BABI A ARBA'IN DA UKKU
Ranar ta kasance juma'a, yayin da daurin auren ya kama k'arfe biyu dai-dai na rana a babban masallacin juma'a dake garin Daura inda kakanta Mal. Baba ke limanci.
Da misalin k'arfe goma sha d'aya na safe k'ofar gidan na Baffa ba masaka tsinke, sai ka dauka anan za'a daura auren, al'umma ce bila-adadin, baza su k'idayu ba, a haka ma da yawa daga cikin mahalarta daurin auren sun dade da isa Daura.
Tunda gari ya waye Jay bata fito a d'aki ba, kuka take bil hak'k'i da gaskiya, tayi har ta gaji, ba tare da jama'ar gidan sun ankara da yanayin da take ciki ba.
Sudanese din da ke mata gyaran jiki ce ta shigo da hadaddiyar khumra ta mik'a mata, tare da cewa ta shiga tayi wanka da ita.
Ba musu ta ansa ta wuce toilet tayi wanka fitowar da zata yi taga Miemie zaune a bakin gado tana aika mata harara.
"Baki da mutunci wallahi. Yanzu ke da Goggo bata sanar da Hajiya ba da sai dai inji labarin kinyi aure ko? Wai me kika d'auki friendship dan Allah? Abun wasa ko? To jira kiji Allah zai iya kama ki da laifi ta wannan hanyar."
Murmushin karfin hali tayi, ta k'araso bakin gadon ta zauna jikinta daure da towel.
"Baza ki fahimta ba Miemie."
Da sauri ta katse ta
"Ai bance zan fahimta ba dama, dallah tashi ki saka kaya ni ba excuse dinki nike son ji ba, tafe nike da Khady's Maquillage zata tsantsara miki make up, dan nasan ke kam ba gwanar shi ba ce ba."
"And who ask you to bring her? To ku tattara ku kama gabanku dan ni ba wani make up da zanyi babe."
"Wannan ne fa baki isa ba, dole ta gyare ki yanzu na daurin aure, kafin kuma na anjima idan zamu fasa dinner."
Bata jira ansarta ba ta juya da sauri tana kiran make up artist d'in.
Lokacin da suka shigo ta saka skirt and blouse na purple and cream din super Sheraton, dinkin ya zauna yadda ya kamata a jikinta, tun ba'a kai ga fara fentin fuskar ba, ta fara wani irin sheki da annurin haske.
"Make yourself comfortable Cute, wannan crazy amaryar ba kirki ta cika ba."
Miemie tayi maganar tana kallon Khady. Ita dai bata ce komai ba, murmushi tayi tana ta kallon Jay, tare da yaba kyau da haduwa irin nata.
"Ya kike?"
Jay ta juya da murmushi tana kallonta.
"Lafiya lau, ya aiki?"
"Alhamdulillah. Idan kin gama gara mu fara dan zamu iya kai two hours bamu gama ba."
"Ina zuwa please, sai dai bana son heavy make up naturally, ki mun light one kawai, shima dan stubborn girl din can ta matsa."
"Oho dai, ana so ana kaiwa kasuwa, abeggi ki sauri ki zo dan nima nan so nike a cancare ni."
Dariya suka yi gaba dayansu, a lokacin ta gama tattara gashinta ta kama da ribbon, sannan ta iso gabansu ta zauna aka fara shafe-shafen.
Karfe d'aya dai-dai ango da bataliyar abokanshi suka iso harabar gidan, ya fito cikin takun isa da kasaita, ya hade cikin danyar farar shaddar Gezna, babbar riga da yar ciki da wando, an zuba wani sassanyan ash din aiki a gaban rigar, kafarshi lullube cikin rufaffen ash din takalmin Kenneth Cole masu masifar tsada, hular PMB da aka sak'a da ash din zare zaune saman kanshi, yayin da wani irin haske da kwarjini ke zuba a jikinshi, duk kuwa da fadawar da idanunsa suka yi.
Baban palon gidan suka tasar ma, sun kai su ashirin, a waje suka dakata, shi kuma ya tura kanshi ciki babu wata fargaba ko faduwar gaba a tare da shi.
Zaune take fuskarta lullube da mayafi, ya iso a kasaitance ya zauna a kujerar da ke fuskantarta.
Ganin bata da niyyar magana, yasa shima ya ja bakinshi ya kulle, domin kuwa ya zo da shirinshi na komai ta fanjama fanjam.
A hankali ta sauke mayafin, ta d'ago da manya-manyan idanunta da Khady's Maquillage ta k'awata da mascara da eyeshadow ta sauke a kanshi.
"Barakallahu fih ahsanil khaliqiiin."
Kalmar da SS ya iya furtawa kenan, a lokaci guda zuciyarsa ta buga dam, tamkar zata fasa k'irjinsa ta fito.
Dak'yar ya dai-daita kanshi, ya juyar da kai, sannan ya maida kallonsa ga silver agogon dake daure a hannunsa.
"Ban san me kike son sanar mun ba. Kin fi kowa sanin a kan hanya nike kuma tare da mutane."
Abinda ya faru da shi, shine ya faru da ita, sai dai har zuwa yanzu zuciyarta bata daina harbawa da sauri ba, domin kuwa a yadda take kallonshi yanzu ji take tamkar bata taba ganin halittar namijin da ya kaishi kyau da cikar kamala ba, duk kuwa da fadawar da ta lura idanuwansa sunyi, wanda ta tabbatar hakan ba zai rasa nasaba da uk'ubar da ta jefa shi a ciki ba, take ta manta dalilin da yasa tace tana son ganin nashi ma.
Ganin bata da niyyar magana yasa ya mik'e, fuskarsa ba yabo ba fallasa, a karo guda ya tura hannuwansa a aljihun rigarsa ta ciki, ya tsaya tare da buda k'afafunsa, hakan ya k'ara k'ayatar da cikakken zubinshi a idanun Jay, sai dai bata da bakin da zata yabe shi.
A tausashe ya fara magana ba tare da ya dubi inda take ba.
"Nasan kina da wanda kike so, ina kuma sane da cewar aure na da ke had'i ne na su Baffa. Ban manta da cewar baza ki taba iya rayuwa da ni ba ko da ni kadai nayi saura a doron k'asa. Ban kuma manta da cewar baza a miki dole ba. Sai dai ina so ki sani ba wannan bane zai sa in watsa k'asa a idon mahaifinki ba. Ba wannan ba ne zai hane ni tafiya d'aurin auren da akai miki dole ba, dan nasan abinda kika kira ki tuna mun kenan. But da zaki birge ni, da sai ki daga waya ki sanar da mahaifinki cewar baza ki iya aure na ba kafin in isa, na san wannan ce kawai hanyar da zata sa su fasa abinda suke shirin yi, tunda ba za suyi miki dole ba, nima da kin yi mun gagarumin taimakon da zanyi ta zuba miki godiya har karshen rayuwarmu, cuz zaki saving dina daga fadawa auren matar da babu ko da digon soyayyata a ruhinta."
Bai jira ansarta ba, ya juya zuwa inda bataliyar abokanshi ke tsaye, suna ganinshi suka fara tsokanarshi, ya maze ya fara bouncing, yana wata makirar dariya ya iso suka shige motocinsu, suka d'auki hanyar ta Abdu tushen Hausa.
Suman zaune Jay tayi, bata ankara ba ta ji wani ruwa-ruwa kwance saman kuncinta, tasa hannu ta shafa da sauri, hawaye ne suke kwarara a idanunta.
Me hakan ke nufi? Ta tambayi kanta.
Ba tare da ta samu ansar ba ta mik'e da sauri da niyyar bin bayanshi, amma ina bata tarda kowa ba illa k'urar da motocinsu suka tayar.
Jiki ba k'wari ta koma cikin palon ta zauna, tunani kala da kala sun cika zuciyarta, ta san muddin ta rasa namiji irin SS baza ta taba samun kamar shi ba, kamar yadda ta san ko ta sha giyar wake baza ta taba iya sheda ma Baffa ta fasa aurenshi ba, haka kuma ko da ita Sadam ne mutane biyun da suka yi saura a duniya baza su kuma zama a k'ark'ashin inuwa d'aya ba.
***Daura.
K'arfe biyu da mintuna goma sha biyar dai-dai aka daura auren.
Tsabar farin cikin da SS ke ciki, Allah kadai ya sani, haka ya fito suka fara gaisawa da mutane suna yi mishi fatan alkairi da samun zuri'a ta gari, daga nan suka wuce Daura Motel inda Baffa ya shirya musu reception, aka ci aka sha, tare da addu'o'i da neman zaman lafiya.
Suna gama sallar la'asar suka d'auki hanyar Ta Dikko d'akin kara.
***
Ko da suka dawo bai bi ta kanta ba, gida kawai suka zarce suka je suka cigaba da shirye-shiryen dinner su, ya dai san koma menene bata da yadda zata yi da shi yanzu, tunda ta riga ta zama mallakinshi.
Shigowarsu kenan Farouq ya tare shi da sauri, hannunsa d'auke da manyan ledoji guda biyu ya mik'a mishi.
"Wai Yaya ka manta da kayanku na dinner ne? Tun safe ina can ina jiran isowarsu."
"Ya Allah. I'm so Glad to have a bro like you. Wallahi na manta. Yanzu komai ya iso ne?"
"Eh komai yayi ready, ga naka nan, wannan na amarya ne ka dauka ka je ka kai mata dan kar ma tayi tunanin sanya wasu kayan."
"Haka ne Farouq, ka shige da nawa, barin samu wani ya kaini."
Ya d'auki ledar kayan yana waige-waigen neman daya a cikin abokanshi da zai mik'a shi gidansu Jay, amma bai samu dole ya kira wayar Farouq yace ya kawo mishi key din mota kawai ya je da kanshi.
Motarshi na shiga motar su kazaure na tura kai a harabar gidan, ya fito hannunshi rik'e da ledar kayanta, yayin da Saheeb k'anin Kazaure ya gyara parking, suka fito hannunshi cikin na Rukayya.
Gabansu SS ya k'arasa ya mik'a ma Sadam hannu suka gaisa.
"How you Daddy's girl?"
Ya duk'a yana shafa kan Rukayya.
"Daddy ina Jafar? Nima ya zo ya ga sabon Daddy na."
"Oh no please. Ni kuma fa?"
"Kai ai Daddyn Jafar ne inji Daddy na ko?"
Ta daga kai tana kallon Kazaure wanda kwata-kwata hankalinshi baya tare da su, jin wasu matasa guda ukku da suke doso inda suke tsaye suna cewa
"Muje ga angon can ma."
Gabansu suka iso suka mik'a ma SS hannu, tare da fad'in
"Allah ya bada zaman lafiya."
"Amin nagode."
Ya fad'a da murmushi sai a lokacin ya ci karo da fuskar Kazaure da ya k'ura mishi ido yana jifarsa da wani mahaukacin kallo.
K'asa yayi da idonsa, a sa'ar da ya kafe shi da nashi idanuwan yana jiran k'arin bayani.
"I'm sorry Kazaure, aurena da Jay Allah ne kawai ya hada shi, wannan ne kawai abinda zan iya cewa."
Daram dam, zuciyar Sadam ta buga tun k'arfi, wato da gaske auren suka yi.
Bud'e baki yayi zaiyi magana, ya ji k'irjinshi ya rik'e, da sauri ya dafe ya duk'e a wurin yana wani irin numfashi.
Jajayen idanunsa ya d'ago, take hawaye suka fara shatata, murmushin k'arfin hali yake da bakinshi da ya bubbushe tsabar wahala yace.
"Thumbs up Tafseer. You did a great job."
Yayi nuni mishi da babban dan yatsarshi yana jinjina mishi.
"No please, kada kace haka mana, abinda Allah ya riga ya tsara kenan Kazaure, none of us can deny this fact. Haka Allah ya tsaro mana rayuwa."
"Indeed."
Ya fad'a yana girgiza kai, wasu zafafan hawaye na kwararo mishi, ya mik'e da sauri ya tunkari inda suka yi parking, SS ya bi bayanshi yana kiranshi amma ina bai tsaya saurarar shi ba, ya bud'e gaban motar ya zauna, kanshi ya kifa a tsakankanin kafafunsa yana wani irin azabtaccen kuka, nan da nan idanunsa suka yi jajur, ya d'ago yana duban SS da hankalinshi gaba d'aya ya gama tashi a halin da ya ga Sadam.
"I'll never forgive you Tafseer. We've been friends for so many years, amma kayi betraying dina ko? Ba zan taba yafe maka ba."
Kafin SS yace wani abu tuni ya juya da wata tsawatacciyar murya yana ce ma Saheeb
"Start the damn car!"
Rukayya na kuka tana musu magana, amma basu saurare ta ba, a razane ya tada motar suka bar harabar gidan, SS ya bi bayansu da kallo, zuciyarsa taf da tausayin abokin nashi, sai dai ya san tabbas ba shi da qualities din da zai sake zama mijin Jay for the 2nd time.
Bai ma shiga gidan ba, ya samu wata ya hada hannunta da na Rukayya tare da akwatinta da suka ajje, ya bata kayan Jay yace ta kai mata, ya cire wayarsa ya typing mata text, kafin ya juya ya shiga motarshi ya bar gidan shima.
***
K'arfe bakwai na dare aka d'auki amarya zuwa gidanta da ke Barhim Housing Estate, babu nisa sosai da gidan Hajiya.
Gida ne k'aton gaske, part biyu ne kowanne part d'auke da manyan bedrooms guda ukku da parlour biyu, da kitchen, da toilets a kowanne d'aki, sai wangamemen guest parlour a tsakiyar parts din guda biyu, an k'awata ko ina da kayan alatu na jin dad'in rayuwar dan Adam.
Kuka take tamkar karamar yarinya, majina ko ta ina tana tirjewa, amma haka aka tura ta k'uryar dakinta, 'yan uwa da Hajiya Miemie babbar k'awa zagaye da ita suna ta mata iskanci.
Tara na dare kowa ya gama shirin tafiya dinner, in banda amarya da ko motsawa ta k'i tayi daga inda take zaune.
Sai da wata k'anwar Goggo tayi mata tatass, sannan ta mik'e tana zunbure baki tayi wanka ta fito, Khady's Maquillage na zaune a gefe ta k'ara tsantsara mata kwalliya, Miemie ma ba'a zauna a baya ba, ta matso aka gwangwaje ta, nan da nan d'akin ya dau sheki da wani lafiyayyan kanshi na wata kalar khumrar da Jay tayi amfani da ita.
Kayan da SS ya aiko mata Miemie ta d'auko ta iso gabanta da su, ta zazzage saman gado.
Tail gown ce ta light Brown din bridal material mai masifar tsada, ta sha kyau har ta gaji, sai light Brown din high hills da clutch dinsu k'irar Jimmy Choo, sai golden necklace, earrings, bracelet da wristwatch suma a cikin wani dan k'aramin akwati.
Bayan ta saka, Cute ta tying mata head, ta gama gyare ta tsab-tsab, cikin d'an lokaci ta fara haskawa tamkar fitilar lantarki, illa rashin murmushi a fuskar tata.
Goma da 'yan mintina anguna suka iso aka fara jidar 'yan mata da iyaye da duk wanda zasu halarci dinner.
Liyafa palace suka dosa, a gefe guda, Miemie ce tare da wani fine bobo abokin ango sun jero, su suka take ma Jay da SS baya suka haura cikin hadadden decorated hall d'in.
Bayan Hajiya Sauda kanwar Goggo ta gama kwarara addu'o'i ga ma'auratan na neman zaman lafiya da zuri'a dayyiba, aka shiga cikin programs gadan-gadan yayin da MC ya umarci masu d'aukar selfie da suka yi tsaye cirko-cirko da su matso kusa. Bayan nan MC ya buk'aci ganin ango da amarya a tsakiyar fili.
Kallonta SS yayi fuskarsa d'auke da lafiyayyen murmushi ya mik'a mata hannunsa alamar ta taso su fita.
Kallonshi tayi ta juyar da kanta, da alama bata da niyyar bashi hannun kamar yadda bata da niyyar mik'ewa.
Tashi yayi daga seat dinshi ya zagaya ta gefenta, bai damu da yanayinta ba, ko kallon da jama'a suka tsare shi da ba, abu daya ya ke tunawa, yin hakan bai saba ma shari'ah ba. Hannunta ya kama, ya mik'ar da ita, a lokaci guda ya sanya dayan hannun yana tattare tail din rigarta da ya shimfidu a tsakiyar wurin.
Wani irin birgewa yayi, hakan yasa wurin ya kaure da ihu, cikin jin kunya ta dora hannunta a kan nashi, tana kallonshi cikin wani salo mai wuyar fassaruwa, suka k'arasa cikin filin.
Flasher ce ke tashi ko ta ina, a tsanake suke taka rawarsu ta masoya har suka gama, suka koma seat dinsu kafin aka fara ciye-ciye ta tande-tande.
***
Har suka iso gida babu wanda ke ma dan uwanshi magana, illa wani irin shock da suke fuskanta daga hannayensu da ke cikin na juna, suna jin yadda zuciyoyinsu ke harbawa da soyayyar junansu, sai dai babu wanda ya iya daga bakinshi, balle ya fayyace ma dan uwanshi sirrin da ke kasan ranshi.
Bayan Farouq ya gyara parking, ta juya idanunta a narke tana kallonshi, hakan yasa ya sake mata hannunta da ke cikin nashi, da sauri ta bud'e motar ta fice, ajiyar zuciya ya sauke, shima ya bud'e nashi 6angaren ya fito suka yi bankwana da Farouq, sannan ya juya zuwa ciki.
Tun daga parlour ya fara rage babbar riga da hular da ke kansa, ya rik'e a hannu yana tasan ma part d'inta.
A rufe gam ya tar da k'ofar da makulli, ya tsaya da mamakinshi yana kallon k'ofar, bai iya yin komai ba ya juya ya shige nashi b'angaren yayi wanka ya kwanta yana tunanin wane irin zama ne za su fara haka.
Dak'yar bacci yayi awon gaba da shi bayan ya yi wanka ya canja kayan jikinshi, ba shi ya farka ba sai da ladan ya k'walla kiran sallar asuba a masallacin da ke gefen gidansu.
Mik'ewa yayi da salati, ya shiga yayi alwala ya fita ya wuce part dinta, ya manta da k'ofar na rufe, sai da ya murda sannan ya tuna, ya koma ya ciro keys din jikin tashi k'ofar ya duba extra nata da ke had'e da nashi, ya bude, ya shiga ya zarce dakinta.
K'aran AC kawai ke tashi, sai k'anshin turarenta da ya had'e da na air freshner mai masifar dadi. Fitila ya kunna, a lokaci guda haske ya gauraye dakin, baccinta take tamkar bata da sauran damuwa, ya zauna a gefe ya tsura ma kyakkyawar fuskarta ido yana kallonta.
Juyin da tayi ne yasa shi saurin mik'ewa ya fara tashinta
"Jay."
Yana yi yana dan bubbuga blanket dinta, ta bud'e idonta a hankali ta sauke kanshi.
"Ki tashi kiyi sallah."
Daga haka ya juya ya fita, ya barta da mamakin yadda akayi ya shigo mata, dan ta tabbatar da sai da ta rufe k'ofar lokacin da ta shigo.
Toilet ta wuce ta d'oro alwala ta fito ta fara gabatar da raka'atanil fajr, tana gamawa aka tada sallah, ta tashi ta bi jam'i, suka gama, yayin da tayi zaune a wurin tana azkar, har zuwa k'arfe shidda, sannan ta mik'e tana k'ok'arin nade abun sallar.
A dai dai lokacin ya dawo daga masallaci, ya shigo ta part dinta domin ya tabbatar da ta yi sallar. D'akin nata ya shiga, ganinta a tsaye ya sanya shi tsayawa a bakin k'ofa yana k'ura mata idanu.
Jin kamar alamun mutum, ya sanya ta juyawa, idanunsu suka hade cikin na juna.
Da sauri ta sauke nata, bata ce komai ba, ta maida kai ga abinda take yi.
A hankali ya k'araso ciki, ya tsaya bayanta tare da ansar abin sallar hannunta, bai damu da yadda take bata fuska ba, ya zare hijabin jikinta, yasa hannu yana shafa dogayen hannayenta, cikin murya marar k'arfin amo, yace
"Good morning Angela."
Tsigar jikinta gaba d'aya suka mik'e, wani abu ya taso tun daga cikin kanta, ya sauka a babban yatsar k'afarta, da sauri ta k'wace jikinta, tayi gaggawar isa bakin gado ta kwanta ba tare da tace da shi uffan ba.
Tsaye kawai yayi, baki bude, zuciyarsa na harbawa da gaggawa, yana tunanin dalilin da yasa take k'yamatarshi har irin haka mana.
Gaban nata ya isa ya duk'a yana kallon yadda tayi kicin-kicin da fuska, ya sauke ajiyar zuciya tare da kama hannunta yana duban k'wayar idonta da suke shirin zubar da hawaye.
Ganin hakan yasa ya sake hannun nata ya mik'e kawai ya fita a sashen nata baki daya.
Tana jin yadda ya buga k'ofar palon, ta fashe da kuka, ita kanta k'arfin hali kawai take yi, ta rasa menene abinda ke damunta, domin kuwa ji take zuciyarta na harbawa da sauri, a hankali ta saki dan murmushi, ta koma ta kwanta tana sinsinar k'anshin turarensa da ya gauraye dakin har ma ya dusashe nata, ta lumshe ido, tana tunano yadda take son namiji dan gayu mai k'anshi, wannan na daya daga cikin abubuwan da suka sa Kazaure ya tafi da ruhi da imaninta
Throw pillow din 1pda ke gefe ta janyo ta rungume, har yanzu k'anshin bai bar hancinta ba, tunanin yadda rayuwarsu zata fara ta tsunduma, a haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Bata farka ba sai wurin sha d'aya, ta sha wankanta tare da tsantsara kwalliya, kwata-kwata ta manta da batun SS, wanda ya kamata ace ta bashi breakfast tuntuni.
Da sauri ta wuce kitchen ta fara kalle-kalle dan bata ma san mai zata fara ba.
Wata dabara ce ta fad'o mata, ta koma daki da sauri ta dauki wayarta, ta kunna data ta shige whatsapp. Group dinsu na Ladies Domain ta leka, dan ta san can ne kawai zata samu recipe cikin gaggawa, cikin sa'a kuwa taga Yasmeen ta turo recipe na Omalet Sandwich.
A gurguje ta karanta, ta tashi ta koma kitchen ta bud'e k'atuwar deep freezer dake girke, ga mamakinta ta samu fresh kayan miya, bata b'ata lokaci ba ta ciro albasa, attarugu da tumatir, dai-dai buk'atarta, ta yayyanka, sannan tasa oil kadan a pan, ta zuba kayan miyar ta saka spices ta soya sama-sama, ta ajje gefe.
Egg and milk ta had'a wuri guda, ta kada, suka had'u sosai sannan ta fito da toaster, ta fara zuba soyayyun kayan miyar a kowanne column, daga bisani ta zuba k'wan, ta rufe, sannan ta jona ruwan zafi a kettle.
Cikin 'yan mintina ya gama yi, ta kwashe a warmers, ta had'a kayan tea a tray ta hada ma SS nashi, ta dauka zuwa sashen da ta tabbatar nan ne nashi.
Da sallama ta tura k'ofar ta shiga, palon shiru babu alamar mutum, sai k'aran television kawai, ta isa ta ajje tray a dinning table, ta juya ta fito.
Ta dawo ta zauna ta na cin1 nata abincin.
*****
Har kusan k'arfe biyu bata ji motsinshi ba, har ta gama hada lunch, ta dauka ta kuma shiga part d'in ta zarce dinning, amma yadda ta ajje na safe haka ta same shi, sai ta ji wani iri, amma ta maze ta d'ora wanda ta shigo da shi, ta kwashe wancen ta koma ta kwanta, dan abincin ma kasa ci tayi tana tunanin abinda ya hana shi cin nashi abincin.
Wayarta ta d'auko ta fara dialling number sa, dan ya fara bata tausayi, haka kuma ya kamata ace ta sassauta horon da take bashi.
Ta kira har ta gama ringing bai daga ba, ta tashi ta koma palonshi, ta zarce bedroom, duk ta duba har toilets, amma baya nan.
Dakin ta kakkabe ta gyara komai a wurinshi, sannan ta fito jiki ba k'wari ta koma dakinta ta kwanta ta rasa me ya kamata ta yi a lokacin.
Har aka yi maghriba aka yi isha'i amma bata ji alamar dawowarsa ba, ta kira shi ya fi a k'irga nan ma bashi da niyyar dagawa.
Har goma tayi, ta gaji da yi ma bakin da ke zuwa ganinsu karya, ta kuma ga ji zama a palon, mikewa ta yi ta wuce d'aki tayi wanka ta shirya kanta, amma zuciyarta sam babu dadi, babban abinda ke damunta shine yadda ko gaishe da shi bata yi ba da safe.
Haka ta kwanta sukuku, sai can wurin sha biyu, sannan ta ji shigowar motarshi, ta tashi ta lek'a ta window tana kallonshi.
A idonta ya shigo cikin gidan ta koma ta kwanta tana tunanin may be zai shigo ya duba ta.
Shiru-shiru bata ji motsinsa ba, ta fara latse-latsen wayarta, har sai da ta ji cikinta ya fara kuka sannan ta tuno da rabonta da abinci tun breakfast, a kasalance ta mik'e, ta zari rigarta da ke gefe ta dora a kan 'yar k'aramar nighty din jikinta ta fita zuwa kitchen.
***
Yana shiga ya hangi jerin warmers saman teburi, ya isa da sauri ya bude, kamshin abincin ya daki hancinsa, duk da ba yunwa yake ji ba amma sai da ya ji marmarinshi, haka dai ya daure ya rufe, ya wuce ciki.
D'akin ma a gyare tsab-tsab ya gani, take murmushi ya kwace mishi, ya fad'a gadon, zuciyarsa cike da son ganinta, amma ba zai iya jurar wulak'anci da k'yamar da take nuna mishi ba.
mikewa yayi zuwa wanka, ya fito ya shirya cikin farin dogon wando Nike marar nauyi, da armless shirt dinsa, ya baza turarenshi, ya koma kan gadon ya kwanta, zuciyarsa na wani irin bugawa, shauk'in so da son ganin fuskarta na neman ya dagula lissafin k'wak'walwarsa.
Juyi kawai ya ke yana tunanin yadda zai iya bacci ba tare da ya ganta ba, ko ba komai hak'k'inshi ne ya tabbatar da tana cikin k'oshin lafiya kafin ya kwanta, hakan yasa ya mik'e tsam, ya d'auki key ko da zai ci karo da k'ofar a rufe, cikin sand'a ya isa ya murd'a k'ofar a hankali, ga mamakinshi ya ji ta bud'e, sad'af-sad'af ya shige ciki, ya mik'e zuwa d'akinta.
K'ofar a bud'e ya same ta, cikin mamaki ya tura kanshi, sai dai babu kowa, illa wayarta da ke ajje kan bedside locker, da duvet din da aka tattare wuri guda alamar mutum ya tashi a wurin.
Bakin gadon ya isa ya zauna, duk a zatonshi tana toilet, ya mik'a hannu ya d'auki wayarta, ya latsa gefe, yayin da haske ya bayyana jikin screen din, inda ya ci karo da pic dinsu na dinner kwance saman screenlock dinta.
Da mamaki yake kallon pic din, a zahiri bai san sa'adda aka d'auke shi ba. Ta wani bangaren yana jin dama-dama, hakan na nuni da akwai yiwuwar soyayyarshi a k'asan zuciyarta.
Murmushin da ke fuskarsa ne ya k'ara fadada, a hankali yake shafa setin fuskarta yana kara yi ma Allah godiya da yasa ta zama mallakinshi.
K'aran fashewar abu da ya ji, shi ya dawo da shi daga dogon tunaninsa, ya juya da sauri, suna hada ido ta fashe da wani irin kuka tana yarfe hannu.
Cikin razana ya isa gabanta, ruwan zafin da ke cikin mug din ya fallatsu a jikinta, da sauri ya kai hannunsa setin wurin, kamar tana jira ta fad'a jikinshi ta cigaba da rera kukanta.
"I'm sorry Angela, garin ya kika 6arar da ruwan zafi haka a jikinki?"
Dagowa tayi tana tura baki, a lokaci guda ta dora hannunta a kirjinshi; idanuwanta cike da hawaye tace
"Ba kai ne ba."
Dariya ma yadda tayi din ya bashi, amma ya gintse, ya kwantar da ita sosai a jikinshi, yana shafa bayanta a hankali, cikin rada yana fad'in
"Maganin mai tsiwa kenan."
Kuka ta sake fasawa, ta fara mutsu-mutsun kwace jikinta, amma yayi mata rikon da duk wacce aka yi ma irinshi dole ta shiga taitayinta.
Rigarta ta sama ya zare, a hankali ya dago da kanta, shiru tayi tana ajiyar zuciya, ya kama hannunta ya zaunar a bakin gado, sannan ya fara tattara wurin da mug din ya fashe, ya fita ya d'auko mop ya goge, duk tana kallonshi, sai da ya gama tsab ya dawo ya zauna a gefenta ya mik'a hannunsa ya dora a kan nata.
"Me sa baki bacci ba?"
Shiru tayi, hawaye suka ciko idanunta, ta matsa daf da shi, ta kankame shi tana fad'in
"I'm so sorry please Ya Sadic. Ka yafe mun dan Allah, kuma kada ka k'ara bari na ni daya ka ji?"
Wani irin yanayi ne ya ke ji a tare da shi, farin ciki, da jin dad'i ne suka kai mishi ziyara a zuciya, a hankali ya ke matsawa setinta, yana jin yadda take kwantar da duk jikinta a kafadarshi, hannu ya sa ya k'ara had'e ta sosai da gaba daya jikinsa, kafin ya tura hannayensa a tsakanin gashinta.
Idanunsa a lullube, yana jin saukar duk wani numfashi da zata ajje, yana jin yadda kauna da shauki soyayyarta ke razanar masa da zuciya, muryarsa a kaikaice ya seta bakinsa a daidai kunnenta ya ke fadin
"Me sa ba zan ba ki space ba? Bayan na san kina da wanda kike so Angela."
Da sauri ta sa hannu ta na toshe bakinshi, idanunta taf da hawaye ta ce
"Kana so Allah yayi fushi da ni ko? Ni bani da kowa duk duniya in ba kai ba. I love you with all my heart."
"But me sa kika rink'a punishing dina da yawa? Me sa kika ce baza ki iya zama da ni ba?"
"Ka manta laifinka ko? And kaima kasan babu wanda ya cancanta da rayuwata bayan kai, is just that I wanted to punish you. I'm so sorry sweetheart."
Ajiyar zuciya ya sauke, dago ta ya yi yana kallon cikin idanunta, itama shi din take kallo, yasa hannu ya shafi gefen fuskarta, kafin ya maida ta cikin jikinsa, a cikin kunnenta ya ke fadin
"I'll always love you Angela. You're my better half. Zan kula da ke in baki farin cikin da baki taba samun irinshi ba, I'll in sha Allah be the best husband to you. I'll make you the happiest woman on earth, nd will make sure that every woman is jealous of you. I love you so so very much Jameela. I love you."
Hawaye take jin suna zubo mata a dai dai lokacin, wanda ta rasa gane ko na meye, domin a zahiri yau ita ce rana ta farko da take jin ta comfortable in someone's arm, take jin duniyarta na tafi mata dai-dai da yadda take so, take kuma gaskata ko wacce kalma ta fito a bakin Sadic.
Idan har zata iya fassara abinda take ji, to baya wuce tace soyayyarta da Kazaure soyayya ce da suka gina bisa son zuciyarsu, domin tunda take da shi bata taba jin yanayin da take ji ba, kamar yanzu da take tare da SS.
Fuskarta ya d'ago, ya saita hancinsa a kan nata, yana kallonta labbansa kunshe da murmushin birgewa, sannu a hankali idanunsu suka fara kullewa, a lokaci guda ya dora labbansa saman nata ya fara kissing dinta cikin wani irin salo wanda shi kadai ya san sirrinshi.
Wani irin SABON SALON soyayya SS ya shiga nuna mata, k'auna ce zalla, wacce babu mix hakan ya k'ara masa wata daraja da k'ima a idanuwanta, ta kuma tabbatar da k'aunarshi halitta ce a cikin ruhinta, wacce ta fi k'arfin a kira ta da SO wanda zai iya tashi daga wannan bishiyar ya koma wata, ta kuma tabbatar da son da take yi ma Kazaure ba komai ba ne, illa kasancewarshi namiji na farko da ta fara so a duniyarta, amma a zahiri, k'auna mai cike da shak'uwa ba kowa take yi ma ita ba bayan Abbakar Sadic Galadima.
Kid sis you need to close your eyes on this😂😂😂 itz_Mjay
Lubbatu😍😙
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro