Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ARBA'IN DA DAYA

"I hope everything is ready?"

    "Good job. I'll be there in a bit. Thank you."
  Ya saki lallausan murmushi, tare da ajje wayar, ya matsa gaban mirror yana k'ara gyara sajensa, ya wanke jikinshi da turare, sannan ya d'auki key din sabuwar BMW f30 dinshi, ya fice, a zuciyarsa yana jin wani sabon nishadi na yawo a duk illahirin jikinsa.
  Titi ya mik'a, yana tafiya cikin natsuwa, hankalinsa, da zuciyarsa, gaba d'aya sun tafi ga son kallon fuskarta, wacce yau kwana ukku kenan rabon da ya dora ta a idanunshi.
  Cikin 'yan mintina ya iso gidan, bai shiga ba illa waya da ya cire ya fara kiranta, ta daga da muryarta mai laushi tana fad'in

    "Hello."

    "Hi."
Ya fad'a a sanyaye, dan yadda tayi maganar ta gama saukar da wata kasala a gabobin jikinshi.

  "Ka iso ne?"

  "Ina waje. I'm waiting for the Queen."

  Murmushi mai sauti tayi, tare da juya manyan idanunta tamkar yana ganinta.

  "Will be right there."

Ta kashe wayar, tana k'ara kallon yadda ta hade cikin black and gold din English gown dinta mai tuttle neck tare da dogon hannu wanda ya matse a k'arshe. Dankunne, agogonta da bracelet dinta duka gold in color, yayin da ta sha turban head wrap da black scalp, tayi light make-up a fuskarta.

  A tsaye ta hange shi in black shima, illa silver agogon da ya daura a hannunsa, yana tsaye bakin motar ya zuba mata idanu yana kallon yadda take taku cikin natsuwa, ta k'araso a hankali ta tsaya a gefenshi.

  "Barka da zuwa Ya Sadic. Ya karfin jiki?"

  Ajiyar zuciya ya sauke, cikin karfin hali ya furta

  "Kinyi kyau Angela."

  Murmushi kawai tayi, tana juyar da kanta.
  Dukawa yayi gaban motar ya bud'e dashboard ya fito da white necktie, ya d'ago yana kallonta.

   "Juya ki ga wani abu."

   "Me ne?"

   "Ki juya mana. Trust me."

Bata kara cewa komai ba, tayi yadda ya buk'ata, ya warware necktie din ya zagayo da shi ta fuskarta, ya daure idanunta.

   "Please Ya Sadic. What's this?"

  "Let's go."

  Ya fada, yana zagayawa ta other side din motar, ya bud'e mata ta shiga.

   "Please don't open your eyes Angela."

   "Ok. But where are we heading to?"

  "Just keep quite please. Yanzu zamu je ba wani nisa ne da wurin ba."

  A lokacin ya tada motar suka doshi titin da zai sada su da Chinese restaurant.
  Duk yadda taso ta bude idonta, SS ya hana, har suka iso wurin ya gama parking, ya fito ya zagaya ya bude mata kofar ta fito, kafin suka mik'a zuwa ciki.
  Babu kowa a restaurent din, illa ma'aikata, a gaba d'aya wunin ranar SS yayi booking wurin, wannan ya sa babu wani mahaluki da ya ci abinci a wurin ranar, k'arshe ma Close kawai suka sa a k'ofar shigowa.
  D'aya daga cikin ma'aikatan ne yayi musu jagora zuwa wani k'aton hall, wanda a k'alla zai iya d'aukar mutum hamsin.
  Duk wasu extra tables sai da aka fitar da su, illa table guda daya, da chairs biyu, a tsakiyar hall din, an yi hadadden decoration  komai red, ga roses an baza a kasa ko ta ina, sai wani lafiyayyen kanshi da ke tashi, wanda shi kadai zai iya sanya nishadi a zuciyar masoyi.

  Dim light aka kunna na red bulbs, tare da candles da aka saka a red containers, wurin ya k'ayatar sosai, dai dai yadda SS ya ke son ganinshi.

A bakin kofar ya tsaidar da ita, ya k'arasa ya dauko bouquet of red roses din da aka yi tying da green ribbon, mak'ale da dan k'aramin card a jiki, ya iso ta bayanta ya warware necktie din fuskarta, ya ziro da hannunshi da flowers din ke rik'e ta gabanta, ya mik'a mata.
  Baki ta sake tana kallon tsaruwar wajen, sosai ya tafi da duk wani imaninta, ta yi saurin sa hannu ta anshi flowers din da murmuahin mai birgewa a fuskarta.

Gaban table din suka isa, ya ja mata kujera ta zauna, har yanzu bata daina mamakin abun da ta ke gani ba.
  Juya flowers din take a hankali, tana scenting daddadan kanshinsu, a jiki ta ci karo da kyakkyawan karamin katin dake mak'ale jiki, da sauri ta bude, fuskarta taf da jin dad'i ta fara dubawa.

  I will always protect you from the thorns.

  Abinda ta gani a rubuce kenan, ta dago tana kallon shi, shima ita din yake kallo fuskarshi na aika mata da sakon murmushi mai cike da salon k'auna.

     "Let's eat."
  Ya fad'a yana nuni mata da rufaffen plate din da aka shigo da shi, aka ajje gabanta, bakinta ya kasa furta komai, wani shauki take ji mai wahala fassaruwa.
A haka ta sa hannu ta bude plate din.
Abinda ta ga ni ne ya sanya ta dawowa da sauri, ta sauke idanunta cikin nasa da ko kadan, basu kauce a kallonta ba.
Yar karamar paper da aka yi ma shape din zuciya, red color jikinta d'auke da fararen rubutu ta dago tana sauke idanunta a hankali.

  Wanna share every meal with me???

  She's totally speechless, ta tsaya kawai tana kallonshi, a lokaci guda tana ganin yadda kibiyar sonta ke yawo a cikin idanunshi.
  Murmushi ya yi, ya mik'e ya ciro wayarshi ya danna kira, within seconds, wani waiter ya shigo, a lokaci guda duhu ya gauraye hall din, sai dan hasken candles din da ke haskawa kad'an-kad'an.

  Cikin yan mintina, hasken projector ya bayyana a bangon da ke facing Jay, yayin da k'aton hotonya ta ya bayyana baro-baro, wanda a zahiri bata san lokacin da aka d'auke shi ba.

 She's My life

Aka rubuta a k'asar pic din.

Hoton zuciya ne ya bayyana, mai dauke da rubutun da ya taimaka wurin bayyanar fararen hakoranta, tana nutsar da kallonta ga abun da ke fuskantarsu.
SADJAY

  Bayan ya d'auke, rubutu ya fara bayyana, wanda gaba d'aya kalamai ne na soyayya masu tsuma zuciyar masoyi tun daga rana ta farko da ya fara ganinta har izuwa randa ya fara sonta, happy memories dinsu a asibiti, da yadda soyayyarsu ta cigaba da kasancewa, a k'arshe aka yi wani rubutun da ya sanya Jay mikewa tsaye da manyan bakake.

  WILL YOU MARRY ME? These memories are great, but I'd like to creat more...

  A dai-dai nan SS ya iso gabanta, murmushi ya ke yana dubanta, ya gagara furta komai, a zahiri ba zai iya tantance yanayinta ba a day dai lokacin.
  Shiru tayi tana k'ura masa idanu, daga bisani ta fara girgiza kai, wasu zafafan hawaye suka k'wace mata, wanda ba komai ya jaza hakan ba, illa tunanin ranar da Sadam yayi proposing dinta.
  A zahiri da zata iya, da babu abinda zai hana tace ma SS a'a, sai dai baza ta iya ba, ta kuma ci alwashin koya ma kanta soyayyarshi ko ta wane irin hali.
  Shiru yayi yana kallonta, a zuciyarsa yana ayyana abubuwa da dama, wanda kuma a take ya gaskata su, ya aminta da su.
  Murmushin dole ta kakalo, tasa tissue ta d'auke hawayenta, amma wasu sabbi na sake gangarowa, ta mik'a mishi yatsanta na biyun karshe, tana hawaye, tana murmushin dole, ya saki nashi tattausan murmushin, ya zaro siririn gold ring din daga gidanshi, ya saka a hannunta.

"I Love you Angela."

Ya fada yana kokarin kama hannayenta.
   Da sauri ta ja da baya, bai yi kasa a gwiwa ba, ya ci gaba da binta, bakinshi kunshe da wani irin kyakkyawan murmushi.
  Ido waje take kallon yadda shiny idanunsa suka fara canja kalarsu, cikin razana ta furta
     "Are you okay?"
 
Bai iya furta komai ba, ya mika hannuwansa yana rike da nata, bai san me ke yawo cikin kansa ba, amma yana jin yadda soyayyarta ke dukan din wata gaba da ke jikinsa, yana jin tamkar zai iya rasa ta daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Yana kaunarta tsakaninsu da mahaliccinshi, ba zai kuma iya jure rashin ta a gefenshi ba.

"I Love you Angela, so very much. I love you with every fibre of my being."

  Flower bunch din da ke hannunta ta wurgar a kasa, cikin idanunsa take kallo, kafin ta fizge hannunta a na shi, ta kalli tsakiyar idanunsa lokacin da hawaye ke zuba a nata idanun.

"Na gode Ya Sadic."

Ta fada da wata raunatacciyar muryarta, ta juya da sauri tana neman hanyar fita.
Bai fahimci mahaifarta ba, amma ya ga bacin rai a tsakanin idanunta,ya ga wani abu wanda ba ya son ya yarda da fassararshi a fuskantar. Bai taba zaton rike hannayenta zai zama wani abu irin wannan ba. Bai bari ta karasa fita ba, ya isa da sauri ya shiga gabanta, bai san me zai fada mata ba.

  "I'm sorry please. I doesn't mean to hurt you. I'm sorry Angela."

  Mamakinshi take sosai, ta rasa me zata ce da shi, cikin zafin nama ta daga hannu ta saita a kan fuskarshi da zumar wanke shi da mari, sai dai kwarjinin da yayi mata, yasa tayi k'asa da hannunta ta fashe da wani irin kuka.
  Cikin tashin hankali ya k'araso yana shirin kama hannunta, tayi gaggawar d'ago manyan idanunta.

   "Don't you dare touch me again."

  Chak ya tsaya a wurin yana kallonta, hankalinshi a tashe domin a zahiri bai san sa'adda zuciya ta debe shi ba har ya kai hannuwansa saman nata.

  "I'm so sorry Angela please. Wallahi ba laifi na ba ne ba."

  Mikewa tayi a fusace ta fita, shima ya biyo bayanta da sauri, tana shirin fita main gate na restaurent din ya dake zuciyarsa ya finciki hannunta, bai damu da yadda take tirje-tirje ba, da kuma yadda ma'aikatan wurin ke kallonsu, ya bud'e gaban motar ya saka ta, ya rufe, kafin ya zagaya da sauri ya shige ya tada motar suka bar harabar wurin.

  Wani irin azababben kuka take wanda ya ki ya ji lallashi da ban bakin da SS ke mata, sai ya zamana tamkar yana k'ara ingiza hawayen da suke ambaliya a fuskar tata ne.
Har suka iso gida ya shigo da shirin gyara parking, bata bari motar ta k'arasa tsayawa ba ta bude da k'arfi ta fice ta fara takawa zuwa ciki, ba tare da ta damu da bakuwar motar da ke girke a gefen da suka yi oarking ba.

    "Jay.."

  Ta ji muryar da ko a wane irin tsanani zata riski kanta, baza ta taba manta mamallakinta ba, bata juyo ba, amma ta tsaya tsab, haka ma hawayenta suka kafe a lokaci guda.
  Jingine yake jikin motar, haka SS shima ya jingine jikin tashi motar ya zuba masu idanu yana kallonsu.
  A hankali ya taka ya isa inda take tsaye, ta juyo tana kallonshi, yayi baki sosai ya rame, dan har wani extra space ke akwai a rigar jikinshi, ta kalle shi tun daga sama har kasa, wani kuka ne ya k'ara kubuce mata, ta juya da sauri zata shige ciki.
  SS ta gani a gabanta, ya zuba mata idanu yana girgiza mata kai alamar kada tayi haka.
  Gabansu Sadam ya isa ya mik'a mishi hannu suka gaisa.

  "Magana kawai nike son yi. Nothing more."

  "Magana?"

  Ta fad'a tana kallonshi,

  "I thought babu wata magana da tayi saura a tsakaninmu."
  Duk wanda yaga yadda tayi maganar ya san cikin k'arfin hali ta yi ta, domin kuwa fuskarta, ta bayyanar da sirrin zuciyarta, ta yadda hawayenta suka dinga sintiri ba kakkautawa, tana yi ma Sadam wani irin kallo mai cike da tausayin halin da yake ciki duk da bata san me ke damunshi ba, amma tana da tabbacin abun ba zai rasa nasaba da ita ba.

"Ki saurare shi please."

  SS yayi maganar dan ya riga ya gama karantar zuciyarta, a lokaci guda ya juya zai koma bakin motarsa.

  "Gaba dayanku nike son magana da, please kada ka tafi."

  Kamar ba zai dawo ba, sai kuma ya ja ya tsaya a inda yake, yana kallon yadda wasu kibiyoyi ke fita daga idanuwansu suna kai suka ma zuciyoyinsu.

  Wani bakin kishi ne ya turnike shi, sai dai bashi da bakin magana, idan yayi duba ga gagarumin laifin da ya aikata mata..

Motar Baffa da ta sako kai cikin gidan ne ta sanya kowa cikinsu shiga taitayinsa, ganin yadda annurin fuskarsa ya d'auke cikin dan lokacin da ya fito yana dubansu daya bayan daya.
  Jay da ke tsaye tsakiyarsu ya zuba ma ido, a zuciyarsa yana tambayar me suke son mayar mishi da gida? Maza har guda biyu sun saka mishi 'ya a tsakiya suna kare ma halittarta kallo.

  "Barka da zuwa Alhaji."

  SS yayi saurin fada, ya juyo ba yabo ba fallasa yana kallonshi.

  "Barka dai Sagir. Lafiya kuwa?"

  "Sannu da zuwa Baffa."

  Sadam ya anshe yana sussunne kai, Baffa ya juya ya k'ura masa ido yana son tuna inda ya san fuskarshi.

   "Lafiya lau. Ehnmm dama.."

  "Ya dai? Ina jinka."

  "Dama ina son yin magana da su ne."

  Sadam ya k'arasa mishi, yana kallon Baffan.

  "Uhhnmm Sagiru?"

  "Na'am Alhaji."

  "Ka jira ni a ciki, dama ina son ganinka."

  Ya juya yana kallon Jay da kanta ke k'asa ta kasa motsi, tana hada yatsunta wuri guda.

  "Me kike jira da baza ki wuce ba ke kuma?"

  Sum-sum ta juya ta shige ciki tana shafe hawayen da suka yi saura a idonta, duk da ta so ta san abinda ke tafe da Kazaure, amma bata da wani zabin da ya wuce mata na Baffanta.
  Ya juya yana kallon Sadam, zuciyarsa taf da mamakin canje-canjen da yake gani a tare da shi.

  "Ya aka yi ne Sadam? Akwai matsala ne?"

  Shiru yayi kanshi a k'asa, dan a zahiri ba Baffa ya zo gani ba, amma tunda ya yi mishi katanga da wacce ya so ganin, zaiyi amfani da wannan damar ya isar mata da sakon da ya zo da shi, watak'ila Baffan ya fahimci halin da yake ciki.

  "Ina sauraren ka."

  "Dama zan ce ne ayi hak'uri da abubuwan da suka faru, komai muk'addari ne daga Allah."

  Juyawa Baffa yayi ya kira drivernsa da hannu, ya iso da sauri ya mik'a mishi jakar hannunshi.

   "Shigar mun da wannan ciki."

  Ya ansa ya wuce, sannan Baffan ya gyara tsayuwarsa, yana k'ara karantar yanayin na Kazaure.

  "Komai muk'addari ne kamar yadda ka fada. Hakan ma yasa kaga ban mayar da kai prison ba, ba don komai ba sai dan albarkacin jini da ka hada da jikata. Dan haka in dai bada hak'uri ne ya dawo da kai gidan nan, to ka kama gabanka, mun riga da mun hak'ura da duk abinda ya gabata."

  Kanshi a k'asa bai iya dagowa ya kalle shi ba, ya fara magana.

  "Baffa nayi nadamar duk wani abu da na aikata, na fahimci dukkan kuskuren da na yi, amma ina neman afuwar a bani dama in gyara laifukana saboda Allah, ba dan halaye ko dabi'una ba."

  "Dama? Kamar ya kenan Sadam? Idan na fahimce ka kana nufin Ummi ta koma ta cigaba da zama da kai?"

  Murmushin dattako Baffa ya zubar yana girgiza kai.

  "Yaro man kaza, bai gasu ba ya kashe wutar."

  Dagowa yayi ya gama k'are mishi kallo, tabbas ba zai rasa matsala a k'walwarsa ba, Baffan yake innatawa a cikin zuciyarsa.

  "To jira kaji Sadam, ko da kai kadai ne namiji k'wallin k'wal da yayi saura a doron k'asa, bazan taba yarda Ummi ta koma maka ba. Haba Sadam, ka yi ma zuciyata adalci mana, ka barni da ciwon da ka dasa a cikinta shekara da shekaru mana, ka kuma so ma dan uwanka musulmi abinda ka so ma kanka. Ka barni inji da haushinkan da nike ji a cikin zuciyata, wanda darajar 'yarka yasa ban iya yin komai a kanshi ba. Dan Allah na rok'e ka, wannan ya zama zuwanka na k'arshe gidan nan da sunan ka zo neman yardar Ummi ta koma gidanka."

  Hawaye ne suka silalo a fuskar Kazaure, wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa. Fuskarsa da ke k'asa ta gama bayyana tsantsar nadamar da ya tsinci kanshi a ciki, hakan yasa shi shafe hawayen, ya d'ago yana duban Baffa.

  "Ba wai nufina kenan ba Baffa, na sani, a yanzu bani da cikakkar lafiyar da zan ba ma Jay farincikin da na hane ta a baya, ba ni da komai, ba ni da kowa sai Allah. Ina nufin a bani dama in dinke 6arakar da ke tsakanina da ita da kuma diyata wacce har a yanzu bata daina gudu idan ta ganni ba."

  Ko bai fad'a ba duk wanda ya kalle shi ya san ba shi da lafiya, sai dai ba hakan ba ne zai sa Baffa yayi sakacin amince mishi, har ma ya ansa buk'atarshi.

  "'Yar taka dai Sadam, amma Ummi babu wata baraka a tsakaninku da tayi saura wacce zaka dinke, dan haka ka bani 'yan mintina, yanzu zan shiga in fito maka da Rukayya, in ya so sai kayi duk yadda kaga dama da ita. Idan ma suma zata yi idan ta ganka, babu abinda zanyi, a sannu dole ta hak'ura, tunda dai kaine mahaifinta."

  Bai iya cewa komai ba, domin kuwa ba shi da ta cewar, ya kuma san a hali irin na Baffa, ya taki muguwar sa'a har ma da ya tsaya yana maida magana da shi.
  Jin haka yasa Baffa ya wuce ciki, inda ya samu Jay zaune a palonshi ta had'e kai da gwiwa, bai san tunanin me take yi ba.

   "Ummi."

  Ta d'ago a razane, domin kuwa bata san sa'adda ya shigo gidan ba.
  "Na'am Baffa."
  "Ina Rukayya?"
  "Tana ciki wurin Goggo."
  "Shiga ki hado mata kayanta, ku zo nan ku same ni."
  Kallon rashin fahimta take yi mishi, sai dai bai bata fuskar tambayar dalili ba, ta mik'e jiki babu k'wari ta fita zuwa cikin gidan.
  Bayan kamar minti sha biyar suka shigo hannun Rukayya cikin nata, Goggo tana bin su a baya.
  Barka da dawowa Goggo ta yi mishi ya ansa, kafin suka samu wuri suka zauna suna jiran abinda zai fad'a.
  Gyaran murya yayi, ya d'ago yana dubansu.

  "Ummi na yanke wannan hukuncin ba don komai ba, sai dan watak'ila wannan itace kawai hanyar da zan iya dakatar da Sadam daga zuwa gidan nan. Bazan boye miki ba, a duk lokacin da na ga yaron nan zuciyata na bak'antuwa, domin kuwa tabon abinda yayi har yanzu ya kasa goguwa a idanuwana. Sai dai ban sani ba ko kina da ra'ayin k'ara zama da shi, domin kuwa ba zan tauye miki hakkin abinda kike so ba."

  Faduwar gabanta ne ya tsananta jin kalaman na Baffanta. Allah ya sani Sadam shine mutum na farko da ta fara so, sai dai yanzu a shirye take da ta bayar da ko da rayuwarta ne domin ta fanshi farin cikin iyayenta. Abinda bata fahimta a nan ba shine ina yake shirin kai mata Rukayyarta?
  Kanta a k'asa tace

  "Bani da sauran wata hujja da zata sa in k'ara kwadayin zama da shi Baffa, a shirye nike in siya maku duk wani farin cikin da zai faranta zuciyoyinku."

  "Masha Allah. Naji dad'in kalaminki Ummi. Ina so ki sani, yanzu Sadam zai tafi da Rukayya, suje can su samu daidaituwar tsakaninsu, domin bana so yana fakewa da 'yarsa, ni kuma yana dagula lissafin tawa diyar."

  "Ya kaita ina Alhaji? Mutumen da bashi da aure, ba uwa ba uba. Gaskiya wannan ba shawara ba ce ba."

  Goggo ta fad'a fuskarta a raunane tana kai duba ga Rukayyar da bata san abinda ke wakana ba.

  "Ina sane Maryama, amma duk yadda za'a yi baza a canja shi a matsayin mahaifinta ba, ku bar shi ya tafi da ita, ta nan ne zasu samu jituwa a tsakaninsu, ala bashshi idan komai ya dai-daita, na tabbatar da ta san shine mahaifinta, na tabbatar zai dawo da ita, amma bana son kara ganin fuskar yaron can a harabar gidana."

  Kukan zuciya Jay ta fara rerawa, bata da yadda zata yi, bata isa kuma tace bata yarda da hukuncin da Baffan ya yanke ba.
  Haka tana ji tana gani Baffa ya kama hannun Rukayya suka fita, suka samu Sadam tsaye a jikin motar da babu wanda ya san inda ya samo ta.
  Da farko bata gane shi ba, har suka iso gabanshi, ya duka a hankali yana shafar gashin kanta da ya sha gyara, ta girma ta k'ara wayo sosai, hakan ya k'ara fitar da ainahin kamanninsu a zahiri.

  Kuka ta saka tana kama hannun Baffa tana k'ank'amewa, haka ya fara lallashinta, shima Sadam din yana yi, har sai da ya kai ga kukan nata ya sa Baffan tausaya mata, amma bashi da yadda zaiyi, hakan ne kawai zai sa su samu sauk'i daga zaryar da Sadam din ke yi musu.
  A bayan motar ya saka ta da jakar kayanta, ya juya da sauri ya koma ciki, ya bar Sadam da aikin lallashi tare da mugun da-na-sani da nadamar halayenshi da suka gabata. A haka ya ja motar ya fita, kuka yake kamar ran shi zai fita, haka itama Rukayya ke nata kukan har suka dau hanya.

  Cikin gidan Baffa ya koma ya same su tamkar masu zaman makoki, yayin da tausayin halin da ya san Umminshi zata shiga ya dabaibaye zuciyarsa.

  "Kiyi hakuri Mamana. This is the best for all of us."

  "Babu komai Baffa. Na san baza ka taba yin abun da zai cutar da waninmu ba."

  Sosai ya ji dad'in yadda ta nuna bata damu da abinda yayi ba, duk kuwa da cewar ya san ta ciki na ciki, hakan yasa yake alfahari da ita, yanzu ne kuma ya san ya haifi 'yar da za'a kira da 'yar albarka.

  "Ummi a zahiri na gaji da wannan tarin matsalolin na yaron nan, yau wannan gobe wancen, idan har kin san ba zaki koma mishi ba gara kiyi aure, ya san kin mishi nisa har abada, amma wannan rayuwar bata da wani amfani, matsalar yau daban ta gobe daban, yau na ganki da Sadam gobe in ganki da Sagir, bazan lamunci haka ba gaskiya. A yau baki ji yadda zuciyata ta rink'a tafasa ba lokacin da na shigo na hange ki a tsakiyarsu, abin takaicin ma da nayi duba ga yanayin shigarki ko mayafin kirki babu a tattare da ke, a matsayinki na uwa, wacce ta san daraja da mutuncin kanta. Kinyi wannan shigar kin tsaya a tsakiyar mazaje, ta ya shaidan ba zaiyi tasiri a zukatansu ba, daga nan sai kiga an aikata abinda ba shikenan ba, duk da nasan ba haka kike ba, amma duk inda mace da namiji suka kai ga kebanta to na ukkunsu shedan ne, idan ba'a yi sa'a ba sai kiga ya samu galaba a kanku. Dan Allah ki natsu ki sanar da ni ainahin gaskiyar zuciyarki, idan baza ki koma ma yaron nan ba, ga Sagiru nan, yaro mai natsuwa da sanin ya kamata, kuyi aurenku ku huta da wannan gallafirin a kan titi, can a gidanki sai ki cigaba da karatunki dan na san ba zai taba hana ki ba."
  Shiru tayi tana sauraren maganganun na Baffa wanda suka sa hawaye fara tsiyaya a idanunta. Gaskiya guda daya ce, haka so guda daya ne kuma ba kowa take yi ma shi ba illa Kazaure, amma furucin Baffanta na cewar duk sa'adda ya ga Sadam zuciyarsa na bakantuwa, hakan yasa ta san har abada baza su taba komawa tare ba, kuma dole ta hak'ura da shi da soyayyarsa, ko dan ta dadadawa mahaifin da ya nuna mata kauna fiye da kowa a doron k'asa.
  Idan tayi duba ta bangaren SS kuwa, ta san yana matukar kaunarta, haka itama ta kan ji wani abu dangane da shi wanda ya sha banban da irin wanda take ji dangane da Kazaure. Watak'ila kaunarshi take yi wacce ita ba so ba ne da zai iya tashi daga nan, ya koma wani gun tana jin zata iya zama da shi har k'arshen rayuwarta, sai dai abinda yayi mata yasa ta fara shakku a kanshi, duk da cewar ta gaskata maganar Baffa da yace shaidan zai iya shiga tsakanin mace da namiji a lokacin da suka kebanta, hakan yasa ta dora ma kanta laifi dangane da wasu abubuwa da suka wakana.

  Shine mutumen da ya fi cancanta da ita, amma dole ta gwada mishi kuskurenshi ko dan zuwa gaba.
  Hawayenta ta shafe, ta juya tana kallonsu.

  "Ina maraba da duk hukuncin da ka yanke a kaina Baffa, idan har kana ganin Ya Sadic shi ya fi cancanta da zama miji a gare ni, to zan yi biyayya gare ka, zan kuma aure shi, dan haka ka daina kawo maganar Sadam a wannan lokacin, bazan taba iya koma ma mutumen da ganinshi kawai zai bakanta zuciyar mahaifina ba."

  Hawaye ne suka wanke idon Goggo, sosai tayi farin cikin jin maganganun nata, tayi magana masu ma'ana da muhimmanci, tayi magana mai kwantar da zuciya da sanya iyaye su zama masu alfahari da 'ya'yansu.

  "Allah ya yi miki albarka Ummi."

  A tare suka fad'a ita da Baffa, bakunansu kunshe da kyakkyawan murmushi.

  "Tashi ki je, zanyi magana da Sagirun."

  Ta mik'e a hankali ta wuce d'aki, yayin da Baffa ya fita zuwa inda SS ke zaune.

Barka da Sallah Beautiful people ❤❤

Kun ga inda SS ya nufa kuma😁😁😁

Will she forgive him?

Lubbatu😍👌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro