi mata yasa ta tsallare da wani irin kukan da yasa Sadam yayi saurin shigewa motar ya ja suka ɗauki hanyar gida.

A k'ofar gidan yayi parking ya fito ya buɗe boot ya ciro kayansu ya watsar, sannan ya juya yana kallonta.
"Me kike jira da baza ki buɗe gidan ba?"
Kallon nashi take itama, lokacin da take k'arasa fitowa a motar.

"Amma ai kana gani yarinya ke hannuna ko? Sai ka rik'e ta in buɗe, ko kuma ka ansa ka buɗe k'ofar kai."

"Lallai kina da aiki yarinya. Babu daya da zanyi a ciki, dan haka ki saɓa 'yarki ki goya, ki buɗe mun gida in shiga Dallah."

Hakan kuwa aka yi, ta goya ta a baya, sannan ta buɗe gidan ta juya tana kallon yadda ya harɗe jikin motar sai cika yake yana batsewa. Yau da tana da wani gata, da babu dalilin da zai sa ta cigaba da zama da wannan mugun mutumen wanda bai san darajar ɗan Adam ba.
Tunaninta ya katse sa'adda ya iso ya bangaje ta, ya shige ciki kafaɗarsa sagale da jakar da ya ciro ta kayanshi daga boot ɗin motar.
Kayanta ta kwasa itama, ta shiga da su ciki, kai tsaye ɗakin da ya koma nata ta wuce, tana k'ok'arin kwantar da Rukayya a saman gado ya shigo a gadarance ya tsaya bakin k'ofar rik'e da k'ugunshi.

Babu riga a jikinshi, daga shi sai singlet da dogon wando, sai slippers ɗin dake sanye a k'afarsa.

"Je ki share mun ɗakin can, bacci nake son yi naga yayi k'ura da yawa bazan iya kwanciya a ciki ba."

"Shara? Haba Sadam ka tausaya mun mana, yau fa duka-duka kwana na ukku da haihuwa. Ka bari jikina ya dawo gare ni mana."

Ta koma ta kwanta a gefen Rukayya, ta juya mashi baya.

"Ke ba magana nake miki ba?"

Shiru tayi bata tanka shi ba, kuma bata da niyyar juyowa ta ansa shi. Hakan ya bashi damar k'arasawa cikin ɗakin ya farɗo k'afafunta da suke rabi saman gado, rabi ta mik'ar da su, ta faɗo tsakiyar ɗakin, bai jira komai ba ya warci hannunta ya shigar da ita ɗakinsa ya wurgar, yana wani irin huci ya fara nuna mata hannu.

"Wallahi, wallahi, kinji na rantse, ko mutuwa kika yi kika dawo sai kin gyara d'akin nan kin wanke mun toilet, I don't bloody care."

Dakewa tayi itama, ta mik'e tana murza hannunta ta isa gabansa fuskarta a murtuke.

"Ba zan share ba Sadam, ai ba jaka bace ni da zaka na treating dina kamar wacce ka samu a arha a garaɓasar yak'i. Nima mutum ce kamar ka, wacce ta san ciwon kanta."

"Oh really? Ashe kinsan ciwon kanki kika wulak'anta iyayenki kika biyo wani wanda baki da guarantee na zai kula da ke ko ba zai kula da ke ba? To bari kiji in gaya miki a wuri na baki da banbanci da wacce na ciyo a garaɓasar yak'i, dan haka dole kiyi abinda nake so, saɓanin haka kuwa ba komai zai jaza miki ba sai bala'i da tashin hankali. Wuce ki fara aikin da na saka ki."

"Ka fad'i duk abinda yayi maka, Amma kada ka manta yaudara da mayaudaran kalamanka ne suka yi tasiri a kaina, har suka sa na bijire ma iyayena na biyo ka, wannan ne ma yasa bazan taɓa yafe maka ba har izuwa k'arshen rayuwata. Kuma bazan yi sharar ba, sai dai kayi duk abinda zaka yi."

Mari ya wanka mata, sannan ya shak'i wuyan rigar ta.

"Ke kin san da wa kike magana kuwa? Zan iya illata ki a banza a wofi, kuma na illata banza wallahi, idan har baki yi abinda nace da ke ba."

Hannuwanta duk biyun tasa ta tokare k'irjinsa, ta fashe da wani irin kuka mai zafi, tana bubbuga gaban rigarsa da hannayen nata, sai dai bai ma san tana yi ba, kasancewarshi mutum mai cikakkar halitta, har sai da tayi iya k'arfinta ta gaji, sa'adda ya cafke hannun, ya wurgar da ita a tsakiyar ɗakin ya fita ya ɗauko mop, da tsintsiya ya wurga mata, ya jawo k'ofar ya datse, ya tsaya bakin k'ofar.

"Idan kin tabbatar kin share kin gama komai, kiyi mun magana in buɗe ki. Marar kunya kawai."

Ya koma Palo ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana girgiza k'afa, zuciyarsa na wani irin tururi na hayak'in bacin rai.
Kuka ta saki tun k'arfinta, ta fara bubbuga k'ofar, Amma Sadam yana ji yayi kunnen uwar shegu da ita, haka tayi zaune a wurin saboda k'arfinta ya kusa k'arewa, ta cigaba da shafe hawayen da ke saukan mata wani na bin wani, har ta fara jiyo kukan Rukayya sama-sama, da sauri ta ɗauki tsintsiyar ta fara share ɗakin, yayin da kukan yarinyar ya cigaba da tsananta, amma ko motsi Sadam bai yi ba balle ayi tunanin zai iya taimaka mata.

A gurguje tayi komai ta gama, ta wanke toilet ɗin ta goge, sannan ta dawo bakin k'ofar tana bubbugawa a hankali.

"Sadam ka buɗe ni dan Allah."

Sai a lokacin ya tashi ya koma bakin k'ofar, ya kara kunnensa, yana jin yadda take magana k'asa-k'asa cikin sheshshekar kuka.
Cikin wata irin kakkausar murya yace,

"kin gama abinda na saka ki ne?"

Shiru tayi bata ansa shi ba, haka yasa ya kuma maimaita maganar a karo na biyu.

"Nace kin gama aikin da na saka ki?"

"Please, ka taimaka ka buɗe ni, baka jin yarinyar can na kuka ne? Have mercy mana, please Kazaure."

Ai kamar ta tunzura zuciyarsa, ya buga k'ofar da k'arfi.

"Ki bani ansa mana, if not sai dai ki kwana a ɗakin nan wallahi. I don't give a damn!"

"Na gama."

Tayi maganar a sanyaye cikin wata irin murya mai ban tausayi.
Key ya ciro a aljihunshi, ya bude k'ofar, tana rakuɓe a gefe tana share hawayen da suke sintiri akan fuskarta.
Da sauri ta mik'e zata fita, yasa hannu ya cafko ta

"Babu inda zaki je sai na tabbatar da aikin da kika yi idan ya gamsar da ni tukun."

A tsiwace ta juyo itama.

"Dallah sake ni inje ga 'ya ta, tunda kai baka san darajarta ba."

Hannunsa ya dunk'ule, ya nuna ta da shi
"ko dai ki rufe mun bakinkin nan, ko kuma in farfasa shi muga na tsiwa. Wuce muje."

Tsaye tayi ta k'i motsawa, ba tare da tace komai ba, sai kunkuni da take ta faman yi, har kuma yanzu hawayenta basu tsagaita ba.
K'eyarta ya tura suka shiga toilet ɗin, sannan ya fito ya dudduba cikin ɗakin, komai dai gashi nan tsab, hakan yasa ya kalleta

"Allah ya taimake ki yarinya, amma yau da sai kin yaba ma aya zak'inta. Fita anan ki bani wuri."

Yayi wurgi da hannunta, ta juya tana share hawaye, ta fita tana yi mishi Allah ya isa a cikin zuciyarta.

**
Zaune take a palo wurin k'arfe biyar na yamma ya fito yayi wankansa ya haɗe cikin bak'in wando da farar t-shirt mai gajeran hannu k'irar polo, k'afarsa sanye da bak'ak'en slippers din maza na Zanotti. Sumarsa da ya taje, ta mik'e tsaye irin ta 'yan duniyar matasan nan, sai hakan ya k'ara fito da kyakkyawar fuskarsa, ba kamar yadda wani saje ya fara kwanta masa luf-luf yayi wa kyawawan jajayen labbansa da suka fara komawa bak'ak'e ado.

Baki ta sake tana kallonshi, tana jin lokacin da wani abu yayi mata karan tsaye a k'ahon zuci.
Soyayyarsa da take dannewa ce ta bijiro mata, har ta rink'a jin tamkar ta mik'e ta rungume shi, ko dan ta shak'i daddaɗan k'anshin turaren da ke fita a jikinshi.

"Bani abinci da Allah kin k'ura ma mutum ido kamar wacce baki taɓa ganin mutane ba. Please kada ki ja in faɗi mana."

Borin kunya ne yasa tayi k'asa da idonta, tana kallon Rukayya, ba tare da tace da shi komai ba.

"Baki ji me nace bane?"

"Amma ai kasan babu wani abu da yayi saura na abinci a gidan nan. Nima fitowarka nake jira."

"Ni zaki faɗa ma haka? Duka-duka yau three months fa da na kawo kayan abinci. Kina nufin kin dafe su kin cinye?"

"Menene kayan abincin da kake magana?

"Oh k'arya zan miki kenan? Kin dai kwashe abinci kin siyar kin zo nan kin zauna kina ce mun ba abinci, wato ni ga mai kudin banza ko? To wallahi sai dai yunwa ta kashe ki."

"Allah ya kiyaye mun wannan halin tsiyar, kai ma ai kasan ban gaji tsiya ba, cikin arzik'i na tashi gaba da baya."

"Ke dallah rufewa mutane baki, ina arzik'in da kike magana yanzu? You better shut that your mouth up kafin in zubar miki da hak'oran kin nan."

Banza tayi mishi, ya juya ya zuba hannayensa a aljihu, ya cigaba da buɗawa, ya fita ya barta a wurin, hakan ya bata damar k'are ma cikakkar halittarsa kallo.


After all, she's still in love with him😂😂😂

Lubbatu✌😍

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro