Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ARBA'IN DA BIYU

Da sallama Baffa ya shigo palon, hakan yasa SS ya mik'e yana ansawa, kanshi a k'asa a karo guda bugun zuciyarsa na tsananta, domin kuwa ya gama yi ma kanshi hisabi tun Baffan bai sanar mishi abinda ke tafe da shi ba.
  Sai da ya zauna, sannan shima ya koma ya zauna yana k'ara gaishe sa, Baffa ya ansa fuskarshi sake, sai dai SS bai fahimci hakan ba kasancewar har yanzu kanshi na k'asa yana jiran abinda zai biyo baya.
  Gyaran murya yayi yana dubansa. Sai ya ji wata sabuwar k'aunarshi ta shige mishi, yadda ya ga ya mik'a duk wani hankalinshi wajen sauraren abinda zai fad'a. Murmushi yayi a zahiri na jin dad'i.
  "Ehnmm Sagiru."
  "Na'am Alhaji."
  "Shin akwai wata alak'a ne tsakaninka da Ummi?"
  A hankali ya d'ago yana kallon Baffan, shima idanunsa a kanshi, hakan yasa yayi saurin yin k'asa da nashi idanun.
  "Hakan da ka yi ya bani ansar tambaya ta. Amma me sa baka sanar da ni ba tun wuri?"
  "Ita din ce bata bani dama ba wallahi."
  "To ni na baka dama. Zan kira Hajiya zamuyi magana, daga nan zamu gana da yan uwan mahaifinka, sai in sanar da su ranar da za'a daura aure."
  A sikwane ya d'ago yana duban Baffa, fuskarshi ta gagara boye farin cikin da zuciyarsa ke ciki.
  "Nagode. Nagode Alhaji. Allah ya tabbatar mana da alkairi."
  "Amin Sagiru, sai dai ina da wata 'yar buk'ata idan baza ka damu ba."
  Shiru yayi yana sauraren shi. Hakan yasa Baffa ya cigaba.
  "Ina fatan zaka bani goyon baya wajen tsaya mata a harkar makarantarta, duk da ina da tabbacin ba za'a samu wata matsala daga gare ka ba."

  "In sha Allah zan yi duk wani kokari dan ganin na cika maka wannan burin, zan kula da ita, zan bata duk wata gudanmawa da ya kamata ace na bayar da yardar Allah. Nagode da wannan karamci, Allah ya k'ara girma."

  "Amin ya Allah. Ina ga iyakar maganar kenan, duk yadda muka yi da Hajiya kuma nasan zata sanar da kai. Allah ya shige mana gaba."

  Daga haka Baffa ya fita, ya barshi baki bude, wani irin farin ciki yake ji har bai san ta ina zai fara bayyana shi ba.
  Wayarsa ya fitar ya fara kiran Jay amma har ta gama ringing bata dauka ba.

***

  Kuka take mai azabar zafi da ciwo a cikin zuciya, ta rasa wace damuwa ce ta fi k'arfi a cikin matsalolinta. Shin soyayyar mutumen da baza ta taba komawa ba, ko rabuwa da 'yarta gudan jininta? Ya za tayi da auren huce haushin da take son lak'aba ma kanta? A zahirance bata da ansar tambayoyin nan, illa addu'a kawai da zata cigaba da yi har lokacin da Allah zai warware mata matsalolinta.
  Haka ya gaji da zamanshi ya tashi ya fita, har a lokacin bai daina kiranta ba, haka kuma bata da niyyar ko da kallon sashen da wayar ke ajje.

***Sadam.

  Har suka iso gida Rukayya bata daina kuka ba, shima idanunsa sun kunbure sun canja launi, haka ya iso yayi parking, ya bude bayan motar da niyyar daukarta da jakar kayanta.
  A hankali ya zauna a gefenta, tana ganin haka ta fara shanye kukan ta, idanunta a waje, ta had'e jikinta wuri guda tana ja da baya har sai da ta matse da k'ofar motar, tana jifarshi da wani irin kallo wanda ke nuni da tsabagen tsoron da ke cikin zuciyarta.

  Haushin kansa yake ji ba kadan ba, murmushin dole ya k'wak'wulo ya mik'a hannu zai taba ta, ta fashe da kuka tana girgiza kanta.

  "I'm sorry Baby. Bazan miki komai ba kinji. Ina son ki. Zo muje ciki in baki abinci da sweet."

  Kuka kawai take tana girgiza kai, ya k'ara kwantar da murya ya kama hannunta.

  "C'mon sweetheart. Daddy ne fa. Kina son in baki ice cream ko? Da chocolates in siya miki sabon kaya, muje park kiyi wasa. Zo muje bazan dake ki ba fa."

  Ai kamar ma yana tunzura ta, kuka take kamar ranta zai fita, haka ya cigaba da lallashinta, dak'yar ya iya daukarta a kafada ya d'auki jakarta a d'ayan hannun suka mik'a zuwa ciki.
  Dakinshi suka wuce ya zaunar da ita, sannan ya fara bud'e jakarta ya cire kayanta ya fara jerawa cikin wardrobe d'insa, teddies dinta da wasu tarkacen kayan wasa da aka zubo a kasan jakar ya fitar, ya gama jera kayan sannan ya iso gabanta ta ci kuka har ta hak'ura tayi shiru.

  "Zo nan Sweetheart."

  Ya bud'e hannayenshi, amma ko motsi bata da niyyar yi.
  Shiru yayi yana kallonta, ya rasa me ke masa dad'i, ga wata irin k'aunar yarinyar da yake ji, sai dai bai san ta ina zai fara shawo kanta ta daina tsoronsa ba.
  Murmushi yayi ya isa ya d'auki daya daga cikin teddies dinta ya fara mik'a mata, amma tana ansa tayi wurgi da shi ta tsallare da kuka.

  "Oh God! I'm sorry Baby. Zo muje in kaiki wurin aunties dinki. Zo nan in goya ki."

  Ya duk'a gabanta yana nuni mata bayanshi, babu gardama ta haye bayan, domin duk a tunaninta wurin Mammynta zai kaita.
  Cikin gidan ya shiga nan fa ya fara cin karo da k'annenshi yan mata, duk ba wanda a yanzu bai san tarihin Sadam ba a gidan, haka ganin kamarsu da Rukayya yasa suka gane itace 'yar tashi.

  "Feena."

  Ya shigo yana k'walla kiran daya a cikinsu, da sauri ta fito tana ganinshi ta fara dariya.

  "Ya Sadam ina ka samo fine girl?"

  "She's your niece. Kina wani tambaya ta. Baki ga kama ba ne?"

  "Ba dai Katsina ka je ba? Tun dazu Ya Sa'id ke nemanka lokacin shan maganin ka yayi babu wanda ya san inda ka tafi."

  "Zan sha yanzu, but please ki kawo mun abinci in bata kinji."

  "Ka kawo ta mana Ya Sadam. Kai da ba lafiya gare ka ba."

  "Na sani Feena, but this is the only thing i can do for her. Kin san komai fa."

  Murmushi tayi ta mik'a hannu ma Rukayya, ga mamakinta sai ta saki dariya ta taho wurinta, hakan yasa Sadam ya sauke ta, Feena ta kama hannunta suka shiga babban palon gidan, yara da manya duk a nan ake zama a sha firar duniya a watse kowa ya wuce dakinshi, dan yanzu gidan dai babu mata, dama Haj. Daso ce tayi saura a matan babansu, ita kuma ta haukace ta shiga duniya, sai wata k'anwar mahaifinsu da mijinta ya rasu ta dawo gidan da zama ita da 'yarta.
  Cikin ikon Allah duk jama'ar gidan sai suka d'auki k'auna suka dora ma Rukayya, kowa sonta yake yana son ta zauna a wurinshi, amma Kazaure yayi katan-katan ya hana a cewar shi shima yana son ya bama 'yarshi soyayya kamar yadda kowanne uban arzik'i ke yi.

  A nan suka ci abincin, inda ya rink'a bata da kanshi, abin ka ga yarinta gashi kuma fuskarshi kawai ta sani a cikin fuskokin wurin, sai ta rink'a ansa tana ci, sai da ya tabbatar da ta k'oshi tass, sannan ya k'ara daukarta suka koma dakinshi ya mata wanka ya canja mata kaya, ya kaita wurin Feena, dan duk ya fi sonta a cikin k'annen nashi, sannan ya koma yayi wanka ya shirya yayi sallar maghriba, yana nan zaune yana lazimi har aka yi ishsha'i ya fita masallaci yayi sallah, sannan ya dawo ya wuce cikin gidan.

  D'akin Feena ya zarce ya gansu suna ta firarsu da Rukayya, ya tsaya a bakin k'ofa yana kallonsu, a lokaci guda soyayyar 'yar tasa na yawo a gaba daya jijiyoyin jikinsa
.
  "Feena ta shi muje a siya ma Rukayya chocolates ko?"

  Ya k'arasa shigowa yana kallonta, itama kallon nashi take yi, sai dai wannan karon bata rushe da kuka ba.
  Gabanta ya duk'a ta haye bayansa, ya mik'e dak'yar, dan ba wata cikakkar lafiya ce da shi ba, haka kuma yarinyar irin chubby kids din nan ce, dan girman jikinta ya fi na shekarunta.
  A motar Sa'id suka zauna shi yana baya da ita, Saheeb na zaune a driver seat suna jiran fitowar Feena.
  D'auke ta yayi ya dora ta kan k'afafunsa, yana kallon yadda take abu a tsorace, ya san har yanzu bata daina tsoronsa ba, ya kama cheeks dinta ya fara jijjiga fuskarta, yana mata chakulkuli.

  "Smile now.."
  Hakan yasa ta fara k'yalk'yale dariya tana kwantawa jikinshi, wani dad'i na daban ya dinga ratsa zuciyarsa, ya tsaya yana kallonta a zuciyarsa yana yaba kyawun smiling face dinta, dan tunda yake a duniya bai taba ganin dariyarta ba sai yau, ashe irin baiwar da Allah ya mishi kenan amma ya guje ta? Hannuwansa yasa ya mak'alk'ale ta, yana jin k'aunarta sosai tana fasa k'irjinsa tana zarcewa cikin zuciyarsa.

  "I love you Cutie pie."

  Ya fada lokacin da ya d'ago fuskarta, ya kuma kama cheeks dinta yana girgizawa.

  "Kina so na?"
  Kai ta girgiza alamar
  "A'a."
  Shiru yayi, jikinshi yayi sanyi, amma ya daure yace
  "Me sa?"
Hannunta ta tura a hancinsa tana wasa da shi, kamar bata ji me yace ba.
  "Me sunana?"
  Ya k'ara tambaya yana rik'e hannun da take wasan da shi.
  Shiru tayi tana kallonshi, a lokacin Feena ta iso, Saheeb ya tada motar suka fara tafiya sannan ta d'ago tana kallonshi, cikin daga murya tace

  "KAZAURE..."

Dariya suka kwashe da har su Feena da ke gaba, Sadam ya kalle ta yana dariya sosai wacce rabon da yayi irinta ba zai iya tunawa ba.
  Dak'yar suka tsagaita, ya sauke ta ya zaunar a kan seat, ya juya yana fuskantarta, tare da kama hannayenta ya rik'e cikin nashi.

  "Sunana ba Kazaure ba ne  ba, daga yanzu Daddy zaki na cewa. Kinji?"

  "Ni ina da Daddy ai, kai ba Daddy na ba ne ba."

  "Noo, nine Daddynki mana. Baki da wani Daddy baya na."

  "A'a fa ni Daddyn Jafar ne Daddy na, yana siyo mun shokolates da iyish kiyiim."

  Shiru kawai Sadam yayi, a zuciyarsa yana innata 'wato bayan fashin mata da SS yayi mishi har ma da na 'ya?' Murmushi yayi ya k'ara matse hannunta.

  "Wancen Daddyn Jafar ne, ni kuma Daddynki. Zan na siyo miki duk abinda kike so nima, in goya ki, in baki abinci in miki wanka, in kaiki yawo ko ina da ina. Because I love you so very much."

  Shiru tayi tana kallonshi kawai, ba wai dan ta fahimci duk abinda ya fad'a ba, a haka suka kawo gaban wani k'aton Store.
  Shopping suka yi dai-dai da dai-dai dan ba wasu kudi ne da shi ba, wannan ma a credit card din Sa'id da ya basu aka cire, suka fito suka shiga motar suna cigaba da dan zagayawa a gari, har sai da ta dan sake da shi, a k'arshe bacci ya d'auke ta sannan suka d'auki hanyar gida.

  Haka ta cigaba da zama tare da shi, so da tattali babu kalar wanda baya bata, duk abinda ya kamata ace mace ce zata yi mata to shi da kanshi yake mata, a bangare guda kuma k'auna da soyayyar Jay na cigaba da azabtar da zuciya, da gangan jikinsa.

***Three Weeks Later.***

***SS.

  Gab da la'asar suka shigo garin Katsina, bayan motar ya juya yana kallon Jafar sai baccinshi yake, sannan ya dawo da kallonshi ga Farouq da hankalinshi ke kan titi.

  "Ku ajje ni ta GRA ku k'arasa gida Farouq. Ina son magana da Jay cuz har yau ta k'i ta d'auki phone calls d'ina, gara ayi wacce za ayi a gama yau, na kasa samun natsuwar zuciyata, kar muje mu muna ta shiri ita kuma ya kasance abin baya gabanta."

  "Haka ne Yaya, amma ka daure muje gida ka dan huta mana, zuwa anjima ba sai in kai ka ba?"

  Shiru yayi yana kallon gefenshi, Allah kadai ya san halin da yake ciki, sai kuma shi da zuciyar ke jikinshi, a hankali ya cika bakinsa da iska ya furzar, fuska a raunane yace
  "Baza ka gane ba Farouq. Wallahi sati ukkun nan da nayi ba tare da na ji muryarta ba ji nike kamar nayi shekara biyu ne. A duniya ban taba zaton akwai wata mace da zata canja tunani haka ba. Ina son ta sosai Farouq, irin son da har bansan adadinshi."

  Murmushi Farouq yayi, ya juya da fuskar tsokana yana kallon shi.

  "Ai ko baka fad'a ba zan iya gane haka Yaya. Cuz ban taba jin kayi firar mace da ni ba, ko Aunty Aysha da kuka yi auren saurayi da budurwa banga kana rawar jiki ba irin wannan."

  Kunya ce ta cika SS, ya juya yana basarwa, Farouq ya sanya dariya, a lokaci guda ya canja akalar steering dake hannunshi.

Sosai SS ya shagaltu wurin tunanin matsayin da yake da shi a wurin jay, duk wani abu da ya kamata na maganar aure an gama gabatar da shi tsakanin iyayensu, kwana biyar kacal ya rage a daura auren, sai dai babbar matsalar a yanzu shine yadda ta ke nuna halin ko in kula a lamarinshi, rabon da ya saka ta a ido sati ukku kenan cif-cif haka zai zo gidan ya gama zamanshi amma baza ta fito ba, ya kira waya tayi ringing har ta gama, amma baza ta dauka ba, har ya gaji ya koma bakin aikinsa.

   A da yana tunanin abinda yayi mata ne ya haifar da haka, a yanzu kam wasu tunane-tunane sun cika k'wanyarshi, sun hane shi sakat, addu'a kadai yake ga Allah yasa ta zama mallakinshi.
  A harabar gidan suka yi parking, ya fito tare da kwashe phones dinshi dake zube a gaban motar, ya daga ma Farouq hannu, ya juya zuwa ciki.
  Zaune ya hange su k'asan canopy tare da malamin da ke koyar da ita littattafan addini, tana sanye da maroon din hijab hannunta rik'e da alqur'ani hankalinta gaba d'aya ya ta'allak'a ga abinda ke gabanta.
  Kallonta ya sake baki yana yi, hakan da ya gani yasa ya k'ara kamuwa da matsananciyar soyayyarta, wacce yake jin ko da sama zata had'e da k'asa ba zai iya daina sonta ba, ji yake ko da tace ta tsane shi ba zata aure shi ba, ba zai taba iya hak'ura da ita ba, he'll fight till end, har sai ya samu cikar burinshi.
  Wayarshi da tayi k'ara ne ya dawo da shi daga tunaninshi, ya maida hankali ga wayar, wani abokin aikinsu ne, ya daga sannan ya k'arasa shigewa palon ya samu wuri ya zauna.
  Sun d'auki kusan mintina sha biyar suna wayar, wadda yawanci duk a kan shirye-shiryen bikin na SS ne, sannan suka yi sallama, ya cigaba da latse-latsenshi har zuwa k'arfe biyar da rabi, ya san lokacin tashinta yayi, kuma dole sai ta bi ta inda yake kafin ta wuce cikin gida.
  Bai kai ga k'arasa tunaninshi ba ta turo k'ofar ta shigo, chak numfashinta ya dakata na wucin gadi, lokacin da tayi arba da doguwar fuskarshi, ya sakan mata shiny idanunsa da suke wani shining yana kallonta.
  Murmushi mai taushi ya jefe ta da shi, amma ta daure fuska tamkar wacce bata taba dariya a duniya ba. Qur'aninta ta k'ara matsewa ta fara takawa zata wuce zuwa ciki.

   "Haba Angela. Dan Allah kiyi hakuri ki sassauta punishment din nan da kike bani, wallahi ina azabtuwa ba wai kadan ba."

  Juyowa tayi a hankali ta fara takowa cikin palon, hakan baya rasa nasaba da tunanin da tayi, ta zauna a daya daga kujerun da ke fuskantarshi tana rungume da Qur'aninta a kirji, hakan yasa shima ya koma ya zauna, hankalinshi a tashe yana kallonta.

   "Please Angela. It wasn't my fault wallahi, duk sharrin shaidan ne, and you didn't gimme a chance to explain myself. I love you, and you know that, bazan taba yin abinda zaiyi hurting feelings dinki ba. Kin sani ai."

  Murmushin k'arfin hali tayi, ta dago da manyan idanunta ta sauke a cikin nashi.

  "At first, I thought you were the one Ya Sadic, I mean the one I'll spend the rest of my life with. But now, ka gama tona kanka, ka bayyana true color dinka. And ka bar ganin su Baffa sun ajje maganar aure tsakanin mu kayi tunanin zasu yi mun dole, NO, that can't be, nasan sunyi hakan ne dan basu san kai din ko wanene ba, amma zan fallasa musu labarinka, zan sanar da su ainahin wanene mutumen da suke shirin hada ni aure da. Cuz ko da ni da kai kawai muka yi saura a duniya bazan taba iya rayuwar aure da kai ba, bazan taba iya zama da mai hali irin naka ba, in takaice maka Ya Sadic dole a kai mun a maganar aurena da kai, amma ni zuciyata tana da wanda take so, wanda da shi kadai ne zan iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar. So, ka daina ba kanka wahala, kaje ka nemi matar aure, dan ko da a ranar daurin aurenmu ne, sai na fallasa sirrin da kake tunanin tsakanin ni da kai ne. Kuma ina mai tabbatar maka hakan zaiyi sanadiyyar rugurgujewar auren na mu."

  Ta mik'e a tsanake ta bi ta gabanshi ta wuce ciki, sai dai ko dan yatsanshi ya gagara motsawa, tunani da mamaki sun gama cika zuciyarsa har sun sa ya rasa gane abinda ya kamata yayi.
  Wani gagarumin tashin hankali ne ya ziyarci zuciyarsa, take numfashinsa ya fara kaiwa da kawowa, zuciyarsa kam tamkar an dora dutse tayi, ya mik'e dakyar dan baya gani sosai, a duniya idan akwai mafi munin magana da ya taba ji to baza ta taba kai wannan da ya ji daga bakinta ba.
  A kafa ya fita gidan, tafiya kawai ya ke, bai san ina zai dosa ba ma.

**Two Days Later**

  Kuka take tsakaninta da Allah wanda ta gagara gane ko na menene, a hankali ta fara shafe hawayenta, ta mik'e da zumar zuwa ta sanar da Baffa gaskiyar zuciyarta, a dai-dai lokacin Baffan ya turo k'ofar dakin nata ya shigo hannunshi rik'e da katuwar Brown envelope guda biyu.
  Da sauri ta koma ta zauna ta kirkiro murmushin dole tana fad'in
  "Sannu da zuwa Baffa."

  "Yawwa Mamana. Ashe dai kina ciki?"

  "Ina nan Baffa."

  "An shi nan kiga"

Ya mik'a mata daya a cikin envelopes din, ta ansa ta zaro paper da ke ciki, admission later dinta ne ya fito, cikin sa'a ta kuma samu law din kamar yadda ta cika, take wani farin ciki ya kai ma zuciyarta ziyara ta d'ago da jin dad'i tana kallon Baffa.

  "Nagode sosai Baffana, Allah ya saka da alkairi."

  "Amin Ummina, anshi wannan shima ki duba to."

  Ya mik'a mata d'ayan envelope din wanda ya fi wancan nauyi ta sa hannu biyu ta ansa tana kokarin fito da abinda ke ciki.
  Wedding invitations ne sun kai guda d'ari biyar masu masifar kyau ta d'auki d'aya daga ciki ta duba, taga dai tabbas shirin bikin suke yi, ta dago idanuwanta taf da hawaye tana kallon Baffa.

   "Lafiya?"

  Ya tambaya yana kallonta, bata iya cewa komai ba ta fashe da wani irin zazzafan kukan da ya tayar da hankalin Baffa.

  "Haba Ummi, babba da ke kike wannan kuka haka? Ko dai baki son yaron nan ne?"

  Da sauri ta girgiza kai, tana shafe hawayen

  "Ba haka bane Baffa, kawai dai ina ta missing Rukayya ne, ya kamata a dawo mun da ita."

  Murmushi mai sauti yayi,
  "Haba Ummi, in dan wannan ai ba matsala ba ce ba, zan aika da kaina a anso ta, ki kwantar da hankalinki da Allah."

  Haka ya cigaba da yi mata nasihohi, a k'arshe ya kwashi wasu daga cikin iv's din ya fita, inda ta kife kai ta rink'a rera wani irin kuka, wata sabuwar k'auna da soyayyar Kazaure ta taso mata, tana jin kamar tana kokarin jefa kanta a mugun hali ne.

  Tun daga wannan rana Baffa, ya fara inviting duk wasu abokananhi na nesa da na kusa, na kudu da na arewa babu wanda bai gayyato ba domin ji yake tamkar wannan ce rana ta farko da zai fara aurar da ita, shirye-shirye kawai suke daga shi har Goggo, 'yan uwa na nesa da na kusa duk sun fara hallara, amarya ce kawai ke rufe kanta a d'aki ta ci kuka har ma ta gode Allah, babu wanda ta gayyato, ko Miemie bata fad'i ma labarin bikin ba.

  Haka ya kasance ta bangaren SS, shiri Hajiya da sauran danginshi ke yi, sun hada gagarumin lefe tamkar wanda za'a kai ma budurwa, latest kaya suka zuba suka dauka suka kai gidan Baffa, haka suma suka cika su da abubuwan arziki, sai dai zuciyar angon ta gagara natsuwa, hankalinshi gaba d'aya baya tare da shi, rabon invitations ma da yawa Farouq ne yayi shi, kasancewar duk babu wasu mutanen SS din wanda bai sani ba.
  Haka abubuwan suka cigaba da wakana, shirye-shiryen biki ake ko ta ina, gidan Baffa ya kacame, hayaniyar dangi kawai ke tashi. Kwana biyu ya rage a daura aure Goggo ta dauka wata Sudanese tazo ta fara aikin gyaran jikin amarya, cikin d'an lokaci kuwa ta fito sharrr da ita abin ba'a cewa komai.

***D'aurin Aure***

And ango da amarya aren't ready😁😁



Lubbatu👏😍

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro