BABI NA TALATIN DA TARA
~
BABI NA TALATIN DA TARA
~
Motar tsit, babu karan komai sai na AC da ke busawa a hankali. Dukkan karfinsa Sayfullah ya ke amfani da shi dan kar ya juya ya kalleta a gefen shi, duk da yanzu ta rufe kyakkyawar fuskarta.
Fa tabarakallahu ahsanal khaliqeen. Abunda kawai ya rika nanatawa a zuciya. Duk yanda ya so dauke idon shi daga kanta a lokacin ya kasa, saida ta mike da sauri ta yi kicin.
Bai taba tsammanin ganinta ba da ya je ajiyewa Habib sako ba, da kamar ba zai zo ba ashe alkhairi ne ke kiransa.
Tunda su ka shiga mota bata ce kala ba, asali ma kanta a duke ya ke tana wasa da yatsunta. Murmushi ya yi, ya na tuna yanda aka yi ta yarda ya maida ta gida. Da kyar Salma ta shawo kanta, ya na jin su daga kicin din.
Tunda ta fito ta gaida shi bata sake ce mai komai ba. Saka da warwara ya ke a ran shi akan yanda zai fara yi mata magana. Mai zai ce mata? Ta ina zai fara? Zata fahimce shi?
Idan ba ka gwada ba ta ina zaka samu amsoshin tambayan ka? Wata zuciyar ta ce da shi.
Boyayyar ajiyar zuciya ya sa ki, daidai lokacin ya tsaya cikin (hold up). Jin motar ta daina motsi ya sa Maimoon ta dago kanta su ka hada ido, da sauri ta kauda kanta.
"Noor, ba za ki mun magana ba?" Shiru ba ta ce komai ba. "I'm sorry, ki yi hakuri. Yanzu na yi mi ki bayani za ki fahimce ni?"
Kai ta gyada ba tare da ta kalle shi ba. Bai san ya daina shakar lumfashi ba saida ta ba shi amsa, a hankali ya yi ajiyar zuciya. Sai dai matsalan ta ina zai fara?
"Kin taba jin inda uwa ta yarda dan ta?"
Janye idanunsa ya yi daga kanta ya maida su kan motocin da ke gaban shi. Ba zai iya kallonta ba dan sai karfin gwiwar da ya samu ya tafi. Ya na jin idanunta na yawo a kan fuskarsa.
"Iyayena sun rabu ina da shekara uku. Tunda mahaifiyata ta bar gidan ba ta sake bibiyar wani hali na ke ciki ba. Aure ta sa ke yi ta bar kasar gaba daya. Ba dan Ammah da Mami ba da ban san a wani hali zan taso ba. Su kadai su ka zame mun inawuna a lokacin da gidan mahaifina ya zame mun tamkar gidan kurkuku saboda azaba. Alhaji ya sake aure, shima ya yi watsi da al'amarina ya bar ni hannun matarsa. Azabar safe daban ta rana daban. Ban sake ganin mahaifiyata ba sai da na kusan shekara ashirin. A lokacin na koma wurin Mami saboda karatu."
Kallon Maimoon ya yi, dukkan hankalinta na kan shi. Bai tsawaita kallon ba ya sake dauke kan shi. Kallon da ta ke mai ya karya mai zuciya.
"A ranan da ya kamata in zo wurin ki naganta, haka ya yi mun (triggering panic attack)." Sayfullah bai so fada mata hakan ba. Sai dai ya ga babu amfanin boye mata. Wata kila fada mata gaskiya zai sa ta fahimce shi sosai.
Tsoron shi daya. Kada girma da kiman shi ya fadi a wurinta. Mai za ta yi tunani? Babba da shi ya na da (mommy issues).
"Shi yasa har na saba miki alkawari Mahnoor. Ina son ki sani ni Sayfullah ba zan taba yin abu da gangan ba dan in bata miki rai ko in yi (hurting) din ki."
"A ina ka ganta? Ka ce ganinta ne ya yi (triggering) din ka, a ina ka ganta?"
Glass din sa ya cire ya na shafa fuskarsa da hannunsa na dama. Ba tare da ya kalleta ba ya bata amsa. "A kofar gidan ku. Ammi, Ammi na gani."
Idanu Maimoon ta zaro kaman za su fado kasa. "Ammi fa ka ce? Ammin da na sani?"
"Matar kanin mahaifinki ba, maman Sameer, Kyda da Waahidah, ita."
A daidai lokacin motoci su ka fara motsawa dan haka Sayfullah ya ta da mota ya cigaba da tuki.
Maimoon na zaune gefe tana sakawa da warware wa. Lallai duniyan nan bata da girma. Yanzu Ammi ce ta haife shi? Kwakwalwarta har yanzu ta ka sa (processing) abun. Ba ta dade da sanin ta ba, amma Ammin da ta sani na da son yara da janyo su jiki. Ya aka yi ta aikata haka? 'Yan uwanta ne ta taso ba su damu da ita, duba irin ciwon da hakan ya yi mata ina a ce mahaifiyarka? Sai ta ji matsanancin tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Idan ita ce Ummi ta yi mata haka mutuwa za ta yi.
Ta na ta tunani ba ta san lokacin da motar ta tsaya a kofar gidansu ba saida ta ji muryarsa ya na kiran sunanta. Da sauri ta kalle shi, zuciyarta na sake rauni.
Kallon da ta ke mai ya sa Sayfullah tsarguwa. Hakan na daya daga cikin dalilan da ya sa bai cika son bada labarin rayuwarsa ba.Yanzu za'a fara mai kallon tausayi, wanda sam ba ya so. Musamman daga wurin mutanen da ya damu da su.
Ta bude baki za ta yi magana ya dakatar da ita. "Ba sai kin ce komai ba."
"Amma..." kai ya girgiza dan haka ta yi shiru. Dukda bata san abunda zata ce mai ba. Magana ce mai tarin yawa a bakinta amma bata san yanda zata furta ko kalma daya ba.
"Shiga ciki Mahnoor, Maghriba ya kusa. Sai da safe."
A sanyaye ta amsa mai sannan ta bude kofa ta fita. Tana tsaye a wurin har motar shi ta bace bata ganinta. Daki ta nufa ta yi sallah, ta na idarwa ta dauki mayafi ta tafi wurin Anwara.
"Ahh Adda Moon, yaushe kika dawo?"
"Ban dade da shigowa ba," Maimoon ta ji dadin samun Anwara ita kadai a dakin dan haka ta turo kofan ta ce, "magana za mu yi."
Gaban Anwara sai da ya fadi. "Allah dai ya sa lafiya."
Zama ta yi a bakin gado. "Dama Sayfullah yaron Ammi ne?" Tasan dama Anwaran ba za ta yi mamaki ba. "Me ya sa ba ki fada mun ba Anwara?"
"Ba hurumi na ba ne, shi yasa." Anwara ta bata amsa. "Yaushe kika sani?"
"Yau ya ke fada mun...." Nan ta fada mata yanda su ka hadu a gidan Adda Salma. Anwara sai da ta tsokaneta da fada mata ya ga fuskarta. "Ni kaina gaba daya ya kulle. Me ya faru haka?"
Dan daga jin yanda ya yi maganan cikin daci kadai ya sanar da ita har yanzu abun na damun shi. Bare a kai kan (panic attack) din ya samu. Da ta idar da sallah sai da ta yi bincike akan kalman. Ta na jin ta amma bata san takamaimai ma'anar abun ba sai da ta duba.
"Ban sani ba Adda. All I know is rabuwar Ammi da baban shi bai yi kyau ba, (it was a messy divorce). Ba'a dade ba su ka yi aure da Baba Nasir, ana auren su ka tafi Pakistan. A nan su ka yi rayuwarsu gaba daya sai yanzu da su ka dawo. Suna dai zuwa lokaci zuwa lokaci."
Ajiyar zuciya Maimoon ta yi. Shigowan Waahidah ya katse musu maganar. Maimoon na ta kallon Waahidah, wai ita kanwar Sayfullah ce. Abun da mamaki sosai!
***
Ammah ba karamin dadi ta ji ba da Mami ta yi mata albishir. Dama ta dade ta na yabawa tarbiyan Maimoon. Sosai wannan al'amarin ya yi mata dadi, ta sani kuma Sayf zai rike ta yanda ya kamata.
A lokacin da Mami ta kirata Alhaji Abdur-Rahman ba ya nan ya yi tafiya. Shekaran jiya ya dawo saboda haka yau ta ke son ta yi mai magana. Amma kafin nan ta na son tattaunawa da jikanta.
"Zo nan, kira mun yayan ki." Ammah ta ce da Ahlaam da ke zaune a falonta. Ahlaam din dama bata da wurin zama inda ya fi wurin Ammah.
"Toh Ammah." Kira daya Sayfullah ya dauka.
"Salamu alaikum Ammah, ina wuni."
"Wa'alaikumus salam, rike gaisuwar ka Saifullahi bana so."
Dariya ya yi. "Haba Ammah na, ki yi hakuri. Wallahi aiki ne ya yi mun yawa."
"Haka fa, kullum aiki kullum aiki. Allah Ya baka sa'a, a dai rika yi ana tunawa da 'yan uwa. Ba ku je ku kunshe kan ku a ofis ba babu abunda ku ke yi sai latse-latse da rubuce-rubuce. A rika sada zumunci, a kwana a tashi zaka wayi gari ka ga lokaci ya ja."
"In sha Allah Ammah. Nagode."
"Ya ya wurin su Mamin na ka, kowa lafiya ko?"
"Lafiya lau Alhamdulillah."
"Wurin Ammin na ka fa, su ma da fatan su na lafiya."
"Kowa lafiya Ammah."
"Toh madallah. Allah Ya yi muku albarka."
"Ameen Ameen."
"Oh ni! Saifullahi ja'irin yaron, Mamin ka ta kira ni. Ni da hada abun ba za ka iya kirana ka fada mun ba."
A dayan bangaren Sayfullah bai san sanda ya kwashe da dariya ba. Ammah ba za ta taba chanzawa ba.
"Ba dariya na ce ka yi mun ba. Yau zan samu mahaifin ka saboda haka karshen satin nan idan ka samu lokaci sai ka zo."
"Toh Ammah. Nagode Ammah, Allah Ya saka da alkhairi."
"Ameen. Kai da Maimunatun za ku zo ku same ni."
Daga nan su ka yi sallama. Da daddare Ammah ta sa aka kira mata Abdur-Rahman. Sun gaisa sannan aka yi hira irin ta uwa da danta.
Ammah ta yi gyaran murya sannan ta sanar da shi dalilin kiran da ta yi mai. Bata boye mai komai ba ta fada mai dangantakar yarinyan da tsohuwar matarsa.
Alhaji Abdur-Rahman ya dade bai ce komai ba, kafin daga baya ya ce, "Alhamdulillah, Masha Allah. Ammah dan ki girma ya zo. In sha Allah zan yi bincike akai sai in sanar da ke."
"Masha Allah. Allah Ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen, ni zan tafi, sai da safe."
"Allah Ya tashe mu lafiya," Ammah ta amsa ta na kallon shi har ya fita.
A kullum ta na mamakin rabuwar danta da Aisha. Abune da har yau ta kasa fahimtar dalili idan ta tuna lokacin da aka yi auren yanda su ke nuna wa juna so da kauna. Sai dai wasu abubuwan ko ya mutum yi kokarin gano bakin zaren ba za ka iya ba, kawai haka Allah Ya kaddara.
Kuma har yau shi ko ita babu wanda ya taba fadan abunda ya faru tsakanin su. Amma sai dai koma menene Saifullahinta ne ya sha wahala.
Ajiyar zuciya Ammah ta yi, ta mike ta yo arwala ta kabbara sallah. Sosai ta yi wa Sayfullah da Maimoon addu'a.
A karshen satin Sayf ya zo Kaduna, (weekend) din gaba daya ya yi a nan. Sun tattauna da Alhaji inda ya mai tambayoyi sosai shi kuma ya ba shi amsoshin da za su gamsar da shi. Ya fada mai komai da ya sani game da ita har 'yan uwanta da ke garin Kaduna.
Sun rabu akan Alhaji zai kira shi idan ya gama kaddamar da bincike.
Sayfullah har ya mike ya koma ya zauna. "Nagode Baba. Allah Ya saka da alkhairi."
Sosai farin ciki ya bayyana a fusakar Alhaji Abdur-Rahman. Rabon da ya ji Sayfullah ya kira shi da Baba an dade. Ya na so ya janyo dan shi jiki sai dai bai san ta inda zai fara ba. Ya sani laifin shi ne tun farko da ya ture shi.
"Ameen Sayf. Allah Ya yi maka albarka. Allah Ya tabbatar da alkhairi. Girma ya zo yanzu sai a kula."
"Ameen."
Daga nan ya mike zai tafi, har ya kai bakin kofa Baba ya dakatar da shi. "Sayf?"
A hankali ya juya. "Na'am?"
A yanda ya ke a tsayan nan Alhaji Abdur-Rahman na ji kaman ya na kallon kan shi a da. "A rika daurewa ana leko gida."
Ƙeya Sayf ya sosa ya na mai jin kunya. "In sha Allah."
Bakin Sayf ya ƙi rufuwa har ya kai falon Ammah. Ta na ganin shi kuwa ta yi ta tsokanan shi iya san ranta.
"Oh ni Dije! Kaman ba nan na riƙa roƙon ka ka kai mata sako Zaria ba."
Dariya Sayf ya yi babu bakin kare kai. Duk yanda su ka yi da Baba ya fada mata.
"Masha Allah! Masha Allah! Abu ya yi daɗi. Allah Ya kaimu da rai da lafiya. Allah na gode Maka da Ka nuna mun wannan ranan. Allah Ya yi muku albarka."
Da Ameen Sayf ya amsa.
"Ita Aishatu ta san abunda a ke ciki ko?" Shiru Sayf bai ba Ammah amsa ba. Ta ko hade rai. "Maza ka yi saurin zuwa ka sanar da ita, har gida kuma za ka je."
"Ammah..."
Da sauri ta katse shi. "Ba na son jin komai. Ka yi yanda na ce."
"Toh Ammah. Duk yanda kika ce haka za'ayi."
"Jiya Maimunatun ta kira ni ta gaishe ni," murmushi Sayf ya yi bai ce komai ba. "Tun farkon haduwa na da ita yarinyan ta shigan mun rai. Ta na da hankali sosai. Allah Ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen Ammah."
Ranan litinin da safe Sayfullah ya koma Abuja. A gajiye ya koma gida bayan sallar isha'i, da yake wurin aiki ya wuce da ya iso garin. A hanyar dawowa kuma (hold up) ya tsaida shi.
Ya samu kowa a falo, tv a kunne Baba Ahmad na kallon news. 'Yan biyu kuma na magana da Mami, Nusayba na gefe ta na danna waya.
Sallaman shi ne ya sa hankulan su ya koma kan shi. Ya gaishe da iyayensa sannan ya samu wuri ya zauna. Mike kafafu ya yi.
"Sannu Yaya," in ji Nusayba. "Bari in kawo maka ruwa."
Duk da gajiyan da ya yi bai mike ba shima ya zauna aka yi hirar da shi. A nan gidan ne kawai ya ke iya sakin jiki ya yi abunda ya ke so.
Har wurin karfe goma suna nan zaune. Hussein ya fara tashi, Hassan ma ya bi shi. Dama tuni Nusayba ta tafi daki saboda gobe ta na da aji da safe.
"Sayf ya kuka yi da Baban ka?"
Sadda kai ya yi hakan ya sanya su dariya. Baba Ahmad ke cewa, "dan na ki kunya ya ke ji. Yaya Abdur-Rahman din ya kirani tun jiya ma, na manta in fada miki."
Murmishin Mami ya ki raguwa sai karuwa ma da ya ke yi. "Alhamdulillah! Bari in zo in kira Aisha in sanar da ita abunda a ke ciki."
Boyayyar ajiyar zuciya Sayf ya saki. Kenan ba sai ya kirata da kan shi ba. Maganar ba ta tsawaita ba dan harga Allah kunya ya ke ji. Bangaren su ya nufa bayan ya yi musu sai da safe.
'Yan biyu su ka yi ta tsokanan shi musamman Hussein. "Ya Sayf ba ka taba hada mu da Aunty Amarya mun gaisa ba fa. Haka ake yi tsakani da Allah. Yaushe za ka je ganinta, zan raka ka."
(Throw pillow) din da ke kusa da shi ya jefa ma Hussein. Da sauri ya kauche ya na dariya. Daki Sayf ya shiga ya bar su a falo.
Duk da gajiyar da ke nukurkusan shi bai hana shi daukan wayan shi ya yi dialing number din ta ba.
Ringing biyu ta dauka sanyayyar muryarta ta daki kunnesa. A take rabin gajiyar da ke tare da shi ta bace.
"Wa'alaikumus salam Noor, ina wuni?"
"Ina wuni," murmshi ya yi, dama ya sani ba zata amsa gaisuwar ba sai dai ta yi tata. "Ya hanya? An dawo lafiya?"
"Lafiya lau Alhamdulillah. Ya shirye shiryen biki?"
"Gashi nan muna ta yi. Yau a kasuwa mu ka yini ba ka ji kafafuwana ba kaman za su balle."
"Sannu, a dai dunga bi a hankali, kar ki yi stressing kan ki da yawa."
"Toh.." haka su ka yi hira inda kowa ke fada ma dan uwansa abunda ya yi yau duk da Sayf bai fada mata me ya je yi kaduna ba.
Jin ya na ta hamma ya sa Maimoon ta ce mai ya je ya kwanta.
"Mmm mm dai Noor, kawai ki na kora na da wayo ne."
Dariya ta yi sosai. Kaman kar ta daina, fuskarta ke yawo a idanunsa. Dukda so daya ya ga fuskarta kuma ba sosai ba ya kasa mantawa. Kullum ya rufe ido ita ya ke gani. Mahnoor din sa, mai idanu ma su haske kaman wata.
"Ba haka bane, ka gaji shi yasa na ke so ka kwanta ka huta. Yanzu ka gama fada mun kar in yi stressing kai ni, (you should take your own advice)."
"Shikenan Noor, duk yanda kika ce haka za'ayi. Sai da safe."
"Allah Ya tashe mu lafiya."
Har bacci barawo ya sace Sayf murmushin fuskarsa bai gushe ba.
•
•
•
•
•
•
•
Sayfullah da Mahnoor din shi🥹❤️
Kar a manta da vote and kwament! Nagode💕
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro