BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
A hankali ya fara takowa, ya koma inda ya tashi ya zauna yayin da zuciyoyin su duk biyun a dagule, babu wanda ya iya cewa komai. SS ne yayi k'arfin halin daga kai ya kalle shi.
"Mun kasance 'yan Adam mafi rinjayen ajizanci, a haka kuma Allah mahaliccinmu yake gafarta laifukan mu. Me yasa mu baza mu gafartawa wasunmu ba ko dan mu samu dace da kyakkyawan rabo? Me yasa baza muyi yak'i da zuciyoyinmu ba, ko dan mu samu nasarar yakice shedan din da ke addabar mu? Kayi hak'uri ka gafarta mata ko kaima ka samu dawowar farincikin da ka rasa shekaru biyar da suka gabata, na tabbata Ummi ta gama gane duk wani kuskurenta, idan kayi duba da yadda kamanni da yanayinta suka canja baki daya. Ka taimaki zuciyoyinku kai da mahaifiyarta da suke kwana su tashi da takaicin rashinta."
"Na san Ummi tayi gagarumin laifi Sagiru. Sai dai ba wannan ba ne ya hane ni gafarta mata ba. Ina jin kunyar yadda zan hada ido da ita a matsayina na uban da ya sanya hannu wurin tabarbarewar tarbiyyarta, a matsayina na uban da son zuciya, da soyayyar da nake mata suka hane ni dora ta akan hanya madaidaiciya. Ka taimaka mun ka rok'a mun yafiyar Ummi domin ban san da wane ido zan daga in kalle ta ba, duk da kaima ina maganar da kai ne cikin jin nauyin abinda na yi maka, ka tambaya mun afuwarta Sagiru, ban ce kuma ka matsa mata akan dawowa gidana ba, ka tambaye ta idan har tana da ra'ayin hakan. Idan kai mun wannan, zan kasance cikin farinciki da jin dadin da baki kadai ba zai iya misalta shi."
Wani irin hamshak'in murmushi SS ya dinga zubarwa, domin kuwa ya manta da duk wani tabo da yake kallon Alhajin da shi, kwata-kwata ya manta da duk wani abu da ya taba wanzuwa na rashin dad'i a tsakaninsu, kalaman da Alhajin yayi kadai sun wadatar da farincikin zuciyarsa, sun dawo ma Alhajin da daraja, da mutuncinsa da yake gani a shekarun baya.
"Babu batun takura ko matsi da zan yi mata. Idan baka sani ba, wannan ita ce damar da Ummi ta rink'a nema tun daga lokacin da ta bar gida, har izuwa yanzu. Da izinin Allah zan dawo maka da ita yanzun nan ba wai sai anjima ba."
Da gama fad'ar haka ya mik'e zuwa inda yayi parking.
"Sagiru."
Baffa ya kira sa, hakan yasa ya k'ara dawowa, sai dai wannan karon bai kai ga zama, yayin da murmushin da ke kunshe a labbansa har yanzu bai gushe ba.
"Yau kasa na ji kunyar da ban taba jin irinta ba. A yau na tabbatar kai din dan halak ne wanda yake rama alkairi ma sharri. Hakan ya k'ara maka wata daraja da k'ima a idanuna. Ashe wannan halaye naka su suka sa Malam ya aminta da kai, ya fifita soyayyarka a kanmu. Ka sani a yau din nan ina da-na-sanin abinda ya gabata duk da kasancewar na yi shi ne cikin k'uruciya."
Tsayuwarsa kawai ya gyara ya cigaba da sauraren yadda Baffa ke magana cikin lallami, tamkar ba wanda ya sani shekarun da suka gabata ba.
"Wannan ba komai ba ne. Domin kuwa abinda kayi a yanzu ya shafe duk wani abu da ya faru a cikin zuciyata. Gafarar Allah ita ya kamata mu cigaba da nema. Barin je in dawo."
"Allah ya dawo da kai lafiya."
"Amin."
Yana fita Baffa ya zaro kyakkyawan handkerchief a gaban aljihunshi, ya cigaba da share hawayen da suke sintiri akan fuskarsa, yana tuna yadda son zuciya yasa ya wulak'anta mutumen da yayi silar dawowar farincikinshi a wannan lokacin.
"Lallai na kasance mutum mai son kaina fiye da kowa. Ya Allah ina rok'on ka da ka dai-daita mun halaye na. Bana son in kuma maimaita kurakuran da na yi a baya."
A fili Baffa ya rink'a wannan bayanan, a k'arshe ya mik'e ya shige ciki zuwa dakin Goggo, inda ya same ta kwance a k'arshen gadonta, da alama jikin nata sai a hankali, domin kuwa tun ranar da ta dora Ummi a idonta, da suka tafi take fama da matsanancin zazzabin da ya k'i jin magani.
Da sallama Baffan ya shiga d'akin, sai dai bata ansa shi ba, domin kuwa wannan karon ba k'aramin haushin abinda yayi take ji ba.
Murmushi yayi ya zauna gefenta, saboda ya san da kwanan zancen.
"Taimaka ki tashi a hada mun abinci ina da bak'in da zasu zo yanzu ba da dadewa ba. Sannan kisa a gyara wancen d'akin na Ummi, domin a nan zasu sauka."
"Wasu irin muhimman bak'i ne haka da suka fiye maka lafiyata?"
"Bak'i ne da za su kawo maganin ciwon da ke damunki. Daure ki tashi."
"Ban fahimce ka ba fa."
"Idan sun zo zaki fahimci komai."
Ya juya ya fita da sauri, hakan yasa ta mik'e itama, dak'yar ta wuce kitchen tasa masu aiki suka fara hada-hadar girke-girke, sannan ta fito zuwa d'akin Jay ta bude, tare da yaye manya-manyan fararen k'yallayen da aka sa aka lullube abubuwan cikin d'akin saboda gudun k'ura.
Zuciyarta a raunane suka fara aikin gyara ɗakin, k'aunar ganin tilon 'yar tata na cigaba da azabtar da idanuwa da kuma birnin zuciyarta, yayin da ta wani ɓangaren take mamakin halaye irin na mijinta, wanda duk idan aka kalli fuskarsa, za'a iya ganin yadda zuciyarsa ke kwana ta tashi da bak'incikin rashin 'yar tasa, amma kafar kai ta hana shi bayyanar da hakan.
A haka suka yi suka gama amma zuciyarta dank'are da tunanin hanyar da zata bi domin dawo masu da farin cikin da suka rasa, wanda ta tabbatar mijin nata ya fi ta azabtuwa nesa ba kusa ba.
Kitchen ta koma, suka cigaba da haɗa k'ayatattun girke-girke na ban mamaki, sai dai duk da cunkushewar da zuciyarta tayi, haka kawai sai ta ke samun wata natsuwa a hankali tana saukar mata, har sai da ya kai ga ta daina jin irin raɗaɗin da take ji a zuciyar tata a lokutan baya.
***
Ba'a yi cikakkiyar awa guda da tafiyar SS ba, suka dawo gidan tare da Jay, Rukayya, Jafar da Farouq, har ma da Hajiya.
Wannan karon da k'warin gwiwarsu suka fito gaba ɗaya suka doshi babban palon gidan, saɓanin wancen zuwan da aka sauke su a palon bak'i.
A zaune Baffan yake, yadda ya tattara hankalinsa ya mik'a ma k'ofar shigowa, shi kawai zai tabbatar maka da akwai abinda yake jira.
Yana ganin an buɗe k'ofar, ya mik'e tsaye, zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, har iyanzu bai daina tarabbabin ganin 'yar tasa ba.
Tunda ta shigo ta gagara sauke idanunta a kanshi, murmushin da taga yana jifarta da shi, shi ya k'ara tabbatar mata da gaskiyar labarin da SS ya je mata da.
Annurin fuskar da take ta son gani, wanda rabon da ta ganshi shekaru biyar kenan da suka gabata, shine take hange shimfiɗe akan dattijuwar fuskar mahaifin nata, masoyinta na farko, domin kuwa da soyayyarsa ta buɗe idanuwanta a duniya.
Da sallama suka k'arasa shigowa ciki, a lokacin da wasu hawaye suka yayyafo a kumatun Baffa, cikin dabara yasa hannu ya ɗauke su, yayin da duk suka zauna su kuma, sannan ya ɗago da hannayensa ya mik'a ma Rukayya alamar ta iso gare shi.
Da Hajiya suka fara gaisawa, duk da kasancewarta ba bak'uwa ba a fuskarsa, amma hakan bai hane shi jin nauyin ɗaga ido ya kalle ta ba. A haka Farouq ya gaishe da shi shima, Jafar kam tuni ya isa ya zauna a ɗayar k'afarsa, inda ya ga Rukayya ta zauna ɗayar.
Duban Jay ya ke, duba mai tattare da so da k'auna irin na ɗa da mahaifin da suka kwashi shekaru basu gana da juna ba.
"Ka yi hak'uri Baffa na.."
Ta fara maganar hawaye sharaf-sharaf a idonta, amma ya dakatar da ita, ta hanyar ɗaga mata hannu.
Mik'ewa yayi, tare da zaunar da yaran a kujerar da ya tashi, sannan ya fara takawa zuwa gabanta, kasancewar palon mai girma, sai ya zamana akwai tazara sosai tsakaninsu. Ganin haka yasa Hajiya ta mik'e, a karo guda ta yi ma yaranta nuni da su tashi suma, hannun Jafar ta kama, suka koma palon bak'i, domin su basu damar ganawa da juna.
Zaune take a k'asar carpet ɗin da ya mamaye palon, ta duk'unk'une fuskarta a tsakanin k'afafunta, banda kukan nadama, babu abinda Jay ke yi, hakan yasa zuciyar Baffa ta k'ara karyewa, sa'adda ya isa gefenta ya zauna, tare da sa hannu ya kama nata hannayen.
"Ya isa haka Mamana."
A tsorace ta ɗago da rinannun idanunta ta sauke a kanshi, tabbas ba mafarki take ba, Baffanta ne a gefenta, shine kuma yake kiranta cikin siga mafi soyuwa a zuciyarta.
Da da ne, da babu abinda zai yi mata katanga da faɗawa jikinsa, sai dai a yanzu, ta kai wani munzali, wanda ta tabbata hakan ne ya hani Baffan nata sanya ta a jikinshi shima.
"Ka yi hak'uri ka yafe mun Baffa. Na san ni mai laifi ce, laifin da ya fi gaban a yafe mun kai tsaye, laifin da ya jefa zuciyoyi da lafiyarku cikin hali na ha'ula'i. Laifin da ya koyar da ni darussa iri daban-daban na rayuwar biladama, ya koyar da ni zama a hali na akwai, da kuma hali na babu, laifin da ya wa'azantar da ni, ya nuna mun irin gagarumin muhimmancin da iyaye suke da shi a rayuwar 'ya'yansu. Na rantse maka da Allah Baffa, bakina kaɗai ba zai iya bayyana halin da laifin da nayi ya jefa ni ba, har sai kace ka gafarta mun, ka kuma bani dama, domin ganin canji a tattare da ni."
Cikin wani irin azababben kuka take wannan jawabin, hakan yasa k'wallar da Baffa ke ta faman taryewa, suka suɓuce, suka silalo saman kumatunsa, hannunta da ke cikin nashi ya k'ara k'ank'amewa, a karo guda ya fara magana.
"Ya isa haka Ummina, ya isa haka kinji. In dai ta nine na riga na yafe miki, na gafarta duk laifin da kika yi, na kuma shafe shi a cikin zuciyata. Nima ki gafarce ni, ki bani damar gyara bayana."
"Ba kai mun komai ba Baffa na, illa k'auna da soyayya da ka nuna mun, wanda ni a nawa rashin wayon na ɗauke su a matsayin wani makami da zan yi yak'i da ku. Duka laifin dai nawa ne, nice na kasa fahimtar muhimmancin abinda ka rink'a nuna mun, a yanzu kam na yi alk'awarin ba zan k'ara bijirewa duk wani umarni da za kai mun ba."
"Alhamdulillah. Allah na gode maka da ka bar ni da raina don ganin wannan ranar."
Suka tsinkayi maganar a bayansu, hakan yasa suka waiga a tare, Goggo suka gani tsaye bakin k'ofar palon, bakinta k'unshe da murmushi, a karo guda kuma hawaye na zuba a idanuwanta.
K'arasawa tayi ta zauna, inda suka sanya Jay a tsakiyarsu, fuskokinsu bayyane da tsantsan farincikin da ke kwance k'asar zukatansu.
A haka duk suka nemi yafiyar junansu, a lokaci guda rayuwarsu ta baya ta dawo musu, har ya zamana tamkar wani abu na bak'inciki bai taɓa wanzuwa a tsakaninsu ba, idan aka yi duba da yadda suke raha, da nuna jin daɗin kasancewa da junansu.
Sun ɗauki kusan awa guda a haka, tamkar sun manta da bak'in da suka ajje a palon bak'i, daga bisani Goggo ta mik'e ta fita, suka gaisa sosai da Hajiya, tare da k'ara yi masu godiya, da kuma k'ara ba ma SS hak'urin abinda ya gabata, domin kuwa yanzu da ta gane shi ɗin ko wanene, sai take jin nauyinsa sosai, a haka suka dawo cikin palon, Goggo ta wuce domin kawo masu abinci.
Kowa ka kalla a cikinsu fuskarsa k'unshe take da murmushi, illa matsala ɗaya da ke damun zuciyar Jay, tunanin halin da Kazaure ke ciki a yanzu, wacce ta tabbatar bata da damar saninta.
Goggo da masu aikinta ne suka dinga shigowa da manya-manyan warmers na abincin da suka girka, a tsakiyar palon suka baje komai, anan suka ci suka sha cikin farin ciki, ta wani fannin cikin jin kunyar SS da mahaifiyarsa.
Bayan sun gama cin abincin ne SS ya basu labarin da Jay ta bashi, babu abinda ya yi saura wanda bai faɗa masu ba, hakan yasa suka k'ara tausaya mata, yayin da zuciyar Baffa ta k'ara tunzura, k'iyayyar da yake yi ma Sadam ta dawo sabuwa fil.
"Kasan Allah, sai na sa an ɗaure yaron nan, sai nasa an nemo shi a duk inda ya shiga a faɗin garin Maiduguri. Sai yayi da-na-sanin wulak'antar mun 'ya da yayi. Yanzu in banda rashin imani, da rashin tsoron Allah irin na yaron nan, bayan tunzura ta da yayi ta bar gaban iyayenta, shine yayi mata sakayya da irin wannan azabar? Zai gane kuskuren da yayi na taɓa gudan jinina, tilon 'yar da na haifa a gaba ɗaya rayuwata."
Kallon shi kawai SS yake yi, dan ya san zai iya yin abinda ya fi wanda ya ambata, sai dai idan son samu ne, su bi komai a hankali, duk kuwa da cewar shima yana da tabon Kazauren a k'asan tashu zuciyar.
"Ka ce bai bata takarda ba?"
Baffa ya tambaya idanunsa k'unshe da tashin hankali.
"Bai ma san inda ta ke ba a halin da ake ciki yanzu."
"Zai sani idan na gurfanar da shi gaban kuliya."
"Kafin nan da ka daure kayi hak'uri na samu ganawa da shi, tunda na faɗi maka abokin aikina ne, ni da kaina zan kawo shi har gabanka, in yaso sai ayi duk abinda ya kamata, amma idan aka je da maganar court, kamar wani tonan asiri ne zamu yi ma kanmu."
Jinjina kai ya fara yi kamar ya gamsu da maganarsa, ko me ya tuna kuma, take ya mik'e, ya ce
"Ba zan iya ba Sagiru. Wallahi sai na ɗaure yaron nan, sannan inga wanda zai tsaya masa, sai na gwada mishi irin gatan da Ummi ke da, wanda ta watsar ta bishi, ta yadda a gaba zai ji tsoron k'ara ɗaukar 'yar wani ya gudu yayi aure da ita."
"Na ji fa, ba wai kuma na hana ka ɗaukar mataki ba, a'a. Ka yi hakuri ka bani wannan damar, domin ni kaina, ina so a gwada mishi irin kuskuren da yayi a rayuwa ko dan zuwa gaba."
Dak'yar SS da sauran jama'ar wurin suka samu Baffa ya tausasa zuciyarsa, a k'arshe ya amince da buk'atarsa. Sai dai kuma Jay ta kasa cewa komai, kuka kawai take yi, ta wani fannin kuma tana tsoron matakin da Baffan ke shirin ɗauka.
Sai wurin k'arfe huɗu na yamma sannan suka fara shirin komawa gida. Bayan duk sun fito, gefe SS ya koma yana kallon yadda ake artabu da Jafar kan sai an barshi a gidan, ganin abun nashi ba mai k'arewa ba ne, yasa yace da su Farouq su shiga motar, bari ya lallaɓa shi su tafi.
Sallama suka yi ma su Baffa suka shige motarsu, su kuma suka koma ciki, shi kuma ya fara takawa a hankali, ya isa inda Jay ke tsaye, hannunta rik'e da na Jafar da Rukayya.
Kasa haɗa ido yayi da ita, kasancewar wani yanayi da yake shiga a duk lokacin da ya k'unace ma kallonta.
Hannun Jafar ya kama, da wayo, da wayo, ya ɗaga shi sama, a kunnenshi yayi mashi maganar da ta sanya shi k'yalk'yalewa da dariya, ya fara ɗaga ma Jay hannu.
"Mammy sai gobe."
Hannun yaron ta rik'e, hakan ya ba SS damar dakatawa sai dai ya kasa juyowa, takowa tayi tana kallon Jafar, amma a zahiri ba shi din take kallo ba.
"Kana ganin ya kamata ace har ka tafi ba tare da nasan ainahin wanene mutumen da ya taimaka mun ba?"
Yadda tayi maganar, ya san da shi take, sai dai ya kasa ansa ta, saboda yadda muryarta ke ansa kuwwa, a cikin k'walwarsa.
"Zan so inji labarinka, idan da hali zan so in san menene mahaɗarka da Baffana. Zan so ka yi mun wannan taimakon shima, idan har ban takura ka ba."
Har yanzu ya kasa cewa komai da ita, hakan da ta ji ita kuma yasa ta shafi gefen fuskar Jafar
"Be a good boy yarona, ina jiran ka gobe tunda safe ka ji?"
Ta juya ba tare da ta jira mai zasu faɗa ba duk biyun, a haka jiki ba k'wari, ya isa wurin motar, zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, ya shiga ya tada suka tafi.
***
K'arfe goma na safiyar washe gari a gidan Baffa ta yi musu, kasancewar a ranar zasu wuce Maid, sai dai kuma baya jin zai iya tafiya ba tare da ya sanar da ita abinda ta buk'ata daga gare shi ba.
Bayan sun gama gaisawa, ya ɗago a daburce, ya sauke idanunsa a kanta.
"Kin shirya?"
"A shirye nike dama, but da naga har goma tayi, sai na fitar da raina daga son sanin labarin, dan a zato na kun daɗe da hawa hanyar Maiduguri."
"Hmmmm, kinsan ai bazan ma fara ba. But ba wani interesting abu a labarin fa, amma tunda kinyi insisting, zan sanar da ke."
"Ko ma yaya ne, haka nan ma ina son in sani."
Jin haka yasa Farouq cire earpiece ɗin dake kunnensa, ya mik'a hankalinshi gare su, yayin da SS shima ya kai duba ga agogon dake ɗaure a hannunsa, sannan ya ɗago ya fara magana kamar haka....
Hello lovers..
I wrote this book since august, 2016. Ina da shi a ajje, editing kawai nike, ina updating muku.
While, Hawayen Zuciya, yanzu nike kan rubuta shi, sau kun yi hakuri da yadda kuke samun tsaikonshi.
Thanks y'all for the love.
Bari mu ji me SS ya zo mana da shi🙌🙌
Lubbatu😍✌
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro