Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ARBA'IN DA BIYAR

Da sauri ya rik'e ta, har ta gama, kafin ya fara tambayar

   "Are you okay?"

   "I'm fine."

  Ta fad'a dak'yar, ya kama hannunta suka wuce toilet, bai damu da yadda jikinshi ya baci ba, ya taimaka mata ta gyara nata jikin, sannan suka fito ya kwantar da ita a kujera, ya shiga rage kayan jikinsa.

  Kitchen ya koma ya gyara wurin da ya baci, kafun ya fito ya same ta hannunta dafe da kanta, idanuwanta a lullube.

  "I'm sorry Angela. Me ke damunki please?"

  Ya k'arasa yana taba wuyanta, sai dai babu alamar zazzabi.

  "Headache?"

  Ya k'ara tambaya hankalinshi duk a tashe.
  Ganin haka yasa tayi k'arfin halin tashi zaune, ta samo murmushi ta dora a fuskarta.

  "Never mind. May be abincin da na ci ne bai kwanta mun ba. But I'm fine."

  "Are you sure?"

  Ya tambaya fuskarsa cike da damuwa, kamar mai shirin yin kuka.

  "I'm Sweedy."

  Ta mik'a hannuwanta ta dora a kafadunsa, tare da tallabo kanshi, ta dora fuskarta saman forehead d'insa, tana kallonshi da murmushi.

  "Alhamdulillah."

  Ya fad'a a bayyane, tare da zagaye hannunshi a kanta, yana lumshe idanu.
  Dakyar ta mik'e tana jin jiri na dibarta, ta shiga ta had'a mishi ruwan wanka, sannan ta dawo ta kwashi kayan da ya cire, ta kama hannunshi suka wuce bedroom, ta cire towel ta mik'a mishi, ya ansa ya daura, kafun ya shige wankan.

  Kayan hannunta ta saka a laundry basket, ta bude jakarta ta fito da PTstrip din da ta siya jiya tana dawowa school, kasancewar sati biyu kenan da ya kamata ace taga period dinta, amma bata gani ba.
  D'akin da ke opposite inda ya ke ta shiga tayi amfani da strip din ta fito, ta barshi a can, kafin ta dawo ta cire mishi kayan da zai saka idan ya fito.
  Tsab ya gama shirinshi, suka fito hannunsu cikin na juna zuwa part d'in shi. Kamar kullun suka samu Rukayya da Jafar sai tsalle-tsalle suke, sai da suka ga shigowarsu, sannan suka natsu suka yo kansu da gudu.

  "Daddy tafiya zamu yi?"

  Rukayya ta tambaya tana kama hannunsa. Sai da ya zauna kasar carpet, ya tank'washe k'afafunsa, ita kuma ta haye kansa yana shafa gashin kanta a hankali yace

  "Ba yanzu ba Rukayya, sai zuwa anjima dai."

  "Daddy ice cream din fa?"

  Bakinta a kunbure tayi maganar idonta cike da k'walla.

  "Oh no, c'mon Daddy's girl, don't be mad. Ok? Zan kai ki but sai anjima. Kinga yau Juma'a ne, ya kamata muyi wani abu da Allah zai yi farin ciki da mu daddare kuma sai in kaiki ki sha ice cream ko?"

  "To me zamu yi ne yanzu?"

  "Karatun Qur'ani mana. Ke dama baki iya ba."

Jafar ya fada yana kallonta.

  "Inji waye to? Ai dai na iya ko Daddy na?"

  "Ba wani kin iya, in kina so mu yadda sai ki karanta muji."

  Jay da ta k'araso da tray din juice da cupcake ta fad'a, kafun ta ajje a tsakiyarsu, ta koma gefen Jafar ta zauna, tare da lankwashe kafafunta itama, irin zaman da suka yi.

  Da sauri suka yi bismillah suka fara karatun, tun suna yi ana musu gyara, har ya kai suma iyayen sun saka bakinsu sun cigaba da yi a tare.
  Sai da suka kai suratul mutaffifin sannan suka yi shiru, domin a nan suka tsaya a islamiya, su Jay ne suka cigaba har An-Naba' sannan suka yi addu'a suka shafa.

  Rayuwar tasu gwanin ban sha'awa, cikin natsuwa da tsabta, tare da kare hakk'okin addini, a cewarta baza tayi sakacin da iyayenta suka yi ba wurin tarbiyyantar da  nata yaran.
   Cake d'in da ta ajje suka fara ci, amma banda ita, ta mik'e ta wuce d'aki domin duba result dinta. Cikin matsananciyar murnar da bata san adadinta ba, ta rungume strip din ta ruga da gudu da shirin fad'i ma SS, sai dai wata zuciyar taji tana shawartar ta da ta fad'a mishi in a romantic way.

  Murmushi tayi, ta koma tayi disposing abun, lokacin an fara kiran sallar maghriba tana fitowa ta ci karo da Rukayya da ta falfalo a guje ta shigo.

  "Ya Allah. Rukayya wai yaushe zaki hankali? Ina yarona?"

  "Sun je masallaci da Daddy."

  "Muje muyi sallan muma ko. Amma dan Allah ki rink'a natsuwa, kullun cikin gudu kike fa"

  Ta rik'e hannunta suka wuce ciki, zuciyarta cike da wani irin farin ciki, marar misaltuwa. A duniya ta na son yara. Tana son ta gansu suna yawo a tsakiyar palon ta, ta kalle su da murmushi, ta tabbatar duka nata ne.

***

  Suna gama sallar isha'i suka fita gaba dayansu, Kalam-wahid shopping mall suka nufa, SS na tuk'i amma hankalinsa gaba d'aya, yana kan Jay da ke zaune gefenshi, ya kama hannunta ya rik'e cikin nashi, fuskokinsu na bayyanar da sirrikan da ke cikin zukatansu.

  "What's the event?"

  Ya tambaya yana matso da bakinsa dai-dai kunnenta, yayi maganar yadda yaransu da ke baya baza su taba jin me ya fad'a ba.

  "Me ka gani?"

  "You look exciting. Shine nike son kiyi sharing moment din da ni."

  "I must be, tunda ina tare da kai. This is the event."

  Ta dago hannunshi da ke rik'e da nata, tana signing mishi da idonta.
  Murmushi yayi, a fakaice ya kai kallo ga yaran da suke ta wasansu, ya d'ago hannun nata yayi pecking, yana mata wani irin kallo, wanda a duk lokacin da ta ci karo da shi take tsintar kanta cikin mutuwar jiki.

  A dai-dai nan suka iso wurin, ya gyara parking duk suka fito, kafun ya shiga tsakiyar yaranshi, ya kama su da hannayensa suka wuce ciki.
  Sun kwashi kusan mintuna talatin a wurin, suka fito da kayan da suka siya, suka saka a boot, kafun suka karasa gidan Baffa.

Zaune suka same shi shi da Goggo a palonshi, da gudu su Jafar suka isa suka fada kanshi, Jay da SS da ke biye da su, suka karasa shigowa da sallama a bakunansu.

  "Haba mana so kuke ku k'arasa dan tsohon nan ne? Ku daga ni ku je ga wata kujera can mai laushi. Ta fini k'wari."

  Yayi maganar yana nuni musu da Goggo da ke fuskantarsu. Dariya duk suka saka har ita, suka k'araso ciki suka zauna tare da gaishe da su.

  Kallonsu Baffa yake cike da birgewa da sha'awa, haka ma Goggo zuciyarta ta samu natsuwa ganin yadda rayuwar tilon 'yarta ta samu canji cikin dan lokaci.
Sun jima a nan, kafun suka musu bankwana suka tafi.

  Ko da suka kai gida su Jafar har sunyi bacci, SS ne ya d'auke su d'aya bayan daya ya shigar da su ciki, Jay ta canja masu kaya zuwa na bacci, ta kai kowannensu dakinshi, ta tofe su da addu'a sannan ta fito.

  Bata ganshi a palon ba, sai kawai ta wuce dakinta domin yi wanka.
   Jakar da ke hannunta ta zubar saman gado, ta d'auki wani abu ta isa gaban wardrobe d'in SS, inda kayan baccinsa ke ciki, ta ajje a hankali tana murmushi, kafun ta rufe, ta cire kayanta ta wuce toilet din da ke cikin dakin.

  Tana gamawa ta fito ta shirya cikin olive green din silky nighty, ta tattara gashinta wuri guda ta daure da dan k'aramin ribbon, sannan tayi wanka da perfs, masu sanyin kanshi, ta tsaya tana kare ma kanta kallo, a lokaci guda tana shafa cikinta, she just can't believe it.
  Jin tafiyar SS yana kusanto d'akin yasa tayi saurin tattare kayanta da ta zubar saman gado, ta boye jikin labule tana kallon shigowarshi.

  A tsanake ya tura k'ofar ya shigo, kanshin turarenta ya sanya shi lumshe ido, ya bud'e amma bai ganta ba.
Gaban wardrobr dinsa ya isa, yana budewa ya ga d'an k'aramin abu, an wrapping da sheet, take ya sake kyakkyawan murmushi, ya dauka ya zauna a kujerar da ke gaban gadon, ya fara budewa.
  Baby's shoes ya gani masu kyau, had'e da paper da ta fad'o daga ciki, ya duk'a ya dauka ya fara karantawa.
 
  "I love you so much Ya Sadic. And I know you'll be the best father a child could ever have."

  Murmushin da ke fuskarsa ya k'ara fadadawa, yana tambayar kansa me hakan ke nufi?
Bai ida rufe bakinsa ba ta bud'e labulen da ta boye ta fito, a cikinta ta saka katon balloon da ta busa, hannunta rik'e da plain sheet da aka yi rubutu jiki, ta seta hannun a dai-dai cikinta.

  Cikin matsanancin farin ciki ya iso gabanta, da sauri ya duk'ar da kanshi setin cikinta, yana shafa katon balloon din da ta dora tare da karanta rubutun da ke jikin takardar.
 
  To Mr. & Mrs Galadima, I'm  sorry it took me kinda late to get here...

   "Yaa Allah! Is this for real Angela?"

  "Ehhhhn now!"

  Ta girgiza kanta bakinta kunshe da murmushi mai kayatarwa.
  Hannunta ya rik'e yana jin dad'i, ya rasa me zai yi ya nuna farin cikinsa.
  Kallonta kawai yake, idanunsa sun fara wani shining da alamar kamar ruwa a ciki, ya bud'e baki zai yi magana, ta had'a lips dinsu, tana mai zagaye hannunta a bayanshi.
  Hakan ya sanya shi gyara tsayuwarsa ya had'a ta sosai da jikinshi, a zuciyarsa yana yi mata addu'a da neman kariya daga ko wanne irin sharri.
  Sun dade a haka, sannan ta sake shi, ta fito mishi da pjs kalar sea green, ta wuce had'a mishi lipton, wanda ya kan sha a kowanne dare.

Lokacin da ta dawo kwance ta same shi ya rungume baby's shoes din da ta saka a kayanshi, idanunsa a lullube, da alama yana jin soyayyar babyn tun bai iso duniya ba.
  Sai da ta kare mishi kallo, sannan ta dora mug din da ta shigo da shi kan bedside locker, ta isa ta zauna gefenshi.

  "Tashi ga tea dinka Ya Sadic."

  A sannu sannu ya bud'e ido, ya sauke a kanta, bai ce komai ba ya janyo ta jikinshi, ta kwanta shiru, ba wanda ke magana cikinsu, bayan wasu 'yan mintuna ya mik'a hannu ya kashe fitilar da ta haskaka d'akin.

***Sadam.

  Sautin karatun al-Qur'ani mai girma ne ke tashi cikin k'ira'ar Sheikh Ahmad Sulaiman, yayin da Sadam ke zaune hannunshi rik'e da goran ruwa yana shirin saka magani a bakinshi, Saheeb ya tura k'ofar dakin ya shigo.
  Maganin da ke hannunsa ya k'arasa sakawa a bakin, ya kora da ruwa, sannan ya d'ago a hankali yana dubanshi.

  "Ya aka yi?"

  "Dama Ya Sa'id ne yace in zo in tabbatar idan ka sha maganinka."

  Murmushi yayi, wanda iyakacinshi fatar baki, hakan ya k'ara bayyanar da tsantsar ramar da fuskarsa tayi, ya ajje ruwan hannunsa a gefe, ba tare da yace komai ba.

  "Yace idan ka gama ka zo akwai maganar da zaku yi."

  "Ta me fa?"

  "Wallahi ban sani ba. Haka dai yace in fad'a ma."

  "Alright, ka je gani nan fitowa."

  Ya komar da kanshi jikin kujera ya jingine, tare da lumshe idanunsa, yana jin dad'in yadda karatun ke ratsa ko ina na jikinshi, yana zarcewa mishi har kasan zuciya.

 
  Mikewa ya yi, kafun ya ja remote ya latsa, ya mik'e ya fita kiran da Sa'id ke mishi.
  Yayyenshi guda hudu ya samu zaune a palon, ya isa ya mik'a ma kowannensu hannu suka gaisa, sannan ya tattare jallabiyar jikinsa, ya zauna a d'aya daga kujerun wurin.
  Shiru na 'yan dakiku ne ya wanzu a palon, daga bisani Sa'id yayi gyaran murya ya juya yana fuskantar shi.

  "Sadam."

  Ya kira sunanshi cikin natsuwa, da muryar da ke nuni da dattako, da kuma tausasawa.

  "Na'am Yaya."

  "Wato a gaskiya na gaji da ganinka cikin halin nan da kake ciki, saboda nayi believing depression yana k'ara tension ma mutum, yana hana zuciya da gangar jikin mutum su samu natsuwa. Haka ne?"

  Ya tambaya yana kallonshi.

  "Haka ne."

  Salis ya bashi ansa da sauri, inda shi kuma ya cigaba.

  "You need to move on Sadam, tun baka k'arasa kashe rayuwarka ba. Ka rungumi k'addararka, ka canja tsarin da kake shirin jefa kanka a ciki."

  A hankali ya d'ago yana kallonshi, take zuciyarsa ta tsinke, amma ya daure yace

  "Yaya ai na dade da yadda da irin k'addarar da Allah ya dora mun. Me sa kake magana haka?"

  A takaice Sa'id yace

  "Ka samu wata matar ka fara sabuwar rayuwa, wannan ne kawai zai tabbatar mun da cewar ka yarda da k'addararka."

  Murmushi yayi mai zafi. Domin bai san abinda zai ce a wannan gabar ba.

  "Wato dariya ma abin ya baka ko?"

  "No, ban san me zan ce bane Yaya, kuma ni a yanzu babu wata mace da zan iya kallo ince tana birge ni."

  "To ni na samo maka, kuma bana son wani dogon bayani, ka ansa mun da ka amince kawai."

  "Amma Yaya.."

  "Amma me? A haka zaka karaci rayuwarka ne Sadam?"

  A hankali ya sassauta murya yace

  "Shike nan, na amince."

  Ba tare da ya san wacece matar da suka zaba mishin ba.

  "Masha Allah."

  Suka had'a bakinsu suna fad'a, daga bisani suka fitar da kudin da bai san adadin su ba, Salis ya mik'a mishi.

  "Wannan shine rabon gadonka wanda aka kasafta lokacin da kake asibiti, ina shawartarka da ka samu business din da zaka fara wanda zai taimaka maka ka tsaya da kafafuwanka, ita dai duniya ba matabbata ba ce ba. Allah yasa mu dace."

  "Amin amin."

  Suka ansa, kafun Sa'id ya cigaba.

  "Na riga nayi magana da mahaifin yarinyar, dama amincewarka kawai nike jira, dan haka next week idan Allah ya kaimu za'a daura aure."

  "Allah ya kaimu lafiya."

  Duk suka mik'e suka fita, suka barshi zaune yana da-na-sanin halaye irin nashi, inda ya rink'a jin inama baya zata dawo, da kuwa ya shimfida rayuwarsa bisa tsari na addinin islama.

  Hawaye ne suka wanke fuskarshi, ya shafe su a hankali, ya mik'e ya koma dakinshi, amma sai ya zamana tamkar an k'ara turo wasu sababbin hawayen ne. Kukanshi yayi mai isarshi, ya gama, sannan ya tashi ya fita jin kiran sallar maghriba da aka fara.

***
  Kamar yadda Sa'id ya fad'a, ranar juma'a ana gama sallah aka daura auren Sadam da amaryarshi Farida, wacce har a lokacin bai san ta ba, illa sunanta kawai da ya sani.
  A part d'in mahaifinsu amarya ta tare, bayan sunyi walimarsu ya su, ya su, dare na yi 'yan uwanshi suka rako shi d'akin amarya.

  A hankali ya tura kanshi cikin palon, gabanshi na tsananta bugu, ya yaye labulen tare da tura kanshi ciki.
  Zaune ya hange ta ta bashi baya, illa daurin kallabinta na ture ka ga tsiya da ya ansa mishi sallama.

  Jiki babu k'wari ya zagaya gabanta, chewing gum take taunawa k'as-k'as, tana ganinshi ta mik'e da sauri ta iso gabanshi.

  Cikin tashin hankali Sadam ya k'walo ido waje

  "Fareeda?!"

Murmushin 'yan duniya ta saki, ta cigaba da nufo inda yake tana shirin unbutton rigarshi.

  "Ni din dai ce. Ka ga yadda Allah yayi nashi ikon ko."

  "No please, you must be kidding."

  "I'm not Kazaure. Allah ne ya kashe ya bani."

  "Ke dallah dakata mun malama. Ina kike tunanin zan kai mace  irinki wacce tayi aurarraki har ban san adadinsu ba."

  Shewa ta saki, ta k'ara hankado kallabinta gaba tace

  "Da na taimaka maka din? To jira ka ji, ni din nan dai nice babu sauyi, kuma zama daram dam a cikin gidan nan, dan dama na dade ina mararinka tun muna 'yan yara."

  "Oh Allah!"

  Shi kadai Sadam ya iya fad'i, ya zube a kujera yana dafe kanshi. Ya san wacece Fareeda, tare suka tashi tun suna yan yara take crushing dinshi, a ganinshi ba ta da qualities din matan da zai iya so kaf a duniyarshi.
Cikin karairaya ta juya tana cewa

  "Kayi ka gama ka zo nan ka same ni, mazaunai nike, dole a zauna da ni. Ba saki ba kuma yaji. Ehee."

  Zuciyarsa cike da damuwa, ya kira wayar Sa'id, yana dauka ya fashe da kuka

  "Haba Yaya, ka rasa wacce zaka had'a ni da ita Sai Faree Social, macen da duk unguwan nan babu wanda bai santa ba da shegen aure-aure. Ni wallahi ban san ya zanyi da ita ba."

  "Daurewa zaka yi ku rufa ma kanku asiri ku zauna lafiya."

  Daga nan ya kashe wayar, ya bar Sadam da cizon yatsa.
  Bashi da yadda zai yi din, dole ya tashi ya bi ta a baya suka shige the other room.

KADUNA

***Four years later***

Excuse the mess, the children are making memories...

  Wadataccen palo ne mai girman gaske, wanda ya kawatu da kayan jin dad'i na more rayuwar dan Adama.
A k'asar lallausan kapet d'in da ke shimfide text books ne kusan guda goma a barbaje ko wanne ya kama gabanshi. Tarkacen su pencils, sharpeners, cleaners da kuma school bags guda ukku yashe a tsakiyar palon
Ta 6angaren haggu kuwa d'an k'aramin cup ne da spoon an had'a cereal an sha rabi, an zubar da rabi a k'asa, ga kuma saura an bari a cikin cup d'in da wasu kananan teddies, da whistle na wasan yara duk a wurin.
  Ta gefen dama yaro ne da zai kai shekaru tara duk'e yana faman rubutu, da alama homework din mai matuk'ar muhimmanci ne, ganin yadda yara ke guje-guje a tsakiyar palon amma shi ya natsu ga aikin gabanshi.
  Da gudu yarinyar da zata yi shekaru takwas ta biyo 'yar k'arama mai shekarun da baza su wuce hudu ba, hannun k'aramar rik'e da mug mai tea a ciki, ta ruga da nufin kauce ma wacce ta biyo tan, cikin rashin sa'a ta fad'a ma Jafar da ke zaune yana rubutu, take mug din ya fadi kasa, ya fashe, tea din ya watse a tsakiyar palon.
  Dagowa ya yi yana kafe ta idanunshi, ya mike da azama yayi kanta, da saurinta ta mik'e ta zura da gudu, itama Rukayya da ta biyo ta ganin ya tunakaro su, ya sa ta juya da gudu, a sa'a guda suka yi kicibis da Jay da ta fito hannunta d'auke da fine boy din da bai wuce watanni takwas ba, idanunsa da kalar lips dinshi, tamkar ace SS ne lokacin da yake k'arami.

  "Da gani wannan laifinki ne Rukayya. Me kuka mishi?"

  Ta kalli Rukayya da tayi girman ban mamaki tana tambayarta.

  "Wallahi Mammy ba ni bace, Fatima ce ta d'auke mun pencil zanyi homework, na bita in ansa shine ta fad'a ma Ya Jafar ta fasa mug ta zubar mishi da tea a kan text book."

  Kunnen 'yar k'aramar ta kama,

  "Ke na rasa wace irin 'ya ce wallahi, me sa kika je kika zuba ma handsome tea jikin littattafai?"

  Kuka mai karfi Fatima ta saka, Jay ta turar da ita, ta isa ga Jafar da har yanzu yake cika yana batsewa.

  "Haba mana handsome nawa, kayi hak'uri mana, kai fa big bro ne. Baza su k'ara ba."

  "To Mammy duk laifin Rukayya ne fa, ita ta tura ta ta fad'a mun fa, ni gaskiya bazan yadda ba."

  "Ku zo nan."

  Jay tayi kiran Rukayya da Fatima, suka iso ita tana kuka, ita kuma tana tura baki tana ma Jafar kunkuni.

   "Ko wacce ta ba shi hak'uri, if not ke zaki share palon nan gaba dayanshi."

  Ta k'arasa tana nuna Rukayya.
  Da sauri suka had'a baki suna bashi hakuri, ya kwashe da dariya ganin yadda 'yar lukutar fuskar Rukayya ta mairairaice tana begging dinshi.

  "Kun sila yara, ku tashi ku je wasanku."

  Ta mik'e tana harararshi ta k'asar ido, tana juyawa ta ci karo da SS da yayi tsaye bakin k'ofa yana kallon duk me suke yi.

  Da gudu suka yi kanshi, ya daga Fatima yana dariya, yaron da ke hannun Jay ma yana ganinshi ya fara daga hannu yana wangale baki.
  Tana ajje shi ya rarrafa ya isa gabansu, ya ajje Fatima ya daga shi sama yana juyawa, yana kallon yaron da ke ta wangale baki ba tare da ya san komai ba.

  Hannun Jafar ta kama suka isa gare su, ta gefen damarshi ta koma ta tsaya, ya sanya hannunshi ta baya ya tallabi kafadunta, yana kallonta dauke da murmushi a fuskarsu, yaran suna tsaye, zagaye da su.
Wani tsantsan dad'i marar misali Jay take ji a ruhinta, yau ga ta tana rayuwa dai-dai da mafarkin Baffanta, ta gina iyalinta nata, na kanta wanda suke cike da kwanciyar hankali da soyayyar junansu, ga shi tana gab da kammala karatunta, a zahiri bata da abun da zata ce illa Alhamdulillah a ko wanne lokaci.

Muryar Jafar ce ta katse mata tunaninta, ta jiyo shi yana cewa
  "Daddy kawo shi mana, kaga so yake in d'auke shi nima."

  Ya mik'a hannu ma yaron, babu gardama ya mik'a masa shi, ya juya zai yi ma Jay magana suka ji yo knocking a bakin k'ofar palon.
   Rukayya ta ruga da gudu ta bud'e ga mamakinta, ta ga Daddy Kazaure da Aunty Faree, har ma da 'yar cute baby mai kama da babanta.
  Kallon-kallo aka fara yi tsakaninsu, domin wannan ce haduwarsu ta farko, bayan shekaru biyar da suka gabata. Daga bisani SS ya isa ya dan daki kafadar Sadam, ya bud'e hannayensa, shima ya bud'e nasa, suka shige cikin jikin juna, sannan suka rufe yana fad'in

   "Long time bro?..."

  Wani sabon knocking din ne ya katse su, Rukayya ta k'ara komawa ta bud'e. Miemie ce ta fara shigowa, da mamaki take kallon mutanen da ke tsaye tsakiyar palon, a lokaci guda ta saki dariya tace

    "Surprise.."

  That fine bobo na dinner su Jay abokin SS mai suna Salim ya bud'e k'ofar ya shigo.

   "Here come my fiancee."

  Duk suka sanya dariya, suka fara gaisawa da SS, sannan suka gaisa da Kazaure, suka koma kan kujeru suka zauna, nan da nan gidan ya k'ara hargitsewa da hayaniyar yara da ta manya.
Hannu Kazaure ya mika da shirin daukar dan yaron da ke hannun jafar, ba musu ya iso gare shi, ya daga shi sama yana kallon SS,

"Sadam.."

SS ya fada yana shafa kan yaron.

"I can't believe this. Kana nufin is yi mun takwara kenan?"

"What are friends for?"

SS ya yi maganar yana daidaita zamanshi.
   Jay, Miemie da Faree Social ta wajen Kazaure suka wuce kitchen domin kawo masu abin sha.

**Verily, with every HARDSHIP, there is ease. (Q94:V06)**

Thank you so very much guys for giving SSDN a chance. I truly appreciates y'all maximum support.

Allah Ya gafarta kurakuren da muka yi, Ya sa jama'a su amfana da darussan da muka rubuta. Amin.

Best regards, Lubbatu_Maitafsir 😍👌

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro