Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA TARA
















~~BABI NA TARA~~













Bayan Hamma Ashmaan ya fita, Maimoon ta koma ɗaki ta zauna. Tunani kala daban daban ke mata yawo a kwakwalwa. Da taga zaman hakan ba zaiyi ba, sai ta tashi taje tayi alwala ta dawo ta kabbara sallah.

Ta ɗaɗe tana roƙon Allah, ta ɗaɗe tana neman kariya, da sassauci daga gare Shi. Tayi wa kanta addu'a mai tsawo, tawa iyayenta, tawa ƙannenta, ƴan uwanta, da kuma al'umma gaba ɗaya.

Ba ta ɗaɗe ta sallamewa ba Ummi ta shigo. Tunda Ummi ta kalli fuskarta ta san da akwai abunda ke damun ta, amma sai bata ce mata komai ba.

"Ummi sannu da dawowa." Maimoon ta ce tana miƙewa daga kan darduma. Kayan hannunta ta amsa sannan taje ta dauko mata ruwa. "Sannu da dawowa," ta ƙara cewa.

"Yawwa Maimunatu, ke kadai a gidan?"

"Mm," ta daga kai. "Basu dawo ba har yanzu."

Ummi bata ce komai ba, kallon ta kawai take, idanunta duk sunyi ja. Ganin irin kallon da Ummi ke mata, sai ta sadda kai ƙasa, dan ma kar mahaifiyarta ta tambaye ta me ya same ta, sai ta tashi zata fita.

"Dawo nan ki zauna." Ummi tayi magana ba alamun wasa a tare da ita. Ba yanda ta iya, ta koma ta zauna. "Mai ya same ki?"

Murmushi ta ƙirƙiro. "Ummi fa ba komai, albasa na yanka shi yasa kika ga idona haka."

"Ban san ki da ƙarya ba Maimunatu. Zan sake tambayan ki, mai ya same ki?"

Kan ta a ƙasa ta faɗa ma Ummi abunda ya faru, bata boye mata komai ba. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke. "Hasina ta zo kenan?"

Maimoon ta girgiza kai. "Ban sani ba Ummi, ban ganta ba."

"To Maimoon ba ruwan ki da ita, nasan baki da fitina amma dan Allah duk abunda zata miki ki share ta, bana son matsala."

Kai Maimoon ta daga. "In sha Allah Ummi." Ina ma zata ganta, Allah ya sa har ta tafi kar su hadu. Dan kwatakwata bata son ganin ta, bata mance abunda ya faru ba wancan zuwan nata.


****

Maimoon ta haɗu da Fa'iz a hanyar dawowa daga makaranta ranan wata lahadi suna dawo daga islamiya ita da Habiba da Safara'u, sun ɗaɗe a bakin titi basu samu abun hawa ba har suka fara ƙosawa. Daga ƙarshe suka yanke shawaran takawa tunda maghriba ta kusa.

Suna tafiya wani mai machine ya wuce ta kusa dasu da gudu, hakan ya firgita Maimoon har ta turgude ƙafa. Tana miƙewa ta saki ƙara saboda wani zafi da taji har tsakar kanta.

"Ƙafa ta, bazan iya tafiya ba."

Salati Safara'u tayi, gashi suna ta tsaida keke napep babu wanda yake tsayawa. Suna tsaye suna tunanin yanda zasu yi wata farar mota, Toyota ta tsaya. Glass ɗin motan mai duhu ne, saboda haka basu ganin mutumin dake ciki.

A hankali aka sauke glass ɗin, matashi ne a ciki da ba zai wuce shekaru ashirin da ɗan ɗori ba. "Assalamu alaikum."

Habiba da Safara'u kaɗai suka amsa ɗan Maimoon azaba ta ishe ta. Bata san mai yace ba, kawai taji Habiba na mai bayanin abunda ya faru. "In ba damuwa ku shigo in kai ku."

Godiya sosai suka mai, sannan suka taimaka mata ta shiga motan, Safara'u ce ta zauna a gidan gaba. Motan tsit take, shi ya fara magana. "Ni sunana Fa'iz."

Safara'u ce ta bashi amsa, ta faɗa mai sunnan ta da kuma na ƴan uwanta. Ita aka fara ajewa, sannan Habiba. Sai ya rage daga Maimoon sai Fa'iz a motan. Motan shiru, dan ita ta ciwon da ƙafan ta keyi take.

"Hajiya kin maida ni driver ko?"

Sai a sannan Maimoon ta daga kanta, tana daga wa suka haɗa ido ta mirrorn dake motan. Da sauri ta dauke kai, tana gyara niqab dinta. Sai sannan ta tuna ashe ita kadai ce a bayan motan kuma ba kowa a gaba. "Kayi hakuri, bari in dawo gaba."

"A'a, yi zaman ki. I don't mind being your driver," shiru tayi, dan bata san abunda zata ce ba. "Ba zaki a duba ƙafarnan ba?"

"In na koma gida zani."

"Bari kawai in kai ki clinic."

Duk yanda tayi akan ya barshi, bai ji ba. Ba'a dade ba yayi parking, sannan yace mata ta jira shi. Tare da nurse ya dawo, ita ta kama Maimoon, ta taimaka mata ta shiga ciki. Akwai layi sosai, amma sai taga kai tsaye sun tafi office ɗin likita.

Cikin minti talatin aka duba ta aka bata magani. Nurse ɗin ta kara taimaka mata ta koma mota, wannan karon gaba ta shiga.

"Ai da kinyi zaman ki a bayan," Fa'iz ya ce idon shi cike da tsokana.

Murmushi kawai tayi bata ce komai ba. Saida suka fara tafiya ne ta mai godiya sannan tace ya faɗa mata kuɗin ta biya shi. Dariya ya mata, idon shi akan titi. "In har kina son biya to ba da kudi ba."

"In ba da kudi ba to da me?" Ta tambaye shi tana haɗa fuska.

"In lokacin biyan yayi zaki sani."

Abun ya ɗaure mata kai, mai yake nufi? Har kofar gida ya kaita, ƙara mai godiya kafin ta fita. Har ta kusan kaiwa bakin gate ya kira sunanta. "Kar ki manta ina binki bashi." Bai jira jin abunda zata ce ba, ya ja motar shi ya tafi.

Ita ta manta da batun wani Fa'iz, sai bayan sati ɗaya kwasam ta gan shi a gaban gidansu. Yi tayi kaman bata san shi ba, tazo zata wuce ta gaban shi.

"Haba Hajiya, ba faɗa mai ya kawo gaba?"

Kunya ta kamata, bai kamata ta mai haka ba. Ko ba komai ya taimake ta a lokacin da take buƙata. "Sorry, ban gane ka ba."

Murmushi yayi yace, "Ba komai. Dama na shigo area din ne nace bara inzo in duba ki. Ya ƙafan naki?"

"Da sauki Alhamdulillah," ta amsa da ɗan murmushinta.

"Ina zaki je?"

"Kasuwa zani, Mamana ta aike ni."

"Muje to in kai ki."

Idanu ta zaro waje. Mai ya kawo wannan maganan kuma? "A'a, ka bar shi. Nagode."

Duk yanda yaso ta yarda, sam! Maimoon taƙi. Ranan ma dan lalura ya sameta ne shiyasa har ta yarda ta shiga motan shi amma banda haka mai ya kaita shiga motan mutumin da bata sani ba?

Tun ranan ya kan zo jefi jefi, wasu lokutan ma takan manta dashi sai kwasam! Ta gan shi. Ita dai bata ce mai dan me ba, amma abun kam ya fara isan ta. Da ta faɗa ma su Habiba, gaba suka sa ta suna ta tsokanarta wai tayi sabon saurayi, abun har yaso ya bata haushi amma sai ta share su.

Bayan wata uku da fara haɗuwar su ranan wata laraba ta shirya zata fita ta same shi a waje. Doguwar riga ce a jikin ta da hijabi ɗan madaidaici da ya tsaya ƙasar gwiwar ta kaɗan. Sai kuma niqab dinta da bata iya fita in babu shi.

Batayi mamakin ganin shi ba, amma lokaci yayi da zata ji dalilin zuwan shi dan yana nema ya sata cikin matsala. Ba'ayi sati ba da Baffa ya tambayeta wani yaro ne yake yawan zuwa wurinta, rasa amsar da zata bashi tayi dan bata san mai zata ce ba. Ce mai zatayi bata sani ba ko me?

"Malama Maimoon, assalamu alaiki." Sanye yake da farar shadda da ta amshi kalar fatar shi, hular shi da ta sha kari ta zauna sosai a kan sumar da ya bari. Ƙamshin turaren shi tuni ya cika mata hanci.

"Wa'alaikumus salam, ina wuni."

Cikin gida suka shiga bayan ya amsa gaisuwarta, ta wurin garage akwai palastic chairs, a nan suka zauna. Tun ranan da Ummi ta mata faɗa basu sake tsayawa a waje ba. Sa'ar ta ɗaya, tunda ta fara shigo dashi bata samu wani matsala daga masu gidan ba.

Ciki ta koma ta kawo mai ruwan sanyi sannan ta koma ta zauna a kan kujerar da tafi nesa da shi. Ƙasa tayi da kanta, tana jira taji abunda zai ce.

"Maimoon," ya kira sunanta da wani irin murya da yasa gabanta faɗuwa. "Nasan kina da tambayoyi da yawa, zan baki amsa yau. Maimoon, tunda na gan ki nasan akwai wani abu special about you, I knew I had to make a move."

Tunda ya fara magana ƙirjinta ke bugawa kaman zai tsage. Kaman ƙasa ta bude ta shige haka take ji. Tunda Ummi ta haifeta wani bai taɓa faɗa mata irin wa'annan kalmomin ba.

"Maimoon," ya kira sunanta da sanyayyar murya. Ta amsa amma ta kasa ɗaga kainta kalle shi. Murmushi Fa'iz yayi, kunyarta na ɗaya daga cikin abubuwan dake burge shi. "I hope baki manta ina bin ki bashi ba. Lokacin biya yayi, ina so ki biyani by giving me a chance to pursue you, dan Allah ki bani dama."

Shiru tayi kaman bata wurin, jikin ta gaba ɗaya yayi sanyi, ya saki. Ji take kaman ma bata da lafiya.

"Maimoon, ki ce wani abu. Say something please."

Kaman wanda ruwa ya cinye haka ta koma, tunda ya fara magana ko nishin arziƙi bata yi ba. Bakin ta yayi mata nauyi, ta rasa abun cewa. To ma ta ce mai me?

Ajiyar zuciya Fa'iz yayi."Toh shikenan, ba sai kince komai ba. Zan baki lokaci kiyi tunani, duk hukuncin da kika yanke zan bi amma ina fatan hukuncin ya zama wanda nake so. Sai anjima Maimoon, na yafe ba sai kin raka ni ba."

Bai jira jin abunda zata ce ba saboda ya san ba zata ce komai din ba. Sai da ya tafi ta lura da ledar da ya bari. Sunan Allah ta kira tana dafe ƙirji, zuciyar ta kaman zata bar ƙirjinta saboda yanda take bugawa da sauri.

Fitar da zatayi sai fasawa tayi, duk yabi ya kashe mata jiki. Kwana tayi tana juya kalaman Fa'iz a kwakwalwarta. Sai bacci ya dauke ta sai ta farka, da taga zama tunanin bai da amfani sai ta tashi tayi alwala dama lokacin yin tahajjud yayi. Bata bar kan abun sallar ba sai da tayi sallar asuba da adhkar sannan.

Iya sanin da ta ma Fa'iz bata san shi da wasu halayen banza ba sai dai in ya boye mata, dan dama ance baka taɓa sanin halayen mutum gaba ɗaya, bare mutumin da ba su ɗaɗe da sanin juna ba. Shi yasa take tsoran bashi dama, kar ya zo mata a sifan da ba haka yake a gaske ba.

Har bayan sati ɗaya Maimoon ta kasa yanke hukunci. Tayi ƙarya in ta ce bata jin komai akan Fa'iz amma tana tsoro, kar yaudarar ta yazo yi. Tana zaune a ɗaki tajiyo sallamar Habiba, taji daɗi sosai dan dama tana da niyan zuwa gidan su yau, tana buƙatar shawara. Duk wani abunta Ummi take samu amma wannan kam ba zata iya ba, ba su taɓa irin zancen da Ummi ba, harga Allah kunya take ji.

"Hajiya munari," Habiba ta ce tana dariya, ta san yanda ta tsani sunan.

"Ke fa daɗi na dake kenan," Maimoon ta harare ta tana mikewa tsaye, kitchen taje ta dauko mata ruwa da abinci. Bayan sun gama gaisawa, Habiba ta ci abinci Maimoon ta lumfasa sannan ta faɗa ma aminiyarta abunda take ciki.  Saida Habiba ta gama tsokanar ta iya san ranta, wai ai dama ta ɗaɗe da harbo jirgin Fa'iz sannan ta bata shawarar da taga ta dace.

****

Fa'iz Yusuf sunan shi, shine babba a gidan su, yana da shekaru ashirin da bakwai. Ƙannen shi biyar, biyu maza, uku mata. Baban shi tsohon dan siyasa ne da ya rike manyan mukamai masu yawa. Wani alaƙa bai taɓa haɗa shi da wata mace ba da sunan so saida ya haɗu da Maimoon. Ba zai iya cewa ga sanda ya fara sonta ba kawai ya samu kan shi da yawan tunaninta, kuma hakan na faranta mai rai ba kaɗan ba.

Sati ɗaya kenan da yaje gidansu, hankalin shi sam yaƙi kwanciya har sai yaji hukuncin da ta yanke. Yana fata ta amsa tayin shi dan bai san inda zai sa kanshi ba in Maimoon tace bata son shi. Lokaci ɗaya ta birkita mai kwakwalwa gaba ɗaya, ya zama tamkar wani zararre, shi kadai yayi ta murmushi. Haka ranan Umma ta kama shi yana murmushi shi kaɗai a ɗaki.

Ƙarar wayar shi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya faɗa. Notification ne daga Instagram wani yayi kwamentin a ƙasan hoton shi, ya san baya wuce wata mace dan haka bai duba ba. Fa'iz ɗan kwalisa ne, akwai shi da son gayu, baya sati bai yi hoto ba ya watsa a yanar gizo wannan ne ya saman mai masoya masu dumbin yawa musamman mata da kuma makiya masu mai hassada.

Bayan sallar magriba bayan ya dawo daga masallaci yaji kawai in baiga Maimoon ba ko yaji muryarta to zai iya hauka. Wayar shi ya fiddo daga aljihu, ƙirjin na bugawa kaman wanda ya sha guda. Kiran farko bata daga ba, sai a na biyu.

"Salamu alaikum," sanyayyar muryarta ta ratsa illahirn jikin shi gaba ɗaya, take wata kasala ta sauko mai.

"Wa'alaikumus salam. Maimoon so kika yi in mutu ko?"

"Subhanallahi!" ta faɗa a razane. "Mutuwa kuma? Mai ya kawo wannan maganar ana zaune lafiya?"

Murmushi yayi yana shafa fuskar shi, har ya hango yanda idanunta suke yi in tana zare su, idanunta na cikin abubawan da suka fara daukar hankalin shi. "Mutuwa mana tunda har yau ban san ko an amsa mun ba ko ba'a amsa ba."

Shiru tayi daga ɗayan gefen amma yana jiyo motsin ta. "So? Maimoon kin amsa tayin soyayyar wannan bawan Allahn?"

Mmm kawai yaji tace kafin ta kashe kiran. Bai san sanda yayi murmushi mai faɗi ba. Sau uku yana kiranta amma bata dauka ba, yasan kunya take ji dan haka ya aika mata da saƙon SMS.

Nagode, nagode. In sha Allah baza kiyi nadamar daman da kika bani ba. I love you.

Amma ba'a je da nisa ba Maimoon ta samu kanta cikin tashin hankali da tsantar nadama.  Fa'iz ya nuna mata so, ƙauna da kulawa a cikin ƴan tsakanin nan, har take ji zata iya zama dashi a matsayin abokin zamanta har karshen rayuwar ta.

Alaƙar su na tafiya lafiya har aka fara maganan sako iyaye a ciki. A ranan da sukayi da Fa'iz zai turo magabatan shi su sami Baffa a ranan Maimoon ta sami labari mai rikitarwa, labari da ya kusan tarwatsa mata rayuwa.

Ta tashi tun da safe suna ta shiri, gaban ta sai faɗuwa yake amma bata kawo komai a kanta ba, ta danganta hakan da take ji da abunda zai faru. Dan ba ƙaramin chanji bane yake shirin samunta, kaman daga sama ta dinga jiyo hayaniya daga waje kaman harda kiɗa. Tasan bazai wuce makwabta ba dan haka ta cigaba da abunda take yi amma sai ƙaran yayi ta matsowa kaman a cikin gidan akeyi.

Wasu kalamai taji an faɗa sai da ganinta da jinta suka gushe na wasu ƴan daƙiku. "Allah ja zamanin ango, ango ka sha ƙamshi. Fa'iz angon Hasina....."

A razane ta kalli ƴan uwanta, shin suma sunji abunda kunnuwanta keji kokuwa? Tashin hankalin da ya mamaye fuskokin su ya tabbatar mata sunji abunda ake faɗa. Daga nan Maimoon bata sake sanin inda kanta yake ba.

Ta farka ta ganta a kwance a ɗaki, ga fanka a kunne amma sai zufa take yi. Bata san sanda ta fashe da kuka ba, dan Allah wani ya ce mata mafarki tayi ba da gaske bane.

Ganin mahaifiyarta da tayi ya sata saurin miƙewa, da gudu nufe ta. "Ummi ba dagaske bane ko? Mafarki kawai nayi. Ina ba dagaske bane. Fa'iz ba zai taɓa mun haka ba."

Hannu ta sa ta goge hawayenta. Ya ma zatayi tunanin Fa'iz zai mata haka? To ma dan kawai ance sunan angon Fa'iz sai a kace Fa'iz dinta ne? Ai ba shi kadai bane mai sunan a duniya.

Amma ganin yanayin fuskan Ummi ya ƙara tsoratata. "Ummi?"

A hankali Ummin ta samu wuri ta zauna, tausayin ƴar ta duk ya kamata. "Maimunatu, na san kin san ƙaddara, na san kin san cewa ɗan Adam baya taɓa tsallake abunda Allah Ya hukunta. Sannan duk abunda kika ga baki samu ba, to dama chan ba rabon ki bane. Baza ki taɓa samun shi ba koda mutanen duniya zasu taru su taya ki, haka in rabon ki ne to babu wanda ya isa ya hana koda duka duniya zasu taru dan yin hakan. Fa'iz ba mijin ki bane, haka Allah ya ƙaddara, an daura auren shi da ƴar uwarki ɗazu da safe."

Babu kalamam da zasu bayyana irin tashin hankalin da Maimoon ta tsinci kanta a wannan lokacin. Fa'iz ya cuceta, ya ci amanarta, ya bar mata taɓon da zaiyi wuyan gogewa.

"Ummi mai yasa zai mun haka?" Ta tambaya tana kuka. Janyo ta Ummi tayi, itama idanunta sun cika da kwalla. An zalunci ƴarta kam, amma ba komai akwai Allah. "Ƙirjina Ummi, kaman zai fashe."

"Kiyi ta maimaita La ilaha illa anta subhanka inni kuntu minaz-zalimin. Allah zai yaye miki, kiyi hakuri Maimoon."

Haƙuri kam ya zaman mata dole. Wannan abu shi yasa ta ƙara shiru, ta ƙara sanyi. Wahala ba kaɗan ba tasha kafin ta saisaita kanta. Wannan ciwon ba irin ciwon da zaka sha wa magani bane ya tafi, ciwon da ba'a  ganin shi yafi illa. Ta rike addu'o'i sosai, ta nemi sassauci daga Allah dan Shi kaɗai zai iya yaye mata halin da ta samu kanta a ciki. Wasu lokutan taji kaman baza ta iya ba amma da yardar Allah haɗe ƙarfin gwiwan da ta samu daga iyayenta, ƴan uwanta da ƙawenta, Maimoon tayi nasarar ya kice Fa'iza daga zuciyarta gaba ɗaya.

Tun wannan lokacin bata sake ganin shi, bata ƙara ji daga gare shi ba. Ya turo mata saƙon text amma bata bude ba, goge shi ma tayi gaba ɗaya ɗan bata ga kuma abunda zai ce mata ba. Har yau bata san asalin mai ya faru ba, kuma bata so ta sani.

Mutane dama abun magana suke nema, magana iri iri ta bazu gari. Wasu sunce mahaifiyar shi ce bata son Maimoon shi yasa ta aura mai zaɓinta, wasu suce ai aikin Hajiya Suwaiba ne saboda bata so taga Maimoon tayi aure ƴaƴanta basu yi ba kuma a gidan da take ganin yafi ƙarfinta. Magana dai gasunan iri iri.

Koma dai meye ya faru wannan ba matsalarta bane. Shine kawai daga sama yau zai tare ta yana faɗa mata maganganun banza. Maza kam sai a barsu, shi baiji kunyan abunda yayi ba ma kenan.

To ko zata yi maganin shi.



Ya sanyi jama'a?

Kar a manta ayi voting da commenting dan Allah. Comment shi ke bamu ƙarfin gwiwan yin rubutu, in kukayi shiru sai inga kaman baku jin daɗin littafin.

Kuma in anga kuskure a gyara mun dan Allah, wannan ne karon farko da nake rubuta littafi da Hausa🙏🏼



~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro