BABI NA TALATIN DA UKU
~
BABI NA TALATIN DA UKU
~
Tana kallon wayar har ta gama ringing. Ajiyar zuciya ta sauke ta jawo littafinta ta cigaba da karatu. Kaman wasa jarabawar su ta karshe a aji daya sai kawo kai ya ke yi.
Lokaci sai gudu ya ke yi, duka yaushe ta ke zaune gida tana jimamin rashin karatunta gashi yanzu har ta na shirin kammala shekara daya a jami'a.
"Wai Maimoon ba za ki dauki wayan ba? Tun dazu ake ta kira fah." Rukayya ta ce ta na kallon wayar da ke ajiye kan tebur.
Shiru Maimoon ta yi bata kula ta ba. Ringing wayar ta kara yi Rukayya ta mika hannu za ta dauka Maimoon ta yi maza ta dauke. Hararar kawarta ta yi. "Me ye haka?"
"Babu kyau dai wulakanci. A ce a yi ta kira ki ki dauka kuma kina gani."
"Ba ki ga karatu na ke yi ba?"
Kai Rukayya ta gyada. "Jacko ba. Cigaba da karatun ki."
Tun daga lokacin kuma karatun ya daina shiga, her mind kept wandering off. Rufe littatafen ta yi ta ce ma Rukayya ita ta tafi daki. Dama ita ta janyo ta su ka fito.
"Ko dai za ki je waya da shi ne ba'a son in ji?" Ta ce cike da zolaya.
Dariyan da bata shirya yi ba ta yi. Dalibai sai hada-hada su ke yi cikin makaranta kaman ba dare ba. Ta na cikin tafiya ta ji ana sallama a gefenta. Gabanta ta ji ya fadi, rike jakarta ta yi gam ta kara sauri.
Bata sake waiwaya ba har ta isa hostel. Ta na shiga ta saki wani irin ajiyar zuciya kaman wacce ta yi gudu. Dakin babu kowa, Anwara da Nanah sun tafi karatu.
Akwai sauran shinkafa da su ka dafa da rana ita ta dumama ta ci. Littafi ta kara daukowa ta cigaba da karatu.
Bayan awa daya ta rufe takardun ta fara shirin bacci. Ta na cikin shirin ne Mimi ta kirata. Sun dade a waya suna hira, da yake kwana biyu ba su ga juna ba kowa karatu ya dauki zafi.
"Ranan assabar zan tafi Abuja in sha Allah." Mimi ke sanar da Maimoon.
"Kin ji dadi har kin gama jarabawa. Ga mu nan ko farawa ba mu yi ba."
"Kaman gobe ne za ki ga kun gama kuma," dan shiru Mimi ta yi sannan ta ce. "Dazu na yi magana da Hamma."
"Wani Hamman?"
"Kai Adda. Hamma nawa kika sani? Hammanki mana. Ya ce ya kira ki ta Whatsapp, ko data din ki a kashe ne."
"Eh," ta ce a takaice. Ta na kallon wayan har ta gama karantan, ko dazu shi ne ya kira. Ita bata san me yasa daga sama kawai ya fara kiranta ba, bayan tunda ya tafi basu yi magana ba.
Ta ya ake son zuciyarta ta warke in za'a cigaba da tuna mata da abunda ta rasa?
Daga nan ta ji hirar ma ta ishe ta, saboda haka ta yi ma Mimi sai da safe. Bayan nan ta kira ta gaida iyayenta. Rabonta da su tun dawowar su daga Abuja, wurin wata uku kenan. Ta na jin dadi duk sanda ta ji muryar iyayenta cike da farin ciki da kwanciyar hankali. Yanzu ta na iya barci hankali kwance saboda ta san Baffanta da Umminta na nan lafiya.
Sadiya ta cika ta da surutu sai kashe wayar ta yi. Tana zaune ta ji kaman an tsikareta a cikinta, lokaci daya cikinta ya kulle, mararta ta fara juyawa. Ta na kan gado ba ta san sanda ta sauko kasa ba.
Da kyar ta rarrafa ta zuba ruwan zafi a (heating pad) dinta ta daura saman cikinta. A wahale barci ya dauketa.
Da safe da ta tashi kuwa ko tashi tsaye ta kasa yi. Kafafuwanta gaba daya sun rike. Wani azabben ciwo ta ke ji daga kasan bayanta zuwa cinyoyinta, ga ciwon kai da ciwon mara. Rabon da ciwon ya mata tsanani haka an kwana biyu. Ta hadiyi maganin amma kaman an kara mata zafin ciwon ne.
"Adda Moon ba za mu tafi asibiti ba kuwa," Nanah ta ce hankalinta a tashe.
"Gaskiya kam," Rukayya ta jinjina kai. "Bai kamata ki zauna ciwo na cinki haka ba. Kin ga fa har an kusan kiran sallan azzahar, kuma tun jiya da dare ki ke cikin wannan halin."
Magana ma wahala ta ke mata dan haka bata ma ba su amsa ba. Ita kadai ta san azabar da ta ke ji. Addu'o'i ta rika yi, wa su ma kam bata san abunda ta ke cewa ba.
Sallaman Anwara su ka jiyo. "Adda Moon har yanzu. Gaskiya mu tafi sickbay."
Ba su taba ganinta haka ba shi ya sa hankalin su ya tashi. Duk zaman su in ta na ciwonta ma ba su sani sai yanzu da abu ya yi tsanani.
Tun safe bata ci komai ba, Rukayya ta hada mata ruwan tea ta bata. Ta na gama sha ta dawo da shi.
Abun ya kara tada mu su hankali. Anwara ta taya Maimoon shiryawa sannan ita da Rukayya su ka kamata su ka nufi asibti da ke cikin makaranta.
Bayan sun samu wuri a (reception) sun zaunar da ita, Anwara ta tafi bude mata kati (file) tunda bata taba zuwa ba.
Maimoon na jingine jikin Nanah ciwo na ta nukurkusan ta. Chan sai ga Anwara dawo ta na masifa.
"Wannan wani irin abu ne? Shikenan idan mutum mutawa zai yi sai dai ya mutu. Nafi minti talatin tsaye babu wanda ya yi attending dina, ga wasu chan tsaye su tun safe su ke nan wai likita bai zo ba. Ta ya za'a ce likita bai zo ba dan Allah!"
Rukayya ce ta rika bata hakuri. "Haka su ke yi wallahi. Da mun kaita asibitin da ke cikin Samaru kawai, dan a nan sai wani ciwon ma ya kamata."
"How good is the hospital?"
"Toh, babu laifi. Nan 'yar dakin mu ta je da ta yi rashin lafiya kwanakin baya. Bari in je waje in tsaida Napep."
Dan babu wani mafita shi ya sa Anwara ta yarda. Ba ta taba da na sanin zuwa makarantan ba sai yau. A ce dalibi ya zo babu lafiya amma likita babu balle ma a duba shi.
Bayan Rukayya ta fita Nanah ta janye jikinta daga jikin Maimoon ta ja Anwara gefe dan su yi magana.
Sosa kai Nanah ta yi. "Uhhh Ya Wara dama....dama anata kiran Adda Moon shi ne na dauka. Ya ce yana Zaria so I told him Adda bata da lafiya, ya ce gashinan zuwa."
Anwara da har yanzu ranta a bace ya ke ta fara mata fada. "Tun farko wa ya ce ki amsa mata waya? Kin san shi ne? Idan kuma bai kamata ya sani ba fah?"
"Naga ya na ta kirane, shi yasa.....Kin ga ni gashinan ma ya na kira, wata kila ya iso." Nanah ta ce ta na nuna wa Anwara fuskar wayar Maimoon inda sunan 'Sayfullah' ya ke rubuce a fuskar wayan.
Karbar wayan Anwara ta yi a hannun Nanah. Kafin ta yi magana, mutumin ya fara ce wa; 'Assalamu alaikum, gani nan cikin sickbay din, kuna ina ne?"
"Wa'alaikumus salam, muna cikin reception."
"Alright toh, gani nan zuwa."
"Ya wara, Ya wara..." Nanah ta kira ta na kallon kofa. "Wancan ba Ya Sayf din su Waahidah ba ne?"
Waigawa Anwara ta yi ta ga wanda Nanah ke magana a kai. "Shi ne. Amma me ya ke yi a nan?"
Suna kallo ya daga wayar shi, a daidai lokacin wayar Maimoon ta yi kara. Ido Anwara ta zaro, ta juyawa su ka hada ido da Nanah. Shi ne Sayfullah din Maimoon!
Amsawa ta yi, da ya ke inda su ke zauna na kallon kofa ya hango su, sai ya kashe. Da sauri ya iso inda su ke.
Tare su ka gaida shi, ya amsa musu sama-sama dan hankalin shi ba a kan su ya ke ba. "Ina Maimoon din? Me ya same ta?"
"Gata chan zaune," Nanah ta amsa shi.
"Zaune kuma? Me ta ke yi a nan? Ba ku ga likita ba ne?" Ya jero musu tambayoyi.
Anwara ce ta mai bayanin halin da ake ciki. Shima ran shi ya baci. Ce musu ya yi su fito da ita bari ya je ya matso da motarshi.
Maimoon ta iya mikewa da kanta sai dai har yanzu kafafuwan a rike su ke. Hannunta daya na wuyar Anwara haka su ka taka suka nufi waje inda suka samu Sayfullah na jiran su.
Da sauri ya zagayo ya bude musu kofa, Anwara da Maimoon su ka shiga baya, Nanah kuma ta shiga gaba.
Cikin kankanin lokaci su ka isa asibitin. Babu bata lokaci a ka shiga da ita dakin ganin likita, tare da Anwara su ka shiga.
Sayf ya kasa zama, sai safa da marwa ya ke yi. Ya zo Kaduna gaida Ammah ya ji kawai ya na son ya karaso Zaria. Bai tsaya ya yi tunani ba ya hau hanya, ashe abunda zai iske kenan. Me ya same ta haka? Daga gani tana jin jiki. Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!
Bude kofar ofishin likitan da aka yi ya sa Sayf waigowa, da sauri ya nufi wurin likitan da ta fito.
"Kai ne kazo tare da Maimoon?" Kai ya daga alaman eh. "Alright. Tana bukatan ayi mata test," ta ce ta na mika mai karamin kwalba da ke dauke da jini. "Ba'a test a asibitin, amma akwai lab nan kusa."
Ba tare da bata lokaci ba Sayfullah ya tafi lab din. Bai dade ba ya koma asibitin inda likitan ta duba sakamakon. "Kaman yanda na yi suspecting typhoid ne da malaria su ka kamata. Uhm sai kuma cramps irin na mata da ta ke experiencing, shi ya taso da ciwon gaba daya haka. Yanzu zan sa mata drip ta samu ta yi barci, ga magungunan da za'a siyo mata. Za'a yi (observing) dinta na kwana daya mu ga yanayin karbuwan magungunan."
A hankali Sayf ya kwankwasa kofar dakin da aka kwantar da Maimoon rike da ledoji a hannu. Bai shiga ba sai da aka ba shi izini.
Mata uku ya samu a dakin bayan mara lafiyan. Biyu wanda su ka taho tare sai wata bakuwar fuska. Akan daya daga cikin kujerun robar da ke dakin ya zauna ya sake gaisawa da kawyen nata, ya tambaye su ya mai jiki.
"Da sauki Alhamdulillah," Anwara ta amsa. "An samu barci ya dauketa."
Sai a sannan Sayf ya yarda ya kalla inda gadon ya ke. Kwance ta ke rufe da mayafi. A karo na farko tunda ya hadu da ita babu niqab a fuskarta. Sai dai yanayin yanda ta kwanta bai bashi daman ganin fuskarta sosai ba saboda bargon ya rufe fiye da rabin fuskarta.
Ledojin da ya shigo dashi ya mika musu. Daya magunguna ne a ciki, sauran kuma kayan marmari da abubuwan da ya san za su bukata.
Agogon da ke daure a hannun shi na hagu ya kalla. Karfe biyar ya wuce, ga shi gobe litinin ya na da meeting a wurin aiki da ba zai iya tsallakewa ba saboda haka babu daman ya kwana. Zai isa Kaduna a yau, gobe da assusba ya kama hanyan Abuja tunda sai karfe goma ne taron.
Badan Sayfullah ya so ba, ya mike tsaye. "Allah Ya bata lafiya. Ni zan tafi amma dan Allah make sure you call me in an samu problem." Hannun shi ya sa a aljihu ya fiddo bandir din kudin da ya ciro sanda ya je siyan magani. "Ga wannan ku rike a hannu, na yi settling bill din gaba daya."
"Mun gode Allah Ya saka da alkhairi."
"Mun gode," Nanah da Rukayya su ka ce suma.
Kai Sayfullah ya daga musu sannan ya juya, har ya kai bakin kofa, ya juya ya kalli yanda Maimoon ke barci. Idan wani abu ya sameta fa bayan ya tafi? Ko dai ya daga tafiyar ta shi sai gobe? A daidai lokacin text din ogan shi ya shigo wayan shi, ya na mai tuni akan meeting din da su ke da shi.
Haka Sayf ya bar garin Zaria zuciyar shi cike fal da damuwa.
****
Bayan Sayf ya tafi Nanah ta matso kusa da Anwara ta rada mata abu a kunne. "Ya Wara bai gane mu ba fah."
Kai Anwara ta girgiza. "Idan banda abunki Nanah yaushe ya gama sanin fuskar kanneshi bare mu."
Kallonta ta maida kan Maimoon. Ina ta san Sayfullah?
•
•
•
•
•
🫣 Salamu alaikum. Da fatan muna lafiya? Ya kwana da yawa?
Abubuwa sai kara gaba suke yi jama'a 💃🏻 Mai kuke ganin zai faru nan gaba?
Toh yaya chapter dinnan? Ya yi ko kuwa? Ku fada mun ra'ayoyin ku a comment section!
Next update ya danganta da yawan votes and comments din ku🤭❤️
~Maymunatu Bukar 💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro