Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA TALATIN DA SHIDA









~
BABI NA TALATIN DA SHIDA
~




Gaba daya dakin ya dauki ni'imtaccen kamshi. Dawowarta kenan daga tasha inda ta amso kayayyakin hada turare da aka aiko mata daga Maiduguri. Hajiya Laila ta hada ta da mutumin bayan ta gama aji a wurinta, kayan shi ingantattu ne da kuma saukin kudi.

Wuri guda ta ware ma kayan a cikin wardrobe dinta. So ta ke yi ta gama ayyukan cikin gida sannan ta fara aikin. Aikin turare ba karamin abu ba ne, ya na da cin lokaci sosai.

Duk da kasuwar yanzu ma sai a hankali. Amma ta san kasuwanci ya gaji haka. Akwai wasu sababbin turare da ta ke so ta gwada hadawa dan jin ya kamshin su zai kasance. Ta na so kuma ta hada kullacham ta jarraba ta gani ko zai amsu wurin mutane.

Tunda aka yi hutu ba ta saida turare ko daya ba. Rabonta da saida turare ma tun kafin ta kwanta rashin lafiya. Hakan kuma ya na damunta sosai.

Ta san harda laifinta, dan tsakani da Allah bata tallata hajarta yanda ya kamata. Amma kuma harda rashin sanin kan (social media).

Ita kadai ce cikin gidan. Sadiya na makaranta, Mimi ta na wurin Jaddati. Ummi kuma ta raka Baffa asibiti check up. Tun dawowar su nan aka hada shi da kwararren likiti, yanzu haka ya daura shi kan magunguna da treatments na wani lokaci. Ya na lura da yanda jikin Baffan ke karban maganin, idan komai ya tafi dai-dai ba sai an yi mai aiki ba.

Su dai addu'ar su komai ya tafi yanda ya kamata.

An share gidan an goge, an kuma kunna turaren wuta ya bade ko'ina. Da ya ke akwai masu aikin da ke zuwa yin shara kullum safe da rana. Ma'aikata ne na musamman wanda sun dade suna aiki a gidajen gaba daya.

Sai dai ma'aikatan iyakar su kasa, sama su ke gyarawa. Ta gama gyara dakin Baffa dama shi kadai ne abunda ya rage mata. Store da ke cikin kitchen ta nufa ta fito da kayan aikin turarenta. Su tukunya, robobi, abun juyawa da sauran su. Ba ta ga camping gas din da ta ke aikin da shi ba, saboda haka ta kira Mimi a waya.

Ba'ayi minti biyu ba sai gata. Cikin store ta shiga ta fito da wani kwali sau ga gas din a ciki. "Adda ina za ki yi aikin?"

"Inaga kawai gwara in yi a waje." Akwai yar farfajiya bayan kitchen din da ya ke a zagaye.

"Toh," Mimi ta dauki kayan ta fara fitar mata da su waje. "Kin san da an baro miki kayan nan a Kaduna."

"Gwara da kuka taho mun da su, dan ko kudin su ban gama maidawa ba. Ku wai ya maganan kayan makulacen, kun watsar ko."

"Ba haka bane. Ba mu samu lokaci mun zauna ba ne. Ni ina chan, ita tana nan. Amma in sha Allahu kafin in koma makaranta zamu san yanda za'ayi. Kinga kuma bamu gama sanin kan garin ba. Ni inaga ma kawai zamu rika siyo kayan aikin daga Kaduna sai a sa mana a mota dan garin nan kaman za'a kwace maka kudi a hannu wallahi."

Maimoon ta yi dariya. Da gaskiyarta wannan. Tana son ta hada turare hudu yau ko sama da haka a yau. Mai saukin ciki ta fara da shi, shine na jikawa, duk ciki ya fi sauki.

Katon drum irin wanda ake sa ruwa ta dauko. Da farko ta zuba kilishin sandal dinta a ciki, sai ta dauko ruwan turare ta zuba, sai garin misik, ambur da jawi da aka daka. Sannan turare na mai (oil perfume) da madaran turare.

Duk sanda ta zuba abu sai ta juya. Bayan ta gama ta rufe shi gam saboda shi turare ana so ya kasance a rufe ko yaushe. Kuma yawan dadewan turare a aje, yawan kamshin shi saboda kayan hadin sun jiku sosai.

Shi yasa wani lokaci bata cika damuwa ba da rashin siya da ba'a yi saboda ta san bata yi asara ba. Ba kaman sauran sanao'i ba da in abu ya dade zai lalace. Turare ba haka ya ke ba, amma fi so a bar shi ya dade sosai, ya jiku inda ainihin kamshin shi zai fito.

Mimi ta kama su ka kai drum din sama. Inda ta yi ma kayan waje cikin wardrobe din a nan ta saka. In ya yi kwanaki a rufe sai ta zo ta saka a kananan robobi, ko kuma ta barshi a ciki har sai an nema.

Humra ta hada har kala uku, sannan ta hada kullacham shima flavor guda biyu. Ta na yi tana rubutawa dan kar ta manta (measurement) din da ta yi amfani da shi. Littafi gareta na musamman, a ciki akwai (recipes ) din da  Hajiya Laila ta basu, sai kuma na ta da ta ke hadawa. Wasu su bada kamshi mai ma'ana, wasu kuma sai a hankali. Abun (trial and error) ne.

Ta gama narkar da sugar dinta kenan ta ji sallamar Anwara. Kashewa gas din ta yi ta tafi falo.

"Kai Adda! Mai kike hadawa haka. Wai kin ji kamshi kuwa, kana karyo kwana ya ke maka salamu alaikum."

Dariya ta yi. Bayan kitchen din su ka koma Anwara sai yabawa ta ke yi. Zama ta yi aka yi aikin da ita, ta na tayata ta na yi mata tambayoyi.

"Shi wannan da kike zubawa ya sunan shi?"

"Kajiji ne. Itacen kajiji. Na narkar da sugar na yanzu zan zuba." Daga karshe Anwara ta karba ta taya ta juyawa har sai da sugar din ya hade da itacen.

Maimoon na zuba abubuwan ta na fada ma Anwara. "Wannan farce ne da ambur, misik, jawi da sandal powder. Su aka kira da dry perfumes."

"Ban taba sanin harda sugar ake sakawa ba. Ki ce a budget dina in yi wa turare wuri na musamman. Adda signature scent za ki hada mun, wanda a wurina kawai za'a rika jin shi, sai kuma gidana."

Maimoon ta fashe da dariya. "Ba ki da matsala kanwata. Allah Ya kaimu lokacin."

"Ameen. Dagaske na ke fa."

"Ai ni ma ba da wasa nake ba."

Haka su ka yita aikin su cikin raha. Sun hada dambu, sannan su ka kara hada kullacham saboda Maimoon na so taba 'yan gidan su gwada su gani kafin ta fara talla. Aikin gab-gab da Hawi kuma sai bayan kwana biyu tunda su sai an jika itacen.

"Ashe haka ake shan wahala. Kin ji kafaduna kuwa?" Anwara ta ce ta na rike kugu.

"Ai juyawan ya fi komai wahala."

"Gaskiya. Amma dai mutum zai yi kamshi," hannunta ta shinshina. "Wannan sai in yi kwana uku in kamshi ai."

"Ai kuwa dai, in yi miki na hausawa su ka ce 'zama da mai turare yafi zama da makeri ko bai ba ka turare ka shafa ba ka ji kamshi....'"

Sama su ka hau tare da abincin da za su ci. Maimoon sai da ta watsa ruwa kafin su ka zauna ci. Ana hira ta ke sanar da Anwara halin da ta ke ciki.

"Adda Moon ai sana'a yanzu dole sai da (social media) musamman Instagram. Dole sai kin hada da (content creation), shine zaki ga cigaba sosai in sha Allah. Yanzu dai bari a fara bude miki account..."

Anwara ta karba wayan ta yi downloading app din sannan tu bude mata. Aka sa ma page din suna 'turarenwutabymoon' Anwara na yi ta na yi mata bayani. "In kina so ki yi (thriving) sai kin hada ads, za ki biya influencers su yi miki talla, hakan na taimakawa sosai. Sannan kuma kaman yanda na fada miki dole ki hada da (content creation), ya kamata ki samu ring-light, background da props."

"Su kuma ina ake samun su?"

"Akwai wurare da yawa. Za mu iya order online ma. Yauwa sai kuma meye ma sunan abun? Hoto! Yauwa hoto! Hoto na da matukan muhimmanci, da packaging. Da kin samu irin cute robobin nan kin yi musu hoto mai dan karen kyau, tuni za ki sha kwana Adda."

Maimoon ta yi ajiyar zuciya. "Na ji abun ne da yawa Anwara."

"Da yawa kam," ta amsa ta na dariya. "Amma kar ki damu, zan taya ki. In fact na nada kai na a matsayin (social media manager) dinki. Amma fa da turare za'a rika biyana."

"In dai turare ba ki da matsala. Yanzu list din abubuwan da kika lissafo za ki yi da kuma kudin su."

Akwai kudi a account dinta sosai da bata san abunda za ta yi da su ba ma. Ita ba mai yawan siye siye ba ce shi yasa duk kudin da su Baba Nasir ke tura musu duk wata ta ke adanawa, ga kuma na wurin Baffa. In an kwana biyu Jaddati da su Anty Maryam su na yi mata ihsani suma. Saboda haka ta yanke shawaran yin amfani da kudin ta kara hannu jari da su.

"Toh shikenan. Zan saka harda kudin stickers da logo."

"Ki sa duka abubuwan da kike gani ya kama a yi."

So ta ke yi ta dage akan harkan, ta san abunda ta taka kafin a koma makaranta.

Akan shawaran nan su ka rabu. Maimoon ta hada Anwara da turarrukan da zata tafi. Sun sauka zata rakata kenan su Baffa su ka dawo sai Maimoon din ta fasa fita.

Anwara ta gaida su sannan ta yi musu sai anjima.

"Sannu Baffa. Ya jikin? Mai likitan ya ce?"

"Jiki da sauki Alhamdulillah. Likitan ya ce babu wata matsala, ya ce in daure in cigaba da kiyaye dokokin."

"Alhamdulillah, Allah Ya taimaka. Ummi bari in kawo muku abinci."

"Sannu Maimu. Hala turare aka hada na ji gidan namu ya dauki kamshi."

Ta na dariya ta ce; "eh Ummi." Bayan ta jera musu abincin ta basu wuri su ci a tsanake.

Kullacham, humra da sandal din ta hada ta sa a leda guda biyu. Ta ba Anwara na su, daya za ta kaima Jaddati, daya kuma na Ammi. Jaddati na barci sai kawai ta barwa Mimi in ta tashi ta fada mata.

Zaman mayafinta ta gyara akanta, ta kwankwasa kofar falon Ammi. Sameer ne ya bude suka gaisa ya ce mata Ammi na ciki ya fita. Falon na mata kyau sosai, Ammi ta iya zabe. Irin abunda ake kira simple but classy. Babu hayaniya amma akwai aji.

Mai aiki ce ta fada mata Ammin ta na sama. Ce mata ta yi ta sanar da ita ta zo, sannan ta samu wuri ta zauna. Ba dadewa sai ga yarinyan ta dawo ta ce ma Ammin ta ce ta hau sama.

Yanda kasa ya ke haka saman ya ke babu hayaniya sam. A falo ta sameta da tabarau a fuskarta ta na duba wasu takardu.

"Maimoon sai ki zauna kasa kaman wata bakuwa."

Murmushi ta yi. "Ina wuni Ammi."

"Lafiya lau. Ya hutu?"

"Alhamdulillah, hutu gashinan ana ta yi."

"Masha Allah. Allah Ya bada sa'a."

"Ameen Ameen."

Ammin ce ta yi ta jan Maimoon din da hira. Suna zaune Baba Nasir ya dawo. Fara'a sosai ya bayyana fuskan Ammi.

"Mamana ce a gidan."

Kai ta sadda da murmushinta. "Ina wuni Baba?"

"Lafiya lau."

"Ka ga ikon Allah duk cikin ku babu wanda ya yi Mama sai Baffa." In ji Ammi.

Dariya Baba ya yi. "Sai fa ikon Allah. Maman ke hanawa ai." Mikewa ya yi ya shiga daki.

"Bari in je in sallami babanku ko Maimoon. Jirani yanzu zan dawo."

Hakanan kunya ya kamata ta gyada mata kai alamar toh. Ammi bata dade ba ta dawo. Mika mata jakar ta yi ta ce mata nata ne ita da Waahidah.

"Masha Allah, masha Allah!" Ammi ta ce ta nu bude robobin ta na shinshinawa. "Yanzu duk ke kika hada wannan?" Kai Maimoon ta gyada tana mai jin kunya. "Masha Allah sun yi kamshi sosai. Shukriya, mun gode sosai. Sai mun zo kari. Allah Ya sa albarka."

Ameen ta amsa ta mike ta ce mata zata tafi. "Har za ki tafi? Nagode sosai Maimoon. Allah Ya yi muku albarka."

Wata jaka ta mika mata. "Ga nawa tukuicin."

"Ammi da kin barshi."

"A'a, kar mu yi haka. Karba kin ji."

Godiya ta yi mata sosai. A daki da ta isa ta bude ledar ta ga dogayen riguna ne guda biyi a ciki. Cikin wardrobe ta tura su.

Tana zaune wayarta ta yi kara. Murmushi ne ya baibaye fuskarta lokaci daya. Ba sai ta duba ba ta san wa ke kiranta. Waya da Sayf ya zaman mata jiki yanzu har ta na jin wani iri in bai kira ta ba.

Bayan sun gaisa ta tuna kwanakin baya ya ce mata zai yi presentation a office yau. "Ya presentation din?"

"Ba ki manta ba?" Ya kasa boye mamakin shi har hakan ya bayyana a muryarsa.

"Mmm ban manta ba."

Murmushi ya yi har ta na iya jiyo sautin. "It went well, duk da dai colleagues dina sun kwabsa mun."

Dariya ta mai, daga nan hira ya barke tsakanin su. Itama ta fada mai abunda ta yi yau. Ya ce mata in tana son sai iya guiding dinta through din business din nata yanda zata gudanar da komai cikin sauki.

"Da gaske?!"

"Of course Maimoon."

"Nagode! Da Anwara ke lissafo mun abubuwan kai na kullewa ya yi gaba daya, wasu ina sauraronta ne kawai."

"Hakane. Business da farko is overwhelming, ga fargaba, sai mutum ya jajirce."

Kai ta gyda. "Sosai. Amma kai yanzu ai ya zaman maka jiki, babu fargaba."

Dariya Sayf ya yi sautin har tsakar kanta. "Wa ya ce miki? Kawai dai na iya boyewa ne ba kaman ke ba matsoraciya. Ko wani dan kasuwa ya na fargaba Noor amma ba shi zai hanaka aiki ba. Ki kwantar da hankalinki nan ba da dadewa ba komai zai daidaita. Mai wuyan shine mutum ya fara."

"Hakane."

"Kar ki damu. Zan ara miki years of experience dina, zan tabbata duk wani kuskure da na yi kin guje mai."

"Nagode sosai. Jazakallahu khairan."

"Wa iyyaki. Anything for you Noor."










Hannuna ya na son janyo mun magana🤦🏻‍♀️ gaskiya zan daina kunna data idan ina typing, na biyu kenan da na je na taba publish ba tare da na gama ba. Kuma idan naga comments din ku bai budewa I feel guilty 😅 hakanan na ke zama in kammala chapter din. So please yanda na daure na kammala, the least you can do is vote and comment 🥹 dan Allah. Ba ku son yin comments gaskiya, kawai zan tafi hutu 🥲 lemme know your thoughts please



~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro