BABI NA TALATIN DA TAKWAS
This is coming late but da fatan an yi sallah lafiya?❤️ Ayi maneji da wannan ina jarabawa a makaranta, a taya ni da addu'a 🥹🤲🏻
~
BABI NA TALATIN DA TAKWAS
~
Ya yi babban kuskure!
Ya san ya bai kyauta ba, ba sai wani ya fada mai ba.
Hannu ya sa ya shafa kan shi ya na ambaton sunan Allah. Maganar shi da Maimoon ya kara kashe mai jiki. Ta yi fushi da shi sosai. Koma waye a (position) dinta zai yi fushi ba kadan ba dan sam bai kyauta ba.
Abun ne ya zo mai a ba zata. Ko a mafarki bai taba tunanin haka zai faru ba. Da ya gan shi a kofar gidan Ammi komai dauke mai ya yi. Har lumfashi kuwa saboda (panic attack) da ya same shi lokaci daya.
Dole Habib ya karba tukin su ka koma gida. Daga nan ya rasa abunda ya ke mai dadi. Babu yanda Habib bai yi da shi ba akan ya kirata ko ya amsa wayar amma ya kiya saboda bai san abunda zai ce mata ba. Ba zai iya dauka ya ce mata ga abunda ya faru ba kuma ba zai iya yi mata karya ba, sam ba halin shi bane.
Da ta tura mai text din address din gidan ya na sha kawai unguwa daya ne dan bai san lambar gidan Ammin ba. Sai da suka isa Habib ya hango ya ce mai ga gidan chan. A take ya daskare. Suna tsaye kuma sai ga mota ta shiga gidan. Ya na hangawa ya ga Ammi da mijinta zaune a baya. Daga nan ya fara jin lumfashin shi ya na sama-sama.
Rabon da haka ya faru da shi tun suna UK lokacin ya na digiri din shi na farko.
Ko da Maimoon ta tambaye shi bai da lafiya ne kasa fada mata ya yi. To mai ze ce mata? Saboda ya ga mahaifiyarsa ya samu (panic attack)? Abun bai yi fasali ba, da girman shi da komai.
Idan hasashen shi gaskiya ne mutumin da ya hadu da shi ranan da su ka je da Mami shi ne Baffa mahaifin Maimoon. Gidan da su ka shiga karshe kuma Ummi ce su ka samu.
Kwanan nan aka gano su na da dangantaka kaman yanda ya ji suna cewa. Kenan shi ya sa suka baro Kaduna?
Mukulli ya dauka ya yi waje. Gidan Habib ya nufa. Ya san ya na gida tunda yau assabar. Da ya isa Habib din ne ya bude mai kofa. Ya na ganin shi ya hada rai saboda jiya ba karamin haushi Sayf din ya ba shi ba.
"To uban 'yan taurin kai, me ka zo yi mun a gida?"
"Na ce maka ka yi hakuri mana Habib."
"Ba ni ya kamata ka ba hakuri ba ai." Ya juya ya shiga ciki Sayf ya bi shi.
Yau ko daga Amira sama ya kasa yi saboda gaba daya jikin shi babu kuzari. Chan sai ga Habib ya dawo tare da matar shi. Sun gaisa ta ce bari ta kawo mai ruwa. Ta dawo da tray dauke da snacks, ruwa da drinks. Ruwan kawai ya sha.
"Yi tambayoyin ka ta baka amsa. Nasan ba wuri na ka zo ba."
Harara Sayf ya makawa abokin shi. "Maman Ikram inda mu ka je nan dinne gidan su Noor ko kuma mun yi batan kai ne?"
Habib ya yi wa Salma kwatancen gidan dan haka ta daga kai. Har ta yi mai describing yanda cikin gidan ya ke. Zuwanta gidan uku tun dawowar su Baffa. Ita ma abunda ya bata mamaki sosai. Allah mai iko!
Kai Sayf ya jinjina. Tabbas haka cikin gidan ya ke. Har zai ce mata to me yasa ba ta fada mai ba sai ya tuna ba su taba zuwa gidan Ammin ba. Tun tuni Habib ke bin kan shi ya rakasu ya ke dojewa.
"Abunda ban gane ba, da ba'a Kaduna su ke ba? 'Yan uwansu na chan fa su su waye?"
Salma ta yi bayani a takaice akan abunda ya faru yanda zai fahimta. "....daga baya ne su ga gano ainihin abunda ya faru bayan matar kanin Babansu ta fallasa. Dan ko shi Baffan bai sani ba. Sanadin zuwan Maimoon makaranta aka hada su daki daya da su Anwara.."
"Anwara?" Sayf ya katse ta. "'Yan uwanta ne?"
Kai Adda ta daga. "Babansu Anwara kanin Baffa ne." Nan ma dai ta yi mai dan takaitaccen bayanin abunda ya faru.
"Idan na fahimce ki," Habib ya ce wa matarsa. "Mijin Ammi, Nasir Lamido kanin Baffa ne?" Kai Salma ta gyada. "Kenan kannen Sayf cousins din Maimoon ne?" Shima Salma ta gyada kai. Jingina da kujerar Habib ya yi. "What a small world."
What a small world indeed! Ruwan sanyi Sayf ya sake zubawa a kofi ya sha.
"Kai dai Sayf rayuwar ka is going in circles. Yanzu dai idan ba ka je ka gaida Ammi a matsayin ta na mahaifiyarka ba ka je ka gaida ta a matsayin ta na matar uncle din Maimoon." Habib ya ce. Jin Sayf ya yi banza da shi ya sake cewa. "Ba dai hakura za ka yi da Maimoon din ba saboda..."
Bai karasa maganar ba saboda wani irin kallo da Sayf din ya mai. Aiko Habib ya kwashe da dariya. Salma kuma ta yi murmushi.
Kai Sayf ya girgiza. Abunda ya fara zuwa mai kai kenan ya yi saurin kawar da shi. Son da ya ke ma Maimoon ya fi karfin abunda ke tsakanin shi da Ammi. Besides, a sanadin Ammi ya rasa abubuwa da dama a rayuwarsa. Ba zai bari ya rasa matar da ya ke matukar so ba saboda ita.
****
Maimoon na gasa ma Sayfullah aya a hannu. Shi bai ma san wani irin punishment ne ta ke mai ba, shi ba (silent treatment) ba, shi ba wani abun daban ba, ga shi nan dai.
Shi har tsoron kiranta ya ke yi. Za ta amsa dan amsawa amma shi zai kare surutun shi na ta daga mm sai mmm mmm.
Har yau ya kasa fada mata abunda ya faru. Ya na fakewa da saboda har yanzu bata sauko daga fushinta ba, amma har kasan ran shi ya na shakkan abunda zai biyo baya.
Hannu ya ji a kan kafadarsa ya juya da sauri dan bai ji karan shigowar wani cikin dakin ba.
"Ya Sayf wai lafiyan ka kuwa kwana biyun nan? Kullum cikin zurfin tunani kake. Da fatan komai lafiya?"
Murmushi Sayf ya kakalo. "Komai lafiya Hassan."
Daga ganin yanayin fuskar Hassan bai gamsu ba amma Sayf ya share shi. Dauko system din shi ya yi dan ya cigaba da aikin da ke gaban shi. Ko minti talatin bai yi ba ya ji ya gaji.
Cikin gida ya nufa inda ya samu Nusayba a falo. Bayan ta gaida shi ta fada mai Mamin ta na daki. Sai da ya yi sallama ya jira ta amsa kafin ya shiga. Zaune ta ke a kan kujera sanye da gilashi ta na latsa waya.
Murmushi ne ya mamaye fuskarta ganin Sayfullah. "Ah ah Sayf, shigo mana. Yaushe ka dawo?"
"Ban dade da dawowa ba," Sayf ya ce ya na zama a kasa kusa da kafafunta. "Ina wuni?"
"Lafiya lau. Ya aiki da hidima da mutane?"
"Alhamdulillah."
"To Allah Ya taimaka."
"Ameen."
Daga nan shiru ya ratsa dakin. Kan Sayfullah na kasa ya na tunanin yanda zai fara fadawa Mami.
Hannu Mami ta daura a kan kafadar shi. "Sayfullah menene?" Yanayin shi ya fada mata akwai abunda ke damun shi. Tun tuni ta ke ankare da shi, jira kawai ta ke yi ya zo ya same ta lokacin da ya shirya.
Sayfullah ya taso babu wanda ya damu da halin da ya ke ciki, babu mai tambayan shi idan ya na da matsala. Ko ya kai kukan shi wurin da ya kamata a magance mai matsololin shi hantararsa a ke yi, a kore shi a wulkance. Mami ce mutum na farko da ta taba tambayan shi mai ke damun shi, ya na da wani bukata.
Ranan na cikin ranakun da ba zai taba mantawa a rayuwarsa ba. Duka lokacin bai wuce shekara sha biyu ba. Tun daga lokacin Sayfullah ba ya shakkan samun Mami saboda ya san zata saurare shi. In na fada ne ta yi mai, in nasiha ne, in shawara ce duka dai za ta yi mai.
Shi yasa yanzu bai boye mata komai ba. Tun daga ranan da ya ga Maimoon a kasan bishiya zuwa aiken da Ammah ta yi mai Zaria har zuwa ranan da ya kamata ya je gidansu.
Tunda ya fara magana Mami ke murmushi ta na gyada kai. Da ya gama ta kamo kumatunsa ta na cewa, "Sayfullah dina ya girma."
Kunya da dariya furucinta ya sa shi.
"Kaman na taba haduwa da ita, ta na yi ma Ammah kitso da ko?" Kai Sayfullah ya gyada. Mami na ta mamakin abun al'ajabi da ya faru da su Maimoon din.
"Masha Allah, masha Allah!" Ta tuna yanda Ammah ke yabon yarinyan a kodayaushe. Hakan kadai ma ya gamsar da ita. "Zan yi magana da Ammah, na san zata yi faran ciki sosai. Daga nan za mu yi magana da mahaifinka. Kafin nan sai ka daidaita tsakanin ka da ita."
Kan Sayfullah na kasa Mami ta gama mai nasihan da ya kamata. Kwalla ya ji ya taru a idanun shi ya maza ya hadiye su. Tsakanin shi da Mami sai fatan alkhairi kawai.
Bayan ta gama mai nasihan ta hau tsokanar shi har sai da ya tashi zai fita. Kafin ya mai kofa ta tambaye shi, "Kai zaka sanar da Ammin na ka ko?"
Da sauri ya juya ya kalleta. Daga mai gira ta yi. "Ka ke kallo na, ba dai ni ka ke so in fada mata ba?"
"Mami..."
"A'a Sayfullah. Ba zata ji dadi ba idan wani ya sanar da ita ko ta ji labari a wani wurin."
Sayf bai sa ke cewa komai ba ya fita. Har yanzu murmushin da ke fuskar Mami bai gushe ba, hannu ta daga sama. "O Allah, Allah Ka sa wannan abu ya kawo gyara tsakanin Sayfullah da Aisha!"
Wayarta ta dauko dan kiran Ammah ta yi mata wannan albishiri.
***
Hira su ke yi tun dazu dakin ya cika da hayaniya. Kasancewa yau juma'a gidan a cike ya ke kowa ya zo kaman yanda ya zame musu al'ada.
Duka suna falon Jaddati daga yaran har iyayen su. Ana zaune Jaddati ta fashe da kuka. Hankalin kowa ya tashi ana tambayanta me ya same ta.
"Allah Ya yi muku albarka. Ko yanzu na mutu zan tafi cikin farin ciki. Allah Ya hada mu haka a aljannah tare da mahaifinku."
Kalamanta sun sa jikin kowa ya yi sanyi. Baba Nasir ya ce to a yi addu'a. Daga nan taron ya fara watsewa. 'Yan matan su ka tafi gidan Ammi.
Kwadiya su ke jin yi dan haka Waahidah ta shiga kicin ta soya musu sauran awara da Ammi ke da shi a fridge. Nanah da Sadiya kuma su ka yi sauce.
A kasa su ka shimfida leda kowa ya sa hannu. Ana ci ana raha, abun gwanin ban sha'awa. Dan kar su yi mata dariya ita da irin na Ammah za ta yi. Bayan sun gama ci babu wanda ya motsa a ka daura hira.
Cikin haka ne wayarta ta yi kara sai hankalin kowa ya dawo kan ta. Kafin ta dauka Anwara har ta fara tsokanarta. "Ahh ahh Yayanmu ne ke kira?"
"Ban sani ba," Maimoon ta ce ta na hararrata. Kitchen ta tafi dan sun cika wurin da hayaniya, ta na ji suna ta tsokanarta har Kydah ke ce wa "Allah Ya sa Sayf din naki ba irin namu bane mai wuyan sha'ani."
Bata fahimta mai ta ke nufi ba sai kawai ta share. Ashe ma Adda Salma ce ke kira. Chan kasan ranta ba haka ta so ba.
Bayan sun gaisa Adda ke fada mata an kawo mata sako daga wurin Hajiya Laila. "...motar Baban Ikram na wurin gyara, ina ta kiran mai delivery din ban same shi ba. Sai dai ki zo ki karba in kina bukatan su yanzu."
"Babu damuwa, gobe zan zo in sha Allah." Kayan hada turaren Anwara ne. Biki na ta matsowa ta na so ta hada su yanzu dan su jiku da kyau.
"Toh Allah Ya kaimu."
Washegari da yamma dreba ya ajiye Maimoon gidan Adda. Bata zo da niyan zama ba, sakon kawai za ta karba ta fito. Sai dai kafin ta shiga Baba Nasir ya kira ya ce dreban ya je ya karbo mai sako. Jin haka ta ce toh ya je ya dawo tunda inda zai je da nisa kuma dole sai ya dawo ta nan din.
Amira da Ikram suka tarbe ta a kofa suna murnar ganinta. Amira ta dauka sannan ta kamo hannun Ikram su ka shiga ciki. Mamansu na zaune a falo hankalinta na kan TV.
"Mamah! Mamah! Ga Aunty Moon!" inji Ikram ta na rugawa da gudu.
"Sannu da zuwa Aunty Moon," Adda Salma ta ce. Bayan an gaisa, ta kawo mata ruwa sannan ta zauna daga inda ta tashi. "Kinji daki na tunda aka kawo sakon nan kuwa? Baban Ikram da bai damu da turaren wuta saida ya yaba. Ko wani turare ne wannan dole a hada dani."
Dariya Maimoon ta yi ta ce mata kada ta damu. Adda ta kawo mata kayan ta ce ta duba ta gani dan Amira ta yi wasa a wurin kar a je ta cire wani abu.
Komai na ciki da ta duba. Adda Salma ta je kicin duba girkin da ta daura. Maimoon ta ce za ta taya ta ta ce ta barshi. Amira da ke wasa a kasa ta baro kayan ta haye cinyan Maimoon.
Ta na ta yi mata surutu, wasu ta gane abunda ta ke cewa sauran kuma biye mata kawai ta ke yi. Da yake ta cire niqabinta sai ta ke yatsine fuskarta wanda hakan ke sa Amira dariya sosai.
Dariyar kanwanta ya sa Ikram ta dawo wurin su itama. Maimoon ta biye musu suna ta wasa. Ikram ta dauko niqab din da ke ajiye kefan jakar Maimoon ta ce, "Anty Maimoon ki saka mun irin na ki."
Dariya ta yi ta ce to. Da yake niqab din ba babba bane, irin kananan ne da ke zuwa da abaya sai bai yi mata girma a fuska ba.
Da gudu ta nufi mamanta da ke fitowa daga kicin. "Mamma kalle ni, na yi kyau kaman Anty Maimoon ko?"
"Sosai ma kuwa, har kin fi Anty Maimoon din yin kyau."
Daga nan yaran su ka cigaba da wasan su, Ikram da niqab din makale a fuskarta.
Kiran Malam Musa dreba ne ya katse musu hira. Salati Maimoon ke ta nanatawa tunda ta amsa kiran.
"Babu wanda ya ji ciwo ko?" Ta tambaya Malam Musa a rude.
"Gaskiya yaron ya bugu sosai, yanzu haka muna hanyar station, mun je asibiti sun ce sai munzo da report."
Sun kammala magana inda ya ke fada mata ya sanar da Baba Nasir. "Ki yi hakuri na bata miki lokaci."
"Ai bayin kan ka bane. Allah Ya kare gaba."
Adda Salma da tun dazu hankalinta ke a tashe ta ce, "Me ya faru, waye ya ji ciwo?"
Maimoon din ta fada mata yanda Malam Musa ya buge wasu samari a kan mashin a hanyar dawowa daga karbo sakon Baba.
"Allah Ya kiyaye."
"Ameen."
Sun yi 'yar hira kafin Maimoon ta mike. "Adda gwara in tafi tun gari nada haske."
"Wani zai zo daukan ki ne?"
"A'a, ni kadai zan tafi."
Wani kallo Addan ta yi mata. "Kin san hanya ne? Nan fa ba Kaduna ba ce, yanzu za ki bace..."
Dariya ta yi. "Adda sai ka ce dai wata yarinya."
"A'a fa, bata babu ruwanta da yaro ko babba. Ki bari mu tafi tare gaskiya, bari in kira mana Uber."
"Su Amiran kuma ki yi ya dasu?"
"Tare zamu tafi."
"Adda naga alama yawo kawai ki ke jin yi. Ki kira Uber din amma ba sai kin wani kai ni ba."
"Bari dai in dauko wayata amma yaushe zan bar ki ki tafi ke kadai ke da baki taba hawa motan haya a garin nan ba, wani abu...."
Adda ta haye sama ta na mita. Kai Maimoon din ta girgiza tana murmushi. Karan doorbell ne ya mayar da hankalinta kan kofa, kafin ta motsa Iki har ta bude.
Gabanta ne ya yi wani irin mummunar faduwa ganin waye tsaye a bakin kofar. Daskarewa ta yi a wurin ta kasa motsi, wata zuciyar na ce mata ta tashi da tafi amma ina, kaman jikinta ba nata ba.
Gashi ta na zaune daidai saitin kofa.
"Baba Sayf!" Ihun su Iki ya cika wurin amma sam hankalinshi ba akan su ya ke ba. Hankalinshi na kan rabin ran shi da ke kallon shi kaman ta ga dodo.
•
•
•
•
•
•
•
💃🏻💃🏻 jama'a! Ni ban san abunda zan ce ba ma. Mu hadu a babi na gaba. I don't know when though
Kar ku manta ku sani a addu'a, Allah Ya sa in yi passing exams dinnan🥹🤲🏻
Idan na gama exams sai kun gaji da ni😂💃🏻
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro